← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 96

Sashe 85

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ma gaba É—aya mutanen palon suka mayar da hankulan su kan sa hadda Momy Rafi'at da tun ganin Yaron nata bata ce komai ba.
Kai harda Afeefah wacca farfaÉ—owarta ke nan taji zancen Uncle Yusuf a sama, sannan kuma babu wanda ya lura ta farfaÉ—o domin kuwa bata nuna alama ba.

Ajiyar zuciya Maleek ya sauke yana tariyo gaba ɗaya girlfriend's da ya taɓayi kaf cikin su, baiga wacca suke tare yanzu ba, gaba ɗaya basa tare domin kuwa tunda daɗewa yabar kalar Rayuwar sa ta baya, shi dai yanzu iya tunanin sa baiga macen da zaice ya taɓa ma ta kallon so ba, ko kuma ya ma ta kallon wani abun ban da ƙawance, ɗagowa Ya yi Yana kallon gaba ɗaya mutanen palon, kamar yadda suma shi Suke kallo.

Murmushi Ya yi kaÉ—an kana ya buÉ—e muryar yadda gaba É—aya zasuji yana faÉ—in

"Husnee ce wacca na zaɓa..." 💞💞

Gaba É—aya palon dariya suka saka ganin yadda Husnee ta É—ago a firgice tana kallon sa hankali tashe.

Uncle Yusuf kuwa babu abin da yake faÉ—i sai

"Masha Allah dama haka ake so, lamari ya yi daÉ—i."

Nan kuma palon ya É—auki hayaniyar murna da jindaÉ—i.

Sai da suka sama nutsuwa gaba É—aya suka yi shiru sannan Uncle Yusuf ya kalla Husnee cikin maganar irin na manya yake tambayar ta

"Husnee Ɗiyata kin amince zaki Aura Yayanki Abdulmaleek kamar yadda shima yace keya zaɓa?."

Kallon jama'ar palon Husnee tayi kamar yadda suma suka zubo ma ta na mujiya suna kallo.😅

Cikin gimtse kyakyawar fuskar ta take faÉ—in

"Uncle Yusuf a bani mintuna biyar zanje yanzun nan nayi shawara na dawo."

Tayi maganar fuska ba rahama, dariya suka saka baki É—aya, sannan Uncle Yusuf yace cikin dariyar shima

"Kinji jeki Ɗiyata ki ɗauki iya a dadin lokacin da kike so domin duka naki ne."🥰

Miƙewa tayi sannan ta zagaya ta bayan kujeru ta wuce kai tsaye bedroom ɗin Lailah, ta wuce tana shiga ta rufe ƙofar harda murza key, sannan ta dawo ta ƙarisa can gaban madubi tana kallon kanta.

Cire mayafin da tayi rolling kanta dashi tayi kana ta daka tsalle tana faÉ—in

"Yes, Yes, sai ni Husnee, wallahi sai ni Husnee, a gaskiya na cire tuta cikin ma ta niÉ—in ma mai sa'a ce cikin masu Nasara, inba hakan ba wannan Diamond boyfriend guda kamar Yaya Maleek Yace Yanaso Ya Aureni.
Haba duk inda aka ji maganar Aure ansan da akwai soyayya, Yasin sai ni Husnee, lallai dawowar Buddy Gida ba kowa Ya yi ma amfani ba sai ni, kai dole ma nayi waƙa, oh toni wata kalar waƙa ma, na iya?..."

Tayi maganar tana zama gefan bed cike da matsanancin nishaÉ—i highly highly,

Murmushi tayi sannan Ta ce "Yeah Wallahi na tuna."💃💃

Buɗe daddaɗar muryar ta Ta yi sannan ta fara Raira waƙa cike da enjoying Mood da take ciki rairawa take yi kamar haka.

"I'm coming home😌 I'm coming home. Tell the world, I'am coming home, 🙂 Let the rain Wash away..☔🌈 All.. the pain of yesterday😥😊 I know my kingdom awaits 💕💕 and... They've forgive my mistake"🤗💝 I'm coming home, I'm coming home Tell the world I'am coming home... { home is not a place it's feeling. }."

Murmushi tayi Bayan ta kai haka a waƙar nata sannan ta ɗauki mayafinta, wannan karon yafashi tayi saman kafaɗarta, sannan ta buɗe ƙofar ta fito bayan ta kuma gimtse kyakyawar fuskar ta.💝

Husnee ta kasance ÆŠiyace ta uku wajen Hajiya Jawaheer.
Husnee, kyakyawar matashiyar budurwa ce wankan tarwatsa, doguwa ga hanci, ba zata Haura shekaru ashirin da ɗaya zuwa da biyu ba a duniya, sa'ar su Afeefah ce, ta kammala karatun degree nata anan Babbar University dake Jigawa State ta Karanci fannin Agriculture, Husnee akwai ta da san barkwanci kamar mene, gata akwai kirki da sauƙin kai, sai dai abin da ba'a rasa ba domin kuwa ɗan Adam ajizine. 😸

Komawa tayi ta zauna kusa da su Ƙarama da Mah'eesha saɓanin ɗazun da take kusa da Lailah da kuma Fateemah da Zakiyya.

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalla Uncle Yusuf Ta ce
"Eh Uncle na amince nima."

Tayi maganar tana rufe fuska wai kunya.🤓

Gaba É—aya fuskokin mutanen wurin idan ka kalla zaka fahimci bawai iya farin cikin dake bayyane a fuskar su bane, harda zuciyoyin su ma.

Murmushi Uncle Yusuf Ya yi sannan Yace

"hakan ake so. Yanzu sai a fara tunanin saka rana ko?."

Zuruf Husnee ta ce "Ah ai Uncle ina ga kawai tunda Already na kammala karatu na, a saka nan da one month kawai, kaga Lokacin Ya yi dai dai da lokacin da za'a kuma gasar SARAUNIYAR KYAU matakin ƙasa ko?."

Tayi maganar iya gaskiyar ta kuma har zuciyarta.

Fashewa da dariya gaba É—aya mutanen palon, suka yi cike da nishaÉ—i.

Lailah da bata gani bata tanka ba, ta ce

"Oh oh ikon God sai Look. Wato yanzu ke Husnee ko kunya babu kike wannan zance gaban mu ko?."

Tayi maganar cikin dariya, muryar da basu yi tsammanin jinta bane, suka ji tana faÉ—in
"Oh ke kuma Lailah sarkin surutu zaki ba, My Aunty to be, kunya cikin society ko?."

Cewar Afeefah tana saukowa daga saman doguwar kujerar da aka kwantar da ita.

Murmushi Husnee tayi sannan ta ce "Batta kawai dai dai nake da ita nima ae, ko tayi tunanin zanji kunyar tane?."

Gaba É—aya dariya suka kuma yi habba daga haka kuma fira ta kuma shiga tsakani cike da nishaÉ—i.
Shidai Maleek shiru ya yi yana kallon Ahalin nasa gaba ɗaya sun canza sosai. Jinsa yake tamkar wani sabo cikin su, sai yaji yau ya kuma yarda da wannan maganar da ake cewa 'Duk Wanda Yabar gida, Tofa Tabbas Gida Ya barsa'. Home is not a place it's feeling for All people.💞

*KANO*

Wannan karon da tsananin mamaki ya kuma kallon mahaifiyar tasa jin abin da take faÉ—i, shifa sam kansa ya É—aure ya kasa fahimtar komai yadda ya kamata.

Murmushi tayi sannan ta ci gaba da cewa

"Umarni nake baka, akan kaje ka nema soyayyar Jiddarh saboda sai da hakan burina na tsawon shekaru fi ye da ashirin zai cika, idan kuma ba haka ba, zan san abin yi."

Murya na É—an rawa Yace

"Ni nifa ina da wacca nakeso kuma zan Aura, sannan kuma da kike maganar na nema soyayyar jiddarh nifa matsayin ƙanwa na ɗauke ta sannan kuma..."

Katse sa tayi cikin tsananin ɓacin rai sannan cikin tsawa da ɗan ɗaga murya ta fara magana

"Heesham, indai ni ce mahaifiyar da ta haife ka ina baka umarni da kaje ka nema soyayyar wannan yarinya jiddarh, domin sai da hakan Burina zai cika."

Sai kuma ta É—an sassauta murya tana tambayarsa da cewa

"Menene sunan ita yarinyar da kakeso ka Aura É—in?."

Wannan karon cikin sanyin murya ya fara maganar domin kuwa mahaifiyar tasa a maimakon mamakin ta da ya faraji, tofa yanzu tsoro ta fara bashi, ganin yadda take maganar cikin kakkausar murya.

"Sunanta Bilkisu ne."

"Bilkisu. Bilkisu.."

Auntie ta maimaita tana ya mutsa fuskar ta, wacca ta ɓaci da Bleaching ta gode Allah.

"Ita ɗin Ƴar ina ce haka?".

"Katsina ne mahaifarta."

Ya bata amsa cikin sauri sauri, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke, jin ba wacca take tunanin ba ce, sannan ta ce

"Babu damuwa ita ma zaka iya Aurenta, amma fah Bayan ka Aura Ƴar uwarka Jiddarh. Zuwa lokacin Burina na tsayin shekaru ya cika sannan...."

Gyara zaman sa Ya yi saman swivel chair da yake kai sannan ya kira ta da sunan da sukafi kiranta dashi.

"Auntie."

Ta amsa sannan ya ci gaba da cewa

"Shin zan iya sannin wannan Burina naki da kike cewa har saina Aura Jiddarh shi ne zai cika?."

Murmushi tayi kalar na cikakkun wayayyun Mata tana kaÉ—a ido ta amsa masa da faÉ—in

"Oh no Heesham har yanzu kai yaro ne ba zaka fahimci komai ba, koda na faÉ—a maka."

"Kai, Auntie ni ne Yaron? nafa Haura Twenty five highly fa."

Cewar Heesham yana zare ido jin an kira shi da Yaro.

Still it's her cheek have clear smile, shiru tayi sannan ta kuma cewa

"Habba My first Born, just chill Boss, mana daga wasa to na yadda kai ɗin, ba yaro bane, Kocin ne."🥳

Tayi maganar tana Æ´ar dariya sannan ta ci gaba da cewa

"Wato Heesham misali kai ne kana da wata Riga wacca wannan Riga ta kasance tana da wani masifar kyau da tsada, kowa sonta yake kaima hakan, kana masifar ƙaunar ta, sai kuma ya kasance ita wannan Riga daga ka ɗaukota ka saka ta a jikinka zata dinga yi maka ƙaiƙayi ta ko wanne ɓangare na jikin ka har sai ka cire ta, ka ƙona ta da wuta da fetur ta zama babu ɓurɓushinta sannan zata dena wahalar da kai shin idan kai ne ya zaka yi da wannan haɗaɗɗiyar Riga da kake masifar ƙauna?, shin zaka a jeta ne gefe ka dinga kallo kanajin daɗi, ko kuwa zaka ƙonata ne ka huta saboda bata da wani amfani?..."

Murmushi Heesham Ya yi Yana nazarin maganar ta, tabbas idan ya fahimta wato dai Hausa take masa cikin Hausa, sai dai kuma daga maganar ta bai fahimci komai ba, saima É—aure masa kai da maganganun nata suka yi, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon ta, sannan ya bata amsa da cewa

"Gaskiya idan ni ne mutum mai wannan Rigar tunda ina ƙaunar ta sosai, kawai zan saƙaleta ne na dunga kallon ta kullum tunda saka ta bazai Yiwu ba."

"Oh Heesham wannan maganar naka is not a efficacy, bazai yiwu ba, kawai kabar zancen nan, domin kuwa yafi ƙarfin tunanin ka."

Heesham zayyi magana yaji Alamar za'a shigo Bedroom ɗin, hakan ne Yasa sa fasa faɗar abin da zai ce, sannan ya mayar da kallon sa kan ƙofar.

A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga jikin ta sanye cikin Elegant Beauty Dress doguwar gown c.green color, wacca daga gaban gown ɗin Anyi ado da wasu stones sky green masu shaining, gown ɗin mara hannu ce, gashi ta matse ta gam gam, kanta babu hula sai gashinta Wanda Yasha gyara ta mishi style in braid.

"Oh Jiddarh lafiya kuwa naga kina faman dafe kan ki haka?."
Chapter 85 · 0% Book details