← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 96

Sashe 73

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan Jaririyar ko, ita ake yiwa laƙani da kinfi nurul'in, Dan Allah please ku taimaka ku tayani kallon wannan haɗaɗɗiyar fatar nata wanda in banda shaining babu abin da take yi, ga manya manyan dara daran kyawawan fararen idanunta masu ɗauke da launin £ye ball's wasu masu shaining su ba blue color ba, kuma su ba green color ba, sannan kuma baza'a kirasu purple color ba, abin dai sai Wanda ya gani wallahi."

Gaba É—aya mutanen dake palon in banda dariya babu abin da suke yi.

Hajiya Zuwairiya ta ce "Ai ina faÉ—a muku wannan jikar tawa, sai an dinga haÉ—a mata da Addu'o'i domin kuwa wannan kyan nata ko, Humm hmmm."

Gaba ɗaya mutanen palon babu wanda bai magantu ba, sannan kuma bai susuce da wannan kyau kyawu irin na na wannan Jaririya ba, tana da kyau sosai, she is so cute and so sweet so sexy and adorable, so and and so ka.!! abin ko humm Alƙalamin Nainarh Kd ya yi kaɗan wajen rubuta kyau da kyawu irin na wannan Jaririya.....ʝυʂƚ ιɱαɠιɳҽ...🥰

Abubakar da tun É—azu ya yi shiru bai ce komai ba, amma idanun sa suna akan wannan kyakyawar furanya, ya sauke wata kyakyawar ajiyar zuciya na farin ciki sannan ya fara magana kamar haka..

"Kun san menene kuwa, jama'a?."

Dariya suka yi jin abin da yace kana suka haÉ—a baki wajen cewa "A'a a'a a'a...."

Yace

"Wannan kyakyawar furanya Insha Allahu wata Rana za'a wayi gari ta zama SARAUNIYAR KYAU ta duniya Insha Allahu Burina ke nan a kanta.📷💃😎

<<<{Tofah masu karatu, kundai ji Burin Mister Mai Kyau, a kan wannan Ɗiya tasa da masoyiyar matarsa son sa Hajarah ta haifa masa, shin Burin zai cika, ko kuwa dai. Akwai Ƙalubale, kudai kawai ku biyo wannan Ƙayataccen labari mai suna *💋SARAUNIYAR KYAU 💋* domin jin irin abin da yake ciki, sannan da darasin da yake tafe dashi 💃💃}>>>

Gaba É—aya mutanen dake palon suka É—auki sowa na farin ciki Jawaheer faÉ—i take

"Ina bayanka Yaya ni ma dai Burina ke nan, akan wannan ÆŠiyar tamu Ahaa muje zuwa *SARAUNIYAR KYAU*

Murmushin farin ciki Hajiya Zuwairiya tayi tana cewa
"To ai sai ku bar wannan Jaririya ta Huta, ga mahaifiyar ta can baku tambaya Lafiyar ta ba, kun tsaya a kan jaririyar ko?."

Dariya suka yi sannan Sakeenah ta miƙe tsaye da sauri tana cewa

"Ni Wallahi in banda Yanzu da kikayi maganar, ni harna manta da Hajarah mai jego, kyawun Jaririyar da ta haifa mana shiya saka hakan."

Tashi suka yi gaba É—aya suka nufa bedroom É—in da Hajarah take ciki

Kwance suka same ta tana kwasar baccin gajiya.
Zazzauna wa suka yi suma suka ci gaba da fira sama sama suna ko É—a kyau irin na wannan Jaririya.

Zuwa can wuraren goma na dare Hajarah ta farka aikuwa tayi kyakyawan gani gaba É—aya mutanen gidan zazzaune suna fira ga ÆŠiyarta da mijinta a gefanta murmushi kawai take yi na farin ciki.

Ganin ta farka yasa Abubakar ya yi murmushi da yake yana kusa da ita ne, a gefan gadon, cikin ƙasa da murya, yadda ita kaɗai zataji abin da zai faɗa Yace

"Nagode miki sosai da kika Haifa min wannan kyakyawar furanya, kyakkyawar Tauraruwa wacca hasken ta yake haske wuri, nagode miki sosai kin san kuwa wani suna zan saka ma ta?."

Fuskar ta É—auke da matsanancin farin ciki na yabon da godiyar da mijinta yake ma ta ta girgiza masa kai alamar "A'a,"
Murmushi ya yi sannan ya matsa da Bakin sa dai dai sai tin kunenta ya raÉ—a ma ta a kunne.

Dariya tayi ba shiri wanda sautin dariyar da tayi Yasa gaba É—aya mutanen ÆŠakin juyowa suna kallon ta domin kuwa babu wanda ya lura da tashin ta.

"Ah ah kunga masoyan zahiri, wato ana jegon mah ana taɓa love ne ko?, Aikuwa Abin naku ya ƙayatar dani sosai, na ɗauki course daga Yau."

Cewar Jawaheer cikin dariya, "Wato ma saka mana ido kikayi ko?."

Hajarah ta tambaya tana jefa ma ta hararar wasa, Jawaheer ta ce "A'a nadai gani ne kawa Aha." 🤣

Habba ai nan kuma wata sabuwar fira ta ɓalle a tsakanin su, gaba ɗaya cike da nishaɗi yi suke yi kamar babu gobe, har wuraren ƙarfe goma sha biyu na dare.

Sannan ne kuma suka fara shirin komawa bedrooms É—in su domin kwanciya bacci, gaba É—aya suka fiffita bayan sunyi wa mai jego da jaririyarta sallama.
Suka bar Abubakar da Hajiya Zuwairiya a cikin bedroom É—in.

Miƙewa Abubakar ya yi kamar mai neman wani abu. Da sauri ya fakaici idon Hajiya Zuwairiya ya haye saman bed ɗin.
Cikin sauri Hajarah ta kalle sa ganin abin da ya yi kana cikin ƙasa da murya ta ce

"Menene haka kuma?, in ace kaima ɓangaren ka zaka wuce, sai kuma gobe ko?."

Dariya ya yi sannan shima cikin ƙasa da murya Yace

"Na fasa anan zan kwana, tare da mata ta da ÆŠiyata domin kuwa wani kalar kewar su nakeji, tun kafin na tafi na barsu."

Shiru yayi kamar mai tunani, sai can ya kalle ta kamar yadda ita ma ta ƙura masa ido tana kallo, cikin sanyin murya yake faɗin

"Kin san menene kuwa?."

Bai jira ta amsa ba, ya ci gaba da cewa,
"Jina nake kamar bani ba, ina jina gaba É—aya jikina a sake, sannan kuma kamar wani abu mara daÉ—i zai faru, gaba É—aya a sanyaye nake wallahi."

Ƙura masa ido Hajarah tayi tana kallo Sannan ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin

"Duk wannan wasi-wasin aikin sheÉ—an ne kawai, ka karanto Addu'o'i komai zayyi Normalcy Insha Allah." ta ci gaba da cewa

"Ka tsaya da kyau ka saurari bugun zuciyar ka ka nutsu zaka fahimci aikin sheÉ—an ne kawai?."

Murmushi ya yi kana Yace

"Ina son ki sosai sosai fi ye da yadda kike sona fa."

Dariya ita kuma tayi sannan ta basa amsa da

"Ni kuma ina ƙaunar mijina abin alfaharina a kullum da ko yaushe ina ƙaunarka obaa, fi ye da ƙaunar da Lailah da Majnun suke ma juna Tabbas." Tayi maganar tana Rumgumo sa tightly.

08081129487
Via WhatsApp
For more enquires
The Nainarh Kd

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

Idan kin shirya Payment, just pay with this details.

_-_-_-_-_-_
*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*

Page *81&82*

Ganin dai abin nasu bana ƙarewa bane. Yasa Hajiya Zuwairiya da tun hawar Abubakar saman bed ɗin, take ankare dashi, miƙewa tsaye tana faɗin
"Toh idan an gama rashin kunyar a gaba na, sai a tashi a tafi inda aka fito, domin zan kulle É—akin."

Da sauri suka juyo suna kallon ta su biyun, aikuwa ta galla musu harara duka.

Ƙasa da kai Hajarah tayi cike da kunya, shikuwa Abubakar ko'a jikin sa ya sauko daga saman gadon idanun sa akan Hajarah harya fi ce daga bedroom ɗin, yana yiwa Hajiya Zuwairiya dariyar ƙeta.

Ajiyar zuciya Hajiya Zuwairiya ta sauke sannan ta kalla Hajarah tana qalla ma ta harara sai dai bata ce komai ba, taje ta kulle ɗakin, ta dawo ta koma can gefe saman wata doguwar stool mai faɗi ta kwanta, domin kuwa wani kalar bacci mara misaltuwa take ji kamar Ƴar maye, Aikuwa ko mintuna biyar batayi da kwanciya ba, bacci ya yi gaba da ita.

Ajiyar zuciyar ita ma dai Hajarah ta sauke sannan ta sauko daga saman mattress É—in, ta shiga bathroom, ta É—auki tsawon mintuna goma a ciki.

Jiyo kukan Jaririyarta da tayi ne, yada da sauri ta kammala abin da take yi sannan ta fito, ta ƙarisa saman gadon jariran ta ɗauka Ɗiyar ta ta tana ma ta wasa, daya ke Jaririyar taƙi karɓan Breast ɗin ta, tun ɗazu kuma ba'asan dalili ba, shi yasa ma batayi tunanin bata ba.

Sai da ta tabbatar da jaririyar ta ta tayi bacci, sannan ta kwantar da ita, kana ita ma ta koma ta kwanta saman bed, bayan tayi duka abin da take yi a al'adarta kafin ta kwanta, bata daɗe da kwanciyar ba, ita ma wani bacci mai ƙarfi Ya yi gaba da ita.

*WASH£-GARI*

Wuraren ƙarfe Bakwai na safiya, Sakeenah ta fito daga bedroom ɗin da ta sauka, jikin ta sanye cikin dogon hijjab blue color har ƙasa.
Hamma kawai take yi domin kuwa baccin bai isheta ba ta tashi, amma duk da haka sai da ta makara.

Tasha mamaki sosai ganin Palon ba kowa, bata kawo komai a Ranta ba, ta wuce kai tsaye tabi ta wani korido Wanda zai sadata ɓangaren Hajarah.

Knocking ƙofar bedroom ɗin tayi, amma shiru ba'a zo an buɗe ba.

Ƙara yi tayi nan ma shiru, ganin haka yasa ta ɗan tura ƙofar da hannunta, aikuwa sai ƙofar ta buɗe.

Sallama É—auke a Bakinta ta shiga bedroom É—in, amma sai taji ba'a amsa ma ta ba.
Ƙarisa shiga tayi aikuwa tayi kyakyawan gani can saman doguwar stool mai faɗi ta hango Hajiya Zuwairiya tana ta faman sauke snored bacci ya yi daɗi.

Dariya Sakeenah tayi tana faÉ—in "Ashe dai bani kaÉ—ai na makara ba, tunda dai ga mai jego da Hajiya suna faman sauke numfashi bacci ya yi daÉ—i da alama."

Qarisa wa gadon da Hajarah take a kwance tayi, sannan ta kai hannu ta fara É—an bubbuga gadon. Tana dai yi irin idan mutum yana so ya tashi wani daga bacci.

Amma ga mamakin ta sai taji shiru Hajarah bata farka ba, É—an waro ido tayi waje, sai kuma a fili take faÉ—in

"Haba Sakeenah sai kace ba mace ba, don't be shy mana haba."

Tayi maganar tana kuma ƙoƙarin tashin Hajarah daga bacci.

Sai dai kuma har lokacin ko motsi Hajarah ba tayi ba zuwa, taƙin fa Sakeenah ta fara tsorata domin ko dama can akwai ta da mugun tsoro.

Hannu na rawa takai sai tin hancin Hajarah domin taji ko tana numfashi, sai dai kuma wani ƙarin tashin hankalin shi ne ko numfashi bata ji alamar tanayi ba, izuwa lokacin zufa kawai take haɗawa, ga jikinta dake faman rawa kamar mazari.
Fa sauri ta kai kunnen ta saitin hancin Hajarah, ko dai zata ji wani alamar amma kuma har lokacin shiru.
Chapter 73 · 0% Book details