Sashe 27
Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"To" Ta amsa tare da fara karantawa cikin natsuwa tana gama karantawa ta shanye, sannan ta karanta suratul iklas ɗin, tana kaiwa ayar ƙarshe sai kuwa ta ji kan nata ya mata wani dumm ya yi nauyi kamar an ɗora mata dutsi a kan nata, da hannu biyu ta dafe kan jin yana barazanar rabe mata a biyu, Malam dai bakinsa bai yi shiru ba tun da ya ga yanayinta ya fara canjawa ya shiga karanto sunanyen Allah.Malama Zainab kuwa sai karanta duk abin da ya zo bakinta take, Baiwar Allah kwa tana dafe da kan nata ta fara zamewa hat sai da ta kwanta a wurin dafe da kan ta, sai jujjuyawa take idan ta juya nan gefen sai ta juya nan gefen.
Ganin haka sai Malam É—in ya taso ya dawo gabanta ya shiga karanto ayoyin qur'ani yana ta tofa mata.
"Bana so! Ka daina ƙonani" Baiwar Allah ta faɗa da wata irin murya kai da ji ka san ba muryarta ba ce.
Maimakon Malam ya dakata da karatun kamar yadda muryar ta faÉ—a sai ma ya cigaba.
"Wayyo ka daina zan fita daga jikinta"
Malam cigaba ya yi, aljanin kwa ya cigaba da ihu da kururuwa a kan a daina ƙonashi sai da Malam ya lura ya jigata sosai yadda duk umarnin da zai bashi ba zai yi musu ko gardama ba.
"Mai ya zaunar da kai a jikinta ka sanya mata cutar mantau? Ni duk tunanina babu wani sihiri a jikinta ashe kai kana jiki ka maƙale"
"Ba yin kaina bane aikoni aka yi, ba ma jikinta ita kaÉ—ai ba ni na sanya musu mantau su biyar sama da shekaru goma sha wani abu, amma yanzu zan fita kuma za ta tuna komai da ta manta"
"Saboda rashin imani ka rabota da kowa nata saboda ba za ta iya tuna su ba, su ma ka sanya ba za su iya tuna su ba"
"Ka yi haƙuri yau zan fita yanzu ma kwa"
"Zan ƙyaleka ka fita amma sai na sanya maka sharɗi"
"Wallahi zan bi kowane sharaÉ—i"
"Inaso ka fita daga jikinta kuma ko da wasa kar ka sake dawo wa , sannan si ma sauran ka sake su a yau ɗin nan idan ba haka ba wallahi sai na ƙonaka ƙurmus yadda ko gawayi sai ya fika kyan gani"
"Na yi alƙawari zan bi dukkan sharuɗɗan, kuma su duka zan sake su, ko kanaso in faɗa maka wanda ya sanya aka aikoni jikinsu?"
"Bana son jin komai daga gareka kun saba haɗa husuma to ni bana son jin komai koma wanene ya je dan kan sa Allah na ganinsa"Malam na gama faɗin haka ya cigaba da karatunsa, take Baiwar Allah ta shiga karkarwa kamar wata mai zazzaɓi tana wani abu kamar mai farfaɗiya, cikin lokaci ƙanƙani ta fara wata atishawa sai da ta yi sau uku sannan ta daina karkarwar da take, a hankali ta shiga buɗe idanunta da suka yi wani ja kamar wacce ta daɗe tana kuka, da kallo ta fara bin saman ɗakin da yake a kwancen take reran, haka ta dinga sauke idanunta a kan gabaɗaya ɗakin lafin daga bisani idanun nata suka sauka a kan Malama Zainab, sannan ta maida kallon nata kan Malam, fuska ta yatsina irin na ka ga wanda baka sani ba, kafin ta fara ƙoƙarin tashi daga kwancen da take tana musu kallon ban san ku ba, su waye ku.
"Ina ne nan?" Ta jefa musu tambayar tana kalle-kalle tana musu kallon rashin sani.
"Ki kwantar da hankalinki kina cikin kulawarmu ne kin jima a tare damu kusan shekaru uku" Malam ya faÉ—a yana kallonta.
"Shekara uku kuma? A nan ɗin, ina Alhajina" Ta tambaya idanunta na kawo ƙwalla.
"Ki yi haƙuri ba mu san kowa naki ba mun taimaka miki ne" Malama Zainab ta faɗa tana kama hannunta.
Da sauri Baiwar Allah ta kalli cikinta tana zare ido ganin babu komai, tsaye ta miƙe a razane tana cewa
"Ina cikin da ke jikina???"
To ni ma dai jiran ta inda amsar za ta fito nake ku kasance tare da ni dan jin yadda za ta kaya.
MMN AFRAHðŸ˜ðŸ˜˜ðŸ¥°
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
💕ALAƘAR YARINTA💞
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
NA
MMN AFRAH
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .
Wannan littafi daga farkonsa har Æ™arshensa sadaukarwa ne ga aminiyar Æ™warai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar Æ™auna tsakaninmuâ¤ï¸
Page 4ï¸âƒ£4ï¸âƒ£&4ï¸âƒ£5ï¸âƒ£
*DUTSE*
*Hajiya Suwaida*
Zaune take a part ɗin Alhaji a falon ƙasa tana danna waya, zaman jiran fitowar mai gidan nata take saboda ba ta son hawa saman dan ta san yanzu zai sakko, dan magriba ta gabato ta san kwa dab yake da sakkowa ya tafi masallaci idan an kira sallah.Sanye yake da farar jallabiya da hula a kansa sai carbi baƙi mai ƙyalƙyali, a hankali yake sakkowa daga matattakalar benen sai da ya zo tsakiya kawai sai ya ja ya tsaya jin ƙafafun nasa na riƙewa kamar an ɗaure masa su da hanzari ya dafe ƙarfen da ke gefen matakalar dan har jiri da ya ji ya ɗaukesa kan sa na juyawa tamkar zai cire bai san lokacin da ya zaune a wurin ba tare da dafe kan nasa da ke sara masa yana ambaton Allah.
Hajiya Suwaida sai a lokacin hankalinta ya kai wajen dan bata ma san ya taho ba hankalinsa a kan wayarta tana karanta wasu saƙonni, ganin abin da ke fatuwa ta taso da saurinta ta nufoshi tana kiran sunansa dan ita gabaɗaya ta tsorata da yanayinsa.
"Lafiya dai Alhaji" Ta faÉ—a lokacin da ta zo wurin nasa hankalinta a tashe.
Bai ce da ita komai ba sai ƙara riƙe kan nasa yake, yana ta karanto addu'o'i ya jima a hakan zuwa can ya yi shiru kamar ruwa ya cinyeshi, Hajiya kwa sai bin sa da ido take hannayen nasa ya cire daga kan nasa sai kuma ya tsaya yana kallon Hajiya Suwaida kamar dai yau ya fara ganinta.
"Alhaji sannu ka dawo dai dai?" Ta jefa masa tambayar tana miƙewa tsaye daga sunkuyon da ta yi a kan sa.
Shiru ya yi bai yi magana ba, jim kaɗan sai ƙwaƙwalwarsa ta jefa masa wata tambaya.
"Ina Ruƙayya???"
A zabure ya tashi tsaye yana waige-waige kamar dai yana son ganjn wani.
"Alhaji mai kake dubawa ne" Hajiya Suwaida ta jefa masa tambayar cike da son jin amsar da zai bata.
"Ina Hajiya Ruƙayya?" Ta tsinkayi muryarsa a kunnuwanta ya jefo mata tambayar da ta sanyata rikicewa lokaci guda a maimakon ya bata amsar tambayarta.
Idanu ta zaro jin wata tambaya mai rikitarwa da rikita lissafi, tambayar da ta kaɗa mata hanjin cikinta tambayar da ta ruɗata tare d sanyata cikin wani zulumi marar misaltuwa saboda ita rabon da ta ji wannan sunan ma a bakin Alhajin sama da shekaru goma sha wani abu amma yau gashi da bakinsa cikin hayyacinsa yana ambaton sunan Hajiya Ruƙayya tare da neman inda take.
"Ina Afrah na ce miki amma kin tsaya kina wani abu da ban" Ya ƙara jefo mata tambayar da ta katse mata gabaɗaya saƙar zucin da take, tare da fara ƙoƙarin haɗo kalmomin da za ta bashi amsar tambayarsa saboda jin tambayar tasa cikin wani amon muryarsa wanda ya ɗauki shekaru aru-aru bai yi amfani da muryar ba.
"Ban...gan...ta...ba" Ta faÉ—a muryarta na karkarwa hakan ne ya sanya maganar daddatsewa ta fito a ciccire.
Wani kallo Alhajin ya mata kafin ya fara takawa cikin izza da sarauta da ta gama ratsa jijiyoyi da jinin jikinsa, da sauri Hajiya Suwaida ta sha gabansa duk da a mugun tsorace take tana cewa.
"Alhaji ina zaka je ne? Ba ka ganin yanzu nan kan ka ke maka ciwo"
Hannu ɗaya ya sanya ya maidata gefe guda, ya cigaba da sakkowa daga step ɗin yana gama sakkowa ya nufi ƙofar fita daga falon, Hajiya Suwaida cikin ruɗewa da fargaba ta biyo bayansa tana fatan Allah ya sa masallacinzai tafi duk da ta ji har lokacin ba a kira sallah ba.Cikin sanɗa take biye da shi tana son ta ga inda ya nufa, abin da ta gani ne ya sanya ta ji wata irin muguwar faɗuwar gaba wacce tafi wacce ta ji lokacin da ya ambaci sunan Ruƙayya (Afrah) ba komai ta hango ba wanda ya sa ta ji fitsari na bin ƙafafunta saboda ruɗewar da ta yi, Alhajin ba ko ina ya nufa ba illa part ɗin Hajiya Ruƙayya.
Bugun zuciyarta ne ya ƙaru gabaɗaya yawun bakinta ya ƙafe, hatta numfashinta kokawa suke da ita saboda tsananin ruɗewa.Part ɗin sa ya zama tamkar maƙabarta saboda yadda ya koma tamkar wata bola. Daker take iya ɗaga ƙafafunta tana bin bayansa shi kuwa tafiya yake cikin marari da son ya ga ya ƙarasa part ɗin masoyiyar tasa domin ya yi tozali da ita.
Tana zuwa dai dai wani ƙarfe da ke jikin wani bango hanyar da za ta sadaka da part ɗin Hajiya Ruƙayya ta kama ƙarfen ta tsaya saboda barazana da ƙafafun nata ke mata na kasa ɗaukarta da suke neman yi.Nan ta tsaya tana kallon yadda zaninta ya jiƙe da fitsari ta ma kasa sanin takamaiman tunanin da za ta yi bare har ta samu makamar abin yi, daga inda take tsaye tana hango shigar Alhajin part ɗin Hajiya Ruƙayya.