← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 3 OF 29

Sashe 3

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Hajiya Hauwa upstairs ta nufa tana zuwa ta kama ƙofar ɗakin Iftihal ta buɗe kwance ta ganta akan gado tana cikin bargo fuskar ta ce kawai a buɗe sai baccin ta take hankali kwance.Wata uwar harara take bin Iftihal ɗin da ita daga ƙarshe ta doka wani uban tsaki tare da rufo ƙofar da ƙarfi ta juya ta koma nata ɗakin, Iftihal kwa da ke ta bacci bata san abin da ake ba.Tana shiga ɗakin ta ta cire ɗaurin ɗan kwalin da ta yi wanda ake kira ture ka ga tsiya wuri ta nema a bakin gado ta zauna har lokacin ranta na ƙuna ta rasa yadda za ta yi da Hajiya Azima kullum maimakon ace Hajiya Azima ta zama bora a wajen miji amma kullum ita ce mowa ita ce tauraruwa ita ce abar so ita duk faɗi tashin da take yana tashi ne a banza, kullum Alhaji cikin ganin laifinta yake a gaban Hajiya Azima sai ya tsinkata yana mata faɗa tabbas da sake dan ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa.

Miƙewa ta yi da sauri kamar wanda aka tsikare ta gaban mirror ta je ta tsaya tana ƙarewaa kan ta kallo tamkar dai yau ta fara ganin siffar kan ta a madubi.So take ta gano muninta so take ta hango makusar ta so take ta ga ta inda Hajiya Azima ra kere mata, kyau diri iya kwalliya ko me? Amma bata hango hakan ba duk da ta san cewa bata kama ko da ƙafar komai ba na Hajiya Azimar ba amma ta san ita ma tana da nata abin yabon, gashin kan ta, ta ƙurawa ido ganin shi iya kafaɗarta ko gama sakko mata bai yi ba sai kuma ta tuno gashin Hajiya Azima da ko ɗan kwali baya iya rufeshi har gadon bayanta yake sauka ga santsi da sheƙi, ai hakan da Hajiya Hauwa ta tuna sai kawai ta miƙa hannu wurin kwalaben turaruka da ke jere akan madubin ta ɗakko wata kwalbar humra ta ɗaga ta jefawa madubin a take ya tarwatse wani ƙara da gabaɗaya part ɗin ya ɗauka komawa ta yi ta zube akan gadon har lokacin zuciyarta na tafarfasa.

Safiya da ke gyaran kicin ta jiyo ƙaran fashewar abu a hanzarce ta fara hawa step ɗin domin zuwa ta ga ko menene dan alamu sun nuna kamar ba lafiya ba.Tana gama hawa upstairs ɗin ta fara waige-waige tana son gano inda ƙaran ya fito amma bata gano ba kukan Iftihal ta fara jiyowa da sauri ta nufi ƙofar ɗakin ta tura ƙofar dan dama idan ranar girkin Hajiyar ne idan Hajiyar ta tafi part ɗin Alhaji to fa ita ke kwana da Iftihal amma a ɗakinta da ke kusa da na Iftihal ɗin da basa kwana a ɗaki ɗaya idan kuma ba girkin Hajiyar bane a ɓangaren su na ƴan aiki take kwana.

Iftihal ɗin ta hango zaune akam gado ta duƙunƙune kan ta a cikin bargo tana takure a wuri ɗaya tana ta kuka, da sauri ta ƙarasa wurin Iftihal ɗin tana kiran sunan ta sannan ta sanya hannu ta yaye bargon aikwa Iftihal ɗin ta faɗa jikinta da sauri tana ƙara fashewa da wani kukan.

"Wayyo Safiya dan Allah ki kai ni wurim Aunty tsorata ni ake da wani irin ƙara"Cewar Iftihal ɗin tana ƙanƙame Safiya.

"Ki yi shiru babu komai anan ni ma na ji ƙaran amma da na zo ban ga ta inda ƙaran ya fito ba"

"Ke ma kin ji kenan ni dai ki kai ni wajen Aunty tsoro nake ji"

"To taso mu je tana É—akinta"

Sakkowa Iftihal ɗin ta yi sai da na duba da kyau sai ma na ga ba wata babba ba ce duka bata fi shekara huɗu ba, hannun ta Safiyar ta kama amma Iftihal ta ce ita dai ba za ta tafi da ƙafarta ba, sunkuyawa Safiyar ta yi Iftihal ɗin ta hau dan dama da wuya ka ga Iftihal na tafiya da ƙafarta rai da rai sai dai a baya, haka suka nufi ɗakin Aunty, nocking Safiya ta shiga musu amma abin mamaki bata bada amsa ba jin shiru yasa Safiya tura ƙofar dan dama haka take sai ka yi ta mata nocking ta ƙyaleka.

Kwance suka sameta ta kifa kan ta a jikin filo da alama kamar tana cikin damuwa daga bakin ƙofar da Safiya ke tsaye da goyon Iftihal suka ga gabaɗaya madubin da ya tarwatse a ɗakin, da mamaki Safiya da Iftihal suke kallon madubin sai lokacin suka fahimci ƙaran fashewar madubin ne ya cika part ɗin har ya tsorata Iftihal.

"Aunty"Iftihal ɗin ta kira sunan Hajiya Habiba tana ƙoƙarin sakkowa daga bayan Safiya.

Shiru bata amsa mata ba

"Kar ki sakko dan kar ki taka madubin"Safiya ta ce tana riƙe Iftihal ɗin dan yadda madubin ya ɓata ɗakin ko ina ya tarwatse Iftihal ɗin za ta iya takawa.Duk bidirin nan da ake Hajiya Habiba bata ko ɗago kai ta kalle su ba.A hankali Safiya ta bi ta gefen tana taka in da babu madubin har dai ta ƙarasa bakin gadon ta sauke Iftihal ɗin akan gadon, ƙarasa wa Iftihal ɗin ta yi ta faɗa kan Aunty ta tungumeta ta baya tare da kwantar da kan ta a bayan Auntyn.Ita dai Safiya daga haka ta fita ɗakin domin samo abin da za ta gyara wurin.

"Aunty ke kika fasa madubi?"Iftihal ta jefa mata tambayar.

A hankali Aunty ta zame Iftihal É—in faga bayanta ta tashi zaune suka fuskanci juna.Iftihal É—in kallon idon Auntyn take ganin ya yi jawur kamar dai kuka ta yi.

"Haba Iftihal ya za ayi in fasa madubi abu na je É—akkowa shi ne ya fashe"

"Amma kuka kika yi?"Ta ƙara jefa mata wata tambayar.

"Kai na ke ciwo shi sa kika ga ya yi ja"

"Sannu kisha magani"

"Yawwa na sha magani ma"

Iftihal kan ta ta kwantar akan cinyar Auntyn, sai kuma Auntyn ke shafa kan nata , shiru suka yi babu wanda ya ƙara magana.

"Aunty yau ma bazan je school ɗin ba?" Iftihal ta jefo mata tambayar.Auntyn na ƙoƙarin bata amsa Safiya ta turo ƙofa ta shigo ɗauke da tsintsiya da abin kwashe shara wurin ta shiga gyarawa sai da ta tabbatar ya gyaru babu sauran wani madubin sannan ta fita daga ɗakin.

"Yanzu time na zuwa school ya wuce, ba a son mutum ya je makaranta a makare saboda bulala malam ke yi amma ki bari za ki je"Cewar Auntyn tana cigaba da shafa kan Iftihal É—in.

"To shikenan, amma dai gobe zan je"

Shiru Auntyn ta mata har sai da Iftihal É—in ta sake mata magana sannan ta ce.

"Kar ki damu"

"Zan je?" Ta sake jefa mata tambaya.

"Ki bari yanzu bana son surutu kai na yana É—an sara min"

"Sannu " Iftihal ta ce tana tashi zaune daga kwancen da take tana kallon Aunty cike da tausayawa.

"Yawwa ai kaɗan-kaɗan ne ma " Aunty ta ce tana ɗaukan wayar ta ta kira telephone da ke falon ƙasa, Safiya na ɗagawa ta ce.

"Ki zo"Kawai ta ce ta katse kiran.

Da sallama ta shigo É—akin bayan ta yi nocking an bata izinin shiga.

"Gani Hajiya" Safiya ta ce lokacin da ta durƙusa a gaban gadon da Aunty take.

"Ki ɗauketa ki je ki mata brush ki mata wanka sannan ki bata abinci ta ci" Auntyn ta faɗa tana miƙa mata Iftihal .

"To Hajiya an gama" Cewar Safiya tana juyo bayanta Iftihal É—in ta hau suka fito daga É—akin.

Bayan ta mata brush ta mata wanka sannan ta shiryata tsaf cikin riga da wando ƴan kanti pink clour masu matuƙar kyau ta gyara mata kan nata sai sheƙi yake, haka ta goyota suka sakko ƙasa ta zaunar da ita da akan kujera, kicin ta shiga ta ɗakko mata soyayyen dankali da ƙwai sai soyayyen plantain.A kan center table ta ɗora ta ɗakko kayan shayi ta haɗa mata tea mai kauri ta zuba abincin ta shiga bata a baki, suna cikin haka sai ga Aunty ta sakko daga saman ta zo ta zauna ta ɗora ɗaya kan ɗaya dan zuwa lokacin ba ta ko so ta tuno da Hajiya Azima dan tun da ta yi kuka sai ta ji zuciyarta ta yi sanyi remote ta ɗauka ta canja tasha zuwa arewa 24 sannan suka sakarwa juna murmushi ita da Iftihal.

Ita dai Safiya ba abin da ta ce tana baiwa Iftihal abinci har sai da ta juyar da kai gefe alamar abincin ya isheta.Ajiye fork ɗin Safiya ta yi ta ɗakko kofin me tea ɗin da ta haɗawa Iftihal a hankali ta shiga ƙoƙarin bata dan gudun yin kuskure dan kaɗan da aikin Hajiyar ta mareta koma ta hanata albashi wannan watan.

"kar ki bani tea ɗin da kai na zan sha" Cewar Iftihal tana miƙa hannu ta karba, Safiya ganin an karɓeta sai ta shiga tattare kayan abincin, ta gama haɗawa za ta ɗago daga sunkuyen da take aikwa Iftihal ta ɗauki wannan shayin da ke hannunta ta watsawa Safiya a jikinta har fuskarta sannan ta ce

"Bana shan abu mai zafi bayan haka bana son ana cika min madara "

Wani haushi da mugun takaici ne ya mamaye Safiya ga tea ɗin da zafi bai huce amma sai ta cije sai dai ta yi ƙoƙarin damƙe hannun ta domin ta ayyana a ranta ko za ta rasa aikinta yau sai ta naushi Iftihal a bakinta domin sai ta nuna mata cewa bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane, sannan ɗan adam Allah ya ɗauka ka shi dole ma ta nuna musu kuɗinsu ba shi bane tun da ba za su iya yiwa kan su abu ba dole dai talakan shi zai musu, hannu ta dunƙule tana duba in da ya kamata ta kaiwa mugun naushi a jikin Iftihal ɗin.

MMN AFRAH😍🥰😘

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Page9️⃣ &🔟
Chapter 3 · 0% Book details