← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 96

Sashe 84

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayin da ita Nainarh ta Aura wani haifaffen ƙasar Eritrea. Wanda haɗuwar social media ce, harta kaisu ga Aure.
Duk da dai kafin Auren sai da aka sha fama da Momy Rafi'at domin taƙi yadda ne.
To daga baya haka ta haƙura aka yi ba yadda ta iya.
Yayin da ita ma Nailah ta Aura wani ɗan ƙasa Nigeria haifaffen Nasarawa State, mazaunin Lagos duk da Ita ma da farko Alhaji Abubakar Mai Kyau.
Yaso ya bada matsala, ace war sa bai amince da mijin da Nailah É—in zata aura ba, saboda Yanayin sana'ar sa, amma daga baya haka komai ya wuce aka sha shagalin biki.

- _-

Rayuwa ta ci gaba da gangarawa ta kowani ɓangare yau daɗi gobe babu, dama haka abin yake ba kullum ake cikin enjoying komai ba.

Shekarun Maleek Biyu da Barin Gida ba ko wai waye.
A lokacin ne kuma xixi ta kammala secondary school nata. Sannan ta ce ita a ƙasar france wurin Uncle Yunus take so ta ci gaba da karatunta, a can tare da Labiba ɗiyar sa wacca suke sa'anni ace war ta gaba ɗaya Gidan nasu babu daɗi tun Barin Buddy nasu.
To koda ta sama mahaifin su Alhaji Abubakar, da maganar da farko ƙin Yarda Ya yi saboda a tunanin sa Sanadin karatu a Abroad Babban ɗan sa Abdulmaleek Tarbiyar sa ta sama matsala.
Ita ma zaynerb kuma sanadin haka ta sama matsalar soyayya. Wanda nan gaba zamuji ainihin abin da ya faru da ita acan Amsterdam É—in.

A lokacin ba ƙaramin wani hali xixi ta shiga ba, dalilin hana ta zuwa faransa domin ɗaura karatun ta na degree.
A lokacin har rashin Lafiyar ƙarya ta kwanta dan dai kawai a barta ta tafi, aikuwa daga baya Alhaji Abubakar Mai Kyau, da yaga babu sarki sai Allah, haka ya barta ta tattare ya nata ya nata ta koma faransa. Wajen Uncle Yunus ta fara sabuwar Rayuwa. Yayin da gefe guda ita da ɗiyar Uncle Yunus Labiba suka fara karatun anan wata hamshaƙiyar jami'a na ƙasar faransa.

Yayinda suke karantar course É—aya.

Nigeria kuwa Rayuwar Ahalin Alhaji Abubakar Mai Kyau, ta ci gaba da tafiya salin alin. Yayin da aka kwashe tsawon shekaru uku hadda watanni da Maleek Yabar gida sai wannan karon ya dawo...💃💃

*Masu karatu idan nace zan ci gaba da tafiya cikin ainihin abin da ya faru a baya*.
To gaskiya ina ga har mu kammala wannan novel baza'a dawo cikin ainihin Labarin ba, saboda haka anyi min afuwa mu koma cikin ainihin Labari.
Yanzu dai kunji ainihin dalilin abin da Ya saka Maleek ya bar Gidan su tsawon shekaru uku da watanni sai wannan Lokaci ya dawo.
Kuma kunji dalilin da yasa Momy Rafi'at bata ƙaunar su Afeefah, saboda wai mahaifiyar su ta Aure mata miji.
Sannan kuma munji wani abu daga cikin ainihin dalilin da yasa Haleesat ta fara zuwa mashaya, wato Sanadin haÉ—uwarta dasu Zuree da Feenah da kuma Jenny.
Sannan again munji ainihin dalilin da Yasa Zaynerb ta dawo Nigeria.
Bayan kuma a Amsterdam ta fara karatu, wato dai Sanadin soyayya, kamar yadda nayi Alƙawari nan gaba zamu ji ainihin abin da ya faru da Zaynerb a can ƙasar NETH Babban Birnin ƙasar wato Amsterdam.
Haka ma Lailah munji wasu daga cikin silly. 😜 dalilanta da suka saka ta tsani soyayya, har ma da maza😕
Sannan kuma munji irin ciwon dake damun Jarumar mu.
To shin akwai maganin wannan ciwo nata ko kuma babu kudai kawai ku Biyo alƙalamin Nainarh Kd domin jin wannan ƙayataccen Novel Na musamman Wanda sai da a tsaya a Ta ce sannan kuma a tsaya aka zuba Basira wajen Taho muku dashi Labari mai Cike da sinqi sinqin chakwakiya_🤩_Cin Amana🤣_Yaudara😏_Zamba cikin Aminci🤕_Ban dariya obaaaaaaaaaa😆_Rikita Rikita🥴_____
Nishaɗantarwa🤪_Game da wa'azantarwa 😜_Buri💫_Fansa_makirci🤮_Hargitsi🤥_____
Game da Tsananin Zazzafar Soyayya Mai Ban sha'awa da Burgewa, da kuma tsindima mutum cikin Shauƙi ba tare da Da ya shirya ba. Labari Mai suna SARAUNIYAR KYAU 💋💋💋__THE GLAM QUEEN 👑💕🌹

💓💓ƚԋҽ ϝαʂԋισɳ ʂԋσɯ.💓💓

*PR£S£NT*
*Ci gaban Labari*

*_-_Masu Karatu, Ina Fatan Dai Baku Manta Ta Wajajen Da Muka Tsaya Ba, To Yanzu Dai Zamu ÆŠaura_-_*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Bayan sun shishshiga ƙayataccen palon, Gaba ɗayan su iyayen suka zazzauna saman Royal sofa's dake zagaye da ƙaton palon, Yayin da su kuma gaba ɗaya yaran suka zazzauna a ƙasa tsakiyar palon harda Maleek wanda kansa yake ƙasa cike da yasa nin komai da ya faru baya.

Yayin da ita kuma Afeefah wacca har zuwa lokacin bata farfaÉ—o ba, aka É—aurata saman doguwar kujera 3sieter Yayin da Momy Rafi'at ta zauna kusa da ita tana ma ta firfita sama sama.

Gaba ɗaya palon shiru ya ɗauka tamkar babu wani hallita mai rai ciki, sai da aka shafe kusan mintuna goma, a haka sannan Uncle Yusuf da ya kasance mutum ne shi mai bala'in sauƙin kai da kuma ƙaunar peaceble.

Gyaran murya Ya yi sannan ya kuma buÉ—ewa da addu'a bayan ya kammala suka shafa sannan ya kalla Maleek cike da kulawa ya fara magana kamar haka.

"Yanzu kai Maleek ka dawo gida Bayan É—aukar tsawon shekaru baka nan, shin zaka iya faÉ—a mana duniyar da kaje ko kuma wurin da ka tafiya ko waiwaye babu?."

Gaba É—aya mutanen palon ne suka mayar da hankulan su kan Maleek suna jira suji amsar da zai bawa Uncle Yusuf da ya yi masa tambayar.
Shikuwa Alhaji Abubakar, babu abin da yake sai faman sauke huci kurum yana kallon ÆŠiyarsa dake kwance bata ko numfashi.

Shiru Maleek ya yi tsawon mintuna uku sannan ya yi gyaran murya yana gyara Yanayin zaman sa ya fara magana cikin murya wacca dai Yanayin ta sai as low.

"Da Farko dai Bayan na Bar Gidan nan kai tsaye Airport na wuce nabi jirgin ƙasar Rasha, to koda na isa Rasha Ban tsaya komai ba. Kai tsaye na fara aiki a Babban asibiti dake ƙasar tsawon shekara ɗaya, sannan kuma na fahimci wani abu, cewar shi baturen mutum kwata kwata bashi da alƙawari.
Wato abin dai da ya faru shi ne, ina gabatar da aiki cikin gaskiya a ƙasar cikin Babban asibitin ƙasar, sai wata Rana ɗaya daga cikin manyan likitocin asibitin da yake ba musulmi bane, shiyasa bama wani jituwa dashi, daɗi da kari kuma na fahimci baya da wani hali na KIRKI..."

Katse sa Alhaji Abubakar Ya yi cikin sauri
"Okay ke nan kai É—in wani Halin kirki ne dakai. Yanzu kaine har zaka ce wani bashi da Halin kirki?."

Da sauri Uncle Yusuf ya katse Alhaji Abubakar cikin sanyin murya Yace
"Ina ga da kayi shiru mun gama jin abin da yake so ya faÉ—a mana."

Alhaji Abubakar bai tsaya sauraron maganar da Uncle Yusuf Yake ba, Ya kalla Maleek cikin daka tsawa yace "Yanzu me kake nufi?, kana nufin kace ka dawo Gidan nan ne, to a matsayin wane ke nan?, ni dai nasan bani da wani Yaro na miji duka Yarana mata ne, kuma ina ƙaunar su duka."

Jin abin da mahaifin nasu yake faÉ—a ne yasa gaba É—aya yaran nasa suka É—ago suna kallon sa, cike da tsananin tashin hankali.

Cike da nadama Maleek ya rarrafa kusa da mahaifin nasu ya kamo ƙafafunsa yana basa haƙuri kamar zayyi hauka cike da tsantsan nadama.
Yayin da shi kuma Alhaji Abubakar yake ture shi cikin tsananin fushi yana tuna duka abubuwan da suka faru baya tamkar yaune suke faruwa.

Maleek faÉ—i Yake yi "Please Daddy ka yafe min, wallahi na tuba, bazan kuma ba, domin nayi nadama highly."

Gaba É—aya yaran kuka suke bama kamar Zaynerb da Nailah har wani shiÉ—ewa suke yi saboda tsananin tashin hankali, tsoro suke karfa tarihi ya kuma maimaita kansa.

Ajiyar zuciya Alhaji Abubakar Mai Kyau, ya sauke a karo na babu a dadi yana kallon gaba ɗaya Yaran sa yadda suke kuka, shi uba ne dole yaji babu daɗi da ƙari ƙin yafewa Maleek da Ya yi bawai yana nufin baya ƙaunar sa bane ko kuma wani abun, kawai dai yanaso ya fahimci shin da gaske ya tuba ko kuwa.

Kallon Maleek dake hawaye kamar zararre, Uncle Yusuf Ya yi sannan ya masa umarni da ya koma ya zauna.

Komawa Maleek Ya yi kusa da ƙafafun mahaifin sa ya zauna dan Bala'i.🥵

Kallon gaba ɗaya mutanen palon Uncle Yusuf ya kuma yi sannan ya ƙara mayar da kallon sa, kan Alhaji Abubakar yana masa kallon nutsuwa, daga ƙarshe dai ya sauke idanun sa a kan Maleek.

Kiran sunan Abdulmaleek Ya yi har sau uku, yana amsawa sannan ya ci gaba da cewa.

"Yanzu dai mu a je maganar wurin da kaje gefe, a gaskiya gaba É—aya Ahali ba muji daÉ—in barin Gida da kayi ba, a kan wani dalili wanda bai kai ya kawo ba, sannan kuma yanzu da ka dawo, ka dawo ka ci gaba da Rayuwa da Ahalin ka ne, ko kuwa dai akwai wani nufi a tare dakai?."

Uncle Yusuf Ya yi masa tambayar yana kallon Maleek ɗinda ya yi shiru kansa a ƙasa.

"Please Uncle ayi min haƙuri na duka abin da ya faru baya, sharrin shaiɗan ne sannan kuma na dawo gida ne saboda na ci gaba da Rayuwa cikin Ahalina kamar kowa."

Wani ƙayataccen murmushi Mister Mai Kyau. Ya yi amma fah na iya gefan fuska, domin kuwa idan ba ƙura masa ido kayi ba, to ba zaka fahimci Ya yi murmushin ba, daga yadda fuskar sa take a tsume, wani sanyi yaji cikin zuciyar sa jin abin da Maleek yake faɗa, a fili kuwa kallon Maleek dake kallon sa. Ya yi sannan yana faɗin

"Indai kanaso na manta komai da ya faru a baya, na bari ka dawo ka ci gaba da Rayuwa cikin mu. Tofa sai dai idan ka amince zaka fito da matar Aure. Idan kuma baka da budurwa ka zaɓa cikin Ƴan matan dangi, duk wacca tayi maka."

Duk wannan maganar Alhaji Abubakar ya yima Maleek ne cikin kakkausar murya da kuma bada zaɓi.

Murmushin enjoying da kalaman É—an uwan nasa Uncle Yusuf Ya yi sannan Ya mayar da kallon sa a kan Maleek É—in.

"Ka dai ji da kunnen ka, abin da mahaifin ka ya faɗa, saboda haka yanzu zaɓi ya rage naka."

Shima Uncle Yusuf Ya yi maganar cikin gimtse fuska alamar dai babu wasa cikin maganar.
Chapter 84 · 0% Book details