← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 96

Sashe 48

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba komai ya ƙaramin gwarin gwiwa ba sai ganin yadda ƴan uwana har uku sun zo kallon Gasa na domin kuwa ɗayan Yayan nawa yazo shima.

Anyi Gasa an gama gaba É—ayanmu Æ´an matan Gasa mu goma muna daga saman floor muna jira muji waÉ—anda suka ci Gasar, wato sama Nasarar zama winner's na shekara.

Haka munaji aka kiran wacca tazo ta É—aya aka kira ta biyu, haka ma aka ta uku amma ba'a kirani ba.

A lokacin kasa jurewa nayi, domin ni macece ina da rauni sosai musamman ma akan abin da nakeso, kuma na sanya a gaba.
A lokacin zuciyata tamin nauyi na gaza jurewa.
Dalilin ne yasa na zube a gurin a sume, sai farkawa nayi na ganni a gadon Asibiti, That's All."

Ta ƙarishe maganar tana kuma goge hawayen fuskarta, Hameeda Sagir harta buɗe baki zatayi magana, Juwairiya ta rigata da kuma faɗar.

"Sai dai kuma yanzu komai yazo ƙarshe na haƙura da zama SARAUNIYAR KYAU, a baya idan mutane suna cewa bazan taɓacin Gasar SARAUNIYAR KYAU ba, saboda ni baƙace bana yadda amma yau na yadda ɗari bisa ɗari 100% baƙaƙen fata basa samun Nasara a Gasa sai dai fararen fata amma yanzu na fahimci komai."

Ta rufe da faÉ—ar

"Inayiwa sauran Æ´an matan da suka sama Nasarar lashe wannan Gasar na SARAUNIYAR KYAU matakin jaha fatan Nasara.

Sannan ina taya ira irena waɗanda suka faɗi a Gasar baƙin ciki da jaje."

Tana faÉ—in haka tayi shiru, gaba É—aya É—akin ya É—auki shiru ana kallon kallo tsakanin juna.

Can Æ´ar jarida Hameeda Sagir ta katse shirun da É—akin ya É—auka da faÉ—in "Malama Juwairiya Jabir Bici nida sauran jama'ar dake kallo da sauraro muna tayaki jin babu daÉ—i, akan wannan al'amari kuma muna fata hakan ya zama mafi alkhairi a gareki dama sauran waÉ—anda suka sama failure a Gasar."

Tana gama faɗin haka ta juyo tana fuskan tar na'urar ɗaukar bidiyon, sannan ta ci gaba da cewa "Yanzu dai mutane gaba ɗaya munji dalilin da ya saka Malama Juwairiya ta faɗi a gurin Gasar daga bakinta, dama Hausawa sukace magana daga bakin mai ita tafi sugar."😋

Ta ci gaba da cewa "A halin yanzu muna jiran ƙarisowar Madam Miracle wato ɗaya daga cikin manyan alƙalan Gasar, domin muji ta bakinta akan wannan al'amari mun sama labarin yanzu yanzu tana akan hanyarta zata ƙarisowa wannan Asibiti domin duba jikin Malama Juwairiya Jabir Bici, sannan kuma ta amsa mana wasu ƴan tambayoyi."

Tana kai maganar suka turo ƙofar room ɗin suka shigo, securities ne mata guda biyu ɗirka ɗirka dasu, suka fara shigowa sai Madam Miracle sai kuma wasu matan biyu suna take ma ta baya.

Da sauri É—an jaridar mai É—aukar bidiyon ya mayar da na'urar akan Madam Miracle da ta zauna akan wata farar kujera kusada Juwairiya Jabir Bici tana ma ta ya jiki, cike da farin ciki Juwairiya take amsawa.

Sai da Madam Miracle ta kammala duba jikin Juwairiya Jabir Bici, sannan ta juyo da kallonta akan Hameeda Sagir ƴar jarida dake zaune a gefanta saman wata farar kujera hanunta riƙe da abin magana.

Murmushi Madam Miracle tayi sannan ta ce ma kyakyawar Æ´ar jaridar dake zaune a kujerar kusada ita.

"Go ahead."

Sai ta abin maganar Æ´ar jarida Hameeda Sagir tayi shima mai É—aukar bidiyon ya sai ta nashi akansu, su duka ukun hadda Juwairiya Jabir Bici.

Gyaran murya ƴar jarida Hameeda Sagir tayi sannan ta kalla sai tin na'urar ɗaukar bidiyon ta ce 'Barkanku dai masu kallon mu da sauraron mu, kamar yadda kuke gani ga Madam Miracle ta ƙariso fa."

Dawo da kallonta tayi kan Madam sannan ta ce "Barka dai Madam Miracle fatan kin ƙariso lafiya.?"

Madam ta amsa da "Yauwa barkanki dai, lafiya ƙlau."

Ƴar jarida ta ci gaba da cewa "Masha Allah, shin Madam zamu iya sanin ainihin dalilin da yasa ba'a zaɓi Malama Juwairiya Jabir Bici ba a Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha?, ko kuwa dai kamar yadda ita Malama Juwairiya ɗin ta faɗane, cewa ba'a zaɓan baƙaƙen fata sai farare?."

Murmushi Madam Miracle tayi sannan ta gyara zaman Medical glass dake fuskar ta kana ta ce "naji duka tambayoyin ki Malama Hameeda Sagir amma mudai a tsarin Gasar SARAUNIYAR KYAU na ko wani mataki ba'abin hasken fata, domin kuwa ba'akan haka aka gina Gasar ba.
Sannan da kika tambaya akan Miss Juwairiya.
Yes baƙar fatace ita. Amma ba wannan dalilin ne ya hana a zaɓeta a Gasar ba ae.'

Cikin sauri Hameeda Sagir ta kuma tambaya, "Shin Madam zamu iya sanin dalilin da ya sa ba'a zaɓeta ba kuwa."

"Of course, zaku iya sani ae, babu damuwa "

Cewar Madam Miracle.

"Babban dalilan da suka saka ba'a zaɓa Miss Juwairiya ba, guda biyu ne zuwa uku, na farko shine batada idanu😳

Ma'ana dai idanunta sunyi ƙanana da yawa wanda hakan yasa ba'a zaɓeta ba.
Na biyu kuma shine tsayinta bai kai yadda akeso ba."

Da mamaki Hameeda Sagir take kallon Madam sannan ta ce Madam bamu fahimci abin da kike nufi ba?. Kenan dai har tsayi ana dubawa wajen Gasar. Ko ince ana buƙata ko?."

Murmushi Madam Miracle tayi kana ta bata amsa da "Sosai ma, ana duba tsayi. Misali ita Juwairiya Jabir Bici, it's her Height is _1.49m take, kinga kuwa babu yadda za'ayi tayi Nasara."

Hameeda Sagir ta ce "Okay, Madam ko zaki iya faÉ—amana yadda akeso tsayin ya kasance?."

Madam ta ce "anaso ya kasance kamar_1.55m zuwa sama da hakan."

Hameeda ta ce "Madam tambayoyi biyun ƙarshe please. Na farko shin zaki iya faɗamana dalilin da yasa kikazo duba lafiyar Juwairiya Jabir Bici?."

"Na biyu shin zaki iya faÉ—amana dalilin ki naba budurwar da ta lashe Gasar tazo ta É—aya kyautar tsadadden Diamond Ring?. Domin mutane da yawa suna so susan dalilin ki nayin hakan."

Wannan karon dariya Madam Miracle tayi har farare jerrarun haƙoranta suka bayyana sannan ta bata amsa da "Duka waɗannan tambayoyin naki Miss Hameeda Sagir amsa ɗaya ne dasu, wannan amsar kuma ita ce saboda naji ina ra'ayin hakan ne, cause it's the personal secret thing."

Hameeda Sagir zata kuma magana, Madam Miracle ta miƙe tsaye tana faɗar

"It's okay, lokaci yaja zan tafi."

Miqewa ita ma ƴar jarida Hameeda Sagir tayi tana faɗin "Okay Madam Miracle sosai munji daɗin wannan taƙaitaccen firan da ya gudana tsakanin mu, muna fatan nan gaba zamu sake zama domin firar kalar wannan?."

Murmushi Madam Miracle tayi sannan ta ce "Babu damuwa, domin a koda yaushe ina mai maraba daku, na barki lafiya."

Juyowa ƴar jaridar Hameeda Sagir tayi tana fuskan tar na'urar ɗaukar bidiyon tana faɗin "Toh jama'a masu kallon mu, da sauraron mu, kamar yadda kuka gani mun tattauna da Madam Miracle kuma munji dalilin da yasa ba'a zaɓi Miss Juwairiya Jabir Bici ba a cikin Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha ba."

# MASU KARATU, IDAN BAKU MANTA BA, DUK WANNAN TATTAUNA WAR KALLON SHI SU JIDDARH SUKEYI A TV.

Kashe T.v É—in Jiddarh tayi sannan ta kalla su Humaira tana faÉ—in "Abin akwai ban tausayi fa, ace mutum bai samu ya cika burin da ya sama rai ba, a gaskiya yarinyar ta bani tausayi ba kaÉ—an ba."

Ajiyar zuciya Humaira ta sauke tana mai faɗin "Ni ma dai hakan ne, amma ya zatayi wannan ita ce ƙaddarar ta gashi abin ya yayatu a social media ta ko'ina maganar ta akeyi fa."

Auntie ta ce "ai kunji irin matsalar yanzu tajama kanta da iyayenta tonon qwaqwaf kenan fa."

Ci gaba da tattaunawa akan lamarin sukayi gaba É—aya jikin Jiddarh yayi laqwas duk tausayin budurwar yabi ya addabeta a zuciya.

Suna cikin haka sai ga Bilki ta shigo bugujin bugujin da ita ga yarinya a hannunta tana tsotsar madara a fida.

A tsakiyar palon ta zube sannan ta kalla Jiddarh tana faÉ—in "Sannu SARAUNIYAR KYAU ta jahar Kano, gaskiya ina tayaki murna sosai."

"Ke tayaya kika san ita tayi Nasara a Gasar bayan kuma bakije Gasar ba?."

Auntie ta tambaya tana kallonta, dariya Bilki tayi ta ce "Hajiya kenan Auntien mu kin manta ina da waya ne.?"

Humaira ta saka baki, "Malama Bilki mai raino, to ya ya yarinyar taki take,?"

Bilki tana washe baki ta ce "Ga yarinyar bata da rigima sam, inajin daÉ—in wannan yayen da nakeyi, ni dama mutane zasu gane su dinga kawomin raino ai dana zama Auntyn Yara."

Jiddarh ta ce "Aikuwa zaki dace da Autyn Yaran highly."

Bilki ta bata amsa da "Kedai bari ai abin ba'a iya cewa komai wallahi."

Jiddarh ta kuma cewa "To ya zakiji idan akazo tafiya da Khausar ranar da kika gama rainonta?."

Bilki ta ce a gaskiya abin babu daɗin faɗa ko'a baki, dan zanyi kewar ta sosai banama fatan ranar da zata zo karɓanta tazo, dan idan tazo sai nayi zazzaɓin yini ɗaya yasin."

Tayi maganar tana zuba uban tagumi.
Humaira ta ce "Ba kewar ta zakiyi ba kenan, tunda dai zazzaɓin yini ɗaya zakiyi kacal?."

Bilki ta amsa da "To ai na yini É—ayan yafi daÉ—in faÉ—ane a baki fa, shiyasa nace hakan."

Dariya sukayi jin irin wautar Bilki fira suka ci gaba dayi sama sama Bilki tana basu dariya da shirmen ta.

*SARAUNIYAR KYAU* 💓

_(The Glam Queen)_ 👑

```Takun Farko```

Story & Written By:

*_The Nainarh KD_*

_In dedication to my dear Classmate Science G.S.S.S BELE ROAD._

*THE ONGOING BOOK'S*

1. *SONKI NE ƘADDARA TA*

MALLAKAR
FATIMA ABDULLAHI
_Batool Kamba_

2. *ZAN JIRA KA*

MALLAKAR
A'ISHA ALƘALI
_Mrs Aysib_

Page *43&44*

ABUJA_NIGERIA

M.M.K, FAMILY💓

Sun isa gida lafiya, cike da farin ciki dukaninsu suka fito daga cikin motocinsu sannan suka miƙa hanya, palo suka shiga bayan Momy Rafi'at ta danna lambobin sirri ta buɗe.
Gaba É—aya saman kujeru matan suka zube cike da gajiya, dama shi M.M.K tuni yayi part É—inshi.

Lailah ta nisa tare da faÉ—in "A gaskiya mun kwaso gajiya, ba kaÉ—an ba, domin kuwa jina nake kamar anyimin dukan tsiya fa."

Tayi maganar tana kwance igiyoyin takalmin ƙafarta da bata samu ta cire ba, saboda tsaban gajiyar da tayi.

Zaynerb ta ce "Kedai bari kawai, dan gajiya akwaita kam sosai, dan yanzu banajin zan iya zama, har saina ji ni ina take shower ko zanji daÉ—i."

ÆŠagowa lailah tayi tana shirin yima Momynsu magana taga ta nufi staircase's ta fara takawa saboda sauri da bibiyu ma take taka staircase's É—in.
Chapter 48 · 0% Book details