← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 96

Sashe 68

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru tayi bata bashi amsa ba, sai ma Tamke fuska da tayi, tuno maganar kishiya.
Murmushi ya yi

"Good ke nan dai har yanzu fushi ake da ni ko?."

"A'ina kaji na faÉ—a hakan?."

Yanzu mana shin zaki iya faÉ—a mana Abin da kikayi ke kaÉ—ai a bedroom kuwa?."

Taji ya kuma antayo ma ta tambaya.
Kallon sa tayi har lokacin fuska a tamke sannan ta ce

"Aljanuna ne suka taso."

Kofin shayi mai zafi da yake ƙoƙarin kaiwa baki ne ya kusa suɓucewa daga hannun sa jin abin da take faɗa, da sauri ya a je tea cup ɗin a gefe sannan ya juyo da kyau yana kallon ta kamar yadda ita ma take kallon sa.

"Me kikace aljanu kuma, to me suka ce da suka zo?."

Ya tambaya yana murmushin tura haushi.

Aikuwa ta shaƙa, gyara zama tayi sannan ta ce

"Cewa su kayi karkayi wannan Auren da kake shirin yi idan kuma ba haka ba Tom tabbas za'aji a jiki...."

Dariya Abubakar yake hadda Riƙe ciki wato aljanu, sai da ya yi ma'ishi suma Yaran da basu san me yake wiya dariyar ba, suna taya shi sannan ya dakata yana kallon ta Yace

"To waye kuma zai ji a jiki idan ban fasa Auren ba?."

"Jikin magayi mana."

Ta basa amsa, dariya ya kuma yi wannan karon Ita ma tana tayasa sai kuma abin ya koma musu na nishaÉ—i.

Tun daga Ranar Rafi'at bata ƙara gigin tado maganar kishiya ba, tunda taji shima ya yi shiru anata silly tunanin wata ƙila anfasa Auren ne tunda taji shiru.

______*_____*

Rayuwa ta ci-gaba da tafiya Yayin da a kullum Bikin Abubakar Mai Kyau da Hajarah ƙara matsowa yake Yayin da Amarya take can gidan su ango.

Ɓangaren Rafi'at kuwa zuwa lokacin ta sadaƙar mijinta Abubakar Abin ƙaunar ta, Aure zayyi da gaske, musamman ma da taga anata gyara gyare a gidan sai dai kuma har zuwa lokacin bata san wacece matar da zai aura ba.

Kuma bata Fatan ta san koda sunan wannan mace da zai Aura ne, domin kuwa shi kanshi Auren da Auren ƙaddara ta kira shi acewarta in banda shiga shara ba shanu irin na Abubakar yana da mace kamar ta a ajiye a gida ai bata ga abinda zayyi da wata macen ba

\\hmm hmm ni kuwa da nake a gefe nace Rafi'at ke nan ana nuna miki gabas kina Yamma zaki bi in banda abinki to su mazan aka faɗa miki kamar dutse suke indayyi shiru kawai kafin su wance suyi waje dani 🤫//

Haka Rayuwar ta ci gaba da antaye ta ko wani ɓangare shirya shirye ake, harya kasance saura one week a ɗaura Aure zuwa lokacin kuma mutanen France, Lagos, Kano Mai Duguri, Adamawa State, gaba ɗaya sun hallara gida ana shirya shirye dasu gasu Zuwaira ma dasu Jawaheer da Jummai gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo dama sauran dangi antaru ana gudanar da shirya shiryen biki.

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Page *71&72*

To abin ma haka yake ta ɓangaren uwar gidan Abubakar Rafi'at da taga abin dai bana wasa bane ita ma sai ta tashi tsaye ta fara shirya shiryen bikin domin kuwa da shawarar mahaifiyar ta Hajiya Zinaru da kuma ƙanwar ta Sailuba tayi amfani na ta kwantar da hankalin ta ta ɗauki komai ba komai ba dadai ira iren su.

Gaba É—aya kayan dake cikin gidan Abubakar sai da ya canza su bai bar komai ba, hatta da kayan bedroom na Rafi'at kala É—aya ya ma ta dana Amarya Harajah.

Ita dai Rafi'at tana daga gefe tana kallon ikon Allah yadda Abubakar yake kashe kuÉ—aÉ—e kamar bai san zafin su ba, to dama taya zai san zafin su abin da akwai ba'asan a dadi ba, an tara masa shi ma ya tarawa kanshi.

Tun ana saura kwana biyu É—aura aure, gaba É—aya dangin ta na nesa da na kusa suka iso aka fara shirin biki Yayin da dangin miji suma suke nasu a can Jigawa State.

Rafi'at ta kwantar da hankalin ta bata tayar da hankalinta ba, ko kuma na mijinta tun daga ranar da yace zai ƙara Aure ta kulle kanta a ɗaki bata kuma Gigin maimaita hakan ba, ko ma ta ɓata Ransa a'a.

Sai ma dagewa da tayi ta danni kanta da zuciyarta ita ma tana bada gudun mawar da ya kamata a wannan Aure. Wanda hakan ba ƙaramin kima ya ƙara ma ta ba a idanun mijinta Abubakar. shi dai bazai yi wannan Aure a domin baya ƙaunar matar sa Rafi'at ba, a'a ai sai da so ake zama wuri ɗaya ballanta ma zaman Aure na har abada.

Yana son ta yadda ya kamata, sai dai har wa Yau da ta kama Jumma'a Ranar É—aura Aure Rafi'at bata san wacece amaryar da mijinta Abubakar zai auro ma ta cikin gida ba, kuma bata damu da ta sani ba, sai ma Sha'anin gaban ta take ba ruwanta tamkar ba ita bace wacca za'ayi wa kishiya.

A tunanin ta Amaryar Ƴar can Jigawa State ce, tunda taga dangin mijin nata suma suna shagalin Bikin a can basuzo nan Abuja an haɗe ba.

"Wata ƙilama Amaryar Ƴar dangi ce suka haɗu dashi shiyasa."

Haka kawai Rafi'at take kawowa cikin tunanin ta sam bata tunanin Amaryar Ƴar wata State ɗin ce ba Jigawa State ba, dalilin ta na wannan tunanin kuwa shi ne tun ana saura kwanaki uku biki mijinta Abubakar ya koma can Jigawa State ana shagalin biki dashi.

Uwar gidan Abubakar Rafi'at da Yamma wuraren ƙarfe biyar na Ranar ɗaura Auren.

Taci kwalliya ta cakare cikin wata Ɗanyar lace golden color ɗinkin Yayi na wancan lokacin, ta cakara ɗaurin sangaya, gaba ɗaya shigar jikinta Ruwan golden color ne, ga wasu arnen Ƴan kunne sarƙa abin hannu komai nata gold, tayi kyau ba'a magana gata dama kyakyawa sai aka ƙara haɗewa, sosai tayi kyau.🥰

Gaba ɗaya ita da ƙawayenta da dangin ta suna zazzaune a ƙayataccen palon gidan suna jiran ƙarisowar Amarya da muqarrabanta, sai faman surutu suke irin na gidan biki, sai dai wannan yasha banban domin kuwa komai cikin nutsuwa irin na cikakkun ƴan boko masu ji dukiya suke yi.🙃

Sai dai kuma me?, wani abin mamaki tun ana jiran ƙarisowar Amarya da muqarrabanta da wuri, har aka kai can cikin dare, amma abu shiru ba Amarya ba dangin ta.

Abu dai kamar wasa har gari ya waye babu alamar dangin Amarya da ita kanta.
Tun Rafi'at tana ɗaukar abin wasa har hankalinta ya fara tashi, ganin har an kwashe kwanaki biyu da biki, amma dangin Amarya ba labarin su, ga kuma mijinta Abubakar shima dai bai dawo ba, gashi a wancan lokacin bama waya kaɗai ba, hatta cibiyar sadarwa ƙaranci yake.

Tsoron ta Allah abu ɗaya take tsoro karfa ace Abubakar ya raba musu gida ne ita da wannan amaryar da ya ƙara ma ta aikuwa da bai kyauta ma ta ba.

A Rana ta uku da ɗaura Aure ne, zuwa lokacin gaba ɗaya dangin ta da ƙawaye sun watse sai dai ƙanwar ta Sailuba ce da kuma wata Yayarta Badi'atu sai kuma wasu dangin ta su uku kacal, suka rage basu tafi gidajen su ba.

Suma dai shirye shiryen tafiya suke zuwa dare.

Gaba É—aya suna zazzaune a palon gidan sunyi jigum jigum, barin ma dai ita Rafi'at da abin duniya ya ma ta yawa a kai.
Tunani take shikenan fa yanzu mijinta Abubakar yana can tare da Amaryar sa a wani gidan suna shan shagali an barta anan jigum gum. 😭

Suna cikin haka kowa da tunanin da Yake yi, suka ji dirar motoci ba É—aya ba biyu ba.
Sai shigowa suke yi, ba bu wacca tayi gigin tashi daga cikinsu, har zuwa can mutane suka fara shigowa, suna nan zaune.

Ba ƙaramin mamaki Rafi'at tasha ba, ganin dangin mijinta Abubakar sune suke shigowa ga kuma wata lulluɓe da mayafin da ya rufe ma ta fuska da jiki da alama ita ce amaryar.

Ko waccensu da buɗa ri-ri-ri take shigowa, har suka wuce ɗan wani korido Wanda kai tsaye zai sadasu da ɓangaren Amaryar.

Ita dai Rafi'at da sauran dangin ta da suke zaune a palon ikon Allah kawai suke kallo.

Sailuba ce da ta gaza haƙuri ta kalla Yayarta Rafi'at ta ce

"Wai Auntie Rafi'at kamar idona dangin mijin ki nake gani sun kawo Amarya, aikuwa indai haka ne, kin kaÉ—e daga ke har ganyenki wallahi."

Shiru kawai Rafi'at tayi bata kula surutun Sailuba ba.

Da dare wuraren ƙarfe Takwas su Sailuba suna zaune a palon Rafi'at suna taɓa fira. Yayin da ita kuma take daga cikin bedroom nata abin duniya ya ishe ta.

Sallamar su Jawaheer ne yasa su Badi'atu da Sailuba dama sauran matan dake Palon suka yi shiru da surutun da suke yi sannan suka amsa musu sallamar.

Ƙarisa shigowa matan wajen su biyar suka yi yayin da da Amaryar take tsakiyar su lulluɓe cikin mayafi kalar kayan jikin ta.
Gaba É—ayan su wuri suka samu suka zazzauna kana aka shiga gaishe gaishe tsakani, dama can Sailuba dasu Jummai sun san juna sosai.

Tashi Sailuba tayi tana faÉ—in "Bari dai na kira Auntie Rafi'at domin naga kamar bata san da shigowar ku ba."

Tayi maganar tana nufar hanyar bedroom na Rafi'at, gaba É—aya suka bita da ido bayan sun amsa ma ta.

Ba'a É—auki lokaci mai Yawa ba, sai gasu sun dawo tare, wannan karon Rafi'at sanye take cikin dogon hijjab blue color, dan haka, ba'a ce. ga kalar shigar jikinta ba.

Zama suka yi a 2sieter sannan Rafi'at ta gaisa dasu Jawaheer, dama can basu samu sun gaisa ba.

Sai kuma aka shiga bawa Rafi'at Amanar Amarya Hajarah.

Jinsu kawai take tana kuma bin su da kallo fuskar ta ɗauke da murmushin yaƙe can ƙasan zuciyarta kuwa

"Humm hmm hmn...."

Har suka gama abin da ya kawo su suka ƙara gaba, Rafi'at bata ce musu ko ci kanku ba, sannan kuma ko fuskar Amaryar bata gani ba, har suka koma inda suka fito, tana zaune tana saƙa abinyi.

Can ma su Sailuba suka ma ta sallama ko wacce ta kama gabanta.
Chapter 68 · 0% Book details