Sashe 39
Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani kalar zallar kyau ne a bedroom É—in, na nunawa a television tundaga kan fenti na É—akin da yake ruwan grey, shikanshi wall na É—akin ba'a ganin shi, an rufe shi da wasu haÉ—aÉ—É—un glass grey color, ga wasu frames na Jiddarh guda biyar da aka jere a jikin bangon.
Tayi kyau a hoton sosai, dama kuma itaɗin mai kyau ce, daga ɗayan gefe na bangon kuwa, wata ƴar ma daidaiciyar plasma tv ne, mai kyau da ita, gefe da wasu dogayen glass vases masu ɗauke da flowers kala kala, masu fidda wani ƙamshi na musamman.
Daga can gefen bangon kuma mirror ne, na dogon yaro wanda yake manne da Wall É—in.
Gefen bangon kuwa shima wasu frames ne, wasu É—auke da hoton Jiddarh ita da Humaira a cikin qanqara da alama ba'a Nigeria sukayi hoton ba, yayinda wasu kuma hotunane masu kyau.
Kallonta ta mayar a tsakiyar madaidaicin palon wanda aka kashe naira wajen tsara shi, kujerune set É—aya suma grey nd milk color, yayinda sofa's É—in suke grey color, su kuma cushions É—in suke milk nd grey colors, haka zalika suma curtains na É—akin grey nd milk color ne, hatta da Droplight na É—akin hasken grey nd milk color suke bayar wa.
Ga kuma wasu kyawawan wind chime masu bada iska suma still grey nd milk color.
Kamar ance ta kalla can gefe aikuwa ta hango wasu haÉ—aÉ—É—un stools, na zama grey color masu faÉ—i an jeresu, guda huÉ—u tsakiya ga kuma wani Glass coffee table daga tsakiyar stools É—in.
Daga saman wani madaidaicin table kuwa 'FISH TANK' ne ga wasu ƙanana kyawawan kifaye ciki, ruwan cikin kuwa yana bada launin sky blue ne.
Ni'ima batasan lokacin da ta koma ta zauna saman 1sieter ba, saboda kaÉ—uwar da tayi, da ganin palon Jiddarh.
Yes tasan mahaifin ta cikaken mai dukiya ne, wanda ba iya Nigeria kaɗai sunanshi ya zagaya ba, hadda ma ƙasashen waje, amma ita tunda take a rayuwar ta, bata taɓa ganin palon da ya tafi da imanin ta ba, irin palon Jiddarh, ya haɗu ƙarshe, idan akace haɗuwa to azo palon Jiddarh kawai magana ta ƙare🤗.
Tanan a zaune tana kuma bin ko'ina na palon da kallo gabaɗaya ta manta abin da ya kawota ɗakin, saboda tsananin kyan palon da ya kasheta, da sauran ranta a duniya😅
Jiddarh ta yaye wani curtains dake a can gefe, ta fito hannunta riƙe da mug na coffee sai faman steam yakeyi, tun lokacin da Jiddarh ta buɗewa Ni'imar ƙofa ta shiga wani ɗan korido da aka rufeshi da curtains, kai ba za ka taɓa cewa da wani abu a gurin ba, ashe wani ɗan ƙaramin kitchen ne, na dafa shayi a gurin.
Da sauri Ni'ima ta miƙe tsaye tana bin Jiddarh da kallo kamar na tsoro, bata jira komai taje ta yaye labulayen da taga Jiddarh ta fito ta ciki, sai kuma ta tsaya cak, wani mamakin yana kuma kamata wai still dai ga wani abun mamakin kuma, kitchen ne a palon daga ke ɓantaccen guri.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma ta zauna tana kallon Jiddarh ɗan murmushin yaƙe tayi ta ce "ina fatan dai ban takura miki ba?."
Jiddarh ta girgiza kai alamar a'a sannan ta bata amsa da "ko ɗaya dama bacci nakeji kuma yaƙi zuwa...Sai kuma gaki, af ga coffee fa, kar yayi sanyi, miƙa ma ta tayi, Ni'ima ta karɓa yawunta har wani tsinkewa yakeyi, batasan lokacin da ta lumshe ido ba, sanda takai coffee ɗin a baki cikin ƙanƙanin lokaci, sai ga Jiddarh da Ni'ima sun ware suna zuba fira, dama Jiddarh gata gwanar surutu.
Ni'ima ta ce "nifa rigar da kika É—inka ne, nazo gani kinsan lokacin da kika fito da ita, kika nunawa su Humaira bana gidan."
Jiddarh tayi murmushi tana amsa ma ta da "ai ba damuwa tana bedroom É—i na, zoki ganta mana."
Miƙewa sukayi tare suka nufi wannan mirror na dogon yaro dake cikin bedroom ɗin, wani waje Jiddarh ta danna a jiki saiga ƙofa ta bayyana, shi kuma mirror ya matsa gefe, ita dai Ni'ima sai zare ido take tana kuma kallon ikon Allah, "wato abin mamaki baya ƙarewa a duniya, yanzu wazayyi tunanin akwai wata ƙofa anan, balle kuma har a shiga bedroom ta gurin." Ni'ima take faɗan hakan a ranta.
Shiga ciki sukayi Jiddarh a gaba, Ni'ima kuma tana binta a baya.
"oh Allah yau dai, bazan gaji da ganin abin mamaki ba ashe," Ni'ima ta kuma faÉ—a a zuciyarta ganin tsantsan kyau da tsari da kuma burgewa na bedroom É—in Jiddarh ashe ma ba komai ta gani a palo ba, a nan bedroom kallo yake.
Wani haÉ—aÉ—É—en glass sif dake manne a bango, taga Jiddarh ta buÉ—e ta ciro wata haÉ—aÉ—É—iyar riga ta shimfiÉ—e ta saman mattress.
Da sauri Ni'ima ta ƙarisa tana bin rigar da kallo kamar idanunta zasu zubo ƙasa, gabaɗaya kyan rigar ya tafi da ita, don ji take kamar ta ɗauki rigar ta ruga a guje, amma ina ba damar haka, akalla takai mintuna talatin tanabin ko'ina da ina na rigar da kallo.
Kallon Jiddarh tayi bakinta na rawa wajen faɗin "Jiddarh dan Allah na roƙeki ki faɗamin a wani company kika siya wannan special princely gown ɗin, wallahi tamin zan siya ko million nawa ne, koda kuwa companyn ba'a nan ƙasar yake ba🤩."
Dariya Jiddarh tayi ta bata amsa da "haba sister Beauty matar yaya H to be, ki kwantar da hankalin ki ba'a company na siya ba, ni ce É—inka abina da kaina."
Waro ido Ni'ima tayi waje, ba shiri ta miƙe tana kallon Jiddarh cike da zaƙuwa take cewa.
"wai dan Allah da gaske, ke ce kika haÉ—a wannan, ko wasa kike."
Tambaya tana nuna rigar, murmushi Jiddarh kawai tayi ta bata amsa "of course ni ce na É—in ka, amma nakai a kalla watanni bakwai ina É—in kawa idan ban manta ba."
Ni'ima ta ce "a gaskiya Jiddarh bazan ɓoye miki ba, kinyi ƙoƙari sosai sosai, wannan zamanin dai, banga telan dazai tsaya ya ɓata lokaci har watanni bakwai domin ɗinka riga ɗaya ba, koda yake ba abin mamaki bane, tunda ɗinkin, ke zaki saka abinki."
Jiddarh tayi murmushi ta ce "haba, baki dai binkcika bane, amma ai ko telolin kowa da halin shi, ai baza'a taru a zama ɗaya ba, dole akwai na gari masu ƙoƙarin cika alkawari."
"E, wata ƙila baza'a rasa ba, amma wai meyasa bakya ɗinkin mutane ne, zafa ki sama kuɗaɗe sosai."
Dariya Jiddarh tayi sannan cikin nutsuwa ta ƙarisa wajen labule ta yaye curtains, ashe nan ma gabaɗaya wall ɗin gurin, glass ne.
Sai ga babban titin birnin Kano ya bayyana, kana ta juyo tana kallon Ni'ima da ta kuma sakin baki tana kallon ikon Allah, wato titi kuma yanzu, abin yayi fa, ba laifi tunda glass É—in irin wanda mutumin da yake waje bazai hango komai bane, sai dai na ciki ya hango na waje.
Kafin Jiddarh ta ce wani abu, Ni'ima ta rigata da faÉ—in, "indai zaki dinga yi ni kuma zan dinga nemo miki customers kala kala, har saikin gaji dasu kedai kawai kice kin amince,"
Murmushi kawai Jiddarh tayi Ni'ima ta tono ma ta gurin dayake ma ta raÉ—aÉ—i, ita batasan menene matsalar ta ba, a baya can, ta fara É—inki mutane suna kawo ma ta tanayi abu kamar wasa har sunanta ya fara zagaye gari qwararriyar tela lamba É—aya a cewar mutane, saikuma batasan meya faru ba aka wari gari ko mutum É—aya an dena kawo ma ta É—inki haka kawai.
Ajiyar zuciya ta sauke tana mai amsawa da "shikenan ba damuwa zaki iya,"
Wani tsallen murna Ni'ima tayi kamar wacca aka ma ta bishara da aljanna, da sauri ta matso ta rungumo Jiddarh tana faÉ—in.
"nagode sosai Jiddarh thank you so much."
"Never mind, haba Aunty Beauty wannan godiya haka, ni zaki ɓallani fa."
Dariya Ni'imar tayi tana faɗin, "ai dole, yanzu kafin a samu tela irinki a wannan zamanin ai sai an tona😉
Jiddarh ta ce "to ai sai a tona ina ga za'a samu,"
Ni'ima ta ce "gaki ma ansamo, da aka tona ɗin😀
Dariya sukayi duka nan Ni'ima ta taimakawa Jiddarh sukayi fold ɗin rigar, sannan suka mayar sif, cikin ƙanƙanin lokaci saiga su suna fira kamar dama can sunsan juna.
Ita dai Jiddarh tana mamakin Ni'ima ashe ta iya surutu haka?, to meyasa da batayi, 'oho' taba kanta amsa.
ᴡᴀsʜᴇ ɢᴀʀɪ
Kamar kullum alarm clock dake a saman locker, a gefen bed É—in ne, ya tasheta.
A hankali take buɗe dara daran kyawawan idanunta, tana mai furta addu'ar tashi daga bacci, yaye tattausar blanket ɗin da ta lulluɓa tayi sannan ta sauko daga saman mattress ɗin, tana miƙa hannu ta ɗauki ribbons da hularta dake can gefen mattress.
Saida ta tufke dogon gashinta da ribbons É—in sannan ta saka hular ta shiga bathroom.
Wanka tayi haÉ—e alwala ta fito a gurguje ta saka doguwar riga da hijjab dogo sannan ta shimfiÉ—a sallaya a gurin da aka tanadar domin yin sallah.
Raka'atainul fajir ta farayi raka'a biyu, sannan ta jira aka kira sallan asuba, kana ta miƙe tayi, Bayan ta idar, bata miƙe daga saman sallayan ba, har sai da tayi azkhar bayan ta kammala tayi folded sallayar ta mayar ma'ajiyar ta.
Shiryawa tayi cikin wando three Quarter white color, da riga t-shirt mai garejen hannu fara, sai hula p-cap fara, sannan ta saka safa doguwa har gwiwarta ita ma fara, earpiece ta ɗauka shima fari ta maƙala a kunenta duka biyun, tayi connecting ɗinshi da wayarta, sannan ta saka wayar a trouser pocket ɗinta.
ÆŠauko takalman ta trainers farare a hannayenta tayi, ta fito palon É—akinta Club ta É—auka /wato sandar wasar golf/.
*💋💋ʂαɾαυɳιყαɾ ƙყαυ💋💋*
*ÆšÔ‹Ò½ É Ê…Î±É± ϙυҽҽɳ*
*☆ʂƚσɾყ & É¯É¾Î¹ÆšÎ¹É³É á‚¦áƒ§â˜†*
*~ƙԋαԃҽҽÊαɾƚԋ. ʂαႦι'Ï…. ყαԋყαԋ🤙~*
{ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ}😇
*page 35&36*
Palon sama ta fito ba kowa, dama ba tayi tunanin ganin kowa ba, tunda safe ne yanzu.
Cikin sauri take taka staircases ɗin harta sauko palon ƙasa Ajiyar zuciya ta sauke, hango Humaira da tayi tsakiyar palon ita ma cikin shigar wasan golf irinna ta.
"Good morning Humaira, hope kintashi lafiya?."