← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 96

Sashe 15

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"E' ƙanin Auntie ne," Jieddarh ta bata amsa a gajarce "To ikon Allah amma kuma bansan suba ae gashi ina shirin zama IN LAW ɗinsu na miki na turawa.
Cewar bilki, "Oh Bilki ke komai sai kin sanine wai" cewar Jieddarh, Bilki ta ce "eh mana ba dole na sansu ba ƙannin suruka tace fah ae dole na sansu Yasin," Dariya Jieddarh tayi ta ce "to dai na farkon mai sanye da shigar hausawa YaYar Auntie ce uwa ɗaya uba ɗaya sunan ta Hajiya Nusaiba sai kuma ɗayar mai ƙaramin yaro sunanta sister Na'ima ɗayar kuma wanda kika ga ta riƙe hannun wannan kyakyawar yarinyar sunanta pretty Nafisah bazawara ce mijin ta ya rasu tun kafin Ta haifa ɗiyarta khausar, Duk tafi su kirki Yaranta biyu, Sai kuma na ƙarshen budurwace ita batayi Aure ba sunanta Ni'ima beauty shekarun ta Ashirin da biyar ita ce Babbar ƴar Auntie Nusaiba a mata YaYa Heesham takeso shiyasa batayi Aure bah🤣😂😅.

💓*SARAUNIYAR KYAU*💓
*Page 15&16*

Da sauri Bilki ta kalla Jieddarh hadda dafe ƙirji ta ce "wani YaYa Heesham ɗin, Badai masoyina ba?,"
"Of course yes, shi fa," cewar Jieddarh, miƙewa Bilki tayi zata bar gurin, Da sauri Jieddarh ta ce "ina zaki je ne, Haka?," "Hmm ke dai Jieddarh barni kawai zanje naga mai son masoyinane," Da sauri Jieddarh ta ce "to ki tsaya na faɗamiki wani abu mana.

Dawowa da baya Bilki tayi to gani faɗamin halayenta ina sauraronki," "haba malama Bilki toki nutsu mana saina faɗa miki yadda kema zaki fi fahimta," zama Bilki tayi cikin ƙosawa ta ce "to faɗamin ina sauraro," Ajiyar zuciya Jieddarh ta sauke sannan ta ce "kedai Bilki na farko dai ko shekara bakiyi a gidannan kina aiki ba watan ki bakwai ne, dan haka baki gama sanin halayyar ƴan gidannan ba ma balle kuma ƴan waje," ɗan shiru Jieddarh tayi sannan ta ci gaba cewa "ita wannan Ni'ima beauty da kika ganta ba'a shiga harkar ta, saboda bata da kirki ko kaɗan sannan kuma tanason YaYa Heesham highly highly kuwa," Jieddarh tayi maganar tana dariya, Ɗan kallon ta Bilki tayi cike da takaici da kishin Ni'ima ta ce "Yasin Jieddarh da nasan wannan shirmen zaki faɗamin da ban tsaya ba, Yo ni Allah na tuba kar tayi kirkin mana ina ruwa na da ita," Da sauri ta miƙe ta shige palon, Jieddarh ta bita da kallon tausayi kawai, Eh mana dole ta tausaya mata saboda wannan makauniyar soyayya da takewa Heesham, Jieddarh tasan halin Auntie yadda ta tsani talaka fiye da yadda ta tsani mutuwar ta da wuya wannan Auren ya yuwu gashi kuma soyayyar ɓangare ɗaya ne sai dai kawai Bilki ta sha wahala.

Bilki tana shiga palon ta samesu zaune sunyi É—aiÉ—ai saman Royal sofa's É—in dake palon sai fira sukeyi da Auntie.
Kai tsaye kitchen ta shiga bayan wani lokaci ta fito hannun ta riƙe da Tray mai ɗauke da cups guda huɗu a saman, ciki juice ne mai sanyi, Ƙarisowa gurin su tayi ta bisu ɗaya bayan ɗaya tana raba musu wannan juice, Saida ta gama raba musu tas sannan ta dawo gurin Yarinyar Nafisah tana mata wasa ita kuwa Yarinyar sai ɓangale baki takeyi tana dariya, Dama ance mai ɗa wawa ganin haka yasa Nafisah cewa "Hi young lady what is your name?," Da sauri ita ma Bilki ta harhaɗa ɗan turancin da ta koya a makarantar gwamnati da tayi ta ce "year Aunty My name is Bilkisu Adam Mai gazon Zinare."
Dariya Nafisah tayi ta ce "aikuwa sunan ki mai É—adi it's deserved to you beauty.
"Na gode highly highly" cewar Bilki a lokacin da take ɗaukar Yarinyar zata fita da ita, Harta kai ƙofa taji Ni'ima na faɗin "Yanzu fisabilillah Mamy Nafisah wannan bagidajiyar Yarinyar zaki bari ta ɗaukar miki ƴa kamar bakisan zafin haihuwa ba kwata kwata Yarinyar nan naki ko shekara batayi ba haba adai duba lamarin," Nusaiba ta amsa da faɗin barta Allah yasa a kwaso mata cutar talakawa babu ruwanmu ciki," ita dai Bilki fita tayi tanajin Nafisah na basu amsa ita kuwa tayi tafiyar ta a zuciyar ta ta ce "wannan Ni'imar anyi shegiya tayi da baki kamar mariƙin lema saina koya mata hankali soon na lura bata da wani cikakken hankali akanta.

Ƙarisawa gurin da Jieddarh take zaune Bilki tayi ita ma ta zauna kallon Jieddarh Tayi ganin Yadda gabaɗaya ta Mayar da Attention ɗinta akan tsadaddiyar Wayarta ƙirar SAMSUNG GALLAXY dake hannunta, Ta ce "lafiya kuwa Jieddarh wannan ƙurawa Salulah ido fah bakya tsoron Ya shafa lafiyar idanunki?".

Ajiyar zuciya Jeiddarh ta sauke Still idonta Yana kan Wayar hannunta Ta ce "kedai Bilki Bari kawai domin kuwa Wani ƙayatacce kuma haɗaɗɗen Labari Nake karantawa shiyasa Banma san Lokacin da kika ƙariso bah," Murmushi Bilki Tayi sannan ta ce "ato ae dama daga ganin Yadda kika Mayar da gabaɗaya hankalin ki akan wannan tsadaddiyar Wayar hannun ki nasan da wata a ƙasa, Toh dai Yanzu Zan iya Sannan Sunan wannan ƙayataccen labari Wanda Ya Tafi da gabaɗaya hankalin ki, Idan akwai dama, ma sai kiyim ƙarin bayani akan Yadda zan samu na siya nima na karanta cikin nutsuwar zuciya."
Ƙayataccen murmushi Jieddarh Tayi sannan ta ce "Tabbas akwai dama highly highly mah Yanzunnan zanyi miki dogon Bayani akan wannan shahararren Labari Wanda Yazo da salo na daban.........
Da Farko dai Sunan Wannan Katafaren Labari shine 🅂🄰🅁🄰🅄🄽🄸🅈🄰🅁 🄺🅈🄰🅄 sannan ya sama rubutu ne daga Alƙalamin sabuwar marubuciya 🄺🄷🄰🄳🄸🄹🄰🅁🅃🄷 𝕎𝕒𝕥𝕠 🆃🅷🅴 🅽🅰🅸🅽🅰🆁🅷 🅺🅳, sannan kuma wannan labari zaki iya samun shi a kafar yanar gizo kamar irinsu, FACEBOOK WHAT'SAPP TELEGRAM WATTPAD, ke idanma kina da buƙata zan iya baki phone number na wannan marubuciyar domin tayi adding ɗinki a what'sApp Group nata da take Tura SARAUNIYAR KYAU ciki fah.

Washe baki Bilki Tayi Sannan Ta ce "ah gaskiya daga Jin wannan Bayani Naki Nasan Wannan Novel zai Bada Jitta obaaaaa ae ina faɗamiki Jieddarh Yanzunnan Zan kwashe What'sApp lamba Nata domin na dunga samun updates wannan ƙayataccen labari don kar a barni a baya🤓
Murmushi Jieddarh Tayi sannan ta ce "aikuwa dai ya kamata don kema ki ƙaru da abinda yake ciki.

Bilki Ta ce ohoo kaji Æ´ar gari kuma Æ´ar birni, yanzu abinda za'ayi kawai phone number na wannan Marubuciya zaki bani yanzu na lalubota, "Zan baki amma ba yanzu ba", "to sai yaushe Bilki ta tambaya jin abinda Jieddarh ta faÉ—a.
Murmushi Jieddarh tayi ta ce "saima gama ja miki aji sannan " Humm amma Yasin Jieddarh kina da wulakanci sai dai ya na iya da saurayin ummata haka zanyi haƙuri ki gama jamin ajin" Bilki tayi maganar Like a orphan tana mai yin alamun tausayi murmushi kawai Jieddarh tayi ba tare da ta ce komai bah.

Haka dai suka ci gaba da fira da Jieddarh sun daɗe suna fira kafin wani lokaci su Nafisah suka fiffito, Da alama tafiya zasuyi gurin su Nafisah ta ƙariso karɓar ɗiyar ta sai dai kuma me aikuwa Yarinya ta fara kuka ba za ta je wajen ta ba, Wai ita harta saba da Bilki dariya Bilki tayi ta ce "Yau na sama ɗi ya ɓagas gashi kuma banma san sunanta ba amma ta maƙale min" Nafisah na murmushi ta ce "sunanta khausar", "wow nice name shiyasa take sona ashe taga ɗiyarta ne" cewar Bilki tana washe baki "da gaske haba kice sunan mama ce da ita Nafisah ta tambaya cikin murmushi, "Yasin kuwa sis" cewar Bilki tana jijjiga khausar ɗin dake kuka, "gashi kuma taƙi ta yarda dake yanzu ya za'ayi gashi kuma jiran ki akeyi Jieddarh ta faɗa ganin yadda Yarinyar kamar wata mai wayo taƙi zuwa wajen mahaifiyar ta😕.

Ni'ima ce ta ƙariso gurin cikin isa da gadara Like a ɗiyar Gwamna "lafiya kuwa Mamy Nafisah kizo mu tafi mana kin tsaya magana da wannan dirty girl ɗin."
"To Ni'ima yarinya dai taƙi yadda dani fah"
"Taƙi yadda dake kuma ban gane taƙi Yarda dake ba, kar dai ace an asirce miki ƴa ne daga raino" Ni'ima tayi maganar tana ɓalawa Bilki harara dan haka kawai taji bata mata.
Ba wanda ya kulata a cikin su, saima bawa kurma da blind da mara aikin yi, Ajiyar ta da sukayi😇.

"Please Mamy Nafisah ki karɓa ɗiyar ki mu tafi mana, dare nayi fah, Ni banma san dalilin da yasa mukazo gidan Mamy Jamila da Yamma ba gashi garin hadarine highly" Ni'ima tayi maganar da iya gaskiyar ta, Da ƙarfi ta karɓa Yarinyar a hannun Bilki tana faɗin "aikin kawai, ke Mamy Nafisah sai ki zo muje ae", tayi gaba abinta haƙuri kawai Nafisah taba Bilki jin an fara ruwan sama, ta ce "karki damu Bilkisu ina nan dawowa wata rana zan dawo, kuma a gurin ki khausar zata wuni, kuma ke zanba yayenta idan lokaci yayi tunda naga tana sonki insha Allah," Murmushin jin daɗi Bilki tayi ta ce "ba komai sis Nafisah, kuma ina sauraron ranar da za'a kawomin lovely Khausar momyna yaye," "Lallai ma wato har kin saka mata suna Lovely momy ko?," cewar Jieddarh cikin murmushi, ita ma Nafisah murmushi kawai tayi sai dai ba ta ce komai ba saboda rashin lokaci, sallama sukayi su Nafisah suka tafi, su kuma Jieddarh suka koma ciki jin ruwa ya tsinke kamar da bakin ƙwarya.

🅱🅰🆈🅰🅽☆🆂🅰🆃🅸☆🅱🅸🆈🆄

ABUJA

Kwance take tayi ɗaiɗai, Tana kallon sararin samaniya kamar mai ƙirga taurarin dake a sararin samaniyar, Ta saka hannun ta ɗaya tana murza dogo kuma baƙin gashin kanta wanda ya baje a saman koranyen ciyawu wato Grass carpet dake a cikin garden ɗin da take ciki kwance, wanda aka qawata da shuke shuke da kuma bishiyu kala kala kamar su mangwaro,gwaiba,taura ayaba. Da dai sauran su, da sauran su.
Headphone ne manne a kunen ta tana sauraron lyrics na mawaƙiwa celline Dion mai taken "A New day has come" ta lumshe idanun ta Yayinda take bin waƙar a hankali cikin ranta.
Chapter 15 · 0% Book details