← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 96

Sashe 65

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Budurwar ta musu tambayar fararen haƙoran ta duka a waje saboda murmushin dake akan kyakyawar fuskar ta.

Har Rafi'at ta buɗe baki zata bata amsa ke nan, likita ya turo ƙofar room ɗin ya shigo yana mai musu sallama.

Shiru Rafi'at tayi kamar mai tunani tana ji lokacin da su Abubakar da wannan budurwa suka amsa masa sallamar amma ita tafasar da zuciyarta take bai bari ta amsa ba.

Bayan wannan likita da Abubakar sun gaisa ne, budurwar ta kuma antayo musu tambayar É—azu.

Murmushi likita ya yi sannan yace

"Kedai Wannan patient nawa kinaso ki gano mutanen da suka taimake ki ko to ai sune waÉ—annan a gaban ki."

Dariya tayi cike Farin ciki ta kalla su Rafi'at da kyawawan Yaran dake a gaban su ta ce

"Barkanku dai."

Amsa ma ta suka yi da faÉ—in

"Yauwa kema barka."

Nan kuma suka shiga gaisawa da ita tana musu godiyar taimakon ta da suka yi.

Rafi'at murmushin yaƙe kawai take bin wannan kyakyawar budurwa dashi amma na ciki na ciki.

Kallon kyawawan Yaran tayi cikin shauƙi ta miƙawa Nainarh hannu alamar tazo, aikuwa Yarinyar ta ɓangale baki kana ta ɓanɓare hannunta daga cikin na Rafi'at ta rarrafa da saurinta irin na Yara, ta ƙarisa bakin gadon da budurwar take zaune sannan ta kama gadon tana kici kicin hawa.

Dariya kawai gaba ɗaya suke ma Nainarh wato shi dai Yaro ba Ruwan shi ƙaunar kowa Yake ba abin da ya dame shi.

Da sauri budurwar ta kamo hannun Nainarh tahau da ita saman gadon tana ma ta wasa, aikuwa ganin haka suma Nailah da Abdulmaleek suka ƙarisa wurin da saurin su aikuwa duka ta haɗa tana musu wasa da alama tana ƙaunar Yara sosai obaaaaa.

Kallon Abdulmaleek tayi da yake Babban cikin su sannan ta ce

"My friend please Tell me, what is your name?."

Dariya Yaron ya yi sannan cikin qwarancin sa na yara Yace

"Body."

/Buddy/

Dariya tayi cike da nishaÉ—i ta ce "Okay wato dai 'Buddy' kake so kace ko?."

Girgiza ma ta kai Yaron ya yi alamar "E," yana dariya.

Ta kuma cewa "To ai na gaskiyar nakeso ka faÉ—amin."

ÆŠan shiru ya yi kamar mai tunani sai kuma can Yayi dariya yace "Abdulmaleek naji Aya Aleem iya kiyana."

"Oh suna mai daɗi."🙂

Ta faÉ—a tana dariya.

'Kema Menene sunan ki, ko baki da suna ne?."

Yaron ya antayo ma ta tambayar wacca tasa ta yin murmushi sannan ta bashi amsa da

"Maleek ke nan ai kowa yana da suna a duniya kamar nima dai suna na, suna na...."

Shiru tayi kamar tana tunani sai da kyar ta iya faÉ—i cikin in'ina

"Suna na Ha-Ja-ah..."

Tayi maganar tana dafe qwoqwon kanta da taji kamar zai rabe gida biyu saboda raÉ—aÉ—in da yake ma ta.

"HAJARAH."

Rafi'at ta maimaita sunan cikin ranta tayi murmushi a fili ta ce

"Sunan ki mai daÉ—i kuwa?."

Murmushin ƙarfin hali budurwar mai suna Hajarah tayi tana kuma dafe kanta ta ce da kyar

"Nagode."

"Ah ah kodai kan yana miki ciwo ne, naga kina riƙewa?."

Rafi'at tayi ma Hajarah tambayar a yayin da take ƙarisawa wurin da take zaune saman bed.

"Eh Auntie sosai yake mugun rasamin jina nake kamar bani ba."

Hajarah ta bata amsa tana rumtse idanun ta.

Jin haka yasa likita ya yi ma Abubakar alama da su fita.

Ba musu Abubakar ya miƙe suka fita daga room ɗin, suka bar Rafi'at tana ma ta sannu haɗe karanto ma ta addu'o'i dan ta fahimci kamar hadda jinnu a zancen.

Kai tsaye office na likita suka wuce bayan sun zauna ne, Abubakar da ya gaza jurewa ya kalla likita cikin son jin ƙarin bayani yace

"Please Dr Khasim ko zan iya samun bayanan Rahoton lafiyar Hajarah kuwa?, danna fahimci akwai abin da yake damunta sosai."

Ajiyar zuciya Dr Khasim ya sauke sannan Ya fara magana

"A gaskiya Mister Mai Kyau akwai abin da yake damun wannan patient Hajarah abubuwa da yawa ma ba abu É—aya ba."

"Okay Inajin ka kamar mai da mai ke nan?."

Abubakar ya tambaya yana kuma gyara zaman sa sannan ya mayar da gaba É—aya hankalin sa akan Dr Khasim yana jira yaji abin da zaice.

"To kamar dai Yadda kaji na faÉ—a Malama Hajarah tana fama da matsaloli daban daban na Farko dai shi ne....

A binkciken da muka gunadanar akan kwakwalwarta shi ne na farko ta manta da gaba É—aya Ahalin ta da kuma ainihin State da take, sai dai abu É—aya da ya ba kowa mamaki shi ne....."

Katse sa Abubakar ya yi yana goge zufar da ta karyo masa kana cikin wata kalar murya yake faÉ—in

"Bangane ba Dr Khasim ban fahimci abin da kake nufi ba kwata kwata wai kana so kace min mutum zai iya mantawa da Ahalin sa ne a dalilin wani hatsari ko kuma taɓin kwakwalwa?."

Murmushi Dr Khasim ya yi sannan ya amsa da

"Of course wannan mai sauƙi ne, amma ka fara dakatawa kaji sauran abubuwan da suke damunta kafin kayi wasu tambayoyin."

Jin haka yasa Abubakar nutsuwa amma zuciyar sa bata bar bugu ba.

Dr khasim ya ci gaba da cewa

"Kamar yadda kaji ne, tabbas ta mance gaba ɗaya memory nata da ya taɓa faruwa a tsakaninta da Ahalinta, sannan kuma ta manta da sunan State da take gaba ɗaya a Brain nata...
Sai dai abu ɗaya shi ne bata manta ko wacece ita ba, ma'ana dai shi ne bata manta sunan ta ba, ko kuma karatun ta ko kuma wani burin ta bata manta dasu ba, sai dai kuma ɓangaren Ahalin ta dai...
A bisa binkciken da muka gabatar shi ne zata iya tunawa da Ahalinta da kuma sunan State nata kamar nanda shekara É—aya ko fi ye da haka a bisa hasashen wasu manyan likitocin duniya...
Amma idan shekara ɗaya tazo ta wuce wata shekarar ta zagayo bata tuna komai ba, tofah sai dai ayi haƙuri domin kuwa har abada ba zata taɓa tuna komai ba...."

Ido waje wannan karon Abubakar yake kallon Dr Khasim saboda tsananin mamaki ma kasa cewa komai ya yi kawai yana tauna maganganun Dr Khasim ne.

Sun É—auki tsawon lokaci a haka ba Wanda ya iya cewa komai, sai can bayan kamar mintuna biyar.
Abubakar ya nisa sannan yace

"Dr Khasim ina da wata tambaya É—aya fa."

Murmushi Dr Khasim ya yi kana Yace

"Okay Go ahead Inajin ka."

Abubakar Yace "To wai dama can an taɓa samun kalar wannan matsalar ne, mutum ya manta memory nasa da ya taɓa faruwa a tsakanin sa da Ahalin sa a dalilin hatsari ko wani Abun?."

"Eh an taɓa samu a ƙasar China Babban Birnin ƙasar wani mutum ya yi hatsarin mota sai gaba ɗaya ya manta da Ahalin sa da sunan garin sa abin da bai manta ba kawai shi ne shiɗin ɗan kasuwa ne, sannan kuma ƙarin abin mamakin bai manta da harkokin kasuwancin sa ba."

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*___________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Page *67&68*

"A ƙasar India an taɓa samun irin haka ba iya nan ba a wasu ƙasashen ma anyi ta samu, amma ni dai a Nigeria wannan ne karo na farko dana tsinci wannan al'amari."

Nan dai Dr Khasim ya ci gaba da yima Abubakar bayani akan matsalolin da suke damun Hajarah.

A taƙaice dai su Abubakar basu suka bar wannan Asibitin ba sai wuraren ƙarfe ɗaya na rana.
Washe gari ma haka suka sake dawowa wurin Hajarah sannan Abubakar ya kuma komawa wurin Dr Khasim ya masa ƙarin bayani akan lafiyar Hajarah.

Sai da suka kwashe tsawon sati ɗaya suna zuwa duba lafiyar Hajarah, zuwa lokacin taji sauƙi sosai, sannan kuma ba ƙaramin shaƙuwa bace ta shiga tsakanin ta da family ɗin Abubakar Mai Kyau dashi kansa dama matarsa Rafi'at, ai ba'a ma maganar Yara su Abdulmaleek domin kuwa wata kalar shaƙuwa ta ban mamaki tayi da Yaran a sati ɗaya kacal.

Zuwa lokacin kuma Abubakar ya gama binkcike akan Hajarah ya gano cewar.
Ita ɗin Ɗalibar psychology ce a wata University dake a nan Abujan, sannan kuma ta kammala karatun gaba ɗaya a Ranar murnar kammala karatun nasu ne ma, bayan an gama, kowa ya watse ita ma tana hanyar ta komawa gidan da take zaune da yake ba'a hostel take zaune ba, shi ne fa wannan hatsari ya auku da ita, Motar da take ciki wasu Ƴan fashi suka tare, ta fito a domin ta gudu wata mota ta bigeta shikuma mai mota yaji tsoron kota mutu ne shi ne ya gudu bai taimaketa ba, shi ne fa su Abubakar suka tsince ta a wurin da abun ya faru hadda jini a jikinta that is all.

To koda Abubakar ya tambaya Hajarah abin da ya faru, anyi sa'a bata manta komai ba, ita ma dai haka ta faÉ—a masa, a lokacin Rafi'at ta tausaya ma ta sosai domin kuwa abin akwai ban tausayi ace mutum ya manta gaba É—aya memory nasa wanda ya faru a tsakanin sa da Ahalin sa daÉ—in daÉ—awa kuma ace hatta sunan State da yake ya manta abin akwai ciwo obaaaaa.

___*_____*

Satin Hajarah biyu a asibiti mutanen Jigawa State, suka diro Abuja sakamakon kiran su da Abubakar ya yi a waya ya faÉ—a musu halin da ake ciki.

Kai tsaye Asibitin da aka kwantar da Hajarah suka wuce suma dai bayan isansu suka kuma tabbatar da abin da Abubakar ya faɗa sun tausaya ma ta sosai, musamman da ya kasance suɗin likitoci ne sun san matsalar abin Especially ma Hajiya Zuwairiya da ya kasance ita ɗin ɓangaren ta karanta wato Brain.

___*

Kwanan su biyu suka juya Jigawa State da Hajarah a bisa shawarar da gaba ɗaya suka yanke na qwara ta koma hannun su da zama, kafin asan abin yi tunda ba za ta iya tuna komai ba, indai ɓangaren da ya shafi Rayuwar ta da family nata ne.

Wannan konawa Jigawa State da zama na Hajarah ba ƙaramin faranta Ran Rafi'at ya yi ba, domin kuwa a da sosai ta damu da inda Hajarah ɗin zata zauna tsoro take kar ta barta a gida ita gata ba mazauniya ba wani abu yazo ya shiga tsakanin ta da mijinta. 🤦
Chapter 65 · 0% Book details