← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 96

Sashe 88

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Buɗe glass windows ɗin tayi duka, Yayin da Yanayin yadda iskan garin yake kaɗa wa Ya yi dai dai da Yanayin nishaɗin da take jin kanta ciki, zuciyarta cike take da nishaɗi sosai sannan kuma bata Fatan wani abu yazo ya gifta tsakanin wannan Rayuwar farin ciki da nishaɗi da take ciki, ita da Ahalinta daɗi da ƙari daga ƙarshen ƙarshe dai ga Yaya Maleek nata ya dawo Gida.

Bayan shafe tsawon shekaru Bayanan.

Tasa ni cewa dukkan wani ɗan Adam Yana tare da ƙaddarar sa, koda kuwa yana ƙarshen duniya ne.

So ita tana fatan ta ta ƙaddarar ta kasance ma ta a Yayin da take cikin Ahalinta, bata Fatan wani abu yazo ya rabata da Ahalinta, Especially ma Daddynta, Auntie Zaynerb nata, Lailahnta, Deejarh da kowa da kowa.

Koda kuwa Aure ne tofah tafiso ta zauna kusa da Ahalinta gaba ɗaya cikin farin ciki da ƙaunar juna.

A Wani mugun tsora ce ta zaro fararen idanunta cikin Æ´an sakannin da suka shuÉ—e tana cikin nishaÉ—i, amma kuma cikin Æ´an wa'innan sakanni da bazasu wuce biyu zuwa uku ba, ta shiga matsanancin violence sosai, dalilin Haka kuwa shi ne.

Hango Auntyn ta Zaynerb kuma abar ƙaunarta cikin swimming pool tana iyo ciki ba tare da numfashi shi ba, to abin da ya faru shi ne, sai da Zaynerb ta cike mintuna biyar cikin ruwan ba tare da numfashi ba, sannan ta fito.

Tofah Wajen fitowan ne aka so a sama akasi, Allah ya kare, domin kuwa wajen riƙe Banister's na madaidaicin Benen da zata fito daga cikin swimming ɗin ne, zata riƙe bata riƙe da kyau ba, shiine fah.
Tayi baya zata koma cikin ruwan ta baya, sai Allah ya kiyaye ta riƙo Banister's ɗin da Left hand nata.🤯

Wata kalar ajiyar zuciya afeefah ta sauke, tana dafe saitin ƙahon zuciyarta. Yayin da idanunta kuwa har wasu qwallan farin ciki ne, suka taru sai faman haki take saukewa, duk da cewa ba ita bace ta kusa anta yawa cikin Ruwan.

Tana tunanin da'ace Zaynerb ta faÉ—a cikin ruwan, idan ba wani ikon Allah ba, da wuya a ciro ta da rai.

Saboda Yanayin yadda tayi bayan, gaba É—ayanta ba wani abu da zata iya.

Shiyasa ita bata damu da wani iyo cikin ruwa ba, ko kuma ta dama kanta da saita Iya tsawon mintoci cikin Ruwa ba batare da numfashi ba.

Tasan Allah shike karewa amma gaskiya hanyar lafiya a bita da shekara.

Koma wa tayi wurin su Lailah suka ci gaba da fira sama sama. Yawancin firan nasu akan Yanayin rayuwar poor people ne.

A taƙaice dai sai wuraren can cikin dare sannan Afeefah da Lailah suka koma bedrooms nasu bayan sun sha fira cike da farin ciki.

*Haleesat Mai Kyau*

Ɓangaren Haleesat kuwa, bayan fitarta daga bedroom na Afeefah, kai tsaye bedroom nata ta wuce, wanka ta fara yi sannan ta shirya cikin sleeping dress fanjama Riga doguwa fara mai taushi.

Sai da ta kammala duk wani al'adarta kafin kwanciya Bacci, sannan ta kwanta saman royal bed nata Yayin da ta zuba wa kyakyawar fuskar wanda ke rufe cikin face mask Souvenir Abin tunawanta ido tana kallo, tamkar ba zane take kallo ba.

Duk da cewa sau ɗaya tak ta taɓa ganin sa.

Tsayin rayuwar ta sannan a lokacin wata kalar ƙaunarsa ta shige ta duk da cewa bata ga fuskar sa ba.

Confirm tasan wasu zasu kirata da zararriya, ko kuma wacca ta sama taɓin hankali, amma ita ba zata damu ba, domin kuwa kyawawan idanun sa, kawai take tunawa a ganin ta yin soyayya ko kuma faɗawa soyayya, ba dole sai da wani dalili ba, domin kuwa yin soyayya ko faɗawa cikinta baya buƙatar wani dalili.

A hankali ta furta a saman laɓɓanta

"My souvenir Yaushe, a'ina wani lokacin na ƙosa sosai, da na ƙara ganin ka na ƙosa highly, Ranar da zanga beauty face naka tazo a Ranar ko'a gaban waye sai Nayi Rawa da juyi."

"Ina son ka daga kallon farko, ina son ka daga haɗuwar farko, hallaudai, I LOVE MY SOUVENIR. Please! sweet Dream Good Night, My love."🥰

Ta daÉ—e hakan cikin magana ita kaÉ—ai da paper É—in hannun ta, har can bacci Ya É—auketa bata san lokaci ba.

_-_ To Miss Haleesat Mai Kyau Zararriyar Your Souvenir Good Night_-_💃💃

"MY Feefah Baby.!"

"My feefah baby..."

"Umhm, My Baby."

"Kin san wani abu kuwa?."

"Umm umhm."

I Love So Very much, Thither I Love For the All My heart, please, Say me. You Love Me please My feefah?."

"umhm umm No Way."

Juyi kawai Take yi gaba É—aya tabi ta haÉ—a uban gumi tamkar Babu a.c cikin bedroom É—in, sai faman faÉ—in "Umhm um."

Take yi tana ƙara wa da kalmar "No Way."😉

A hankali ta buÉ—e kyawawan fararen idanunta, kai tsaye ta sauke su saman haÉ—aÉ—É—en ceiling.

Shiru tayi tana tariyo gaba É—aya mafarkin da tayi.

Gaba É—aya yasha banban da kalar wanda take yi kwana biyu, wancan tana yi ne akan Haleesat da wata mummunar Mata take so ta cutar.

Wannan kuma wanda tayi a yau, wai ita da wani haɗaɗɗen ƙasaitaccen matashin saurayi ne, wai Yake roƙonta akan ta soshi, sai dai kuma bata samu ta kalla fuskar sa ba ta farka.😇

Juya idanun ta tayi tana ƙarewa bedroom ɗin kallo, gaba ɗaya pillows ɗin sun zube ƙasa, kowanne da ɓangaren da Ya yi shi Kanshi bedsheet Tayi dai dai saman mattress ɗin a taƙaice dai, gaba ɗaya saman bed ɗin nata ya koma tamkar ansha bidiri saman sa.💃💃

Murmushi tayi ganin yadda bedroom ɗin ma gaba ɗaya ya koma, sannan ta miƙe tsaye, juya idanunta tayi kan clock, ƙarfe Biyar saura wasu mintoci.

Ajiyar zuciya ta sauke kana ta nufa bathroom Hannu tasa ta kama handle na door É—in sannan ta buÉ—e ta shige ciki.

Sai da ta kwashe tsawon mintuna goma sha shida ciki, sannan ta fito zuwa lokacin an fara kiraye kirayen sallan asuba. Dan Haka Hijjab ta É—auka sannan ta tayar da sallah.

Bayan ta iddar bata tashi daga saman sallaya ba, sai da ta kammala dukan wasu al'adunta bayan iddar da sallah.

Zuwa Lokacin shida da Rabi tayi Don Haka ɗan motsa jiki tayi irin su Lanqwasa can, dawo nan saqalo tana nan. Juya can, malƙwashe, Haka dai sai da ta shafe tsawon mintuna talatin tanayi sannan ta dakata.

Zama tayi gefan bed tana goge gumin da ta tara tsaban motsa jiki takai mintuna uku a Hakan sannan ta miƙe, kai tsaye ƙofa ta nufa sannan ta buɗe ta fita daga bedroom ɗin.

Bedroom na Zaynerb ta nufa aikuwa taci sa'a a buÉ—e yake, Don Haka kutsa kanta tayi ciki bakinta É—auke da sallama.

Can saman doguwar stool ta hangota tana rubuta cikin wata ƴar ƙaramar jotter.
A hankali Zaynerb ta juyo tana amsa sallamar da Afeefah É—in tayi fuskarta É—auke da murmushi.

Qari sawa wurin tayi sannan ita ma ta zauna tana kallon Æ´ar uwan nata cike da farin ciki Ta ce

"Auntie Zaynerb, Menene kike Rubutawa cikin wannan jotter É—in?."

Tayi maganar tana ƙoƙarin ɗaukar jotter ɗin, da sauri Zaynerb ta kai hannu ta riga ta ɗauka tana faɗin wannan sirri ne.

Murmushi mai bayyana dimples Afeefah tayi sannan ta ce

"Okay tunda Haka ne yanzu wani shiri kike yi wa zuwa Kano State da zamuyi zuwa anjima?."

Zaynerb ta ce

"Shiri dai shi ne muna zuwa bazan dawo ba, sai nanda two weeks."

Zaro ido Afeefah tayi waje cikin shiga violence Ta ce

"Amma dai wasa kike yi ko?, Yanzu idan Wani Abu Ya sameni fah, kinsan fah bazan iya zama wurin da baki ba ko?."

Dariya Zaynerb Tayi tana faÉ—in

"Lallai Afeefah na lura fah har Yanzu ɗaukar kanki kike matsayin ƙaramar Yarinya, wacca bata Haura shekaru huɗu ba."

"Eh mana ae Haka ne indai ina tare da ke, ko kuma Daddy tofa ɗaukar kaina nake tamkar wata ƙaramar Yarinya wacca bata wuce shekaru Biyu a duniya ba."💃

Afeefah tayi maganar tana dariya.

Kama Baki Zaynerb tayi tana dariya ta ce

"Afeefah lafiyar ki kuwa?, idan kikayi Aure fah?."

Afeefah Ta ce

"Wani Aure aeni indai kika ga nayi Aure, tofa sai dai idan shi mijin ya kasance zai barni na zauna anan gidan tare da Ahalina sannan Zanyi."🥸

"Tirƙashi ah lallai Afeefah kina ruwa tsundum highly ma kuwa."

Cewar Zaynerb tana dariyar silly tunani irin na ƙanwar nata.

Afeefah ta ce

"Allah da gaske nake yi.
"

"Tohm ni dai bazan taɓa Yarda ba."

Cewar Zaynerb.

Afeefah Ta ce

"Ae zaki gani nan da watanni nawa ne kwata kwata."

"Okay...👌

Kice ƙanwar tawa ta antaya soyayya, to da Yaushe Hakan ta faru ni ban sani ba kuwa?."

Zaynerb ta tambaya ah mamakance.

Afeefah..

"Oh Auntie Zaynerb tawa ni fa ba wani soyayya. Dana antaya, kawai dai na faÉ—a ra'ayi na ne."

Zaynab...

"Ni dai ban Yarda ba gaskiya sai an faÉ—a min gaskiyar lamarin, ah gaskiya."

Zaynerb ta faÉ—a cike da nishaÉ—i.

Ae fah nan suka Shiga compromise tsakanin Afeefah da Zaynerb, ita Afeefah ta tsaya akan cewa ba wani soyayya da ta faÉ—a yayin da ita kuma Zaynerb ta tsaya akan cewa lallai lallai fah Afeefah ta faÉ—a soyayya.

Shigowar Deejarh ne yasa firan nasu ta tsaya, kiran Afeefah tayi suka fita a tare zuwa kitchen.

Anan suka haɗu dasu Elina da Ummi wa'inda suma suka ƙariso kitchen ɗin, da yake a gidan suke kwana akwai part na musamman wanda suke ciki, daga backyard na gidan.

Nan suka shiga aikin haɗa breakfast da yake Gidan akwai baƙi waɗanda suka kwana, shiyasa breakfast ɗin da suke yi yafi na kullum.

Suna aikin suna taɓa fira tsananin su da yake Afeefah ta saba dasu sosai, dan ma Yawancin types na girke girken da ta iya a wurin sune.

"Nifa har Yanzu ban gane wannan kyakyawar Budurwar ba, nasan dai ba xixi bace kodai, ita ma cikin Dangi take ne?, amma fah kyakyawa ce highly Allah kuwa."

Duk wannan zanen Ummi ce take zubosu da yake ita ma É—in gwana ce wurin iya surutu.

Murmushi Afeefah tayi wato dai shi ɗan Adam baya iya ganin Abu bayyi magana akai ba ko?.😇

Kallon Ummi Tayi sannan Ta ce "Sunanta Deejarh ƙanwar mu ce ita ma."

Tana maganar ne tana miƙa ma ta wasu onions da spinach dasu cabbage sannan Ta ce
Chapter 88 · 0% Book details