Sashe 5
Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Hakan ya sa ya koma ya shiga ta ƙofar baya wacce ake bi ta cikin kicin sa'arsa ɗaya ƙofar ba a kulle take ba amma a rufe take.Yana shigowa ya kunna fitilun sannan ya haura sama, ɗakin Iftihal ya fara zuwa ya buɗe ya kunna ƙwan ɗakin kwance take tana ta bacci abinta, tashinta ya yi sai kuma ya kira telephone na ɓangaren ƴan aiki, yace a turo masa Safiya ta zo sashen Hajiya Hauwa yanzu.Ba a ɗauki wani lokaci ba sai gata ta zo ya umarce ta data yiwa Iftihal ɗin shirin makaranta.
Yana fitowa ya nufi ɗakin Hajiya Hauwa a buɗe ya samu ƙofar bata sanya makulli ba, yana buɗe ƙofar ya kunna futilar ɗakin, sai bacci take gabaɗaya ta cika ɗakin da munshari filon da ta yi matashin kai dashi ya shiga bugawa amma ko gizau ba ta yi ba.Kallo yake ƙare mata da alama ma ko sallah ba ta tashi ta yi ba dan dama Hajiya Hauwa ibadar nan da sauƙi dan mace ce wacce bata damu da ibadah ba.
"Hajiya, Hajiya, Hajiya"Sai da ya kira ta sau uku tana ɗan bubbuga kafaɗarta sannan ta yi wata miƙa tana, tare da saurin sanya hannu ta make masa hannu dan bata ma san wa ke tashin ta ba.
"Wai ba da ke nake ba, kamar wacce ta suma ko kuma mai baccin mutuwa sai wani magagin bacci kike kamar wata yarinya" Cewar Abie a fusace dan gabaɗaya ransa a ɓace yake.
"Alhaji kai ne" Ta ce tana mai tashi zaune tare da sakin wata hamma ko bakin bata rufe ba.
"Ni ne mana kin zo kin kwanta kina ta faman bacci, babu sallah ba salati, sannan baki ji na ce yau Iftihal za ta je makaranta ba, amma maimakon ki tashi da wuri ki sanya a shiryata shi ne kika kwanta kina baccin asara sai ta makara ki ce ba za ta je makaranta ba"
"Wai yanzu Alhaji akan shirin zuwan Iftihal makaranta kake waÉ—an nan maganganun?"
"Ba dole na faɗa ba kina so ki koyawa yarinya ƙin makaranta tun tana ƙatamarta"
Baki ta taɓe ta fara jan jiki ta sakko daga kan gadon ta nufi hanyar bayi tare da cewa
"Koma dai makarantar neman lahira ce a barni in shiga bayi in fito in fara gaishe da ubangiji" Ta ce tana shigewa bayin ta banko ƙofar saboda ta tsani maganar zuwan Iftihal makaranta amma ta ga alama Alhaji ya kasa fahimta, dan gaka ma ta ƙudurta a ranta cewa sai ta ɗauki lokaci mai tsawo za ta fito daga bayi sannan ta san likaci ya ƙure dan bata da masaniyar Abie ya tashi Iftihal ɗin har ma ya sanya Safiya ta shiryata.
Kai Abie ya girgiza ya juya ya fito daga É—akin nata sai da ya bi ta É—akin Iftihal É—in ya ga har an mata wankan ana sanya mata uniform sai murna take yau za ta je makaranta.
"Abie har an kusa gama shirya ni sai in yi sallah, ba sai na ci abinci ba ma dan kar lokaci ya ƙure"Cewar Iftihal dan bata son yau wani abu ya hanata zuwa makaranta.
"Kar ki damu Iftihal har kya ci abincin ma dan da sauran lokaci yanzu 6:50"
"Toh Abie" Ta ce lokacin da Safiya ta gama sanya mata ƙaramin hijab domin ta yi sallah.Tana yin kabbara sai Abie ya cewa Safiya idan ta gama sallah ta kawo ta part ɗin sa domin ta yi break fast acan saboda ba ya so Hajiya Hauwa ta sanya su makara.Amsa masa ta yi ya juya ya sauka ya nufi part ɗinsa, lokacin kuku har ya fara jera wasu abubuwan na break fast akan dinnig ɗin.
Sama ya haura domin zuwa shi ma ya shirya sabida tafiya office.
Safiya ce goye da Iftihal sai ta rataya school back É—in Iftihal É—in a kafaÉ—arta suka taho part É—in Daddy, abin da take so ta zuba mata ta fara bata a baki.
Hajiya Hauwa ta daɗe a bayi sannan ta fito ta yi sallah ko azkar bata yi ba ta tashi ta naɗe dardumar sannan ta koma ta kwanta, sai da ta ga ƙarfe bakwai da arba'in sannan ta taso domin zuwa ta tashi Iftihal ta san dai yanzu kafin ta kira Safiya ra shirya yarinyar har ta ci abinci lokaci zai ƙure sai dai a haƙura da zuwa makarantar.
Tana zuwa ta tura ƙofar ta ga wayam babu kowa a ɗakin, kofar bayi ta buɗe shi ma ta ga Iftihal ɗin bata nan dan haka da mamaki fal a fuskarta ta fito daga ɗakin tana tunanimninda yarinyar take da sanyin safiyar nan.Ƙasan ta sauka nan ma bata nan, wayar ɓangaren ƴan aiki ta kira ta ce a turo mata Safiya domin ta je ta dubo ta a cikin gidan amma sai aka sanar da ita Safiyar ta fito domin amsa kiran Alhaji.A fusa ce ta kama hanyar part ɗin Alhajin tana fatan kar hasashen ta ya zama gaskiya tana zuwa kwa ta ga Iftihal riƙe da lunch box ɗin ta har direbanta ya zo za su tafi, Alhaji da Hajiya Azima kuma zaune a dinning area ɗin.
Wani ƙaton abu ne ya tokare mata maƙoshi har yaushe ne Alhaji zai fahimci cewa bata ƙaunar Iftihal take halartar makaranta tana da ƙuduri mai girma akan yarinyar amma bata ƙaunat yarinyar ta yi wano abi wai shi karatu.Tana ji tana gani hwkw Iftihal ta fice ita da Safiya za ta rakata wurin mota, Iftihal ɗin sai ɗagawa Hajiya Hauwa hannu take amma ko ta kulata har sai da kowa ya fahimci hakan, shi kwa Alhaji ko ta kan Hajiya Hauwa bai bi ba ita ma Hajiya Azima banza ta yi da ita dan ta ga abin nata ya zama hauka, ace ƴar ƙwaya ɗaya amma ana hana ta zuwa makaranta ita ko kunya ma Hajiya Hauwar bata ji.
Ganin kowa ya shareta yasa ta koma part ɗin ta ranta na suya tana yin wani ƙudirin akan lallai sai ta ƴara tashi tsaye dan ta ga abin na Alhaji ba ƙarami bane ita kwa ta sanya a ranta cewa sai dai su yi ta fafatawa.
_ALHAJI HAMZA_
Ɗan asalin garin kano ne a unguwar zoo road, iyayensa shi kaɗai suka haifa,suna kiransa da Hamzan sa, ya tashi a garin kano tare da mahaifansa anan ya yi karatunsa tun daga primary har zuwa zuwa digree ɗin sa.Iyayensa basu da wani arziƙi sai dai suna da rufin asiri, bayan ya kammala karatunsa bai samu aiki ba sai ya fara ɗan sana'a har dai daga bisani Allah ya sa ya samu aiki a wani kamfani garin Abuja, hakan yasa ya fara zuwa wajen aiki yana dawo wa a week end, tafiya ta yi tafiya har ya samu ya samu ɗan gida madaidaici ya siya ciki da falo sai banɗaki haka ya dawo da mahaifansa kusa dashi suke zaune tare.
Daga baya yana ƙara samun buɗi sosai domin Hamza ya kasance mutum mai gaskiya da riƙon amana hakan ya taimaka masa da wurin aikinsa suka riƙeshi da kyau sanadin gaskiyarsa, Har ake ƙara masa girma.Bayan ya sayi gida mai ɓangare biyu sai mahaifansa suka ce ya yi aure haka kuwa aka yi ya auri budurwarsa Azima ƴar garin Kano ce sun daɗe suna soyayya, da suka tare a sabon gidan su a ɓangare ɗaya iyayen Hamza ma a ɓangare ɗaya haka suke zaune lafiya dama Azima uarinya ce mai biyayya da kuma girmama na gaba hakan yasa zaman nasu yin ƙarƙo.
Wata rana da ta zame musu rana mafi muni a cikin tarihi shine hatsarin da iyayen Hamza suka yi daga Kano zuwa Abuja domin sun je sada zumunci wurin ƴan uwa da abokan arziƙi hakan ne ya yi sanadiyyar rasa rayukasu.Haka aka yi zaman makoki aka tashi sai dai mu ce Allah sa mu yi kyakkyawan ƙarshe amin.
Shekaru kusan bakwai kenan su Hamza Allah bai basu haihuwa ba, gashi a lokacin har ya je ƙasar India ya ƙaro karatu, ga buɗi na arziƙi ta ko ina amma kuma babu wani labari na haihuwa hakan yasa Azima ta ɗaga hankalinta amma shi Hamzan ke kwantar mata da hankali akan komai lokaci ne.Ya sake musu gida na gani na faɗa domin yanzu shi ma ya mallaki kamfano ni da dama sai dai ma wasu su ci abinci a ƙarƙashinsa.Yanzu ma yana aiki a ɗaya daga cikin kamfanonin sa kuma mutanen da ke tate da shi suna jin daɗin aiki da shi domin mutumin da ya san kima da darajar ɗan adam
Watarana ya je Kano ziyara ya dawo sai motarsa ta lalace a Suleja, hakan yasa ya rasa yadda zai yi, wani gida da yake kan hanyar inda motarsa ta lalace mai gidan ya bashi tarbarma sannan ya bashi abinci har dai bakaniken da ya masa gyara ya kammala, sosai Hamza ya ji daɗin karramawar da mutumin ya masa hakan yasa alaƙa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu duk da cewa mutumin ya haifi Hamzan amma haka suka ƙulla alaƙa mai kyau, har ta kai Hauwa ta ƙyalla ido ta ganshi hakan yasa ta ɗauki alwashin sai ta aureshi duk da kasancewar mahaifinta talaka amma dai bata da buri da ya wuce auren mai kuɗi, shi yasa da ta ga Hamza ce sai ta aureshi ko ta halin ƙaƙa, haka suka shiga suka fita ita da mahaifiyarta, sai da Hamza ya auri Hauwa.
Tun da ta tare a gidansa ta ga yadda yake ji da uwar gidansa hakan ya ƙara rura wutar kishi a ranta, ta ji duk duniya babu wacce ta tsana irin Azima haka ta sa a ranta ita ce za ta haifawa Hamza magaji dan ta zama tauraruwa kuma ta cusawa Azima haushi na rashin haihuwa.
Makkah kwa sai da ta je sannan hankalinta ya kwanta,dan ta tsani ta ji ana kiran Azima da Hajiya.