← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 96

Sashe 4

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta buÉ—e fararen idanunta ta ware su akan fuskar Êœumaira dake mata magana.

maƙalƙale ʜumaira tayi ta miƙe tsaye tana rawa da juyi saman bed ɗin ita ma ʜumaira tana taya ta.

Da sauri ta dira daga saman bed ɗin. ᴛa fita daga bedroom ɗin gabaɗaya. ɪta ma ʜumaira ta rufa mata baya. ᴅa gudu ta ɗare jikin wata ƴar ƙyaƙyawar dumadumar mata baƙa,ᴅake palon wacca ba za ta wuce shekaru arba'in da huɗu zuwa da biyar ba.

Tana faÉ—in "Auntie nayi nasara zan fito gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha nanda one month"...
Da sauri Æ´ar dumadumar matar da jieddarh ta kira da "Auntie tayi saurin yin, rijecting É—in wayar da takeyi sannan ta juyo da jieddarh gabanta tana tambayarta,abinda ke faruwa.

Cike da farin ciki jieddarh ta ce "Auntie an zaɓeni, zan fito gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha fa"..
Ƙayataccen murmushi Auntie Tayi,ba tare da tace komai ba.

Ita ma jieddarh bakinta washe yake kamar gonar auduga, ᴢama tayi saman two sieter kusa da ʜumaira tana faɗin "Auntie yau ina cikin farin ciki burina Ya kusa cika zan zama SARAUNIYAR KYAU" ta faɗa tana rungumo hannun ta a ƙirji Tana lumshe kyawawan idanun ta kamar mai jin bacci.

"murnar mai akeyi ne BRITISH QUEEN?" muryar ʜeesham taji yana magana da sauri ta juya tana kallon ƙofar palon ta wajen da ta jiyo muryar shi, tsaye yake jikin ƙofar ya rungumo hannun shi ta baya yana sakar mata ƙayataccen murmushi.

Da gudu ta miƙe tsaye ta ƙarisa gurin shi, ʏi tayi kamar zata rungume shi, sai kuma ta fasa ta tsaya a gaban shi tana sauke ajiyar zuciya, cikin murya mai sanyi tace "Yaa .H. yau ina cikin farin ciki burina zai cika an zaɓeni a cikin waɗanda zasu fito gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha.

"Da gaske take, ku rantse mana" ya tambaya yana kallon Êœumaira dake murmushi É—aga mishi kanta tayi alamar haka ne.

Gyara tsayuwar sa sayayi a gaban ta kamar wani soja yayi saluting É—inta yana dariya.

Ita ma salute ɗin shi tayi tana murmushi ta ce "Yaa .H. kaga daga na zama SARAUNIYAR KYAU ta jaha sai ta ƙasa daga ta ƙasa saina duniya ko", ta tambaya tana kallon shi.

Dariyar da ba shiri Auntie Tayi ta na faɗin "yarinya kenan waya faɗa miki daga na jaha saina ƙasa akwai wasu gaba"..

"Wanne da wanne kenan jieddarh ta tambayi Auntien tana zama a kujera, ʙayan ta dawo gurin.
Dukansu gyara zama sukayi suna kallon Auntie murmushi Auntie ta yi a zuciyar ta ta ce "anzo gurin Yarinya Jieddarh GO AHEAD Muje zuwa"...

Muskuɗawa tayi sannan "ta ce na farko dai da ace a ƙauye kike to saikin fara cin na local government sannan azo na State idan shima na state kinci sai azo.
Na state`s talatin da shida na ƙasar nan, shima sai kinyi winning sannan kuma azo na ƙasa, Bayan wasu ƙananu da za`ayi waɗanda su ba dole,bane domin ko anyi ko ba`ayi ba za`a iya shiga na ƙasa.
Kana azo a haɗa ƴan waɗannan ƙasar da wacan ƙasar shima idan kinyi winning akwai wasu da yawa sannan kuma azo uban gayyar na DUNIYA!.

Jikin jieddarh ne yayi sanyi jin waɗannan uban lissafi ita awa na state ɗinma ya aka ƙare balle na duniya Allah yasa taci na jahan ma tukunna, Toh dama Haka Abin Yake Idan akazo maganar sai taji jikinta Yayi sanyi laqwas....

"Aini nasan indai jieddarh ce zata cinye waɗannan tuni, wae bakuga wannan kyau ɗin bane ae ko wata ƴar american albarka come on mana Jieddarh yane wae da rasa qwarin gwiwa haka, haba mana keɗin fa, kece SARAUNIYAR KYAU ta gidan mu", Humaira ce duk tayi waɗannan maganar a domin kwantar ma da jieddarh hankali, fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi, "Ko ba haka ba Yaa .H. da sauri yace Haka ne mana na yarda highly.

Ganin yadda jikin jieddarh É—in har yanzu Yake a sanyaye yasa Auntie faÉ—in "kuma ae nasan yarinyar tawa kyakyawace zata ciyo mana kyauta na musamman,nasan da wannan.

Washe baki jieddarh tayi dan kuwa a kullum tanaso taji ana yabon ta, ana ƙara mata ƙarfin gwiwa, ana ƙara zugata kanta na hayaƙi😇.

"Kinga yanzu sai a fara shirya shirye ko?" cewar Êœumaira, Da sauri jieddarh ta ce "eh Haka ne to amma dame za'a fara?.
"Ku shirya kawai na kaiku kuyi shopping tun yau kuma yanzu ku zaɓo duk abin da ranku ke so, nauyin payment na ɗauka", Heesham ya faɗa yana kallon Humaira ɗin da ita Jieddarh.

Da sauri suka miƙe tsaitsaye harda ruga ruge "kabamu minti biyar kawai Yanzu zamu shirya no wasting time suka faɗa a tare suna nufar hanyar staircases domin shiga bedroom don shiri domin kuwa a kullum Burinsu a fita shopping basa gajiya sam ko kaɗan da outing🥰.
Sallama suka ma Auntie Bayan sun shirya suka fita shopping mall aikuwa dai sun jido kaya kala kala a gurare daban daban Wani ma, ba amfani zayyi ba,kawai don a kashe kuÉ—aÉ—e suka jido.
Basu suka dawo ba sai da suka biya suka sha ice cream cheese Burger e.t.c.

Daga ƙarshe ma sai da aka biya dasu sukayi salon sannan suka dawo gida.
Aikuwa dai a gajiye suka dawo gidan,domin kuwa ko gurin Auntie basu biya ba don ko ba ƙaramin gajiya suka kwaso ba.zuwa lokacin Dare ya lula kowannen su wucewa bedroom ɗinsa yayi domin samun Hutuu...

WANNAN KENAN

ABUJA!

___Lailah

Ɓangaren Lailah tsaf ta shirya cikin sleeping dress payjamas pink color mai taushi, har zata kwanta ta tuna bata amsa wayarta wajen Afeefah ba,don haka hijjab ta sanya jikinta sannan ta fito daga bedroom ɗinta sai da ta fara biyawa kitchen ta haɗa black coffee mai kauri sannan ta nufa bedroom ɗin Afeefah, knocking ɗin ƙofar tayi, Daga ciki Afeefah ta bata izinin shiga.

Kwance tasa meta tayi daidai saman Royal Bed ɗinta tana ibadar da aka saba wato chatting😅.

Zama tayi kan stool na dress mirror sannan ba tare da ta kalleta ba Ta ce "malamar chatting bani wayata".

Ita ma Afeefah Ba tare da ta kalleta ba saboda yadda gabaɗaya hankalin ta yana kan tsadaddiyar wayarta dake hannun ta, chatting da ƙawaye ya ɗauke mata hankali, Ta mata nuni da kan bed daga gefanta, ƙarisawa Lailah Tayi sannan ta ɗauka handbag ɗin ta ciro wayarta a ciki kana ta koma ta zauna saman wata doguwar softened stool dake ɗakin kana ta kunna Wayar dayake a kashe take.

Aikuwa kamar jira ake ta kunna saiga saƙonni nata tururuwar shigowa,Can kuma saiga kira ya shigo unknown number ne.
Dan haka batayi picking call É—in ba saboda tsarinta kenan, sai da aka jera kira wajen uku sannan da ta gaji da kiran ta saka Wayar a silent..
Ganin taƙi ɗaukar kiran da ake mata ne gashi kuma shi mai kiran yaƙi haƙura Yasa Afeefah da ringing ɗin wayar ya isheta ta ɗago tana kallon Lailah kana Ta ce "Lailah ta ana kiranki fah ko bakiji bane?."

Tsaki Lailah taja sannan Ta ce "kinsan dai bana ɗaukar unknown number ko?", "Ki ɗaga kiji ko waye mana tunda anƙi dena kira kikasani ko wani abu mai muhimmancine?",
Ya mutsa kyakyawar fuskarta Lailah tayi "banajin haka kawai dai mara aikin yine".

Saukowa Afeefah tayi daga kan bed É—in tana shirin É—aga kiran wayar ta yanke saboda haka Komawa tayi ta zauna ta ci gaba da latsa wayar ta, Lailah zatayi magana wani kiran ya sake shigowa, Picking Tayi amma batayi magana ba, ta dai saka wayar a hands Free.

Jin ba'ayi magana ba sai Faman ajiyar zuciya da ake saukewa yasa Tayi kamar zata katse kiran,da sauri Afeefah tayi mata alama da karta katse ta Jira tukunna.
Cikin wata irin murya mai sanyi daga can ɓangaren mai kiran wayar Yayi sallama.
Cikin ƙyawawan yaran mister mai ƙyau dake bedroom ɗin wato Afeefah da Lailah rasa wanda zai amsa sallamar akayi, Sai can Lailah tayi ƙarfin halin amsawa da...

Wslm ta faɗa a gajarce kuma a taƙaice sannan a fusace,wata kalar ajiyar zuciya aka kuma sauke wa ta can ɗayan ɓangaren mai kiran,Sannan aka fara magana kamar haka.

"Lailah ta to ya kike kin isa gida lafiya, inata kira baki É—auka ba har na karaya fah, sai naji kamar bansama shiga ba. Hala dai duk gajiyar birthday É—inne?."

Shiru yayi da maganar Jin kamar hankalin ta Baya kanshi Tunda batayi magana ba. "Hello Lailah ƙawa ta did you hearing me?, please say something mana!.

Da sauri Lailah da mamaki ya kusa kasheta ta ce "wrong number, Malam kai waye kuma sannan miye haÉ—ina da kai?",

Jin tana ƙoƙarin katse kiran ya sa shi faɗin Lailah Abubakar Mai Kyau koh ko ba ita bace?,
A mugun fusace Lailah Ta ce "ni ce sai akayi Yah Yah,huh Nace sai akayi YahYah zaka takumin fa, Tayi maganar a fusace domin kuwa akwaita da saurin hawa,kamar momy Rafi`at Mahaifiyarta.

Oh baki gane mai maganar ba kenan,Bangane ba,Oh sabbir salis mai Naira ne, Da muka haÉ—u dake wajen birthday party É—in classmate É—in ku, É—azunnan.

Dariya ne ya kusa kama Afeefah amma tayi saurin ƙumshe wa,Ita kuwa Lailah mamaki ya hanata cewa komai,"Kinajina kuwa sabbir ya faɗa daga ɓangarenshi.

Uhhhm ta faɗa a taƙaice tana hamman gajiya da wannan futile maganar.
"it's okay My friend Bacci kikeji bari na barki kawai,kiyi mafarkina fah kinji ko friend É—ita bye bye!!
Tana shirin yin magana ya katse kiran..
Baki sake Lailah take bin wayar da kallo tana mamakin yaushe har suka haÉ—u dashi wai har ta bashi numbar ta, ita da ko lambar namiji É—aya, babu a wayarta daga na dady saina uncle's É—inta da kuma YaYYinta maza na Dangi shikenan.

Ganin yadda Lailah take bin wayar da kallo kamar wacca bata cikin hayyacin yasa Afeefah taɓota....
Firgigit ta dawo hayyacin ta tana kallon ta, "menene Haka kuma ba saurayin ki bane zakiyi wani pretend a gaba na" Afeefah ta faÉ—a tana cin magani kamar da gaske....
Chapter 4 · 0% Book details