Sashe 2
Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read
Ana fitowa break ya je ya kamo Ridallah ya ɗakko abincinta ya zo ya zauna yana bata a baki, sai da ta ci ta ƙoshi sannan ya ci sauran, sai kuma suka je ya siyo ɓata abin da take so da kuɗin makarantarsa da nata ya haɗa ya kaso mata sai da suka zauna tana cin abubuwan da aka siyo ɗin sannan take ɗauka tana bashi a baki dan itama bata iya cin abu ta hanashi ko lokacin da ba a sanyata a makaranta ba idan aka bata abu yana makaranta sai ta ajiye masa har sai ya dawo ta ɗauka ta bashi abin da ta rage masa domin akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu bata san kowa ba sai shi sai Baba, daga ta ga bata ganshi ba za ta tafi gidansu nemansa idan kwa ɗaya bashi lafiya to ɗayan ma zai kamu da rashin lafiya.
Bayan an taso su suka kamo hanyar gida suna zuwa gidansu Hizbullah suka fara shiga ya cire kayansa ya É—akko abincinsa suka tafi gidan Baba itama Ridallah ta cire uniform É—in ta sanya wasu kayan sannan suka zauna suka cinye abincin Hizbullah sannan Baba ta zubo musu wani suka ci tare dan haka suke yi basa yarda su ci abincin gida É—aya wai su ciyayya suke yi.
MMN AFRAH
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
💕ALAƘAR YARINTA💞
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
NA
MMN AFRAH
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
Page 5ï¸âƒ£&6ï¸âƒ£
_BIRNIN TARAYYA ABUJA G.R.A_
Wani ƙaton gida mai tafkeken get na shiga, na tsaya ƙarewa gidan kallo girma da yanayin tsaruwar gidan gida ne da ya amsa suna gida, kana kallon gidan ka san mamallakan gidan sun amsa sunan manyan attajirai.Gini ne sashe -sashe ga motoci nan bila adadin a wurin da aka tanada dan ajiye motoci wasu a buɗe wasu kuma an rufe su.
Girma da haɗuwar gidan yasa na saki baki ina bin gidan da kallo lallai wannan gidan shi ake kira da aljannar duniya! Tafiya na fara na doshi wata hanya da ta ɗan miƙe wacce idan ka kai ƙarshenta ne za ka ga ta rabu zuwa sashe -sashe, sai da na tsaya ina tunanin wane ɓangare ya kamata na fara zuwa sai kawai na nufi wanda ke gaba na.Ƙofar part ɗin na tura sai kuwa gani na shigo wani fili mai girma da wasu shuke -shuke na fulawoyi da abubuwa masu ƙawata wuri.Ƙarasa wa na yi na buɗe ƙofar da za ta sadani da babban falon.
Wani sanyi da ƙamshi mai daɗi ne ya fara ziyartar hancina, ƙarasa shigowa na yi cikin falon tsaruwa da haɗuwar falo kaɗai abin kallo ne, ban gama ganin tsaruwa da haɗuwar falon ba idona ya kai kan dinnig area inda wata mata ke zaune akan dinnig ɗin tana danna wayarta sai wani yatsine-yatsine take tana harare -harare tana yi tana kallon agogon wayar ta dan ranta sai suya yake yadda har yanzu Alhaji ba su fito ba dama duk ranar girkin Hajiya Azima Alhaji ba ya son fitowa da wuri sai ta rasa uban me suke a ɗakin matar da ba haihuwa take ba menene abin ɓata lokaci a kanta.
A hankali yake sakkowa daga upstairs ɗin sanye yake da cofee yadi mai ɗan haske ɗinkin tazarce hannunsa riƙe da agogon sa ƙirar Gucci yana ƙoƙarin ɗaurawa Hajiya Azima biye da shi riƙe da jakar office ɗinsa sai zance suke suna dariya abin su.Ƙaran takalma su shi ya maido da Hajiya Hauwa daga saƙar zucin da take.Yadda kan ta ke akan wayarta bata ɗago ba dan wani tuƙuƙin baƙinciki ne ya turnuƙe mata zuciya saboda sautin dariyarsu kaɗai sai da yasa ta ji kamar zuciyarta za ta buga.Amma da yake ta iya takunta sai ta danne abin da take ji ta ɗago kan ta tana kallonsu fuska sake.
"Barkan ku da fitowa"Ta ce musu lokacin da suka ƙaraso dinnig area ɗin.
"Yawwa barkan ki"Suka haÉ—a baki wurin faÉ—a.
Alhajin ne ya jawa Hajiya Azima kujera ta zauna lokacin da ta dawo daga tsakiyar falon da ta je ta ajiye jakar office ɗin Alhajin akan kujera, kallonta yake fuskarsa ɗauke da murmushi har dai ta zauna kafin shi ma ya sanya hannu zai ja kujerar Hajiya Azima ta yi saurin sanya hannu ta ja masa kujerar ya zauna suna yiwa junansu murmushi tamkar dai sun manta da Hajiya Hauwa da ke zaune tana hararsu ƙasa-ƙasa.
"Barka da safiya Alhaji" Cewar Hajiya Hauwa tana murmushin yaƙe dan ji take kamar ta rufesu da mugun duka tsabar takaici.
"Kin tashi lafiya" Alhajin yace cikin sakin fuska.
"Lafiya ƙalaw" Ta ce tana masa wani kallo na soyayya dan ta ɓatawa Hajiya Azima rai.
"Masha Allah"Yace lokacin da ya sanya fork zai fara cin abincin da Hajiya Azima ta zuba masa.
"Hajiya fatan kin tashi lafiya"Hajiya Hauwa ta faÉ—a cikin kissa.
"Lafiya Alhamdulillahi fatan ke ma haka"
"Lafiya nake"
"Masha Allah"
"Ina Iftihal ne ko har ta tafi school" Alhajin yace lokacin da yake kurɓar tea.
"Bata tashi daga bacci ba ai" Hajiya Hauwa tace tana É—an sanyaya muryarta dan kar ya yi mata faÉ—a.
"Haba Hajiya sau nawa kike so na faɗa miki ki daina yiwa yarinyar nan wasa da karatun ta, ace an sanya yarinya a school amma ba za ta je ba to me kike so ta miki a gidan idan bata yi karatu ba haka jiya ma monday fa bata je ba, hatta islamiya ma bakya so ta je, gaskiya bana so kar a ƙara barinta a gida" Alhajin yace cikin ɓacin rai dan ya kasa gane Hajiya Hauwa wace irin mace ce da bata ƙaunar ƴarta ta je makaranta kullum ana ɓacin rai akan abu ɗaya.
"Allah huci zuciyarka Alhaji hakan ba zai sake faruwa ba" Ta ce tana wasa da cokali a cikin plate ɗin dan tun da ya sako maganar karatun Iftihal sai ta ji gabaɗaya abincin ya fice mata a rai dan babu abin da ta tsana irin maganar zuwan Iftihal makaranta, shi kuma ya kasa gane wa cewa bata ƙaunar Iftihal ta yi wani karatu daga na bokon har na arabiya.
"Haka kike cewa kullum amma kin kasa canjawa amma inaso ki sani akan maganar makarantar Iftihal za mu saka ƙafar wando ɗaya da ke" Ya kai ƙarshen maganar yana goge bakina da tissue, ita dai Hajiya Azima bata ce komai ba dan bata son sanya baki a abin da bai shafeta ba amma itama har ga Allah bata son sangarta Iftihal da Hajiya Hauwa ke yi musamman ma a ɓangaren karatu.
"Hakan ma ba za ta faru ba" Ta ce tana marairaice murya.
"Yanzu ma dan na ga lokaci ya ƙure har takwas da kwata kafin ace an mata wanka an shiryata amma da sai ta tafi yanzu ma" Yace yana miƙewa, domin tafiya office, Hajiya Azima ma miƙewa ta yi domin rakashi, wata uwar harara Hajiya Hauwa ta bisu da ita dan gabaɗaya haushin su take ji dan tun da ake cin abincin sai wani satar kallon juna suke kamar ba tare suka kwana ba.
"Allah tsare" Hajiya Hauwa ta ce a takaice.
"Amin "Shi ma yace ba tare da ya kalli ko inda take ba.
Hajiya Azima jakar ta ɗauka take masa baya, suka fita, a ƙofar fita daga part ɗin suka samu Sa'idu direba yana jiran fitowar Alhajin, gaishe da su ya yi cikin girmamawa suka amsa cikin sakin fuska jakar hannun Hajiya ya karɓa ya jiya ya tafi ya bar su suna sallama, sai da ta ga tafiyar su tana ɗaga masa hannu shi ma yana ɗago mata duk da akwai ɗan tazara daga part ɗin zuwa parking space amma suna hango junansu ana wangale get motar na fita Hajiya Azima ta juya ta koma ciki domin ta gyara masa bedroom ɗin nasa na upstairs inda suka kwana dan bedrooms a saman ma guda huɗu ne sai dai ɗaya wanda suke kwana Alhaji da Hajiya Hauwa ɗaya kuma inda yake kwana da Hajiya Azima kowacce da ɗakin da ya zamana shine turakar da take kwana da miji dan basa sharing na turaka sauran biyun kuma kawai dai an ƙawata su ne da kayayyakin ɗaki amma ba wai ana kwanciya a ciki.
Tana dawo wa bata tarar da Hajiya Hauwa a dinnig area ɗin ba ta koma part ɗin ta dan kowacce akwai ƙofar da za ta sada ta da part ɗin ta, sai kuku yana kwashe kwanuka, ya gaishe da ita ta amsa masa tare da hayewa sama domin yin gyaran dan ita a tsarinta bata yarda ƴar aiki ta gyara mata turakar mijinta ba saɓanin Hajiya Hauwa da mai aiki ke gyara mata.
Hajiya Hauwa rai ɓace ta ƙarasa part ɗin nata dan har lokacin bata daina jin haushin faɗan da Alhajin ya mata a gaban Hajiya Azima sai dai ta sha alwashin sai dai ya yi falansa ya gama amma dai ba za ta taɓa yin abin da yace ba ko da ta fara ba zai ɗore ba.Mai aikinta Safiya ta samu tana ta faman goge -goge cikin girmama wa Safiya ta mata barka da dawo wa amma ko inda take bata kalla ba dama ita ma bata sanya rai cewa za ta amsa mata ba dan ta san hali, shegen wulaƙanci ne da ita.
MAMAN AFRAHðŸ˜
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
💕ALAƘAR YARINTA💞
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
NA
MMN AFRAH
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
Page 7ï¸âƒ£&8ï¸âƒ£