← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 96

Sashe 16

Sarauniyar Kyau Takun Farko Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gefen ta kuwa Afeefah ce, zaune a kujera mai lilo dake a garden É—in Al qur'ani ne a hannunta tana tilawa.
Riga ce top fara a jikin ta sai wando crazy jeans black kanta kuma Baby hijjab ne black shima, shiga kala ɗaya ne a jikinsu su biyun kammala karatun nata ne yayi daidai da haske da wayarta tayi alamar dai kira ne ya shigo, waƙar shani'a Twain, "Forever and for always," ya karaɗe gurin hannu tasa ta ɗauki wayar dake a gefenta, nan sunan SISTER NAINARH, ya bayyana saman screen ɗin wayar, sallama tayi bayan tayi picking call ɗin.
Zuba mata ido Lailah dake Kwance saman Grass carpet Tayi, shiru taga tayi da alama magana ake ta ɗayan ɓangaren, Can sai kuma taga Afeefah ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "eh da sauƙi dai......Shiru ta kuma yi can ta kuma cewa "a'a nima dai ba na ce ba kawai dai muna zaune a palon ƙasane mukaga ta faɗo daga saman step's na staircases mu kuma muka kaita asibiti kuma koda muka dawo mun duba bamu ga komai a ta gurin da ta faɗon ba, sannan mun tambaye ta ta ce ita ma bata san meya faɗo da ita ba kawai dai abin ya faru ne in insticnt.."
Ɗan shiru ta kuma yi alamar sauraron maganar da mai kiran nata takeyi, Zumbur ta miƙe tsaye fuskar ta cike matsanancin farin ciki take faɗin "Please sis ki rantse, yaushe kuma a wani airport ɗin gamu nan zuwa Yanzunnan," sai kuma ta katse wayar tana kallon Lailah data zuba mata kyawawan idanun ta tana kallo.
Ta ce "Hello babe Aunty Nainarh ta shigo ƙasar fah, Yanzu take faɗamin, don haka ki taso mu tafi airport mu ɗaukota kawai ba saimun tsaya jiran drivers ko escort bah."
Ɗan waro ido Lailah tayi alamar mamaki ta ce "sister Nainarh kuma ita kaɗai ce, ko kuwa dai." Cike da ƙosawa Afeefah ta ce "ke dalla malama ki taso mu tafi mana, ita kaɗai ne mana dan kema kinsan wannan mijin nata mai kama da zabiya ba zuwa zayyi ba.
Ɗan taɓe baki Lailah tayi "well koma miye ae ita taja ma kanta ace mahaifiyar ta guda ta sama karaya amma sai da akayi sati biyu shine zata wani ɗauko ƙafa ta taho" Lailah tayi maganar cike da takaici, tana miƙewa, suka shiga cikin gidan su fara shiryawa sannan su wuce airport ɗin.

****
💓💔💓
****
"Wai kuwa gwaggo na nace yanzu muna sauka a motar nan shikenan mun shiga birni ko kuma ma a birnin garin habuja ko?, daga yau shikenan bani ba ƙauyenmu,bah su delu babu ƴan ƙauyenmu balle kuma na rama abinda sukamin shikenan sun shani a musilla."
Wata kyakyawar matashiyar Budurwar Yarinya ce duk take wannan zubo zancen ga gwaggon ta a cikin motar da suke zaune a gidan baya ga sauran mutane nan a motar gaba da baya.
Ta ci gaba da cewa "waima gwaggo na yanzu aikin me zan dinga yine idan munje gidan aikin da zaki kaini?, bata tsaya ba ta ci gaba da cewa "kuma shikenan kina kaini zaki dawo gida kiyi auren ki, abin ki, Ki barni a Habuja ni kaÉ—ai bansan kowa ba kowa bai sanni ba, kawai saita fashe da kuka, Gwaggo ta kalleta cike da takaici ta ce "au yanzu dije tun kafin na kaiki gidan aikin zaki faramin kuka kamar na dake ki faÉ—amin na dake kine ko kuwa gidan aikin kikeyi ma kukan ban sani bah."

Cikin muryar kuka budurwar ta ce "toh gwaggo ba kece kika ce a birni zaki barni ba ni kaɗai ba, kuma ae nace miki kiyi hakuri bazan ƙara faɗa dasu hanne ba, kuma fah su suka fara tona na shine ni kuma na rama kuma ke gwaggo ma ae kinsan sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi shine sukamin duka, gefe ɗaya kuma ga dukan da wannan matar tayimin gashi jiki na baigama warkewa bah, fuska ta ma haka shi ne kika kawo ni aiki don a ƙarisani."

ÆŠan tausayinta ne ya kama gwaggon nata, a hankali gwaggon ta ce "ae ke ce dije na hanaki wasan banza dasu hanne amma ba kyaji sannan kuma da kike cewa na kawoki aiki birni ae mahaifin ki shine ya ce a kawo ki aiki birnin bani ba.".

shiru budurwar tayi tana kallon gwaggon sai kuma tayi murmushi ta ce "toh gwaggo makaranta na fah zan ci gaba da zuwa anan abujan kuwa?, ɗan shiru gwaggon tayi kamar mai tunani sai kuma can ta ce "eh to idan kika nutsu highly, ƴan gidan suka ga irin nutsuwar ki wata ƙila su iya saki a makarantar.

Dariya tayi cike da farin ciki da yarinta kamar ba ita ce mai kuka yanzu ba ta ce "shikenan yanzu sunana ya tashi daga dije sai dai Nanah ko kuma ace min Deejarth ko Deejarh irinna ƴan birni, na bar su hanne da wahalar ƙauye da sunan ƙauye," ta kuma gyara zaman ta a motar tana kallon cikin garin abuja ta glass ɗin motar, sannan ta kuma juyowa tana kallon gwaggo ta ce "gwaggo yanzu fah, su ƴan birni sunan su bah irin na ƙauye bane koh?," gwaggo tayi dariya ta ce "sosai ma, aisu ƴan birni sunan su na daban ne, special ne in miki na turawa.

Dije ta ce "ae ina faÉ—amiki gwaggo na muna zuwa gidan aka tambaye ni sunana zance Deejarh ta faÉ—a tana nuna yadda zatayi wajen faÉ—an sunan nata idan aka tambaye ta, wannan karon ba iya gwaggo ne tayi dariyar ba hadda sauran Æ´an motan wata mata a motar ta ce "Deejarh aikuwa suna mai daÉ—i, it's nice name."

Dije tana yanga ta ce "tnx" wai irinna ƴan birni matar ta kuma cewa "hala daga ƙauye kike, Ah ah su Dije an sama guri ga abokiyar hira ta samu ta ce "Yasin kuwa kamar kin sani, daga ƙauye nake amma yanzu na shigo birni ae," matar da alama ita ma "A" ce a gurin surutu ta ce "to su sunan ƴan ƙauyen da naji kina faɗa ya suke?.
wannan karon kallon matar Dije tayi highly, ta dai ga alama gilama ko sunan ƙauye matar bata sani ba.

Hadda sauke Ajiyar zuciya tayi sannan ta ce "sunan ƴan ƙauye yanzu kamar dai ace sunan ki Hafsat a birni tofah a ƙauye ina faɗamiki sai dai a kira ki da hanse ko kuma ace hansi ko kuma hansatuwa 🤣😂😅.

ko kuma sunan ki sa'adatu a birni tofah ina faɗamiki idan a ƙauye ne sai dai ace miki sa'ade ko kuma a kira da sa'a duk da dai sunan gwaggo nane sa'aden amma Yasin na faɗa.

Gwaggo dake gefe ta ce "ae dama kin rainani shiyasa kike kiran sunana haka gatsal" Dije tayi dariya ta ce "gwaggo kenan ae wannan bayani nakeyi shiyasa kikaji na faɗa sunan ki a haka," Dije ta kuma kallon matar ta ce "ni kuma yanzu kamar ni sunana "khadeejah" amma a ƙauye kinsan me ake cemin kuwa?, matar tana dariyar Dije ta ce "a'a saikin faɗa ae zan sani ko?."
Dije ta girgiza kai alamar takaici sannan ta ce "wai fah Dije ake cemin, wasu ma har magajiya suke cemin, a birni kuwa ae sai dai kiji ance deejarth Deenah ko kuma ace Nanah ko Nainarh koma hadiza ga sunan nan dai kala kala sai wanda mutum ya zaɓa a birni.

Wata budurwa ce ta ce "ni kuma sunana AYSHA idan a ƙauye ne, me ake kiran mai sunan?... Dije ta kalli budurwar da ta kira kanta da AYSHA gata ƴar gayu kyakyawa da ita, sannan tayi murmushi ta ce "ae Yasin ina faɗamiki Yadda kike da kyau ɗinnan a ƙauye ba ruwan su sai dai kiji ankira ki da a'i ko kuma indo ko esha ko ma shatu, bah wani sunan ki AYSHAN NAN Yasin, AYSHA tayi dariya ta ce "amma za'a iya cemin Humaira ko A`ishatu acan ɗin ko?," Dije ta ce "idan kinci sa'ah ba."

KUYI HAƘURI DA WANNAN PAGE ƊIN, BANA JIN DAƊI NE SHIYASA.
SARAUNIYAR♥ƘYAU♥FAN`S♥GROUP♥LOVE♥U♥ALL💝

✍️𝖙𝖍𝖊 𝖓𝖆𝖎𝖓𝖆𝖗𝖍 𝖐𝖉 𝖈𝖊📲

*💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋*

𝑀𝐴𝐿𝐿𝐴𝐾𝐼𝑁☆☆𝐾𝐻𝐴𝐷𝐸𝐸𝐽𝐴𝑅𝑇𝐻

{𝑇𝐻𝐸 𝑁𝐴𝐼𝑁𝐴𝑅𝐻 𝐾𝐷}

*Page 17&18*

Haka dai Dije ta ware da ƴan motar sunata kwasan fira kamar dama can sunsan juna dayake ita haka take bata da wuyar sabo da mutum, kowa ya faɗamata sunan shi saita faɗa yadda ake kiran sunan nashi a ƙauye a haka har suka sauka a tasha, sannan suka hau napep izuwa gidan da gwaggon nata take aiki.
A napep Dije ta kalla gwaggo ta ce "wai gwaggo na miye sunan unguwan da gidan aikin naki yake ne?," gwaggo tayi murmushi, tambayar da Dije ta mata, tuno mata da ƴan gidan da tayi musamman ma Afeefah, cike da fara'ar da ya bayyana saman fuskarta ta ce "MAI KYAU DISTRICT" a taƙaice.
A hankali Dije ta maimaita sunan a ranta a fili ta ce "kilama unguwan zatayi kyau tunda naji sunan da daÉ—i fa, kai Yasin ma daga ji bama KYAU kaÉ—ai ba, harda kyan gani."
Ita dai gwaggo bata ƙara kulata ba har suka isa unguwan, zare ido kawai Dije takeyi ganin fantsama fantsaman gidajen da suke wucewa sunƙi su ƙare.

Dije ta ce "lah lah lah gwaggo Yasin gidajen masu shegen kyan kyawu ne, Allah kai sai kace fadar aljannar duniya," ta faɗa tana ƙanƙame gwaggon nata kamar za'a ƙwaceta daga hannun gwaggon nata, Humm ae Dije bata ƙara tsurewa ba, har sai da taga ƙaton Jibgegen katafaren gidan da mai napep ɗin ya saukesu a bakin gate ɗin shi, numfashin ta ne ya kusa tsayawa cak saboda tsantsan kyan gidan wai danma dare ne shiyasa amma ae ba ta ga komai ba. A fili ta ce "aljanar duniya kenan wannan ƙato kuma gandameman gidan haka Yasin ni Dije ta ƙauye naga gurin zama🤣.

Ƙwanƙwasa ƙaramar ƙofar gate ɗin gidan gwaggo ta fara, gate man ne ya leƙo ganin gwaggo ne yasa shi ya buɗewa, da sakin fuska da alama sun saba da gwaggon.
Chapter 16 · 0% Book details