Sashe 21
Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Ta ruɗe ta ma kasa tambayar ƴar aikin takamaiman abin da ke faruwa, ita ma kuma ƴar aikin ba ta san abin da ke faruwa ba kawai dai ta hango wasu dogarai guda biyu sun riƙo Alhaji, sannan direba da mai gadi sun riƙo Hafiz dan duk sai da aka shiga kafaɗarsu. A can part ɗin Alhaji Sunusin an zaunar da Hafiz da Alhajin a kan kujerar sai aka jinginar musu da bayansu a jikin kujerar, a dai dai nan Hajiya Sakina suka ƙaraso ita da mai aikinta.
"Subhanallahi! Me ke faruwa da su ne? Ko guba aka zuba a cikin abubuwan da aka ci a wurin taron ne?" Hajiya Sakina ta faÉ—a cikin gushewar hankali dan gabaÉ—aya ta tsorata da yanayin da ta gan su.
"Wallahi Hajiya ba haka bane, bayan an kammala taron ne ma suka haɗu da Sarkin yaƙi daga haka kar ki ƙara kar ki raga, shi ne gabaɗaya suka kasance a cikin wannan halin har gwara ma shi Sarkin Ƴakin a kan su dan su sai da mai martaba ma ya bada umarni dogaran nan su tayamu mu kawo su gida" Direban ya mata bayani ai ambaton sunan Sarkin Yaƙi da ya yi sai da kan ta ya sara mata da mugun ƙarfi har sai da ta dafe da hannu ɗaya sannan a hankali ta zauna.Ganin halin da ta shiga yasa ƴar aikin nata yin sauri tana mata sannu.Shiru ba ta yi magana ba sai zuwa can ta ce
"Yawwa"
Sai ta maida hankalinta kan mai gidan nata da É—an nata, ta taso ta zo garesu tana tambayar mai je damunsu dan har ta manta da labarin da direban ya bata hakan ne ya sanya kan nata ma ya saka mata.
Daga dogaran har direban da mai gadin kallon kallo aka shiga yi jin tambayar da ta fito daga bakinta, babu wanda ya sake wata magana dan su ma sun lura kamar akwai halin da ta shiga lokacin da aka faɗa mata dalilin da ya sanya suka shiga wannan halin.Sallama dogaran suka musu tare da musu fatan samun sauƙi, shi ma direban fitowa ya yu shi ma mai gadin ya koma bakin aikinsa.
Sun É—auki tsawon awa guda sannan suka dawo hayyacinsu, dan dama ba dai bacci suke ba amma yanayinsu kamar na wanda suka sha abin maye suka bugu.Ganin sun farfaÉ—o yasa Æ´ar aikin nata ta fita ta koma bakin aikinta, ita kuma sannu ta shiga musu dan daga ita har su sun riga da sun manta takamaiman abin da ya faru.
Sun dawo kamar ma babu abin da ya faru dan abin kamar wani shafar aljannu, alwala suka yi suka yi sallah Alhajin ne ya ja su sallar har Hakiya Sakina dan lokacin har an riga da an idar da sallar azahar ɗin, bayan sun idar suka ci abincinsu cikin kwanciyar hankali suna taɓa hira cikin farinciki da barkwanci.
"Sannu da zuwa Baba Malam Baiwar Allah ta faÉ—a cikin girmamawa.
"Yawwa sannu Baiwar Allah, wanki ake"
"Eh"
"Ke dai bakya gajiya da aiki" Ya ce yana murmusawa.
"Kai ma dai ka faÉ—a Malam ni ma yanzu na gama faÉ—a"
"To ai shikenan tun da tana son yin aikin ai shikenn"
"Wlh kwa dan yanzu ma ta gama kwashe tuwo ta ɗora miya, ni ce ma na ce zan ƙarasa miyar daker ta yarda shi ne ta ƙara tsirar wanki" Malama Zainab ta ce tana ɗaukan ledojin da Malam ya iyo tsaraba, daga wani ƙauye da ya je wurin wani babban Malami abokinsa domin su haɗa wani magani da za a haɗawa Baiwar Allah.
Bayan ya ci abincin dare suna hira a tsakar gida ya ce Malama Zainab ta ɗakko masa wata baƙar leda da ya zo da ita a hannunsa ɗazu da ya dawo ya faɗa mata inda ledar take dan ɗazu ma da ya zo da ita a cikin aljihun babbar rigarsa dan maganin ne sanadin tafiyarsa tun bayan sallar asuba.
Bayan ta ɗakko ya buɗe ledar ya fito da gora mai ɗauke da rubutu, sai kuma wani ƙullin magani ya ce
"Wannan rubutun da kike gani, idan aka zuba maganin nan ta sha na tsawon kwana uku to duk wani abu da ta manta za ta tuno da shi, ba ma ita kaɗai ba matsawar sihirin mantuwar nan ya bar jikinta to duk su ma wanda aka musu tare sai ya bar jikinsu, domin su biyar ne aka yiwa sihirin duk da ban san sauran ba amma nasan ba za su wuce makusantan da ba saboda su manta da ita ba za su tuna da ita ba ma bare har su nemi inda take amma cikin ikon Allah komai ya kusan zuwa ƙarshe kamar yadda haukar ta bar jikinta da izinin Allah haka ma mantau ɗin zai bar su" Cewar Malam Idi yana buɗe gorar ya since maganin ya shiga zubawa a ciki.
"Alhamdulillah! Na yi matuƙar farinciki da samun wannan magani Allah ƙara muku sani da basira Allah kuma ya taimakeka ya baka ladan abin da ka yi" Malama Zainab ta faɗa cikin farinciki dan tana jin Baiwar Allah tamkar ƴar uwarta ta jini iya zaman da suka yi na kusan shekaru uku da wani abu.
"Ai nake faɗa miki maganin ne samun sassaƙensa akwai wahala, shi yasa gashi ba mu da bishiyoyin a nan wajen a can ma da na je sai da muka yi tafiya mai nisa kafin mu je ga inda muka samu bishiyoyin muka sassaƙa, na daɗe ina neman inda zan samu sassaƙen amma ki ga cikin hikimar Allah yanzu da lokacin ya yi na samun lafiyar warakar mantau ɗin nata sai a abokina da na tambaya ya ce akwai a wajen ƙauyensu ana samu, gashi dai mun haɗo mun kuma rubuto ayoyin da za su taimaka sai da ya tayani duk muka rubuce sannan aka wanke aka ɗiga nonon jikin bishiyar saboda kafin azo nonon ya ƙame, hatta sassaƙen ma sai da ya sanya matarsa ta daka min"
"Kai gaskiya an gode Allah bar zumunci ya barku tare"
"Amin, ki mata magana ta fito ta sha maganin"
"To bari na kirawo ta tun da ta shiga ta yi sallar isha'i da ta idar ba ta fito ba ko kwanciya ta yi, ka san ba ta sakewa idan kana nan tana ganin girmanka" Malam Zainab ta faɗa tana tashi ta kwashe kwanukan tuwon ta shiga ɗaki ta kira Baiwar Allah, bayan ta fito ta zauna a kan tabarmar da Malama Zainab take zaune, Malam ne ya tsiyayo maganin a ƙaramin kofi ya miƙawa Malama Zainab ta miƙawa Baiwar Allah, Bismillah ta yi ta kafa kanta ta shanye dan ko ɗanɗano maganin bashi da shi babu ɗaci babu komai haka ta shanye ta ajiye kofin tare da musu godiya, cikin jin daɗi suka ce ba komai dan an zama ɗaya babu batun godiya sai dai fatan dacewa maganin ya yi aiki.
MMN AFRAH
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
💕ALAƘAR YARINTA💞
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
NA
MMN AFRAH
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .
Wannan littafi daga farkonsa har Æ™arshensa sadaukarwa ne ga aminiyar Æ™warai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar Æ™auna tsakaninmuâ¤ï¸
Page 3ï¸âƒ£8ï¸âƒ£&3ï¸âƒ£9ï¸âƒ£
*HIZBULLAH*
"Dan Allah Hizbullah ka nutsu ka saurareni, bana so ka sanya kan ka a cikin matsala, wannan yarinyar da ganinta ba yarinyar arziƙi ba ce bare kuma shi mutumin da suke tare zai iya maka komai idan ka bisu dan Allah abokina ka dawo hayyacinka" Abulkairi ya ce lokacin da ya ƙara riƙo rigar Hizbu daga baya da ya yi yinƙurij bin su Iftihal.Wani ruwa ne ya ciko cikin idanun Hizbu saboda bai san da kalaman da zai yi amfani da su ba Abulkairi ya bar shi ya bi bayansu kuma ba ya so su ɓacewa ganinsa gashi duk kan sa ya kulle baisan ta ina zai fara tsayawa yiwa Abulkairin bayanin cewa ita ce Ridallah ɗinsa da da yake kwana da rashinta yake tashi yake cike da damuwa a cikin zuciya da ruhinsa wanda babu wanda ya san hakan sai shi sai kuma Allah da ke ganin zukatan bayinsa.
" Ka yiwa iyayenka ka barni bana tsoron komai ya faru da ni matsawar zan cimmu su kafin su ɓacewa gani na, ka bari zan maka bayani daga baya, saboda kasan dai idan har ta ɓacewa gani na bani da tabbacin ƙara ganinta amma idan na bi bayansu a ƙalla zan san inda take zaune"
Shiru Abulkairi ya yi yana nazarin halin da abokin nasa yake ciki, sosai tausayinsa ya kamashi domin ya ga rauni sosai a tare da shi bayan kuma ya san abokin nasa akwai dagewa da kuma jajircewa ba ya taɓa bari mutum ya ga gazawarsa amma kuma yau gabaɗaya rauninsa ya bayyana duk da dai dama ba abin mamaki bane a ga komai a tare da shi in dai a kan Ridallah ne, shi ya ma kasa gane takamai man inda batun ya dosa dan ya dai san wannan ba Ridallah ba ce duk da bai santa ba amma ya yadda yake bashi labarin Ridallah da irin soyayyarsu bai kamata ace ta nuna bata san shi ba ma tabbas akwai lauje cikin naɗi akwai wani abu a ƙasa da yake ganin kamar shi kan sa Hizbullah ɗin bai sani ba bare kuma shi d...
"Ka sakar min riga" Muryar Hizbu ta katse masa tunaninsa.Kafin ya ce wani abu Hizbullah ya ƙwace rigarsa da ƙarfi ya tafi.Sho ma bashi da wani zaɓi da ya wuce bin bayan Hizbullah ɗin, lokacin da ya zo inda mutane ke cin abinci ya tsaya waige-waige ko zai ga Hizbullah ɗin dan kan meye wannan har ya ɓacewa ganinsa amma bai ga ko da alamarsa ba hakan yasa ya bi ƙofar fita daga wurin ya fito waje, yana ta dube-dube bai ga Hizbullah ɗin ba tafiya ya lan fara yi aikuwa ya hangoshi can wajen parking space ya tsaya hankali tashe yana ta dube-dube.