← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 96

Sashe 41

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Humaira ta kuma bata amsa, Jiddarh ta ci gaba, "idan kuma kece kika cinyeni, wato kika rigani ƙarisawa, sai ki zaɓa abin da kikeso a kayana, ni kuma zan baki, ba tare da wani musu ba."
Murmushi Humaira tayi tana faɗin, "nidai wannan ƙaton frame ɗin, dake manne a bangon bedroom ɗin ki, zaki bani idan naci, don shi nakeso."
"wanne kenan?." Jiddarh ta tambayeta tana ma ta kallon 🤬.

Humaira ta ce "wannan dai mai É—auke da hoton Babban birnin Indonesia 'JAKARTA',"
Jiddarh ta ce "kima dena sa ranki akan wannan a bun Tarihin a gurina, dan ba samu zakiyi ba,"
Humaira ta ce "to a gwada mana, a gani, ai sai da kira karen bebe yake gane gida." jiddarh ta ce to a gwadan mana."

Humaira ta fara ƙirƙe, "One Two Three Go.!"
Da gudu suka nufa ƙofar palon, nanfa aka fara daga ƙarshe dai da Jiddarh taga alamar dai, Humaira da gaske take zata wuce ta.
Ta dage iya ƙarfinta ta qwala ihu, wanda hakan yasa Humaira juyowa slowly tana kallonta, wannan juyowar da Humaira tayi, shiya ba Jiddarh damar kwasa da gudu, ta isa bakin ƙofar palon, tana sauke haki.

Ganin kalar wayon da Jiddarh ta haɗa, yasa Humaira ta sadaƙar kawai sai ta dena gudun ta tsaya ta huta, sannan ta ƙariso bakin ƙofar ta tarar da Jiddarh sai faman ihun murna takeyi, tana faɗin "nayi winning na cinye, dan haka dole a bani guitar."

Ita dai Humaira bata kulata ba, ta buɗe ƙofar ta shiga ciki, ganin haka yasa ita ma Jiddarh tabi bayanta tana faɗin ta jirata.

Suna shiga a palo suka tarar da Auntie da Abba zaune daga can gefe, suna cin breakfast a ƙasa. Da sauri Jiddarh ta ƙarisa gurin, tana faɗin.
"Abba, yau kuma anan ake karin kumallon?."
Alhaji Komai Naka, yana murmushi ya shafa kanta yace. E, Mamana, angama wasan golf É—in kenan?."
Murmushi tayi ta ce "E, Abba, yanzu ma wanka zanje nayi," kallon Auntie tayi ta ce "ina kwana Auntie," fuska cike da fara'a Auntie ta amsa ma ta.
Sannan ta ce "ai ina jira ku gama gaisawa ne, tukuna." murmushi Jiddarh tayi.
"Auntie kenan, bari na haura sama nayi wanka, na dawo akwai labari fa."
Tayi maganar tana hawa bene bedroom, ta shiga tun a palo ta fara rage kayan jikinta, tana shiga bedroom É—in kuwa kai tsaye bathroom ta shige.

Takai tsawon mintuna talatin, sannan ta fito sanye cikin bathrobe milk color, ga wani ƙaramin towel milk tana goge sumar kanta dashi, zama tayi a kan swivel chair na dress mirror, sannan ta ɗauki hairdryer ta busar da dogon gashin kanta, kana ta ɗauki hair brush ta tace gashin, lotion ta shafa kala kala kana tayi light make up.

Ba wani sosai tayi kwalliyar ba, hoda kawai ta shafa sama sama sai kwalli da ta saka a idanunta, sai kuma lip gloss da ta shafa a saman siraran laɓɓanta.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya cikin riga da skirt na a tamfa mai launin kore da ruwan hoda, rigar tayi ma ta ɗass a jiki haka ma skirt ɗin ribbons ta ɗauka mai launin kore da ruwan hoda suma, sannan ta kamo dogon gashin kanta ta ɗaure da kyar saboda tsayin gashin, kallabi ta ɗauka babba ne sosai dan sai yafi rabin falle.

A hannunta ta riƙo kallabin ta fito palon bedroom ɗin ta, a gaban madubin dogon yaro ta tsaya, tana kici kicin ɗaura ɗan kwallin, amma ta kasa, haka dole ba yadda ta iya ta fito palon ƙasa.
Da sauri ta ƙarisa gurin su Auntie dake saman 3sieter ita da Abba suna kallon wani Indian Drama 'Bruce Lee The Fighter'.{ Na Ram Charan Da Rakul Preet Singh.} dayake ranar saturday ne ɗarshen mako ba zuwa office.

Da sauri ta ƙarisa gurin Auntie ta miƙa ma ta ɗan kwallin sannan ta ce "Auntie ayi min taimakon muslunci, kallabi yaƙi ɗauruwa min fa 😂.

Karɓar ɗan kwalin, Auntie tayi tana mita faɗi take, "ni dai Jiddarh banga ranar da zaki girma ba, koda yaushe baki iya ɗaurin kallabi ba, haka za'ayi auren baki iya komai ba?."
Tayi maganar a yayinda take É—aura ma ta kallabin. Dariya Jiddarh tayi ta ce.
"Auntie kenan, ana zaune lafiya, zaki kawo wani zancen aure kuma."

"au kina nufin dai bazakiyi ba, sai dai ki ƙare a nan gidan, to baki isa ba, don rana ɗaya zan haɗaku da Humaira na aurar." Alhaji Jafar ne, yayi wannan maganar cike da zaulaya.

Dariya kawai Jiddarh takeyi, bayan Auntie ta kammala ɗaura ma ta ɗan kwalin, ta dawo kusada Abban ta zauna a tsakiyar su, sannan tace "Abba kenan, ae Aure lokaci ne dashi ba'ayin shi lokaci bayyi ba dole sai an jira. ka sani lokaci ɗaya wani zayyi wuff dani 😄."

"Kuma fa, kin faÉ—a gaskiya sister shiyasa nakeson ki, domin akwai ki da faÉ—in gaskiya, a koda yaushe, sannan komai rintsi."
Humaira ce tayi maganar a yayinda take saukowa downstairs hannayenta ƙiqe da wani abu ta ɓoye a baya, ita ma kalan kayan jikin Jiddarh ne a jikinta ƙarisowa palon tayi, sannan ta zagayo da hannunta dake riƙe da guitar waje.

Miƙawa Jiddarh tayi tana faɗin, "ga kyautar gasar da kika ci fa, duk da dai kinyi zamba ciki."
Da sauri Jiddarh ta karɓa tana ma ta godiya cike da farin ciki.

"keda kika ci gasar tsere, miye na min godiya, ai keya kamata ayima godiyar."
Cewar Humaira tana zama a 1sieter. "Wani ƙoƙarina ba wani ƙoƙarin da nayi, nida nayi cuta a wasar."
Jiddarh tayi maganar tana komawa ta zauna ita ma saman 2sieter, Humaira ta ce "a kullum Jiddarh ƙara burgeni kikeyi, saboda akwai ki da faɗin gaskiya.

Alhaji Jafar yace "ai haka a keso koda yaushe mutum ya kasance mai faɗar gaskiya a rayuwar sa🤳.

ƚԋҽ ɠʅαɱ ϙυҽҽɳ

Ⴆყ

💅тнє ɳαιɳαɾԋ ƙԃ💅

𝚖𝚒𝚜𝚊𝚕𝚒𝚗 𝚔𝚊𝚛𝚏𝚎 𝚝𝚊𝚔𝚠𝚊𝚜 𝚍𝚊 𝚛𝚊𝚋𝚒 𝚗𝚊 𝚍𝚊𝚛𝚎

Afeefah tana zaune a palo saman doguwar kujera mai mazaunin mutum É—aya.
Hannunta riƙe da Alqur'ani mai girma, tana karatawa cikin zazzaƙar muryarta.
Yayinda Deejarh dasu Lailah suke zazzauna a sauran kujerun suma alqur'ani mai girma ne, a hannunsu suna tilawa a kalla sunkai mintuna talatin sunayi, kafin suka idar a tare sannan Afeefah tabi duk ta karɓa alqur'anan dake a hannayensu, ta mayar ma da kowa bedroom ɗinshi, sannan ta dawo suka ci gaba da fira.

Suna cikin yi saiga Mister Mai Kyau, da Mrs Mai Kyau, sun shigo palon a tare, da alama daga ɓangaren Daddyn suke.

Guri suka samu suma suka zauna a saman 3sieter ganin haka yasa su Zaynerb suka koma ƙasa suma suka zazzauna, sai ya kasance Daddyn da Momy Rafi'at suna daga saman kujera su kuma.
Nainarh, Nailah, Haleesat, Zaynerb, Afeefah, Lailah sai Deejarh suna daga ƙasa cikin girmamawa suka gaisar dasu suka amsa cike da kulawa.

Daddy da yake cikaken ɗan boko ne, na bugawa a mujalla, gashi kuma mai dukiya lamba ɗaya akaf faɗin Nigeria. Ga kuma Momy Rafi'at ita ma cikakkiyar likata ce, wacca take da hospital nata na ƙashin kanta a garin Abuja, ga ilimin boko da ya ratsata ciki da wajen ta.

Kallon su Daddyn yayi yana murmushi, sannan ya mayar da kallonshi akan Afeefah.

"Shalelen Daddynta."
Ya kirata dq sunan da yafi yawan kiranta dashi, tana murmushi ta amsa da, "na'am Daddyna,"

Daddyn yace

"Tomorrow is championship day, toh a halin yanzu ya ya kike jin kanki?."

"Cike da farin ciki Afeefah ta ce "ai Daddyn ina faɗamaka, jina nake a sama, sai naji kamar gari ya waye na buɗe ido, na ganni a filin gasar, jina nake a sama can ƙololuwa fa."

Da sauri Deejarh ta ce "shine kuma muke ganin ki anan, kuma naji kince jinki kike a sama?."

Dariya sukayi gaba É—aya Lailah ta ce "Deejarh kenan idan mutum yace yana jinshi a sama, yana nufin bazai iya bayyana irin farin cikin da yake ciki ba. Misali idan wani abu na farin ciki ya sameshi kuma sayya kasance wannan abun yana da muhimmanci sosai a gurin shi, toh ina fata dai kin fahimta?."

Dariya Deejarh tayi tana cewa, "sosai ma, Auntie Lailah nima jina nake a sama fa."

"Saboda me?,"

Nainarh ta tambaya, Deejarh ta ce "saboda gobe Balarabiyar India zataje gasar sᴀʀᴀᴜɴɪʏᴀʀ ᴋʏᴀᴜ😆.

Dariya suka kuma yi, nan dai suka ci gaba da fira sosai, basu suka tsagaita ba, har sai da Daddyn ya du ba, wristwatch É—in dake manne a tsintsiyar hannun shi, yaga lokaci yaja da yawa sannan yace, a tashi domin a kwanta, sannan sukayi wa juna sallama ko wacce ta shige bedroom É—inta.

AF££FAH

Tana shiga bedroom É—in ta wanda ya gaji da haÉ—uwa, kai tsaye bathroom ta shige a kalla takai fifty minutes tana wankan sannan ta É—auro alwala ta fito sanye da bathrobe light blue.

saman stool na dress mirror ta zauna, tana goge sumar kanta mai yawa da kuma tsayi santsi game da taushi ga wani ƙamshi na musamman da yake fitarwa, da wani farin ƙaramin towel, dake hannunta takai minti goma tana kuma gyara gashin, sannan ta shafa lotion sama sama a fatarta mai taushi da santsi har wani shaining takeyi da glowing, saida ta kammala shafa lotion ɗin, sannan ta saka lip gloss a red lips ɗinta...

https://chat.whatsapp.com/FlMq3Ol15mlBd3nRTr9c1t

*💋💋SARAUNIYAR🎀KYAU💋💋*

______________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

*Page 37&38*

Wardrobe ta buÉ—e ta ciro sleeping dress, shiryawa tayi cikin vest red color, sai kuma wando crazy iya gwiwa red color, ribbons red colors ta É—auko ta tufke gashinta. Bayan ta gama ta saka hula ita ma red color.

Saman bed ta koma ta kwanta cike da zumuɗi pillow ta rungumo a chest ɗinta, ta kwantar da kanta saman mattress, bacci takeso yazo ya saceta, kodan gobe ta farka da wuri amma ina baccin yaƙi zuwa.

Ganin baccin yaƙi zuwa yasa ta janyo wayar dake gefe, ta shiga £nglish stories ta fara karanta wani english novel TH£ KING AND HIS HAWK.

Labarin yana nishadantar da ita sosai, har lokaci yaja bata sani ba, sai da taji ta fara gyan gyaɗi sannan ta haƙura ta mayar da wayar a ma'ajiyar ta, kana ta janyo blanket ta lulluɓa addu'a tayi kana ta safe jikinta tabi lafiyar bed😎
Chapter 41 · 0% Book details