← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 96

Sashe 30

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*👑𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛👑*

*𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔 & 𝑆𝑡𝑜𝑟𝑦 𝐵𝑦*

*𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖`𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ*

{♥︎𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝑘𝑑♥︎}

💘*𝘓𝘈𝘍𝘈𝘡𝘐 𝘞𝘙𝘐𝘛𝘛𝘌𝘙𝘚 𝘈𝘚𝘚𝘖𝘊𝘐𝘈𝘛𝘐𝘖𝘕*💘🤙

<><><><><><><><><><><><><><<><><><><><><><>><><><><><><><

*Page 27&28*

Kallon Haleesat dake hawaye, Momy Rafi'at tayi, sannan murya ƙasa ƙasa ta fara ma ta magana, "Haleesat ina kika shiga ne?, yau ba'a ganki ba a gidannan ba, gabaɗaya lungu da saƙo na gidannan babu inda bamu duba ba, amma bamu ganki ba, faɗamin Menene ya faru dake kuma daga ina kike yanzu?, please tell me, everything my dear."
Duk a lokaci É—aya Momy Rafi'at ta jerowa Haleesat waÉ—annan tambayoyin kuma É—aya bayan É—aya.

Shiru Haleesat tayi taƙi tayi magana sai faman matsar qwalla takeyi.
"wai nace bada ke ake magana bane, da zaki tsaya kina ma mutane kukan banza da hofi," a wannnan taƙin Nainarh ce tayi maganar ranta a mugun ɓace, dan ji take kamar ta tashi ta shaƙe wuyan Haleesat ɗin, har saita faɗa ma ta gidan uban da ta kwana, ta tabbatar da Haleesat ba'a gidan ta kwana ba.

A hankali Haleesat ta buÉ—e bakin da tsaban tsoro har kakkarwa yakeyi, ta ce "Kidnapping É—ina, akayi jiya da dare."

Tayi maganar a gajarce, kuma ta faɗa ne, tana tauna laɓɓanta na ƙasa.

GabaÉ—ayan su suka haÉ—a baki cike mamaki gurin faÉ—in "what kidnapping, fa kikace, anyi naki, to a'ina kuma su waye."

Dukansu suka haÉ—a baki wajen yi ma ta wannan tambayar, amma banda mutum biyu, cikin waÉ—anda sukayi tambayar, wato Zaynerb da Momy Rafi'at.
Zaynerb kwata kwata bata yarda da abin da Haleesat ɗin ta faɗa ba, musamman ma da taga yadda take tauna laɓɓanta na ƙasa, tasan Haleesat farin sa ni bata iya qarya ba, inma tayi sai an gano ta, saboda indai tayi qarya saita dinga cizan laɓɓanta na ƙasa da ƙarfi, shiyasa ma Zaynerb ɗin kwata kwata bata yadda da abin da Haleesat ɗin ta faɗa ba.

Momy Rafi'at kuwa bazan iya cewa ga ainihin abin da ke ranta ba, saboda yadda tayi act, komai qwaqwafin mutum sai dai ya batta kawai😇

"Ki bamu amsar, mana ana tambayar ki, kinyi shiru su waye sukayi kidnapping ɗin naki?, kuma mai suke nema, sannan kuma garin yaya kika kuɓuta idan ma sacekin akayi da gaske?."
Wannan karon Nailah ce tayi maganar ranta a mugun ɓace, da rainin wayon da Haleesat ɗin takeso tayi musu.
Afeefah kuwa kasa cewa komai tayi dan mamaki, haka ma ita Lailah, sai zubawa sarautar Allah ido kawai.

"Dan Allah kuyi hakuri, zan faɗa muku, amma please kubarni, ba yanzu ba, please ku bani lokaci dan Allah na roƙeku," tana maganar ne, cikin haɗa hannaye alamar roƙo, tashi tayi da gudu ta shige bedroom ɗin ta, ta rufo ƙofar da key sannan tabar key ɗin ajikin ƙofar.
Saman bed ta faɗa tana kuma fashewa da wani sabon kukan, saida tayi ma'ishi sannan ta miƙe ta shige bathroom, wanka tayi sannan ta fito wardrobe ta buɗe, ta ciro wata doguwar Gown ta Abaya ash color nd red, ta saka sannan tayi rolling ɗin mayafin Abayar akanta, ko lotion bata shafa ba, ta kwanta saman royal bed ɗinta.
Lumshe idonta tayi tana tariyo abin da ya faru gabaÉ—aya daga jiya da dare zuwa yanzu, rayuwarta ta sauya akala, cikin brain É—inta take tuno komai, tamkar lokacin komai ya faru.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buɗe beautiful eyes ɗinta, zumbur ta miƙe tsaye, tana zazzare idanu, ganin wacca take gabanta, a tsorace ta ce "ta ina kika shigo ɗakin nan?,"

Guri Zaynerb ta samu ta zauna fuska a turɓune, sannan ta bata amsa da faɗin.

"Ba wannan tambayar ya kamata kiyimin ba, kamata yayi kice meya kawo ni, bawai 'ta ina na shigo ba."

Gyara zama Haleesat tayi, ita gabaɗaya tension ɗin da take ciki yasa, ta manta da akwai wata ƙofar ta bedroom ɗin Zaynerb, wanda kai tsaye zata kawoka bedroom ɗin Haleesat ɗin.

Ajiyar zuciya Zaynerb ta sauke, da niyyar zatayi magana, da sauri Haleesat ta ɗaga ma ta hannu, sannan ta ce "ba yanzu ba, dan Allah Zaynerb ki rabu dani, nayi alƙawari zan faɗamiki abin da ya faru, amma ba yanzu ba please please please.

Kallon ta Zaynerb tayi da kyau sannan tana nodding kai, alamar gamsuwa, ta ce "na yarda dake Haleesat, kuma nasan kinsan haka, ni nasan ba zaki bamu kunya, Sannan karki manta Daddy yana ƙaunar mu, yana sonki sosai, dan Allah karki bashi kunya Haleesat, shawara na baki a matsayin ƴar uwa ta gari, kuma mai ƙaunar ki, fatan zaki fahimce ni."

Da sauri Haleesat ta kalle Zaynerb É—in, jin abin da ta ce, É—a ga ma ta kai Zaynerb tayi sannan ta ce "ki fito zamu tafi shopping kuma yanzu."

Tashi Haleesat tayi ta sauko daga kan bed É—in, wardrobe ta buÉ—e ta ciro wani zumbulelan hijjab ash color, ta saka sannan ta juyo tana kallon Zaynerb É—in ta ce.

"na shirya, zamu iya tafiya,"

Da É—unbin mamaki Zaynerb take kallon Haleesat É—in, ganin wai yau kuma hijjab tasa da kanta, a yau, ba'a tilas ta ma ta ba.
Gaza jurewa tayi saida ta kalla Haleesat É—in sannan ta ce tana murza idanu " anya kuwa, Haleesat ce a gaba na?,"

Murmushi Haleesat tayi ita kanta mamakin sauyawarta lokaci guda take.
"Ni ce mana, me kika gani, kikamin wannan tambayar?,"

"naga kin canza, sosai fa, Zaynerb ita ma, ta bata amsa tana murmushi, Haleesat ta ce "a hakan, na canza ko?," Zaynerb ta ce "E, mana."

Fitowa palo sukayi anan suka tarar da gabaÉ—aya Æ´an matan gidan duka, Afeefah, Lailah, Deejarh sai su Auntie Nainarh da Nailah.

Gabaɗayan su sanye suke cikin tufafi iri ɗaya dukansu, Abaya ne ajikin su farare sai kuma mayafin Abayar, shi kuma baƙi hadda Zaynerb, da take tare da Haleesat ɗin.

Deejarth ne kawai sanye cikin doguwar rigar atamfa sai kuma hijjab da ta saka iya gwiwa fari.

Gabaɗayan su kallon Haleesat suke wanda hakan yasa tasha jinin jikinta, Lailah ce ta kasa hakuri ta ce "Auntie Leesat, yau kuma kece kika saka hijjab, hijjabin ma dogo haka, lallai yau akwai story na ɗaurawa a status😀

Ko kula Lailah dake suruntu irinna tsokana, Haleesat batayi ba, saima hannun Zaynerb da ta kamo suka fita daga palon.

Ganin haka yasa suma suka mara musu baya, Afeefah ce take faÉ—in "yau dai muna ganin sauyi da yawa a gidannan."

GabaÉ—ayansu a parking space suka hallara, Haleesat da Zaynerb suka shiga mota É—aya driver yaja.
Yayinda Nainarh da Nailah suka shiga mota É—aya suma driver yaja.
Sai kuma Afeefah da Lailah da kuma Deejarh suka shiga mota guda suma da driver yaja suka bar gidan a nutse.

Momy Rafi'at dake kallon su, ta saman balcony na ɓangarenta, ta sauke ajiyar zuciya tana gyaɗa kai fuskar nan a haɗe kamar hadari yayi baƙi.
Bedroom ta koma da sauri ta É—auka wayarta dake gefan drawer, wata privet number ta lalubo wanda akayi saving da rubutun chinese sannan ta danna ma ta kira.

__🎀____

A bakin wani kata faren shopping mall motocin nasu guda uku duka farare sukayi parking, a tare ko wannensu ya fito daga motar da yake hanyensu cikin na juna.

Habba nanfa kallo ya koma sama wai akace shaho ya ɗau giwa, gabaɗaya hankalin ƴan mata da samarin, dake wajen ya dawo kansu, kyau iya kyau malam, To dayake ita ma Deejarh farace saita haɗe dasu kai sai kace ƙaramar ƙanwar su ce ita saboda yadda sukayi similar.

Cikin nutsuwa da wayewa irinna cikakuna Æ´an boko, kuma waÉ—anda ilimin addini ya ratsasu highly, suke tafiya abinsu a tare.

'MAI KYAU ABBAN FEEFAH SHOPPING MALL'

Deejarh ta karanta abin da taga an rubuta a saman Ƙaton shopping mall ɗin da suka nufa, babban plaza ne mai kimanin hawa ashirin da biyar ciki, kusan komai na glass ne a gurin, ga security nan, masu kula da shige da fice.

Shiga ciki sukayi, baki da hanci kawai Deejarh ta saki, ganin irin kyau da tsaruwa irinna na gurin, gabaÉ—aya ma'aikatan gurin sun taru guri guda suna kawo gaisuwa, ga Æ´aÆ´an 'MISTER MAI KYAU' idan wannan ya kawo gaisuwa aka wuce gurin da yake, wanda akazo kanshi shima yayi, Deejarh bata gama shan mamaki ba, har saida taga wasu daga cikin ma'aikatan gurin sun jero kekunan da ake zuba siyayya a ciki in Aisle, sun taru guri É—aya suna jira su Afeefah su fara zabar abin da suke so, su kuma suke turo kekunan suna binsu a baya, har sai sun kammala.

Hannun Deejarh da ta dage tana nuna ainihin kalar ƙauyanci a gurin, Afeefah taja ganin yadda ta saki baki da hanci tana kallo.
Ɓangaren kayan sawa ta kaita, kallon Deejarh ɗin Afeefah tayi, murmushi ta ma ta sannan ta ce.

"ki zaɓi kalar abin da ranki keso kinji, baki da matsala,"
"to shikenan," Deejarth ta ba Afeefah, amsa sannan ta fara ruwan ido, tsaban haɗuwar gurin rasa dame zata fara tayi, sai faman ruwan ido take tama rasa me zata zaɓa, gane hakan ne, yasa Afeefan tayi murmushi sannan ta fara jidan ma ta kaya kala kala iri iri.

Tun daga kan abayoyi, atamfofi, materials masu tsada, laces, shadoji, £nglish wears, jakun kuna, gyalulluka, takalma, sarƙoƙi na gold, abin hannu.
Zobe, kayan kwalliya, da dai sauran su.

Kallon Haleesat da tayi shiru, Zaynerb ta kuma a karo na ba adadi, tana ƙara karantar yanayinta, ta lura tunda suka shigo gurin Haleesat bata ɗauka favorates ɗin ba, wato €nglish wears ko wasu ƙananan kaya ba, saima atamfofi da yadin hijabai dama hijaban da kuma abayoyi da taga tana faman jido ido rufe.
Sosoi mamaki ya kamata highly, sai dai bata ma ta magana ba, ta rabu da ita.

Hango wani perfect perfume, irin na musamman É—innan kuma wanda ta daÉ—e tana neman kalan shi, bata samu ba, sai yanzu, yasa ta saki murmushi sannan in over rushing, ta nufa gurin, ta kai hannu kenan zata É—auka, taga wani hannun da ba nata ba, yayi gaggawan É—auka kafin nata hannun ya É—auka.
Da sauri ta É—ago dan ganin wani mahaluki ne, haka.

"Tabarakallahu ahsanul khalin😍 Masha Allah😎 Anya kuwa wannan mutum ne tsaye a gabana a wannan TAKUN?,"

Wato tsaban kyau da irin haɗaɗɗiyar surarar, jikin wannan kyakyawan Mutumin dake gabanta ne, yasa tayi wannan maganar, tare da yiwa kanta wannan tambayar, yayinda kyawawan idanunta, suke kafe ta ƙure wa, mamallakin haɗaɗɗiyar kyakyawar surarar dake gabanta😇
Chapter 30 · 0% Book details