← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 22 OF 29

Sashe 22

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Cikin hanzari ya nufi wurin abokin nasa, yana zuwa ya ga Hizbullah na zubar da hawaye yana ta magana shi kaÉ—ai

"Ridallah dan Allah kar ki min haka, ina sonki a hakan ma, babu wani hali ko yananyi da za ki tsinci kan ki a ciki wuya ko daɗi kyakkyawan hali ko akasin haka babu wani bau da zai ragu daga cikin ƙaunar da nake miki, ganinki da na yi yau ya ƙara rura min wutar son ki a cikin tai da zuciyata, amma ya aka yi kika ƙara tafiya kika barni bayan ni ba zan iya barinki ko da na lokaci ƙanƙani ba amma ke kin tafi kin barni tsawon wasu shekaru yanzu kin dawo amma kika ƙara guje min? Shin kin san wani irin hali zan sake shiga ta dalilin hakan? Haba Ridallah mai ya sa za ki guji wanda ya fi ƙaunarki fiye da kan sa a rayuwarsa? Wanda ya fifita son ki a kan kowacce mace bayan mahaifiyarsa a rayuwarsa, wanda ya ƙudurta zamar miki bango abin jingina a rayuwarki, wanda zai riƙe miki maraicinki ya kyautata miki ya zamar da ke sarauniya har iya ƙarshen numfashin da Allah ya ɗaukar masa, mai yasa Ridallah, mai yasa zaki min haka, mai yasa bakya tausayin mai ƙaunarki da gaskiya!!! " Yana kaiwa ƙarshen maganar ya durƙushe a wurin yana sakin wani kuka mai tsuma zuciya, dan gabaɗaya sai yau ya ƙara sanin ba zai iya rayuwa in ba Ridallah, haƙiƙa ƙaunar gaskiya wata aba ce mai wuyar ƙanƙaruwa daga zuciya sai dai kullum take ƙaruwa tana hauhawa a zukatan masu yin ƙauna dan Allah ba masu yin soyayyar yaudara ba soyayyar da babu komai sai sha'awa da tarin yaudara.

(TSOKACI ki nutsu da kyau ki gane mai ƙaunarki da gaskiya, wanda ke son ki da aure ba waɗannan samarin ba wanda babu komai a ransu sai yaudara ba komai yake so ba sai jikinki bashi da buri kullum sai yadda zai yi amfani da kalamai da kuma kaifin harshe wajen jan hankalinki ki mallaka masa kan ki da zarar kuma ya samu abin da yake so da ke da bola duk ɗaya.Mutuncinki shi ne ribarki shi ne ribar iyayenki kada soyayyar shan minti tasa ki siyar da darajarki ta ƴa mace darajar iyayenki da ta ahalinki bakiɗaya.Bayan nan darajarki ita ce mutuncinki da ta ƴaƴanki domin kema uwa ce wata rana ki zama wacce ƴaƴanki za su yi alfahri da ke a matsayin uwa domin duk abin da kika yi ƴaƴan nan naki fa zasuyi kin ga kin jefa rayuwarsu a matsala, saurayin da zai ke taɓa miki jikin ki wallahi wallahi ba mai ƙaunarki bane! Allah tsaremu daga azzalumai).

Tausayin Hizbullah ne ya shiga zucouar Abulkairi ji yake ina ma yana da iko da ya cikawa Hizbullah burinsa ko dan kasancewarsa mutumin kirki amma tabbas rangwame irin na raɗaɗin soyayya sai wanda ake yin soyayar domin shi, shi ne zai iya faɗawa masoyin kalamai wanda za su tausasa zuciyarsa, haƙiƙa wannan aikin Ridallah ne sai dai shi ya masa addu'a akan Allah warware wannan ƙullin da ya sake tunkaro rayuwar Hizbullah.A hankali ya ƙarasa kusa da shi hannu ya sanya ya dafa kafaɗarsa ya ɗan ranƙwafo ta gefensa ya ce

"Haba Hizbullah ka zama namiji mana"

"Wane namiji kuma kasan zafin so kwa Abulkairi? Kasan yadda nake ji kwa yanzu, kasan halin da zan cigaba da kasancewa yanzu da na yi tozali da wacce soyayayarta ta rayu a cikim zuciyata tun ALAƘAR YARINTA, soyayyarta ta girma a raina ina bege da muradinta, duk da bana ganinta amma hakan bai rage ko kaɗan na daga soyayyar da nake mata ba, ka sanya kan ka a matsayin ni yau gashi na gan ta amma ta nuna bata ma sanni ba har tana iya ɗaga hannu za ta mareni, Ridallah nutsatstsiyar yarinya kamila wacce tun tana ƙarama nake rainonta da ɗabi'u masu kyau amma yau na ganta a wani yanayin marar kyan gani ko wannna kaɗai ya isa tashin hankali a gareni"

" Na sani Hizbu, na sani bu ne mai ciwo abu ne mai girma amma haƙuri da dangana shi ne babbar mafita...

" Haƙuri da dangana su kaɗai ba zan samu sauƙin a zuciyata ba sai dai addu'a kaɗai ce za ta sanya na samu salama" Ya katse Abulkairi ta hanyar yin maganar cikin ƙaraji tare da fashewa da kuka mai ciwo.

Zagayowa gabansa Abulkairi ya yi gaban Hizbu shi ma ya zauna a ƙasan, tare da zuba masa idanu shi ma a take nasa idanun suka ciko da hawaye tausayin abokin nasa ya tsarga masa a cikin ƙoƙon zuciyarsa ji yake ina ma bai riƙeshi ya hanashi tahowa wajensu ba, dama ya barshi ya cim musu da duk hakan bai faru ba duk da yana ganin da ya barshi ya tarar da su Allah kaɗai ya san abin da zai faru, dan ba ya so Hizbun ya je ya yi abin da zai taɓa masa karatunsa.

Zabura Hizbu ya yi, ya miƙe tsaye shi ma Abulkairin

miƙewa ya yi ya sha gabansa da ya ga yana ƙoƙarin bin wata hanya da ban

"Wai ina za ka je ne?"

"Taxi zan samu na tafi gida, so nake kawai na jini a kwance jj nake ƙafafuna ba za su iya ɗaukana ba saboda halin da zuciyata ke ciki, idan aka jima ma zan iya faɗuwa ka rabu da ni dan Allah'

" Wane irin gida kuma Hizbullah mu da za mu koma scul, ka san fa ba mu gama da scul É—in ba yunwar da kake ji yasa muka baro makaranta saboda ka ce ba ka son siyan abincin restuarant makarantar ba sai dai mu zagayo wannan Restuarant É—in ka ga ganin babu nisa da scul É—in muka zagayo kuma maimakon mu koma sai ka ce gida za ka tafi?"

" Ka bar maganar scul É—in nan kawai"

Shiru ya yi yana nazarin halin da abokin masa ke ciki tabbas ko shi ya fahimci ko da sun koma scul ɗin Hizbu babu abin da zai iya taɓukawa, hakan ya sa ya tare musu taxi suka shiga dan shi ma ba ya jin zai iya barinsa a halin da yake ciki ya tafi gidan shi kaɗai gwara dai ya kasance a kusa dashi ko zai samu sassaucin a cikin zuciyarsa kuma idan yana kusa da shi ɗin zai rage zurfin tunani a maimakon idan shi kaɗai ne tunanin zai yi yawa sosai.

Suna zuwa gidan ya hau sama da sauri ya buɗe ɗakinsa ya shiga ya rufo ƙofar ya sanya mukulli, dan haka Abulkairi na hawo wa saman ya murɗa ya ji ƙofar a kulle cikin sanyin jiki ya koma ya buɗe nashi ɗakin ga shige, sai a lokacin ma ya tuno sun bar handout ɗin a Restuarant ɗin kai kawai ya kaɗa ya shiga yin wasu hidimomin.

Hizbullah kwa na shiga ya wuce ya É—akko É—ankunnen da flower da Ridallah ta bashi ya shiga kallon su yana maganganu shi kaÉ—ai dan shi duk gani yake kamar ya rasa Ridallah dan shi duk tunaninsa Ridallah ce Iftihal É—in.

MMN AFRAH😍🥰😘

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

Page 4️⃣0️⃣&4️⃣1️⃣

*IFTIHAL*

Suna fitowa ita da Alhajin daga Restuarant ɗin ta ja ta tsaya, shi kuma ganin tana wani shan ƙamshi tana haɗr rai sai duk ya ji ba daɗi, amma hakan bai sanya ya ji kp da haushinta ba shi dai kawai so yake buƙatarsa ta biya.

"Kinsan fa wani abokina da ke zaune a nan ne ya sanya direbansa ya kawoni yanzu kuma sai dai mu shiga taxi mu je Hotel ɗin in kama mana ɗakin da za mu huta ko baby?" Ya faɗi hakan yana wani murmushi tare da washe haƙora sai wani lasar baki yake kamar wani tsohon maye.Ƙasa ta yi da glases ɗin nata ta masa kallon up nd down ta sauke idanunta a kan ƙaton tumbinsa tari guda kamar mai cikin wata tara, ɗauke kai ta yi gefe tare da maida glases ɗin nata yadda yake ta ɗago wayarta ta duba time.

"No kar ma ki yi la'akari da wannan cuki ba wai tsufa bane ya sanya y yi girma hakan tsabar cin daÉ—i ne da kwanciyar hankali kinsan idan akwai kuÉ—i to mutum bashi da matsala sai wacce ba a rasa ba"

"Ok ni ai ka san daga gidan talauci na fito"

"Ba haka nake nufi ba baby, inaso na sanar da ke yau idan ki ka tashi tafiya za ki tafi da maƙudan kuɗaɗe wanda kowa sai ya san kin yi tarayya da wanda ke matashin kai da kuɗi" Ya faɗa yana washe baki.

Jin ba ta ce komai ba ya sanya ya ƙara cewa

"Mu je ko muna ɓata lokaci" Dan shi gabaɗaya wannan shan ƙamshin da take burgeshi take yi sabod yana son ya ga mace mai aji ya fi son hakan dan an fi daidaitawa da shi.

Ita ta fara yin gaba, ganin ta nufi wajen wata mota da ke fake a wurin ya gane cewa da mota ta zo, hakan ya ƙara tabbatar masa da babban yarinya ce saboda har mota gareta ta kan ta.Suna isa ta sanya mukullin ta buɗe ta shiga wurin direba ta zauna sai dai ƙafafunta a waje suke, jakarta ta jefa kan ɗaya sit ɗin mai zaman banza, shi kuma cikin sauri ya nufi ɓangaren mai zaman banzan zai buɗe ya shiga sai washe haƙora yake kamar gonar auduga.

Iftihal na ganin ya gewayo ta maida ƙafafunta cikin motar ta rufe ƙofar, gabaɗaya ta kulle motar Alhajin na kama ƙofar zai buɗe ya ji ta a kulle, ƙwanƙwasawa ya yi amma maimakon ta buɗe sai ta sauke glass ɗin ta sanya hannu ta yi ƙasa da glases ɗin fuskarta ta masa wani kallon ƙasƙanci ta ce
Chapter 22 · 0% Book details