← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 96

Sashe 74

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A mugun tsora ce ta fara ja da baya, sai kuma da gudun gaske tabar wurin, ta ƙarisa wurin da Hajiya Zuwairiya da take a kwance, ta fara bugunta cikin matsanancin kuka da tashin hankali take tashin ta, ganin ko motsi taƙi yi ne yasa ta ƙarisa wurin wani ɗan madaidaicin fridge a ɗakin ta buɗe, sannan ta ciro ruwa mai sanyi a ciki, kana ta dawo ta buɗe gorar ruwan ta watsawa Hajiya Zuwairiya a fuska.

A firgice Hajiya Zuwairiya ta tashi daga zaune tana karanto duk Addu'ar dake zuwa bakinta, sai da ta É—an dawo nutsuwar ta sannan ta lura da Sakeenah dake faman rizgar kuka tamkar ranta zai fita.

"Ke, lafiyarki kuwa, Menene ya faru kike wannan kuka kamar anyi miki mutuwa?."

Hajiya Zuwairiya ta tambaye ta hankalin ta a É—an tashe.

Sakeenah bata tsaya amsawa Hajiya tambayar da take ma ta ba, ta kamo hannunta ta ƙarisa da ita bakin gadon da Hajarah take kwance, sannan cikin kuka da wahalar fitar numfashi taƙe faɗin

"Hajiya Dan Allah ki duba Hajarah taƙi tashi fa, tun ɗazu, tsoro nakeji kar mu rasa ta."

Da jin haka yasa Hajiya Zuwairiya ta ƙarisa wuprin Hajarah ɗin nan ta shiga duba ta cikin sauri.

A hankali a hankali ta fara ja da baya babu abin da take karantawa a bakinta sai kalmar "Inna lil lahi."
Har ƙarshe saboda tsananin tashin hankali ta ma kasa magana, a matsayinta na cikakkiyar likita ta fahimci komai saboda haka kasa magana tayi.

Ganin Hajiya ta kasa magana ne, yasa Sakeenah ta fita da gudu daga bedroom ɗin saboda tsananin tashin hankali bata ma san inda take jefa ƙafafunta ba, a dai dai tsakiyar palon ta hango Abubakar da Jawaheer da kuma Rafi'at da Yusra suna magana.

Da gudun bala'i ta ƙarisa wurin tana kuka na fitar hankali, gaba ɗaya suka yo kanta suna tambayar ta ko lafiya, tama kasa magana, sai faman nuna musu bedroom na Hajarah take yi Yayin da wasu siraran Hawayen suke biyo idanunta suka wanke ma ta fuska.

Lura da inda take nuna musu ne, yasa gaba É—aya suka nufa bedroom É—in cikin tashin hankali ita ma ta mara musu baya.

Can gefe suka hango Hajiya Zuwairiya tana zaune kamar bata cikin hayyacinta saboda zaman Ƴan borin da tayi, Yayin da idanunta suke akan gadon da Hajarah take kwance saman shi.

Da sauri Abubakar ya ƙarisa wurin gadon ya fara kiran sunan Hajarah, amma ina rai Ya yi halinsa, gata dai Tamkar zata amsa masa, amma ina.

"Ta mutu, ta tafi shikenan ta tafi ta barmu, da Yaranta da jaririyar ta, ta tafi gidan ta na gaskiya, ba tare da ta cika Burinta na haɗuwa da Ahalin ta ba, shikenan kuma ta faru ta ƙare, Hajarah ta tafi ta Barmu a duniya, shikenan fa munyi Rashin mace ta gari, ga kirki, ga Haƙuri, Yah Allah bazan iya jurewa ba."

Duk wannan maganganun Hajiya Zuwairiya ce take yin su a Yayin da har lokacin idanunta suke akan gadon da Hajarah take kwance saman shi.

Tamkar Saukar Aradu haka zantukan Hajiya Zuwairiya suke shiga kunnen Abubakar Wanda ya tsaya cak da ƙoƙarin Tashin Hajarah da yake yi.

Zai iya cewa tunda Yake a duniya bai taɓa shiga matsanancin Tashin Hankali ba, irin na Ranar har Ranar kuwa da Haleesat Rashid Rayyan ta Rasu, komawa Ya yi Tamkar Statue a wurin gaba ɗaya zuciyar sa da gangar jikin sa sun tafi Hutun Rabin lokaci.

Yayin da gaba É—aya mutanen palon suka É—auki kalmar "Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un."

Suke faɗa cikin tashin hankali, amma banda Sakeenah wacca tuni ta sume a wurin.😭

A taƙaice dai faɗin irin tashin hankalin da wannan Ahali na Alhaji Sameer Lamiɗo suka tsinci kansu a ciki Tofah Tabbas Baki ko Alƙalami Ya yi kaɗan. 😓😥

Koda mutanen Jigawa dana Kano da sauran Ahali suka zo da Farin cikin na ganin mai jego da jaririyarta, suka sama wannan mummunar Labari na rasuwar Hajarah ga kyakyawar Jaririyarta da ta Bari.
Gaza jurewa da yawa daga cikin su suka yi domin sai da suka yi kuka.

Haka Rayuwar ta ci gaba da tafiya gaba ɗaya ɓangarorin babu daɗi sam, musamman ma ɓangaren Abubakar domin kuwa Rasuwar Hajarah ba ƙaramin taɓa Ya yi ba sosai sosai.

A Ranar da Hajarah ta cika sati biyu da Rasuwa Yusra matar Yusuf ta É—auki Jaririyar Hajarah wacca taci suna 'AFEEFAH' /Tagari/

Ta koma Mai Duguri da ita da umarnin Abubakar domin kuwa da yardansa sannan kuma da amincewar sa Yusra ta ɗauki jaririyar domin ta ci gaba da kulawa da ita har zuwa wani lokaci, Wanda kuma wannan shawarar da ya Yanke, ba ƙaramin daɗi yayiwa gaba ɗaya Ahali ba.
Yayin da ita kuma Zaynerb ta koma Jigawa State hannun su Dr_Raheemah da zama.

Wanda Hakan ba ƙaramin haushi yaba Rafi'at ba, domin kuwa a cewarta ita Yafi kamata da ya bawa riƙon Zaynerb da kuma Jaririyar domin kuwa ta kusa haihuwa sai ta haɗa da Wanda zata haifa ta kula dasu duka, shiru kawai dai tayi ta shanye duka ɓacin Ranta.
Don karta kuma saka mijinta cikin wani hali bayan Wanda yake ciki.

Tofah haka suka ci gaba da gudanar da Rayuwar.
Tsakanin Rafi'at da Abubakar kuma zaman nasu dai abin babu yabo balle kuma wani abu wai shi Fallasa.

- *-
-
Hajarah nada wata Biyu da rasuwa, ranar wata Alhamis ita ma Rafi'at ta haifo ÆŠiya mace, sai lokacin kuma Abubakar ya É—an fara dawowa Nutsuwar sa.
Ranar suna Jaririya taci suna Lailah, zuwa lokacin Jaririyar da Hajarah ta Bari wacca Yusra take Riƙo duk da cewa madara take sha tayi ƙiba gata da kuma yi, ga wani kyau na musamman da ta ƙara.

Aikuwa a Ranar da Yusra taje da ita Abuja a hannun mahaifinta ta wuni yana bata wani kulawa na daban, duk cewa a duk ƙarshen wata Yana tafiya can Mai Dugurin domin ganin ta sannan ya wuce Jigawa State ma domin ganin Zaynerb.

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉

*

Page *83&84*

___**

Rayuwa ta ci gaba da tafiya da sauri sauri.
Yayin da dukiyar Abubakar Sameer Lamiɗo ta ci gaba haɓɓaka ta ko wani fanni dukiyar sa ƙara nin kuwa take yi sosai.

Wanda zuwa lokacin ya buÉ—e makarantar Islamiya da Masallatai da kuma Orphanage, da nin yar ladar ya dinga tafiya kai tsaye ga maragayya Hajarah matar sa.

Lailah ÆŠiyar Rafi'at nada shekaru biyu a duniya Yayin da Haleesat take da shekaru huÉ—u twin's kuma Nailah da Nainarh suke da shekaru shida, shi kuma Abdulmaleek da Yake Babba Yake da shekaru Tara a duniya.

Zaynerb ÆŠaya ga Maragayya Hajarah kuma take da shekaru huÉ—u a duniya ita ma.
Yayin da ƙanwar ta Afeefah dake can Mai Dugurin wurin Yusuf da matar sa da Yaran su da zama take da shekaru biyu kacal a duniya.

A lokacin ne kuma Rafi'at ta kuma Haihuwa ta haifa mace again Yarinya taci sunan mahaifiyar Rafi'at da ta Rasu ba jimawa wato Zinaru Yayin da Yayyinta suka saka mata xixi suna kiranta hakan.

A lokacin ne kuma Abubakar ba kunya ya amso Ɗiyarsa Afeefah a hannun Yusuf da matar sa, amma ita Zaynerb ya barta a Jigawa State a cewar sa ita ma zai karɓe ta amma sai bayan wani lokaci.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya tana sauri sosai, Yayin da Abubakar Yake kula da Yarinyar sa Afeefah ko sauro baya bari ya taɓa ta, to a'ina ma sauro zai ganta.🤔

Afeefah ta taso Yarinya ce mai matuƙar kaifin basira da wayau, Sannan kuma sosai take ƙaunar Ƴan uwanta duka kamar yadda suma suke ƙaunar ta musamman ma dai Lailah, amma tsakanin ta da Momy Rafi'at kuwa sai dai kallo daga nesa, ko kuma gaisuwa amma in banda wannan, babu wani abu da yake shiga tsakanin su.

Dhekarunta uku a duniya aka saka su a school ita da Lailah Yayin da suke tafiya tare da sauran Yayyin su Haleesat da Nainarh Nailah sai kuma Abdulmaleek tsakanin ta da YaYarta Zaynerb kuwa duk da cewa ba'a tare suke ba, amma shaƙuwa ce ta musamman mai zaman kanta a tsakanin su, a dalilin kuwa duk a ƙarshen wata Abubakar yake haɗa kan Yaransa suje Jigawa State ziyara wani lokacin Momy Rafi'at tana binsu, amma wani lokacin saboda yanayin aikin ta haƙura take yi, Especially ma da mahaifinta ya gina ma ta asibiti nata na ƙashin kanta sai ya zama bata cika samun lokacin kanta ba.

_****______

Shekarun Afeefah Takwas a duniya Abubakar ya ɗauko Zaynerb daga Jigawa State, ya dawo da ita Abuja cikin Ƴan uwanta.
Rayuwa ta ci gaba da tafiya da yake Zaynerb yarinya ce mai masifar wayau da kaifin tunani shiyasa bata shiri ko kaɗan da Momy Rafi'at, domin kuwa ta fahimci ba ƙaunar su take ba, musamman ma idan ya kasance da mutane a wuri to nan ne fa zata dage ta dinga nuna musu ƙauna ta musamman, amma kuma suna kasancewa daga su sai ita, wahala take basu ba kaɗan ba, domin kuwa tasha ta zane Zaynerb ba sau ɗaya ba kuma ba biyu ba, amma kuma ita Afeefah ko tayi nin yar dukan ta kasawa take yi domin kuwa Zaynerb shiga tsakani take sai dai ita a dake ta amma bata bari ko ƙuda ya taɓa ma ta ƙanwa, wacca take shalele a wurin mahaifin su, Alhaji Abubakar Mai Kyau, sai dai kuma duk da ƙiyayyar da Momy Rafi'at take yi wa su Afeefah da Zaynerb bata taɓa nuna wa a gaban Yaranta ba, ko kuma mijinta cikin taku da tsare gida take abin ta.

A wata Ranar Jumma'a ne Ahalin Alhaji Sameer LamiÉ—o suka tashi da wani mummunar Labari na Rasuwar Alhaji Sameer LamiÉ—o ta farar É—aya cikin dare, wuraren uku na dare ya rasu, Yayin da kafin gari ya waye ita ma matar sa Hajiya Harirah ta ce ga garin ku nan tabi mijinta.

A lokacin ba ƙaramin Tashin Hankali gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo suka shiga ba, musamman ma Abubakar domin kuwa zai iya cewa wannan ne mutuwa ta uku da aka taɓa masa waɗanda ba ƙaramin Tashin Hankali ya shiga ba.

A lokacin kuma sai mutuwar masoyiyar sa Haleesat Rashid Rayyan da kuma matar sa Hajarah Ya dawo masa sabo a zuciya.
Chapter 74 · 0% Book details