← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 96

Sashe 71

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin in banda dariya babu abin da su Sakeenah da su Zuwaira suke masa nan ya shiga É—aukar jariran, idan ya É—auki na Hajarah sai ya a je ya É—auki na Rafi'at haka yake ta yi abin gunin burgewa.

Wani ƙarin ikon Allah kuma gaba ɗaya jariran biyu, mugun kama suke da juna tamkar mace ɗaya ce ta haife su, aikuwa nan mutane suka dingi magana a kan wannan abin mamaki.

Ranar suna kuwa ɗiyar Hajarah taci suna Zaynerb a Yayin da Ɗiyar Rafi'at taci suna Haleesat, wato dai har lokacin Abubakar bai manta da Haleesat Rashid Rayyan ba masoyin gaskiya ke nan, Allah sarki Rayuwa a lokacin har da yawa sun manta da ita.😞

Ba ƙaramin daɗin wannan sunan da Abubakar ya sakawa ɗiyarsa dangin Rafi'at suka ji ba, a lokacin wasu daga ciki har sai da suka yi kuka na tunawa da maragayya Haleesat Rashid Rayyan mutumiyar kirki.

Ita ma dai Hajarah sai lokacin take sanin wacece Haleesat Rashid Rayyan a wurin Abubakar.

Rayuwa ta ci gaba da antayewa yayin da Abubakar yake kula da matan sa duka domin kuwa ƙin bari ya yi su Hajiya Harirah su ɗauki Hajarah wankan gida, a lokacin sai dai Hajiya Harirah ce tazo ta zauna dasu tana kula da Hajarah, yayin da ita kuma Rafi'at wannan Dattijuwar mata da ta amsa haihuwar su take kula da ita.

---**

Wani Abun mamaki da ya taɓa faruwa Wanda gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo ba zasu taɓa mantawa dashi ba shi ne.

A wata Ranar Alhamis da safe lokacin Rafi'at da Hajarah suka cika watanni uku da Haihuwa, Ranar Abubakar bai fita Company ba.
Wuraren goma na safe suna zaune a palon gidan shida Rafi'at da Hajiya Harirah da kuma sauran Yaran gidan suna taɓa fira sama sama.

Sai ga Hajarah ta shigo tamkar an jefo ta, sai faman goge gumi take ga fuskar ta ɗauke da matsanancin Farin ciki saboda tsananin saurin da take yi har Ƴarta Zaynerb dake hannunta ta kusa faɗi ƙasa, ta taro ta.

_-_Mgnr Payment da nace. Tabbas Book 2 is paid fa_-_

_Duk Wanda Ya shirya ayi tafiyar da shi, kuma ya shirya Payment_

_-_Just Pay With This Details_

_-_-_-_-_-_
*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Page *77&78*

Qarisowa tayi sannan ta tsaya a tsakiyar palon tana faman sauke ajiyar zuciya game da haki, ganin yadda ta shigo a hargitse kamar wani ya biyo ta yasasu gaba É—aya tashi suna tambayar abin da ke faruwa.

A hankali ta buÉ—e kyakyawan idanunta waÉ—anda saboda tsananin farin cikin da take ciki yasa suka kawo ruwa, ta kallesu dasu sannan ta fara magana.

"Ina cikin farin ciki wanda tunda nake a Rayuwata ban taɓa shiga ciki ba. Yau kuma a dai dai wannan lokaci na tuna WACECE NI, Yau bayan shafe tsawon shekaru ɗaya da wata biyar da kwanaki biyar da mintuna goma sha biyar da sakanni, a Yau ni 'Hajarah Haleed Mai Waje: na tuna Asalina na tuna Ahalina na tuna sunan State nawa, na tuna komai da komai duka...'

Tayi maganar ne a Yayin da wasu siraran Hawayen Farin ciki suka wanke ma ta fuska.

Gaba ɗayansu jama'ar dake a palon kabbara suka saka cike da tsantsan farin ciki, shikuwa Abubakar gaza jurewa ya yi har sai da ya yi sujadar shukur yana kuma miƙa godiyar sa ga Allah wato dai maganar bahaushe ce da yake cewa INDA RAI DA RABO ikon Allah, gashi dai daga ƙarshen ƙarshe, Hajarah zata kuma haɗuwa da Ahalinta a karo na biyu, Allah ke nan buwayi gagara misali.

Da gudu Rafi'at ta ƙarisa wurin Hajarah ta Rungumo ta gaba ɗayanta a jiki tana faɗin

"Na tayaki murna sosai sosai Abokiyar."

Da yake haka suke kiran juna, murmushi Hajarah tayi tana kuma damƙe hannun Rafi'at dake cikin nata Sannan ta ce

"Nagode sosai Abokiyar, Allah ya bar ƙauna."

Hajiya Harirah kuwa tun ɗazu fuskar ta ɗauke take da matsanancin Farin ciki, saboda haka sai ta kasa magana, kawai tana binsu da kallo, ƙari sowa wurin ta Hajarah tayi Bayanta miƙawa Abubakar Zaynerb kana ta Rungumo Hajiya Harirah faɗi take

"Hajiyar mu kita yani murna da farin ciki Yau ina cikin nishaÉ—i obaaaaa..."

Sai da gaba É—aya suka sama nutsuwa suka zazzauna sannan kuma Abubakar ya É—auki waya yana kiran gaba É—aya dangi yana faÉ—a musu Abin farin cikin da suka wayi gari da shi.

Aikuwa nan aka dingi tayasu murna barinma dai su Zuwaira, Jawaheer, Jummai Sakeenah waɗanda suka ɗauki Hajarah matsayin Ƴar uwa ba matar ɗan uwansu ba, ai nan mutanen Jigawa State suka ce gasunan ƙarisowa Abujan ayi farin ciki tare dasu.

A Ranar gaba É—aya Ahalin sun wuni ne cike da farin ciki mara misaltuwa.

Misalin ƙarfe bakwai na Yammaci mutanen Jigawa State tun daga kan Alhaji Sameer Lamiɗo Dr_Raheemah Hajiya Zuwairiya, Zuwaira, Jawaheer, Jummai hatta Sakeenah dake Aure a Adamawa State sai da ta hallara a garin Abuja gaba ɗayansu sun ƙariso.

Wuraren ƙarfe Takwas da Rabi na dare gaba ɗaya sun hallara a Babban palon gidan, suna fira cike da nishaɗi bayan komai ya lafa ne Alhaji Sameer Lamiɗo ya kalla Hajarah cike da kulawa Yake faɗin

"ÆŠiyata Hajarah gaba É—aya nida Ahalina muna tayaki murnar tuno Rayuwar ki da Ahalin ki da kikayi.."

Murmushi tayi cike da jindaÉ—i ta amsa da

"Ina godiya sosai Abbhee..."

"Tohm ni dai har Yanzu banji sunan State É—in namu ba."

Cewar Jawaheer cike da zoyala, murmushi Hajarah take saboda farin cikin da take ciki ma haƙoranta sunƙi rufuwa gyara zama tayi kana ta fara magana kamar haka.

"Da Farko dai kamar Yadda kuka sani sunana Hajarah sunan mahaifina kuma Alhaji Haleed Mai Waje, ni ɗin cikakkiyar Ƴar Garin KADUNA STATE ce dake a nan AREWA cikin Nigeria Yankin Africa."🌍

"Alhamdullilah.

Masha Allah..

Hakan akeso..."

Haka kawai gaba ɗaya mutanen da ke zazzaune a palon suke faɗa nan kuma aka ƙara tayata murna daga nan kuma Sabuwar fira ta ɓalle a tsakani daga ƙarshe sun yanke shawarar cewa gobe tun daga kan Alhaji Sameer Lamiɗo da matansa da kuma Zuwaira da Abubakar sai kuma ita Hajarah ɗin zasu wuce Kaduna Garin Gwamna domin haɗuwa da Ahalin Hajarah, daga haka kuma taron ya watse dama lokacin dare Ya yi sai kowa ya sama makwanci, dama kuma Hajarah ita keda girki sai kawai tabi mijinta tura karsa.🤭

*WASH£-GARI*

Wuraren ƙarfe goma sha ɗaya na safe gaba ɗayansu Ahalin tsaye suke a filin ajiye motoci na gidan. Yayin da waɗanda zasuyi tafiyar suna shirye tsaf, Yayin da kuma waɗanda ba da su za'a tafi ba, suka tsaya daga gefe suna musu ban kwana cike da Fatan Nasara.

Bayan sun gama ban kwana É—in ne gaba É—aya suka shiga motoci da yake motocin ba kalar na wannan zamanin bane, shiyasa sai da suka yi mota uku sannan gaba É—aya suka shiga ciki.

*SAIDAI KUMA ME?.*

Wani Abun mamaki shi ne duk Yadda a kaso motar da Hajarah take ciki ta tashi Abu ya cutura.
Abu dai kamar wasa tun ana gwadawa cikin daÉ—in rai har aka koma gwada mota mota amma wani ikon Allah shi ne, duk motar da Hajarah ta shiga ciki ba zata tashi ba, amma kuma tana fita wannan mota zata tashi.

Abu fa kamar wasa anata abu ɗaya har wuraren ƙarfe ɗaya na rana ana kan abu ɗaya, sai daga ƙarshen ƙarshe ne, bayan Addu'o'i da suka dingiyi aka samu mota ta tashi.

Ajiyar zuciya ko wanen su yake saukewa gaba É—aya sun haÉ—a uban zufa barin ma dai Hajarah da takeji kamar me?.

Sallama suka kuma yi da kowa sannan suka ɗauki hanya, Bayan gate man ya wangale musu gate.💃

_____*

Sun bar Garin Abuja wuraren ƙarfe ɗaya da rabi na Rana sannan suka fara wuce garuruwa sun wuce Minna ba daɗewa ke nan suna shirin shiga Garin Kaduna.

Jikin Hajarah ya fara wani irin rawa ta ko'ina haɗa zufa take ga wasu ƙuraje da suka fara fitowa daga ko'ina na jikinta, da yake su uku ne a Motar ita da Dr_raheemah da kuma Hajiya Harirah, da Farko basu lura da abin da ke faruwa da ita ba, sai da suka ji ta fara nishin wahala, aikuwa nan take suka ba driver umarnin tsayawa.

Gefan kwalta ya samu sannan ya tsayar da Motar da yake suna a gaba ne, shiyasa suma sauran motocin da ke bayansu suka sama wuri suka tsai tsaya, sannan gaba ɗaya suka fiffito suna kallon Hajarah dake faman haɗa uban zufa ga wasu ƙuraje da suke feso mata tashi ɗaya, Abin gunin ban tausayi.😰

Da sauri Abubakar ya ƙarisa wurinta kana ya kamo hannunta cike da tausayawa ya kira sunan ta.

Kasa amsawa tayi saivma kallon sa da tayi cikin jin azaba ta ce

"Dan Allah mu koma gida, idan ba haka ba kuma mutuwa zanyi, zafi nakeji ta ko'ina a jikina jina nake kamar bani ba..."

Daga jin irin abin da take faɗa da kuma ganin yadda gaba ɗaya jikinta yake rawa ga wasu ƙuraje, Yasa Alhaji Sameer Lamiɗo Ya yi gyaran murya, gaba ɗaya suka juyo suna kallon sa, suna jira suji abin da zai ce.

"Ina ga mu juya gida kawai domin kuwa na lura wannan lamarin dasa hannun Jinnu a ciki, mu Fara komawa gida a ma ta magani sannan koma menene daga baya a yi."

Gaba ɗaya sun gamsu da maganar sa kuma sun fahimci abin da yake so ya fahimtar dasu, saboda haka ba tare da ɓata lokaci ba, gaba ɗaya suka shishshiga motocin su suka koma.

Su Rafi'at suna zazzaune a palon gidan suna taɓa fira tsakanin ta dasu Zuwaira suka ji dawowar motocin.

Mamaki ne ya kamasu ganin su Hajiya Zuwairiya sun shigo.

"To kodai har sun dawo ne?."

Jawaheer ta tambaya tana miƙewa tsaye kamar yadda suma sauran suka mimmiƙe suna binsu Hajarah da kallon neman ƙarin bayani.

Gaba ɗayansu zama suka yi a saman kujerun palon jiki a mugun sanyaye, ganin haka yasa suma su Jummai suka zazzauna sannan ne kuma suka lura da Hajarah da ƙurajen da suka fara fiffito mata a jiki.

"Ya Allah.! Menene kuma wannan?."
Chapter 71 · 0% Book details