← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 96

Sashe 50

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Janyo swivel chair na Dress Mirror tayi sannan ta zauna akai tana fuskantar Mirror, Hairdryer ta É—auka bayan ta jona a charge ta fara drying hair É—inta cike da jindaÉ—i.
Ta É—auki lokaci tana hakan, sannan ta É—auki Hair Brush bayan ta mayar da Hairdryer É—in ma'ajiyar shi, sai da ta ta je sumar kanta yadda zata iya sannan ta shafa lotion, bayan ta gama bata tashi daga wajen ba, sai da ta tsaya tayi make-up sama sama, domin kuwa ba wani iyawa tayi ba, danma Afeefah tana É—an koya ma ta ne.

Powder ta fara shafawa sannan ta zizara kwalli a idanunta, sai kuma ta saka jam baki Maroon color, harta ɗauka Masraca zata saka a idanun ta sai kuma ta fasa, a fili ta ce "Ba sakawan da zanyi Natural gashin ido nawa ma ya isheni Blush ta ɗauka wato barbaɗa kumatu a hausance😘 ta barbarɗe kuwa a fuskar ta da ya ke fara ce sai yayi ma ta kyau sosai.

Tashi tayi ta nufa Wardrobe ta buɗe sannan ta ciro tufafin da zata saka cikin ƙaramin lokaci ta shirya cikin £nglish Gown Maroon color mara hannu iya gwiwa, sannan ta saka Dogon wando shima Maroon color wanda ya matseta Ribbons ta ɗauka guda uku Maroon color da fari sai black color.
Gaban Dress Mirror ta dawo kana ta kamo dogon gashin kanta na fulanin ainihi ta tufke da Ribbons É—in da kyar.

Ɗaukar after dress na Gown ɗin dake jikinta tayi Maroon color mai adon flowers pink and stones sky Maroon tayi, ta saka sannan ta ɗauki flat shoes glitter stilettos mai shaining launin sky Maroon ta saka a madaidaitan ƙafafunta.

Komawa tayi ta buÉ—e Wardrobe ta ciro wani abu a ciki sannan ta rufe, cikin trouser pocket É—inta ta saka abin da ta É—auka.

Bakin ƙofar Bedroom ɗin ta dawo ta tsaya tana so ta fita amma tana jiyo muryoyin mutane kala kala a palo gashi batasan kowa ba a ciki dan bataji muryar ƴan gidan ba, a cikin muryoyin da take iya jiyowa daga gurin da take a tsaye.

Daurewa kawai tayi ta murza key ɗin dake a jikin ƙofar sannan Door ɗin ta buɗe.

A hankali ta zura kanta ta waje tana leƙen palon, ganin da tayi kamar hankalin mutanen palon baya ata wurin da take, yasa tayi shahadar fitowa gabaki ɗayanta.

Cikin sanɗa take taku a palon duk dan kar a ganta, kai tsaye Bedroom ɗin Afeefah ta nufa, cikin sanɗa takai hannu zata buɗe ƙofar Bedroom ɗin kenan.

Tajiyo wata murya ta bayanta, cak ta tsaya ta kasa juyowa sai da taji an kuma magana sannan ta juyo da kanta a hankali tana fuskan tar mai maganar, amma kuma idanunta a rufe ƙam.

A hankali ta buÉ—e kyawawan idanunta ta saukesu saman fuskar wata kyakyawar matashiyar budurwa dake tsaye a gabanta tana binta da kallon rashin sani.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Sunana Khadeejah bawai 'Ke! ba."

Da tsananin mamaki budurwar take kallonta sai kuma ta ce "Khadeejah kuma dama akwai budurwa kamar ki, anan gidan?,"

Murmushi Deejarh tayi sannan ta bata amsa da "A'a ni baƙuwa ce ae, shiyasa baki sanni ba."

"Ohoo, to meyasa kike sanÉ—a kamar mara gaskiya.?"

Budurwar ta tambaye ta tana kallonta, dariya Deejarh tayi ta ce

"Balarabiyar India nakeso naba tsoro ai,"

"Balarabiyar India kuma, wacece ita. Kodai Auntynki ce?."

Budurwar ta kuma tambayarta tana dariya dan da alama ita ma gwana ce wajen surutu.

Cike da gajiya Deejarh ta ce "E, mana Balarabiyar India ae yayata ce sosai ma, uwa É—aya uba É—aya muke da ita."

Tayi maganar tana juyawa ta buɗe ƙofar Bedroom ɗin Afeefah, ta shige ciki tabar budurwar tsaye a wurin.

Tana shiga Bedroom ɗin ta sauke Ajiyar zuciya, sannan ta ƙarisa shiga ciki, can saman doguwar kujera ta hango Lailah zaune taci ado iya ado, ga tsadaddiyar wayarta a hannunta tana kafta selfie, daga gefe kuma Afeefah ce tsaye gaban mirror tana goga kwalli a kyawawan idanunta.
Suna taɓa fira da Lailah ɗin sunyi kyau sosai cikin the same shiga komai kala ɗaya, sai dai kalar ɗinki da ya banbanta, domin kuwa Lailah tana sanye ne cikin riga da skirt na atamfa ga ɗaurin ɗan kwali nan da tayi ɗaurin ture kaga tsiya mai style, fuskar ta tasha make-up, sai kuma Afeefah sanye cikin doguwar riga atamfar irinna Lailah rigar atamfar ammata ɗinki mai style na eshap wacca ta ma ta kyau sosai, sai dai saɓanin Lailah, ita Afeefah hular bat ce akanta golden color, saman hular an rubuta beauty ga atamfar jikinsu golden mai tsadar gaske, gaba ɗayansu sunyi kyau kai saika rasa wacca tafi ƴar uwanta kyau a ciki.

Cikin sanÉ—a Deejarh tabi ta bayan kujerar da Lailah take akai, taje ta tsaya ta bayan Afeefah tana dariya, ta mirror Afeefah ta hangota, murmushi tayi ma ta tana faÉ—in "Ke kuma yaushe kika shigo bamu sani ba?."

Juyowa Lailah tayi domin taga wacca ta shigo, daidai lokacin Deejarh take faÉ—in "E, mana cikin sanÉ—a na shigo, dan naga mutane da yawa a palo, kuma duka bansan su ba, shiyasa nazo nan fa."

Dariya Afeefah tayi tana cewa "Indai kinaso ki sansu yanzunnan zaki sansu duka Insha Allah."

Da zaƙuwa Deejarh ta amsa "E, inaso na sansu dukansu gaskiya."

Juyowa Afeefah tayi tana fuskantar Deejarh ta ce "To Ƴan Mata ya ya nayi kyau kuwa?."

ai ba Deejarh ba hatta Lailah dake zaune batasan lokacin da ta miƙe tsaye ba, ta ƙariso wurin Afeefah ɗin, bakinta tana mai furta kalmar

"Masha Allah."

"Nima dai yau bari na qwada kiranki da wannan sunan gaskiya, cikin washe baki Lailah ta ce

"Balarabiyar India kinyi kyau sosai sosai, idan nace sosai to ina nufin over fa, a gaskiya wannan kyawun bazai wuce a banza ba, dole sai munyi pictures kala kala da *SARAUNIYAR KYAU* ta Garin Abuja."

Tayi maganar tana kuma shiga camera ta wayarta.

Dariya kawai Deejarh da Afeefah sukeyi ganin yadda Lailah duk tabi ta ruÉ—e na ganin tsantsan madarar kyau wajen Afeefah.

Ƙarisowa wurin Lailah tayi sannan ta ce "To ku shirya muyi pictures na tarihi domin wannan kyawun dole saida pictures zafafa."

Gyarawa sukayi gaba ɗaya za'a fara kafta hotuna, da sauri Deejarh ta ce "Nifa kunsan bani da tsayi bazan kai tsayin ku ba, ya ya za'ayi kenan?."🤣

Dariya Lailah tayi ta ce "To ki hau kan kujerar mirror mana,"

Aikuwa Deejarh bata jira komai ba, ta kwantar da stool na Dress mirror sannan ta hau kai, suka fara kafta selfie's kala kala iri iri, mai kyau, da mara 😏 sai da sukayi ya ishesu.

Sannan Afeefah ta ce "A barshi haka ana jiransu a waje, ɗaukar scarf ɗinta mai adon stones tayi ta yafa, ita ma Lailah ta ɗauki nata golden color ta yafa a gefan kafaɗarta, sannan suka nufi ƙofa a tare zasu fita.

Kallon Deejarh Afeefah tayi tana faɗin "A haka ne zaki fita da gashi a waje kai ba hula. kamar wata 🤥?."

Dariya Deejarh tayi tana mai bawa Afeefah amsa da
"Balarabiyar India mana, nafa saka Ribbons har guda uku na tufke, ae shikenan sun isa."

"To dan kin saka Ribbons kin tufke sai akace ki fita a haka, ko bakisan akwai maza ba a palon?."

Wannan dai dariyar ta ƙauyanci Deejarh ta kumayi ta ce
"To ai naga ni yarinya ce, ba dole sai na saka mayafi ba."

''Ta ina kike yarinya bayan kin fara Breast haka ki ji ki fa."

Lailah tayima Deejarh tambayar iya gaskiyar ta.

Cike da kunya Deejarh ta rufe ido wai kunya, kana ta ce

"Auntie Lailah mana,! bakyajin kunya wai?,"
Lailah ta ce
"Kunyar mai zanji ko zakice baki fara bane, kujimin yarinya kam da wani pretending."

Qara rufe fuska Deejarh tayi ta ce 'Kai Auntie Lailah Allah kina bani kunya da yawa fa "

Dariyar mugunta Lailah tayi "Ashe dai kinada kunyar."

Dawowa wurin Afeefah tayi hanunta riƙe da hular bat sky maroon, miƙawa Deejarh tayi tana faɗin

"Oya saka mu tafi."

Amsar hular Deejarh tayi ta saka, Lailah ta kuma gyara ma ta gashinta da ya sauko har gadon bayanta sannan suka fita a tare.

Tun kafin su ƙarisa palon ƙamshinsu ya isa hancunan mutanen da ke zazzaune a palon.

Habba ae nan kallo ya koma sama wai shaho ya ɗau giwa.🤐

Gaba É—aya mutanen palon suka juyo suna kallon su fuskar ko wannensu su cike da fara'a da walwala, wata daga cikin Æ´an matan ce tayi magana

"Amazing kunga *SARAUNIYAR KYAU* ta iso tana baza ƙamshi."

Gaba ɗayansu su ukun suka sama wuri a 3sieter suka zazzauna nan suka shiga gaisawa da mutanen palon cike da farin ciki suke amsawa amma yawancinsu idonsu yana akan Deejarh wacca take zaune kusada Afeefah tayi tsumu da ita kamar tsumma a randa 🤓

Afeefah ta lura da irin kallon neman ƙarin bayanin da mutanen n palon sukeyiwa Deejarh, amma ta sha re suka ci gaba da fira yayinda Deejarh take buga game na *Streetchaser* da wayar Afeefah.

Suna zaune sai ga mazan sun shishshigo dama can suna part É—in Daddyn ne gaba É—aya suma suka sama wuri suka zazzauna dayake palon Babba ne sosai kuma kujeru set biyu ne, yasa duk ya ishesu suka zazzauna nan suka shiga sabon gaisha gaishe yayinda Deejarh take buga game É—inta hankali kwance tunda ta gaishesu suka amsa.

Wata ce daga cikin ƴan matan ta gaza haƙuri ta kalla Haleesat tana tambayarta

"Wai Leesat a'ina kuka samo wannan Beautiful Baby É—in, Æ´ar Kyakkyawa da ita?."

Tayi tambayar tana nuna Deejarh sai kuma hankulan gaba É—aya mutanen palon ya dawo kan Haleesat É—in suna jira suji mai za ta ce, ganin ta kasa magana ne sai dai ta kalla Deejarh ta kalla mutanen palon.

Yasa M.m.k gyaran murya sannan yace "ÆŠiyata ce sunanta Khadeejah."

Kallon Afeefah yayi yana murmushi yace "Shalele yima É—iyata Khadeejah bayanin kowa da kowa."
Chapter 50 · 0% Book details