← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 13 OF 29

Sashe 13

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Har kiran ya katse ba a ɗauki wayar ba, ƙara kiran ta yi ranta baƙiƙƙirin kamar ta saki kuka ko ta samu sassauci.Wani kiran ta shiga doka mata har sai da ya kusa tsinkewa sannan ta ɗaga cikin murnar ganin aminiyarta ta.

"Aminiyata kin fi ta kowa" Cewar Hajiya Suwaida tana neman wuri ta zauna akan kujera dan fitowarta kenan daga bayi ta jiyo ƙaran wayarra ta shi ne ta zo domin kawo wa wayar ɗauki sai kuma ta tarar da kiran ma na aminiyarta ne.

"Suwaida dan Allah ki saurara ki jini wannan kiran ba na lafiya bane, akwai gagarumar matsala da ta tunkaro ni"

"Ikon Allah ya na ji muryarki haka? Allah sa dai ba sakin ki Alhaji Hamza ya yi ba zai tona mana asiri"

"Ba saki na ya yi ba amma abin ba ƙarami bane wallahi ina cikin tashin hankali"

"To ki nutsu ki mini bayani ko menene domin mu san yadda za mu yi mu shawo kan matsalar, dan babu wani abu da zai tunkaro mu face mun yi maganinsa"

"Wai Alhaji ne zai kai Iftihal karatu ƙasar Chaina, wallahi yana neman ganin bayan samun kuɗina yana kuma ƙoƙarin karya jari na"

Wani mugun wuntsilowa Hajiya Suwaida ta yi daga kan kujerar, sai ga ta a ƙasa tsabagen ruɗew da ta yi, dan duk tunaninta matsalar ƙarama ce sai ta ji girman matsalar na neman wuce gona da iri.

"Shi Alhaji Hamzan ne ya yanke wannan É—anyan aikin, saboda shi bai san burinmu akan yarinyar ba"

"Wallahi kema dai kya faɗa amma hankalina ya tashi dan kin ga gabaɗaya so yake ya karya ƙudirinmu akan ta"

"Lallai kuwa dole a nemi mafita dan babh yadda za a yi mu haƙura da burinmu ya ma za a yi mu da bama ƙaunar yarinyar ta yi karatu shi ne zai wani ce har ƙasar waje zai kai ta ta yi karatu ba ma a Nigeri'a ba"

"Wallahi kuwa ni kai na duk ya kulle amma ki samo mana mafita"

Shiru Hajiya Suwaida ta yi tana nazari da tunanin yadda za ta samo musu mafita akan haka tun kafin haƙƙar Alhaji ta cimma ruwa.

"Yawwa akwai wata ƙawata a ƙasar China, ƴar nan Nigeri'a ce aiki ne ya kai mijinta China ina ganin za mu samu mafita a gunda dan itama shegiyar kan ta ce"

"Ta yaya? Kinsan fa shi Alhajin ya ce ba a makaranta za ta zauna ba, bare ki ce za a ruÉ—eta, ya ce gidan abokinsa zai kai ta"

"Mun shiga uku asirinmu zai tonu na samun kuɗi lallai da alama burinmu na zama hamshaƙan mata ba zai ciku ba"

"Ni ma shi ne damuwata wallahi da ace makaranta zai kai ta da mun samu mafita amma kuma gida ne zai kai ta"

Runtse idanu Hajiya Suwaida ta yi tana ta saƙa da warwara tana son gano mafita, can sai cewa ta yi.

"A Nigeri'a a ina abokin nasa yake É—an wane gari ne?"

"ÆŠan Kano ne...

"Haba dan Allah ya sunansa ina fatan ma ya kasance mijin ƙawar tawa dan ita ma ƴan Kano ne?"

"Sunansa Alhaji Sani Habu ana kiransa da...

"Ana kiransa da Soja" Hajiya Suwaida ta katse Hajiya Hauwa ta hanyar ƙarasa mata sunansa dan ta fahimci shi ne mijin ƙawarta Wasila da suka yi F.U.D anan Dutse.

Wani ihu mai ƙarfi Hajiya Hauwa ta sanya, jin am samo mafita.Ita ma Hajiya Suwaida sai wata dariya take ta mahaukata jin komai ya zo da sauƙi.

"Yadda za a yi zan kira ta mu yi magana nasan babu abin da zai gagara, in yaso sai a É—ora neman kuÉ—in a can Chinan a É—ora daga in da aka tsaya dan ai ko'ina ma akwai kalar mutanen da kake son rayuwa da u wla na banza wala na kirki" Cewad Hajiya Suwaida suna dariya cikin farinciki.

Haka suka ƙarƙare maganar su, cikin jin daɗi suka yi sallama akan cewa Hajiya Suwaida za ta kirata Hajiya Hauwa ta sanar da ita duk yadda suka yi da Wasilar haka suka yi sallama.

Sosai Hajiya Hauwa ta ji daÉ—in a ranta ta ajiye wayar tana furtawa a fili cewa

"In kasan wata ai baka san wata ba wallahi Alhaji da ni kake zancen mu zuba mu gani" Wayar ta ƙara ɗauka ta kira Iftihal ɗin cikin yan sakanni sai gata ta turo ɗakin ta shigo tana shigowa ta faɗa jikin Auntyn nata tare da sakin wani kuka.Bayanta Hajiyar ya shiga bubbugawa tana lallashinta har sai da ta samu ta yi shiru sannan ta shiga kora mata jawabi kamar haka.

"Ki daina kuka Iftihal babu abin da zai faru kuma ma gidan da zai kai ki na san matar gidan kuma ƙawar Hajiya Suwaida aminiyata ce dan haka ba za ki takura ba za ki yi duk abin da ranki ke so, dan kin san su dama maza ba mazauna gida bane bare ya takuraki shi abokin Abien naki.Hajiya Suwaida za ta kirata ta mata jawabi dalla-dalla.

Wani daɗi ne ya ziyarci zuciyar Iftihal ɗin ta rungume mahaifiyarta ta cikin farinciki dan dama ita a rayuwarta ta tsani takura bare yanzu da idanunta suka buɗe ba ta jinnza ta ɗauki kulle a gida kamar wata matar aure.Haka dai su ka yi ta tsara yadda komai zan kasance idan Iftihal ɗin ta je Chaina maimakon a gan su suna ɓacin rai sai aka ga saɓanin haka saboda aun riga sun samo mafita basu da matsala.

A ɓangaren Hajiya Suwaida ma ta kira Hajiya Wasila ta rattaba mata bayani, aikuwa ta ji daɗi dan dama mijin nata ya faɗa mata cewa abokinsa zai kawo ƴarsa ɗaya tilo gidansa domin ta yi karatu.Jin cewa kuma ƴar gidan aminiyar ƙawarta ce kuma ga ƙudurinsu kuma ita ma fama ƴar harka ce dan haka kwa suka ƙudurta neman kuɗi sai sun ga abin da ya turewa buzu naɗi.

Suna gama wayar Hajiya Suwaiba cikin azarɓaɓi ta kira aminiyarta ta labarta mata yadda suka yi, daɗi a wurin Hajiya Hauwa kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YATINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

PAGE2️⃣5️⃣&2️⃣6️⃣

_Umma Sadiya_

Zaune take akan tabarma bayan magriba, Malam Auwalu ne ya shigo ɗauke da sallama amsa masa ta yi tana masa sannu da zuwa, zaunawa ya yi akan tabarmar ita kuma ta tafi ta kawo masa abincinsa tuwon masara da bushashshiyar kuɓewa.Ruwan da ta ɗakko masa a wata ƴar roba mai faɗi ya wanke hannayensa, miƙa masa ta yi ya yi Bismillah ya fara ci suna ɗan taɓa hora yana ta yabon daɗin da girkin ya yi.

"Wallahi lamarin yaron nan yana ɗaure min kai, duk da dai nasan halin da zai tsinci kan sa a ciki sanadin ɓatan su Ridallah amma yadda na ga ya ɗauki abin ya girmama kar abin ya taɓa karatun sa" Ta ƙarasa faɗa tana kallon Malam ɗin da ya dage sai cin abincinsa yake da alama daɗin ya wuce inda ake zato.

Sai da ya kai lomar ƙarshe ya ture kwanon da ta zuba masa a ciki gefe sannan ua wanke hannunsa da bakinsa ta miƙa masa ruwan da ta zuba masa a ƙaramin kofi ya karɓa ya sha sannan ya fara bata amsa.

"Duk maganganun ki haka suke amma sai dai babu yadda za a yi Hizbullah ya ki maida hankali a karatu sanadin damuwar da yake ciki, ke kan ki kin san halinsa baya wasa da karatu duk da yana da damuwa a ransa amma haka ba zai sanya ya yi watsi da abin da ya kai shi ba"

"Hakane Malam amma yadda ya damu ne abin ke tsoratani wallahi kullum fa sai ya kira ya fi a ƙirga yana tambayar an gan su ko an samu labarin su"

"Wannan duk ba wata matsala ba ce kuma ke kan ki kinsan irin yadda ya shaƙu da yarinyar a yadda ma ya yi ai ba ƙaramin yaƙi ya yi da zuciyarsa ba kuma kiran da yake yana tambaya kar ki ɗauka wani abu yana yin hakan ne da ya samu sauƙi da salama a cikin zuciyarsa saboda Allah kaɗai ya san yadda yake ji abin da nake so kawai mu ƙara dagewa da addu'a akan Allah ya bayyana su, kuma duk lokacin da ya kira ki rinƙa kwantar masa da hankali"

"Wannan haka yake, kuma insha Allah za mu cigaba da addu'a kuma zan cigaba da kwantar masa da hankali dan ya samu nutsuwa ya yi karatun"

"Yawwa to Allah mana jagora su kuma Allah bayyana su"

"Amin amin" Ta faÉ—a tana tashi ta shiga kwashe kayan da ya ci abincin.

_GAGARAWA L.G_

Tafiya take wasu dandazon yara biye da ita suna tafi suna mata waƙa.

"Mahaukaciya ta É—an Bala,mahaukaciya ta É—an Bala" Haka suke ta faman faÉ—a suna tafi suna dariya haÉ—e da tsalle-tsalle ita dai bata musu komai ba hasalima kamar ba da ita suke ba dan ita dama bata faÉ—a bare kuma yanzun da take tafiya kamar a gabaice ma take da alama wani abu na damunta, a daidai wata kwana kawai sai gani suka yi ta yanke jiki ta faÉ—i cikin razana da tsoro yadda suka ga ta yi yasa yaran ja da baya suna cewa.

"Ta mutu!!! " Suna ta maimaitawa, a guje duk suka fara watsewa suka barta anan yashe da yake layin babu mutane sosai shi yasa babu wanda ya gan su bare ya san mai ya faru.

Malam Idi mai almajirai ne tafe shi da wasu almajirai guda huɗu daga gonarsa suke suka yi aiki shi ne suka taso ganin magriba ta kawo kai, dan dama da yamma ne suka koma gonar saboda daman sun je da safe.Kwanar da suka shawo sai ganin mace suka yi kwance a ƙasa cikin hanzari Malam Idi ya yi kan ta tare da almajiran nasa, haka yasa almajiran suka kamata da yake matasa ne da ɗan girmansu kuma dama a layin gidan nasa yake.Haka yasa suka kai ta har cikin gida yasa matarsa Malama Zainab ta shimfiɗa tabarma da yake ita ma mace ce mai kirki ko yadda jikin mahaukaciyar yake bata ƙyamata ba bare ta ce ba za a ɗora mata ita ba akan tabarma.
Chapter 13 · 0% Book details