← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 12 OF 29

Sashe 12

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

ÆŠankunnen ya É—ago da yatsunsa biyu yana kallonsa duk da É—ankunnen ya daÉ—e amma babu abin da ya yi kasancewar sa azurfa, nan take ya shiga tuno da ranar da ta bashi warin É—ankunnen yana zaune a É—akinsa yana gyaran littattafan makarantarsa yana sanya su a jaka ta shigo da É—ankunnen a hannunta.A kusa da shi ta zauna ta ce

"Ya Hizbu É—ankunne na kawo maka"

"ÆŠankunne kuma Rida ni da ba mace ba mai zanyi da É—ankunne?"

"Dama Baba ce ta siya min sabo ta sanya min saboda É—ayan wannan ya faÉ—i shi ne na kawo maka, tun da maza ba kwa sanya É—ankunne ba sai ka ajiye ba" Ta faÉ—a tana nuna masa É—ankunnen da aka siya mata sabo a kunnenta.

Jakar ya ajiye a gefe ya miƙo hannunsa ta basa ɗankunnen yana ta murmushi itaɓa tana yi.

"Yawwa to godiya nake" Ya faÉ—a yana buÉ—e zip É—in Babbar akwatinsa ya fito da É—an kit É—in da ya siya ya sanya flower da ta bashi, ya buÉ—e ya sanya É—ankunnen a ciki.

Bai ankara ba sai jin hawaye ya yi suna gangarowa a kumatunsa, tabbas ya yi kewar Ridallah, kewar da shi kan sa bai san yawa da adadinta ba kewar da ya san babu ranar da zai daina har sai ranar da ya sanya Ridallah a idanunsa.Juyawa ya yi, ya koma ribda ciki ya shiga yin kukan yana jin zafi da raɗaɗin rashinta na ratsa dukkan sassa da gaɓoɓin jikinsa, tabbas shaƙuwa wata aba ce mai wuyar fita daga rai, shaƙuwa tana yin zama a cikin zukata tamkar yadda kayana kayan ciki ke zaune cikin jiki, tana haɗuwa a zukata har ta zama abin da bai rabuwa wato hanta da jini.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YATINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

PAGE2️⃣3️⃣&2️⃣4️⃣

"Wallahi duk abin da kike ganin za ki yi sai dai ki yi, dan tafiya babu fashi dole Iftihal ta je china ta yi karatu tun da na ga abin naki babu hankali a ciki.Kamar ba ke kika haifeta ba ƴar ƙwaya ɗaya amma ace ta tashi babu arabi ba boko sai yawon banza da kike sanyata da bin gidajen ƙwaye" Abie ya kai ƙarshen maganar tare da buga kan kujerar da yake zaune da hannunsa dan ya lura abin na Hajiya Hauwa ba na ƙare bane sai an zage dantse an nuna mata iyakarta.

"Dan Allah Alhaji ka yi haƙuri kar ka kai min ƴata karatu ƙasar waje, na yarda zan barta take zuwa makarantar anan amma ya za a yi ace kamar Iftihal har nawa ma take da za ace an fitar da ita karatu har wata ƙasa"

"Da can baki san da karatun nata ba kika ƙi kullum muna magana ɗaya amma kin ƙi ji yanzu ban da shegen yawo da yarinyar ke fita ba tare da sani na ba, ni ma yanzu ban yarda da ke ba akan zaki barta ta yi karatu kuma da kike maganar nawa take zan aikata ƙasar waje karatu ai na faɗa miki gidan abokina Alhaji Sani Habu da yake zaune acan zan kaita acan za ta yi karatun ta dan haka kisa Safiya ta haɗa mata kayanta dan bizarta tana fitowa za ta tafi"

"Alhaji ka yi haƙuri a sasanta mana tun da dai yanzu ta amince ka haƙura da kaita chaina"Momma ta faɗi hakan cikin sanyin murya da lallashi.

Idon Abie Hajiya Hauwa ta faka ta aikawa da Momma wata uwar harara me nuni da ke kika sani munafuka, sai zare ido take kamar idanunta za su faɗo ƙasa.Ita dai Momma yi ta yi kamar ma ba ta san tana yi ba dan ita tsakaninta da Allah take faɗar abin da ke ranta dan ita ma bata ƙaunar hana Iftihal ɗin zuwa makaranta da take sannan ta tsani yawon da aka buɗewa yarinyar idanu da shi, dan ta san shi Abie bai ma san har samari suke kawo Iftihal ɗin gida a mota ba, abin na damunta amma ba ta so tayi magana ace baƙinciki take saboda ba ita ce ta haifeta ba, dan akwai wata rana da ta fara ganin an sauke Iftihal ɗin a mota wani mutum ne babba da shi, a lokacin Momma ta dawo daga unguwa direba ya kai ta lokacin da hancin motarsu Momma ya danno ƙofar gjdan ita kuma Iftihal ta buɗe ƙofar ta fito suna ɗagawa juna hannu ita da na cikin motar, baki sake Momma ke kallonsu dan kwata-kwata hankalinta bai kwanta ba Iftihal ɗin na ganin su Momma ta yi saurin tura ƙaramar ƙofar get ɗin ta shige cikin gida. Horn direban ya yi aka wangale musu get ɗin suka shiga dan ko da Momma ke tambayar direban ko ya san mai motar cewa ya yi ai yanzu motoci ne kala-kala ke kawo Iftihal ɗin gida su ajiyeta a bakin get.

Dan haka tana tana fita daga motar hankali tashe ta yi part ɗin Hajiya Hauwa dan ta yi alƙawari ko me Hajiyar za ta ce mata sai ta faɗa mata abin da idanunta ya gani dan ta sani dan ta san idan ta sanar mata ko nan gaba ta fita ko a girin Allah ko da wani abu ya faru duk da ba a fatan hakan.Tana kaiwa dai -dai ƙofar da zata sada ta da falon Hajiya Hauwa sai jin wata magana ya dakatar da ita daga shiga ta tsaya tana sauraron maganar hankali tashe.

"Yanzu Alhajin da ya dawo da ke gida shi ne ya baki wannan maƙudan kuɗin Iftihal"Cewar Hajiya Hauwa muryarta cikin farinciki.

"Wallahi kwa Aunty shi ya bani dan da kuɗin da ya bani bai kai haka ba, aikuwa da muka fito daga Hotel ɗin zai kawo ni gida na marairaice murya kamar yadda kika koya min ina kashe masa ido ai nan da nan ya ƙara buɗe aljihunsa ko irgawa bai yi ba ya zuge jakata ya zuba mini"Iftihal ɗin ta ce tana dariya.Momma bata ankara ba sai jin ƙaran tafawar hannayensu ta yi alamar sun tafa dan jin daɗin halin da suke ciki.

Saurin sanya hannu ta yi ta rufe bakinta gudun kar aji ta dan abin da take saurara ya wuce hankali da tunaninta ace ƴarka ta cikinka ka zama sanadiyyar lalacewar rayuwarta sai ka ce a mafarki ko kuma a film, lallai zamanin nan da muke ciki ya ƙazanta ta ce a cikin zuciyarta.

"Ai sai kin zama abar kwatance a kaf faɗin Abuja sai an san da zamanki, ke bake ba ma hatta ni sai na yi sunan saboda za mu tara kuɗaɗen da za a yi ta kwatance da mu"Maganar Hajiya Hauwa ta katsewa Hajiya Azima tunani, a hanzarce ta bar ƙofar falon tare da baro part ɗin ma gaba ki ɗaya cikin tashin hankali dakyar take iya ɗaga ƙafafunta saboda sanyi da suka mata tana jin wani ƙunci da tashin hankali na maganganun da kunnuwanta suka jiyo mata.

"Hajiya Azima dan Allah kar ki ɓata bakin ki dan na gama yanke hukunci, babu wani abu da zan sauya daga haka" Muryar Abie ta dawo da ita daga tunanin da take.

Wani tashin hankali ne ya ziyarci Hajiya Hauwa tana ganin Alhaji Hamza zai datse mata hanyar samun maƙudan kuɗaɗen da take samu wanda shi ba zai taɓa iya bata su ba, dan idan har ya kai Iftihal China to haƙiƙa ya ɗauke mata jarinta dan ita yanzu bata ga wata sana'a ba da ke saurin kawo kuɗaɗe sama da wacce Iftihal ɗin ke musu.

"Iftihal ki tabbatar kin haɗa komai da zaki buƙata Safiya kuma ta shirya miki kayanki dan tafiya za ta iya kasancewa ko da wane lokaci"Abie ya ce yana kallon Iftihal da take ta zubar hawaye amma shi ko a jikinsa wai an tsikari kakkausa tun da ta sna wannan shi ne babban gata da zai mata.

"To Abie" Shi ne kawai abin da ta iya furtawa dan ta san dai ita a da tana ƙaunar karatu amma yanzu ko sh'awar shiga aji bata yi bare ya yi sha'awar ɗaukan karatu musamman yanzu da idanunta suka buɗe da samun kuɗi ta hanyar sai da mutuncinta da mahaifiyarta ce ummul aba'isin hakan tana ƙaramarta amma ta san bin maza amma ta san ba ta isa ta ja da amaganar Abie ba shi yasa ma ta aminci amma ba wai dan ranta ya so ba.

Hajiya Hauwa ce ta tashi buguzun-buguzun ta bar falon tamkar za ta tashi sama, tana fita ita ma Iftihal ɗin ta miƙe cikin sanyin jiki za ta tafi daga ɓangaren Abie.

"Kin dai ji abin da na gaya miki, kuma ki sani ko kin shirya ko baki shirya ba biza na fitowa za ki tafi" Maganar Abie ta katse Iftihal da ke bakin ƙofa za ta fita.

"Zan yi ƙoƙarin yin hakan kafin lokacin" Tana gama faɗar haka ta sanya kai ta fita.

Ran Momma fari tas jin wannan hukunci na Alhaji wai a hakan ma aho Alhajin bai san cewa Iftihal ɗin har maza take bi ba.Nan dai suka cigaba da yin hirar su dan yau Momma ce da girki yau Auntyn ta fita daga kwananta sai Momma ta karɓa, to dama a dinner ne da aka zo aka ci a part ɗin A bie shi ne ya ce idan an kammala yana da magana, shi ne suka tattaru a falon ashe da wannan maganar Abie ke tafe wannan kenan.

Iftihal na fita ta koma part ɗin Auntyn ta ɗakinta ta buɗe ta shiga, ta kwanta akan gado ta ɗakko wayoyinta har guda uku kowacce ta doshi 300k ta shiga waya da ƙawayenta na banza da suka haɗu a harkar bariki da kuma samarinta na wofi.

Hajiya Hauwa cikin fushi ta koma part ɗin ta, wayarta ta ɗakko cikin ɓacin rai ta zauna a bakin gado ta shiga laluɓo number ƙawarta aminiyarta Hajiya Suwaida, Hajiya Suwaida aminiyarta ce tun ta ƴanmatanci, Hajiya Suwaida ƴar garin Dutse ce da ke Jihar Jigawa sai dai tana zuwa Suleja hutu wurin ƴan uwan mamanta, to acan suka haɗu da Hajiya Hauwa suka ƙulla ƙawance da yake ta su ta zo ɗaya sai ƙawancen na su ya yi armashi har yanzu.
Chapter 12 · 0% Book details