← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 18 OF 29

Sashe 18

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Ridallah babu abin da yake damuna, kawai dai wani lokacin na kan tsinci kai na a cikin damuwa idan na tuno da mahaifinki" Ta faɗa tana sanya hannu ta goge ƙwallar idanunta.Ita ma Ridallah ƙwallar ce ta ciko mata idanu jin maganar ta Baba ta sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi dan duk lokacin da aka yi zancen mahaifi sai ta tuna nata bare kuma aka yi magana a kan mahaifinta ta kan tsinci zuciyarta cikin rauni hakan yana tuna mata cewa ita marainiya ce ba ta mahaifi a raye dan ita ko a hoto ba ta taɓa ganin mahaifinta ba kawai dai ta san Baba ta ce mata kamarsu ɗaya da mahaifin nata babu abin da ta bari na mahaifinta to idan ta kalli kan ta a madubi ta hakan take ganin fuskar mahaifinta a jikin fuskarta.

"Ki yi haƙari Baba kawai mu cigaba da masa addu'a Allah lulluɓesa da rahamarsa"

"Amin Ridallah" Baba ta ce tana rungumo Ridallah jikinta cikin tausayinta dan ita ba wannan tunanin mutuwar bane kaÉ—ai damuwarta akwai wata damuwar da ita kaÉ—ai ta san da ita ko Ridallah ba ta san da hakan ba.

Haka dai Ridallah ta cigaba da lallashin mahaifiyarta a haka har Iya Rahma ta dawo lokacin dab da magriba ne ta kaÉ—a miyar sannan ta shinfiÉ—a musu sallayoyi akan tabarma ta ajiye musu carbinsu aka sannan ta wuce ta yi alwala.Bayan sun gabatar da sallah suka É—ore hirarsu har sai da aka yi sallar isha'i suka yi sannan Ridallah ta zubo musu tuwon su ka ci.

Haka suka yi hirarsu har wajen ƙarfe goma ganin an kawo wuta sai Ridallah ta sanya musu gidan sauro a ɗaki da yake ita Iya Rahma a nata ɗakin take kwana su kuma a ɗaki ɗaya, hakan ya sa ta shiga ɗakinta su ma suka mata sallama suka shiga nasu ɗakin.Bayan sun yi addu'a suka kwanta suna ƴar hirarsu har bacci ya yi awon gaba da su.

Cikin dare wasu samari guda uku suka diro daga saman katanga, sun tsaya suna ƙarewa gidan kallo.

"Baaba ka san fa ba mu san É—akin da yarinyar take ba kar fa mu je ka hakewa tsohuwa" ÆŠaya daga cikinsu ya faÉ—a yana kallon wanda ya kira da suna Baaba.

"Kai fa gara ne wa ya ce maka a duhu za a aiwatar dole ai a haska fitila kuma ko ma ba a haska fitila ba ai babu yadda za a yi na kasa banbance tsohuwa da yarinya sai ka ce wani kai" Baaban ya bashi amsa.

"Mu shiga nan ɗakin ka ga takalmi biyu da alama wannan ƙaramin na yarinyar ne ka ganshi na soso mai ɗan tudu" Ɗaya ma ya faɗa yana washe baki, gabaɗayan su suka bushe da dariya dan da alama ma ƴan shaye-shaye ne dan daga maganarsu ma ana iya fahimtar su waye su.

"Fito da bindigar nan" ÆŠaya ya faÉ—a cikin raÉ—a-raÉ—a

"An gama Oga" Ya faɗa yana ɗaga rigarsa ya fito da bindiga daga inda ya soketa a ƙugunsa.

Karɓar ya yi ya jujjuyata a hannunsa yana dariya, su ma dariyar suka yi kafin suka ɗunguma suka shiga ɗakin da su Baba Habiba suke dan ƙofar buɗe take hatta da labulen a ɗage yake saboda zafi sai ƙaran fanka da ke ta aikinta suka sai baccinsu suke hankali kwance.

Da fitilar wayarsu suka yi amfani suka gano makunnar ƙwan ɗakin suna kunnawa kwa haske ya gauraye ɗakin, hango su Ridallah suka yi cikin net suna ta bacci Ridallah sanye da rigar bacci mai ƙaramin hannu.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

Page3️⃣2️⃣&3️⃣3️⃣

Hannu ɗaya daga cikinsu ya sanya ya ɗauki ruwa a wani jug ya zuba a hannunsa ya watsawa su Baba Habiba da ke bacci, gabaɗaya suka tashi suna dube-duba Ridallah tana murtsuke idanu, a tare suka sauke idanunsu akan ƙartan mazan da ke tsaye suna rarraba jajayen idanunsu sai wani wari ke tashi a jikinsu.

"Baby ya kike kallonmu a tsorace wurinki fa muka zo" Ogan nasu da ke riƙe da bindiga ya faɗa yana washe baki.

"Subhanallahi! Dan Allah ku yi haƙuri ku rufa mana asiri" Baba ta faɗa tana ƙoƙarin gyara ɗaurin zaninta dan har sun fito daga cikin net ɗin nasu.

"Tsohuwa idan ba so kike a haÉ—a da ke ba ya kamata ki yiwa bakinki mukulli ki fito ki jira oga a waje ya kammala aikinsa"

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Dan Allah ku taimaka min"Ridallah ta ce a kiÉ—ime tana É—ora hannu aka, dan lokacin ta fahimci abin da suke nufi dan har Ogan nasu ya cirw belt É—insa.

"Dan Allah ku yi hakuri ko me kukeso na baku zan baku amma kar ku keta haddin marainiyar Allah" Baba ta faɗa tana durƙusawa a gabansu hawaye na zuba a idanunta.

"Ko ki fita ko mu fitar da ke da ƙarfin tsiya, in kuma kina son gani akan idanunki a karɓi amarcin kyakkyawar ɗiyarki to zaki iya neman wuri ki zauna dan muma fita za mu yi"Ɗayan ya faɗa yana karɓar bindigar hannun Ogan nasu ya nuna Baba da ita, dan Ogan nasu ya raja'a da son ɓalle maɓallin jikin wandonsa dan so yake su yi su gama dan gudun kar a samu matsala.

Cikin tsananin tsoro Ridallah ta kai kallonta kan bindigar da aka saita Baba Habiba da ita, wani abu ne ya ɗarsu a ran ta lokacin da ta kafe bindigar da ido, dan dama da ganin samarin nan ta san da wuya su mallaki bindiga dan kawai kana ganinsu kasan kawai ƴan iskan unguwa ne irin masu dira gidajen mutane su saci waya da sauransu ba wasu riƙaƙƙun ɓarayi bane.Fakar idon su ta yi dama a tsugunne take ta kai hannu ta janyo ledar yajin daddawa da suka ci tuwo cikin hikima ta ware ledar da hannu ɗaya ba tare da kowa ya kura da abin da take yi ba tana gama warewa ta shammacesu ta miƙe tsaye ta watsawa Ogan nasu a ido, wani ƙara ya saki kafin ka ce me ta ƙara watsawa ɗayan ma, shi ma ihu ya saki mai mugun ƙara, a take ɗayan da ke riƙe da bindigar ya saki bindigar ya fita a guje yana cewa sai kun taho Oga, da gudu ya bi hanyar ƙofar gida ya buɗe ƙofar a cikawa rigarsa iska ya barsu suna dawur wurin neman hanya sai miƙa hannu suke kamar makafi.

Ƙaran nan ne ya tashi Rahma da ke ɗakinta, a tsorace ta ƙudundune a bargonta gabanta na faɗuwa dan ta tabbatar ƙaran a cikin gidan ne kuma muryar ƙartin maza lalai yau ɓarayi sun ziyarci gidan.Ridallah kwa wata sanda ta ɗakko a bayan ƙofa ta shiga dukansu da ita suna ta ihu ga yajin ba kaɗan bane ya shiga idanunsu haka suka shiga kuka suna bata haƙuri cikin halin ko in kula ta fara magana.

"Ku kama hanya ku fitar mana a gida, kuma daga yau idan kuka sake zuwa sai na muku wanda ya fi wannan dan da aljannu na zan haÉ—a ku su kai min ku birnin sin"

"Wallahi ba za mu sake zuwa ba, ko wani gidan mun daina shiga da sunan sata ko fyaÉ—e daga yau É—in nan"

"Ku yi yamma kuke tafiya zan ke faÉ—a muku inda za ku bi"

Haka suka rinƙa tafiya suna lalume tana faɗa musu inda za su yi, idan kwana za su yi ta faɗa musu dan ko buɗuwa idanun basa yi saboda tsananin yaji, a haka har suka fita ƙofar gida dan har karo suke yi da juna suna fita ta banka ƙofar gidan ta sanya sakata tare da komawa ta jingina da jikin ƙofar tana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya dan ta san ba ƙaramin jarumta ta yi ba yau dan dukan maza kamar wannan gaskiya ta yi ƙoƙari duk da tana ganin hakan kamar ganganci amma kuma idan ta tuna ba wasu ɓarayin kirki bane illah ƴan jagaliya ne sai warin kayan maye suke dan kawai ƴan shaye-shaye ne na unguwa.Tunowa da ta yi da abin da ya bata ƙarfin gwiwa har ta aikata hakan shi ya sanya ta taho cikin gidan cikin sauri, Baba ta gani da Rahma suna tsaye suna maida yadda aka yi.

Dan suna fita Rahmar ta fito daga É—akin dan jin ana dukan ana ihu ya fargar da ita me ke faruwa, shigowar Ridallah ya sa suka nufota suna murna, ita kuwa murmushi kawai ta musu tare da shiga É—akinsu ta É—akko bindigar da suka bari ta nufo su Baba da ita.

"Innalillahi wai anan suka bar mana bindigar dama? Mun shigesu "Rahma ta ce tana kama baki da mamaki.

"Bari ku ga bindiga"Cewar Ridallah tana kama kunamar bindigar ta matsa, sai kawai suka ji ƙaran bindigar yara har danjar jiki tana kawo wa.Ƙyalkyalewa Ridallah ta yi da dariya ta ce.

"Kun san ya akayi na gane ba bindigar gaske ba ce"

"Ja'ira sai kin faÉ—a"Baba ta ce ita ma tana dariyar.

"Kawai fa lokacin da Ogan ya miƙa masa bindigar sai na hango batiri dan wurin batirin ba murfi, shi ne na fahimci bindigar wasan yara ce"

"Ikon Allah kawai Allah ne ya cecemu ya kuma ceci mutuncinki Ridallah, amma da bindigar yaran ce za ta musu amfani dan da ita za su yaudaremu mu tsorata har su ida nufinsu a kan ki sai kuma Allah ya kawo hanya mai sauƙi ido ya juye da mujiya dan gashi nan sun ɗanɗani kuɗarsu"Baba ta ce tana karɓar bindigar daga hannun Ridallah take ƙarewa bindigar kallo.

" Wallahi kawai dama ƴan iskan unguwa ne, in ba haka ba ina na taɓa jin an tafi ko sata da bindigar wsan yara"Rahma ta ce tana jimanta abin.
Chapter 18 · 0% Book details