← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 96

Sashe 92

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Assalamu Alaikum, Ummi Ni ce feefah mai kyau, please kai tsaye maganar dama ita ce ki daure kiyi tunani akan Yaya mah'fuz ɗina, domin kuwa ƙaunar ki yake yi da gaskiya, shiyasa ma kika ga Yana miki wannan kallon ɗazun nan, please karki masa wani mummunar fahimta domin kuwa Yaya mah'fuz mutumin kirki ne shi, zai riƙe da amana Bayan Aure, saboda Haka ki daure kiyi tunani kafin nanda two days zamu dawo daga kano State, sai ki faɗamin abin da kika yanke, kinga ae sai ah haɗa bikin naku kawai dana Yaya Maleek shida Husnee.
Idan kina buƙatar lambar wayansa ba saikin nemeni ba, domin kuwa ga lambar nan ta ƙasa. Good Luck, Feefah Mai Kyau ce. Bye bye."😇

Ta karanta wannan message yafi sau goma, tana ƙarawa da dai ta gaji ne, ta tsaya dan kanta.

Murmushi tayi sannan a fili take faÉ—in "Afeefah ke nan Æ´ar Gidan Babanta. Yanzu haka ake rubuto kalaman huÉ—ubar saurayi a garin ku Abuja?. Wannan saiki saka naji ya gundureni fa."

Murmushin ta kuma saki tuno drama ɗin ta dashi na Safe, a lokacin sai da Auntie Yusra matar uncle Yusuf da ta ƙariso wurin ta tarar da abin da ke faruwa, ta saka Baki sannan ya haqura Yaci abincin.

"Ikon Allah shi kuma irin na shi salon ƙaunar ke nan?, amma fah hakan ya tafi da Ummu Sulaym highly highly, ae Afeefah Mai Kyau, karki damu ranki, domin kuwa tuni mah'fuz Ya yi nisa cikin heart na Ummu Sulaym tun kallon Farko Ya sace heart ɗina." 👩‍❤️‍👨💃

*KANO STATE*

Misalin ƙarfe 2:00 na rana Jirgin su Ya yi Landing a babban Filin Saukar Jirgin sama na garin Kano.

Aikuwa batare da da ɓata lokaci ba, gaba ɗaya suka shishshiga motocin Gidan Uncle Sagir, da Yazo ɗaukarsu shida kansa.
Nan suka Bar Filin Saukar Jirgin suka nufi Katafaren Gidan Uncle Sagir dake nan New Life Kano State.

Da Isar su Katafaren Gidan na Uncle Sagir Sameer Lamiɗo. Nan securities da Suke tsaron ƙaton wagameman gate na gidan Suka buɗe musu gate ɗin cikin sauri.

A Jere sannan kuma a tare tsadaddun motocin guda Bakwai suka yi parking a wangameman Filin ajiye motoci dake Katafaren Gidan.

Sannan gaba ɗaya Suka fiffito a tare, to da yake tare da matar Gidan Suke shiyasa basu tsaya ɓata Lokaci ba.

Gaba ɗaya suka nufa cikin Ainihin Gidan, da Shigar su Katafaren daular duniya ƙaton palon Gidan Uncle Sagir. Wanda yasha ya gaji da shan kayan Mo re Rayuwa Ba'a magana, gaba ɗayan su zama su kayi saman Royal sofa's da aka ƙawata ƙaton palon dasu.

Yayin da mutanen gaba ɗaya waɗanda akazo dasu tun daga kan Mah'eesha, Haseeya, da kuma mahaifiyar su Auntie Suwaiba suka shiga kitchen domin Bawa masu aiki umarnin haɗa lunch Wanda Baƙi zasu ci. Yayinda mah'fuz shi da Yasir ɗan Uncle Yusuf kuwa ko tsayawa a Palon basu yi ba. Kai tsaye ɓangaren mazan Gidan suka wuce domin sauke gajiya.😘

Shima dai Uncle Yusuf da shigowar sa Gidan tuni ɓangaren da Amma wato Hajiya Raheemah take ya nufa tare da Uncle Sagir domin gaisheta da kuma duba lafiyar ta.

Sai ya kasance gaba É—aya mutanen palon su Afeefah ne da kuma yaran Uncle Yusuf ma ta sai kuma Auntie Yusra matar sa da tabi Auntie Suwaiba kitchen domin tayata wasu ayyukan.

Tunda suka shigo wannan Katafaren Gidan har ƙuka ƙariso palon Suka zazzauna Deejarh tana maƙale da Afeefah. Yayin da take ƙarewa ƙaton palon wanda komai Ya yi zam zam domin kuwa ba ƙaramin kuɗaɗe aka zuba ba, sai dai kuma ita haryanzu bai kai kyan Gidan Mister mai kyau ba, mahaifin su Afeefah ba a wurinta, domin kuwa shi wannan Gidan part's part's ne da yawa gare shi. Tundaga kan na yara ma ta da kuma na maza sai kuma na Amma sai kuma na Uncle Sagir sai wannan wanda Suke ciki da ya kasance na Auntie Suwaiba matar Uncle Sagir.
Yayin da shi kuma Gidan su Afeefah a haÉ—e ginin yake kuma a tsare yake.

Kallon Afeefah Deejarh tayi sannan ta raÉ—a Mata magana a kunne Muryar ta rawa.

Da sauri Afeefah ta kalle ta, amma bata ce komai ba, ita kuma Deejarh ta Ma ta alama da ido, wai zata fita, miƙefwa Afeefah tayi sannan ta kamo hannun Deejarh suka bar palon.

Sai da suka fita daga palon sannan Afeefah ta saki hannun Deejarh da ta riƙe, kallon ta tayi tana faɗin

"Da gaske kike yi wai?."

Tayi maganar tana ƙarewa Deejarh ɗin kallo, ko zataga alama.
Rau Rau Deejarh tayi da idanunta kamar zatayi kuka ta ce

"Allah Balarabiyar India haka kawai naji jikina kamar Ruwa yana tsiyaya. Nifa tsoro nake ji ƙilama saboda nahau Jirgine, shiyasa nake zubar da jini ta da yawa kuma."

Ta ƙarishe maganar tana shirin fashewa da kuka.

Ganin Haka yasa Afeefah ta kamo hannunta sannan suka nufa wani ɓangare daban ba wanda suka fito daga ciki ba.

Kwankwasa ƙofar palon da suka tsaya gaban sa, Afeefah tayi sannan kuma har lokacin hannunta yana cikin na Deejarh wacca gaba ɗaya ta gama tsurewa, saboda tsoron wani Abu kamar Ruwa da take ji yana ma ta Yawo a jiki. 😲

Wata kyakyawar Budurwa ce ta buɗe musu ƙofar palon, jikin ta sanye da kayan bacci, da alama daga Baccin ta farka.
Ganin Afeefah tsaye yasa budurwar sakin ihun murna sannan ta ƙarisa da sauri ta Rungumo Afeefah tana faɗin

"Feefah mai kyau kece, Yaushe ku ka zo, ah ah ina su Haseeya da Mah'eesha ɗin ne, waima ya ya banji ƙarar shigowar motocin ku ba, saida fah na faɗa wa Dad idan zai tafi Airport ɗauko ku yayi min magana shi ne yaƙi ko?."

Budurwar ta ƙarishe maganar cike da Rashin jindaɗin ɗaukosu Afeefah da bata sama Damar yi ba.

"Oh My Auntie Hameeda zaki ɓallani fah."

Afeefah tayi maganar cikin murmushi, ita ma Hameeda murmushi tayi sannan ta saki Afeefah daga Rungumar da tayi ma ta tana kallon Deejarh, cikin murmushi ta ce

"Feefah wannan kyakyawar fa, daga ina kuka samo ta?."

"Wai Deejarh bari zan faÉ—a miki, yanzu dai Bari mu shiga ciki."

Afeefah tayi maganar tana kamo hannun Deejarh Sannan suka yi cikin palon.

Ita ma Hameeda ta mara musu baya, a tsakiyar palon suka tsaya.

Cire mayafin kanta Afeefah tayi sannan ta a je saman sofa, kallon Hameeda tayi tana cewa

"Please Auntie Hameeda Bari muyi amfani da bathroom na bedroom É—in ki Abin is urgently."

"Okay babu damuwa ku Shiga ciki."

Hameeda ta bata amsa sannan Afeefah da Deejarh suka nufa wani bedroom dake cikin palon. Yayin da ita kuma Hameeda ta zauna saman 2sieter.

Suna Shiga bedroom ɗin sai da Afeefah ta mayar da ƙofar ta rufe, sannan ta juyo tana kallon Deejarh kana ta ce

"Oya cire doguwar gown dake jikin ki mu gani."

Da sauri Deejarh ta kalla Afeefah cikin mamaki ta ce

"Balarabiyar India in cire riga na fa kika ce, mai zakimin?."

"Oh Deejarh ina nufin ki cire muga jinin da kike zubar ne fa."

Cewar Afeefah.

Ae jin Afeefah ta ambaci jini kawai sai Deejarh ta fashe da kuka faÉ—i take
"Shikenan zan haihu, waiyo gwaggo na ki taimake ni zan haihu, daga zuwa Birni na shiga ukuna ni Deeje."

Ganin zata tara ma ta jama'a ne yasa Afeefah saurin kamota kai tsaye ta shiga bathroom da ita. Yayin da har zuwa lokacin Deejarh bata yi shiru ba.

"Ke deejarth kiyi shiru kiji abin da zan faÉ—a miki mana, kina kuka taya zakiji please my Deejarh wiping your tears okay."

Hannu takai ta sha re hawayen sannan tac e nayi.

Murmushi Afeefah tayi sannan ta ce ''Yauwa ina ce dai kin san wannan abun da ma ta suke yi duk ƙarshen wata ko?."

"A'a bansan shi ba. Menene shi haka?."

Deejarh ta tambaya. Afeefah ta bata amsa da cewa

"Wannan abun fah wanda idan mace takai shekaru goma sha huɗu ko fi ye da Haka ko kuma ƙasa da Hakan. Idan ta fara yi sai ace ta girma, wai bakisan shi ba?."

Da sauri Deejarh ta ce

"Nasan shi mana shi ne ma wanda Deluwa ta taɓayi a kasuwan garin mu, mutane suna ta kallon ta."

"Okay to shi ne fah yazo miki yanzu ae baki gane ba."

Afeefah ta faÉ—a hakan da son fahimtar da ita.

Zaro ido Deejarh tayi cike da tashin Hankali ta buÉ—e Baki ta ce

"Lah Balarabiyar India.!"

Shiru tayi tana zare ido domin kuwa bata san abin da zata ce ba.

Murmushi Afeefah tayi sannan ta ce "Yanzu dai kin fahimci komai ko?."

Da sauri Deejarh ta girgiza kai alamar e,

"Yauwa yanzu bari na fita na barki kiyi abin da zaki iya."

Afeefah tayi maganar sannan ta buɗe ƙofar bathroom ɗin ta fita.

Ganin haka yasa Deejarh cikin sauri sauri ta cire doguwar gown na atamfa dake jikin ta sannan tayi hanging nata Jikin ƙarfen shower curtain, sannan ta wanke duka inda jinin ya ɓata ta sannan tayi wanka gaba ɗaya bayan tayi na tsarki.

Knocking ɗin ƙofar bathroom ɗin da taji ana yi ne yasa tayi saurin ɗaukar orange towel dake saman bathtub ta ɗaura, sannan ta ƙarisa ta buɗe ƙofar Afeefah ce tsaye hannunta riqe da sanitary pads.

Miƙa ma ta tayi "Ga wannan ki saka ina fatan kinyi wankan tsarki?."

"Eh Nayi, amma Balarabiyar India a'ina kika sama wannan abin?."

"Oh wannan Hameeda ce ta bani ae, akwai matsala ne?."

Zaro ido Deejarh tayi tana furta "Shikenan kuma tasani ko?."🥺

Wata dariya ce ta kusa kwace wa Afeefah ganin yadda Deejarh ta zaro ido tana tambaya, danne wa tayi sannan ta bata amsa da faÉ—in

"Deejarh ni banma san abin da zan faÉ—a miki ba, ga wannan kawai."

Tayi maganar tana miƙa ma ta sanitary pad ɗin.

Karɓa tayi, har Afeefah ta juya zata fita, sai kuma ta juyo kallon ta tayi sannan ta ce
"Rigar ta ɓaci ne?."

Da sauri Deejarh ta ce "A'a bata ɓaci ba, amma dai dogon wandon ya ɓaci sosai, da kuma pant ɗin."

"Okay to a cikin wannan ledar na hannun ki akwai pant sai kiyi amfani dashi, sannan kuma idan kin fito."

Ta nuna ma ta wardrobe sannan ta ci gaba da cewa

"Ki buÉ—e ki É—auki leggings wanda zai miki ki saka, kinji ko?."
Chapter 92 · 0% Book details