← Book details Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 28 OF 29

Sashe 28

Alakar Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Alhaji kwa na zuwa part ɗin tun daga waje ya fara ganin sauyi dangane da part ɗin, kamar dai babu alamar ana rayuwa a wurin.Cikin fargaba ya fara dosar ƙofar da za ta sadashi da falon farko da ke cikin part ɗin Hajiya Ruƙayya. Yadda ya ga ƙofar a rufe amma ba ruf ba ba a ƙarasa rufeta ba bare a yi tunanin an sanya mukulli, hannu ya sanya ya tura ƙofar amma ya ji ta ƙi buɗuwa alamu sun nuna ta daɗe a haka dan kamar ɓa ƙasa ta tokare bayan ƙofar. Sai da ya zage ƙarfinsa ya dinga tura ƙofar sannan ta buɗu, kallon falon yake da mamaki ganin irin tarin ƙurar da ke danƙare a falon hatta kayan kujerun da na kallon baka iya ganin komai sai ƙasa da ta baibayesu, kafet ɗin ma tamkar ƙasa ce a wurin dan ko alamarsa ba a gani, cikin ɗacin rai da fargaba ya sanya ƙafafunsa cikin falon hakanya shigo yana bin ko ina da kallo, ganin babu kowa sainkawai ya nufi upstairs da gudu ya hau faɗuwar gabansa na tsananta dan ba ya so ya je bai tarar da ita ba domin ba ya fatan hasashensa ya zama gaskiya, domin a iya tunaninsa ya kasa tuna rabon da ya sanya Ruƙayya a idanunsa, ya manta rabonsa da ita jiya ne ko kuwa yau ne?

Yana hawa ya shiga bubbuɗe ɗakunan amma gabaɗaya babu kowa a ciki yana fitowa daga ƙofar ƙarshe ya durƙushe a wurin cikin ƙurar nan ya dage ƙarfinsa ya ce

"Ruƙayya!!!" Gabaɗaya ɓangaren ya ɗauki amsa kuwwar muryarsa.

Amon muryarsa ne ya doki kunnen Hajiya Suwaida da ke riƙe gam da ƙarfe tana ganin kamar idan ta saki ƙarfen faɗuwa za ta yi.Saboda yadda take a tsorace, tana cikin wannan ruɗanin ta tsinkayo takun tafiyar Alhajin, tana ɗago kanta ta hangoshi a firgici ya nufota, idanu ta fara zazzarewa tana ganin kamar ya gano cewa da sanya hannunta, kamar dai ya san ita ce ummul aba isin faruwar komai, tabbas idan har hasashenta ya zama gaskiya to yana ƙarasowa shaƙeta zai yi har lahira.

"Ina kika kai min Ruƙayya???" Ya jefo ɓata tambayar tun kafin ya ƙaraso inda take ido ta ƙwara masa tana hango tsantsar tashin hankali a tare da shi da alama ma baya cikin hayyacinsa.

MMN AFRAH😍🥰😘

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA

MMN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .

Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️

Page 4️⃣&6️⃣4️⃣7️⃣

*GIDAN HAKIMI ÆŠAN BURAN*

Hajiya Sakina ce tsaye a dining area tana jera kayan abincin dare, ta gama jerawa tsaf tana É—an goge kujerun dining É—in, Mai gidan nata ne shi da Hafiz suka shigo cikin shirinsu na zuwa masallaci dan har an fara kiran sallah ma a wasu masallatan.

"Ammi wai har abincin ya kammala" Cewar Hafiz yana dariya.

"To acici ka dai bari ai ku dawo daga masallacin dai ko, kai ne sarkin ci" Ammi ta ce tana kallonsu da murmushi.

"Barshi ya ci ai dan shi nake nemowa" Abban nasa ya faÉ—a cikin barkwanci.

"Yawwa Abba ci dama ai ba laifi bane" Hafiz ya ce yana kallon Ammi.

"Wato ma dan shi kake nemowa" Ammi ta ce tana kafe mai gidan nata da idanu.

"Har da ke mana" Ya faÉ—a yana dariya ganin yadda ta yi dan ya ce dan Hafiz yake nemowa.

"Ka ce fa, ai da dan shi kaÉ—ai kake nemowa ni ma sai in daina dafa muku abincin in ga ko kwa ci abincin É—anye"

"Dafa abinci aiki ne dama" Ya faÉ—a ckn sigar zolaya.

" Ba aiki bane bacci ne, shi yasa ma na ga baka iya cin abincin masu aiki"

"To gaki mai zanyi da abinci wasu masu aiki, ai zaƙin hannunki kaɗai bai barin mutum ya ji ɗanɗanon abincin kowa sai...

Kafin ya kai ƙarshen maganar sai kawai suka ga fuskarsa ta sauya, yana yatsina fuska sai kuma suka ga ya dafe kansa.

Da sauri Ammi da Hafiz suka nufoshi, kafin su ƙaraso har ya durƙushe a wurin Hafi ma na zuwa sai kawai ya yanke jiki ya faɗai, wani ƙara Ammi ta fasa ganin su duka biyun sun shiga wani yanayi marar kyan gani dan a take ta fara tuniwa da yanayin da suka shiga lokacin naɗin da suka je a fadar Sarki da aka maido mata da su basa hayyacinsu.Ai ita ma bata gama tantancewa ba sai jin kan ta ta yi yana juyawa take ita ma ta kwance a wurin.

Ƙaran da ta saki shi ne ya janyo hankalin ƴar aikinta da direban gidan da wani mai ban ruwan fulawa, dan koea ya ji ƙaran ya san ba na lafiya bane. A kusan tare suka shigo dan dama ɗabi'ar gidan ce masu aikin gidan tamkar ƴan gidan haka suke.Sun same su kowa dafe da kai sai dai kowa da abin da ke fitoww daga abakinsa na addu'a da ambaton sunayen Allah, wannan yanayi da suka samesu ya ɗaga musu hankali dan haka suke ta ƙoƙarin yadda za su tafi da su asibiti amma kuma ba a ɗau wani lokaci mai tsawo ba suka dawo hayyacinsu sai dai su duka daga farfaɗowarsu mutum ɗaya suke ambato wato Ruƙayya..

Daker Abban ya umarcisu da su gabatar da sallah kafin su tafi gidan Ruƙayyar dan su duka sun zaƙu su ganta dan sun kasa gane ko tuna rabon da su ganta, dan ko a waya basa son kiranta ita kawai suke son gani.Bayan sun idar da sallar dan a gida suka yi Abban ya ja su dan an fito daga masallaci lkcn, haka suka ɗunguma direba yana jan motar Hafiz a gaba Ammi da Abban a baya.

Abba sai cewa direban yake ya yi sauri domin ganin ɗiyar tasa yake son yi ji yake kamar ya fi su Ammi da Hafiz ɗin son ganinta ma.Suna zuwa direban ya yi horn mai gadi da hankalinsa ke kan radio yana saurara ya ajiyeta a kan bencin nasa da sauri ya leƙa ganin motar gidan sirikin mai gidansa ya wangale musu get ɗin suka shigo yana ɗaga musu hannu.Ko gama parking direban bai yi ba suka fara buɗewa suna fitowa kowa hankalinsa na ga son ganinta.

Hanyar part ɗinta suka nufa su duka, suna tahowa suka fara jiyo hayaniyar mai gidan yana ta amboton ina Ruƙayya.Mamaki da al'ajabi ne suka cika su jin su ma ita auka zo nema amma gashi nan shi ma yana nemanta to ina take? Kowa ya jefawa kansa tambayar a zuciyarsa.Tun kan su ƙaraso suka ashe da shi da matarsa Hajiya Suwaida ne, gabaɗaya fuskokinsu cike da tarin tambayoyi ganinsu yasa Alhaji Sagiru ya nufosu tun kan su ƙaraso yana tambayarsu ina Afrah???

"Mu ma wurinta maka zo" Abba ya faÉ—a yana kallon Alhaji sagirun.Dan dama abokai suke shi ne ya auri É—iyarsa dan zumuncinsu ya cigaba da É—orewa.

"Ni da ina zan san inda take da zai sanyani a gaba yana cewa sai na nemota" Hajiya Suwaida da ee ta faman share hawaye take faɗa, dan zuciyarta kamar ta faso ƙirjinta ta fito saboda baƙinciki dan ita kukan daowarsu hayyacinsu take dan ganin dangin Ruƙayyar suna nemanta ya ƙara tabbatar mata da karyewar asirin, gashi so take ta keɓe ta yi waya dan ta kamata a ce ta fara shirin ɗaukan mataki tun kafin Ruƙayyar ta bayyana dan ta san ita ma duka inda take in har tana raye to ta dawo hayyacinta, gwara tun kafin ta jiƙa mata aiki ta sanya a ƙara matar da su kan su, su duka a ƙara nisanta tsakaninsu idan ma ta kama a kashe Ruƙayyar gabaɗaya.

"Wai dama bata nan ne" Ammi ta jefa wa Hajiya Suwaida tambayar.

"Da safe fa ta fita unguwa shi ne fa har yanzu bata dawo ba, ni kaina bansan ina ta tafi ba" Hajiya Suwaida ta faÉ—a cikin kissa da kisisina.

Shiru kowa ya yi, Hafiz kwa sai hararar Hajiya Suwaida yake dan ya san bata ƙaunar ƴar uwarsa ko kaɗan dama bai zama lallai kishiya ta ƙaunaci kishiyarta ba kuma ma ba kowace mace ba ce za ta ce tana ƙaunar kishiya sai dai ana samun masu zama da kishiya tsakani da Allah ba cuta ba cutarwa sai dai ita Hajiya Suwaida tsanarta da ban take ƙiri-ƙiri take nuna tsanarta a fili dan ba zai manta ba duk da ba wani wayo ne da shi ba amma kuma tabbas ya san lokacin da take nunawa ƴar uwarsa tsana a fili har da shi ma idan ya zo wajen Aunty Afrah.

"Ya aka yi kika san unguwa za ta je?" Hafiz ya jefa mata tambayar.

Idanun mutanen ta faka ta jefa masa harara kafin ta bashi ams da cewa.

"Na dai hangota ne za ta fita"

"Amma yanayin yadda na ga part ɗinta babu alamar akwai wata halitta da ta rayu a yau a cikinsa dan ko a shekaru bana jin ɗan adam ya shig sashen , dan haka ya akayi bansan bata nan ba? Ya aka yi kuma kika ce yau ta fita da safe? Shin mai kike ɓoyewa dan nasan kin san komai dan haka ki faɗa min gaskiyar ina take, tunda iyayenta ma ba su san inda take ba, da alama su ma a yau suka nemi inda take kamar yadda ni ma a yau na nemeta, ki faɗi gaskiya idan ba haka ba kuwa in har na gano gaskiya na gane da sa hannunki sai na ɗaureki har igiya ta yi saura" Cewar Alhaji Sagiru yana nunata da yatsa.

"Billahillazi huwar rahmanu bansan komai ba, wato ni kamar bani da kowa shi ne za a ce da sanya hannu na a ciki" Ta faÉ—a tana fashewa da kukan makirci.

Ammi kwa sai share hawaye take jin wai sashen Rauƙayyar ma babu alamar ana rayuwa a ciki, kenan ƴarta ta ɓata ta yi ko kuma mutuwa ta yi ko kuma kasheta aka yi.
Chapter 28 · 0% Book details