← Book details Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 32

Sashe 9

Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dago Wani magani a kwali mai kamar Abin wanke baki yace wannan zaki dinga shafashi safe da rana a gurin wannan kuma zaki dinga daukar kwaya daya kina saka kwayar maganin jikin jikinki ga abinda zaki dinga Amfani dashi in kinzo sawa ya nuna mata wani irin Sirinji mai kauri na roba!

Su kuma sauran magungunan safe da rana da dare zaki na Sha iya dadin Dana fada miki "
"Kinga na farko ke Ba yarinya bace I Dan kikayi wasa da magani kanki kika cuta bani Ba sabida haka Dan Allah na roqeki ki mai da hankali a kai"
Sannan ina so kicire maganar Auratayya a tsakaninmu a yanzu domin a gaskiya bazan iya kwanciya dake a haka Ba Siyama. Ai gaskiyace kin San ni kin San Halina bana son qazanta bana shiri da mai yinta bana son wari ko qarni nan da nan nake fita hayyacina idan da tsautsayi ma kiga har kwanciya nake jiyya mutukar na shaqi wani Abun da ya dagan hankali
Yanzu ni dake zamu cigaba da Neman magani har Allah yasa a dace ina son kiyi tawakkali da duk Abinda zai biyo baya ! Kinjiko ki kaddara ke haka raki jarrabarwa take zan tayaki da Addu'a iya karfina kuma zan yi kokari in kuyi "yan dabarun da 'kike fada yanzu domin in faranta miki Amma sai kin kwantar da hankalinki"
Dazu kina tambayata yaushe daurin Aure yau saura kwana Uku juma'a za'a daura zamu tafi jibi nida su Faruk zamu dawo a ranar domin gudanar da sauran sha'anin biki!!

"D'ija dai kin Santa kin San halinta to kar'inji kar'ingani dukkaninku babu wacce zan ware a cikinku in fifita da "yar Uwarta sai wacce tafi kyautata min banason tashin hankali da rigima kin fi kowa sanin halina ciki da bai kece babbah kiriqe girmanki babu ruwanki da'ita idan ma tayi miki wani Abu bance ki dauki mataki da kanki Ba idan nadawo ki fadamin mutukar nayi binkice na tabbatar da kece da gaskiya zakiga irin hukuncin da zan mata!
Bana son tashin Hankali wallahi tallahi kukace zakuyi min shirme cikin gida ranku ne zai baci!!
"Ina fatan duk kinji Abinda nace miki?

Cikin Kissa tace habadai yaya Aliyu insha Allahu zaka sameni mai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidanka D'ija ai kanwata ce koda dakaga muna yawan samun sa6ani wallahi sharrin shaidan ne Amma in Sha Allahu zamu zauna lafiya tafada kamar gaske!

"Yace Alhmdullh haka nakeso ita ma D'ijan zan same ta inyi mata fada a kanki tabaki girmanki mutukar kika riqe girmanki Allah kasa mudace ya mike tsaya yace yakamata kije kisha magani ki kwanta haka Amma ki kula sosai Allah yakara sauqi!!
Bin shi da ido tayi bayan yagama Maganar ko wai wayota baiba yaje ya bude kofar dakinsa ya shige yamayar da kofa ya datse harda saka Dan mukkuli!!

*MRS AHAMAD GWADABE*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADIJA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*🅿184*

Kuka Siyama ta rushe dashi na fitar hankali hannu a ka cikin kukan takecewa Wallahi D'ija kin tabowa kanki bala'i D'ija kin tarowa kanki Masifa zan'iya babbaki in dai a kan Ali ne ina yaso ina a kashe ni akan in bari kiyi rayuwar Aure dashi ni ina zaune INA kallo duk in da zanshiga in fita sai nashiga nasa anyi muku muguwar Farraqu da ko hakan zansaya Sai an Sha jina ne ko bukatar jin wani dabbah ko Dan Adam in dai kudi na magani ni Siyama sai na Farraqa tsakanin Ku sai na dasa miki mummunan tarihi Wanda idan akace miki gani a guri zaki kiyayi gurin kinyi ganganci n shiga gonar Siyama yarinyar!

Kamar mahaukaci ya ta kwashi ledodin Maganin Fakam fakam tabude daki ta Afka kan gado tare da watsar da ledodin maganin babu Alamun zatasha su
Da sauri ta tashi daga gadon ta diro kasa tana fyatar majina ta bude durowar da take aje kayan mayanta ta dauko wata kwaya cikin wata farar Leda kananu ta dibi biyu ta mayar ta'aje ta dauki kwalabar benalin guda daya da Wata karamar kwalba da wani Abu aciki kirtif dashi taje ta zauna kan gado ta sanya kayoyin cikin bakinta kana ta Dora da wannan Abinda ke cikin kwalaben
*innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Ubangi Allah kashiryi bayinka*

Tun kafin tagama tsotse kwar dake bakin rafara jinta A sama bingirwa tayi nan kangado bacci yana fizgarta sai kuma ta tashi zumbur taje ta murza mukkuli jikin kofar dakinta tadawo tafada gado rigijib babu sallah babu salati!!
*wa'iya zubbulahi*

********************

6an garan Amare kuwa sai shiri Ake Nene da delu sai faman gyara Amare suke Ummi ba'a barta a bayaba dama tuntuni tayiwa wata kawarta Hajiya Rakiya Maganar wasu turarrika da hajiyar take sai dawa ita dakanta take aikinsu dake mutuniyar mai duguri CE Ummi tace tahadawa yaranta Nafitar Hankali kama daga na jiki zuwa na itace na turara daki Dana tsugo sannan Dana ruwan Wanka duk ta hada masu kyau Hjy rakiya tace kar kidamu Aminiya in Sha Allahu za'ayi masu kyau !!!
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

Hajiya Rakiya tace a kwai magunguna ma masu kyau da zan hada musu Ummi tace ok toum Allah yasaka da Alkairi Aminiya ai ranar daurin Auren zamu dawo in Sha Allah yjy Rakiya tace ai babu damuwa in Sha Allahu gobe ma zan kammala hadawa Allah dai ya sanya Alkairi! Ummi tace Ameen Ameen sannan sukayi sallama ko wacce taka she wayarta!!

To gidan Nene yafara daukar harami "yan Uwa da Abokan Arziqi sunfara halarta gwoggo Altune ta tara su D'ija wai lailai sai tayi musu kunshi kunshin ma dungulmi Ma'ana duk kafafunsu babu wacce ta yadda a cikin su duk ba'la'inta tace yanzu haka za'ayi daurin Auran a rasa gane suwaye Amaran sabuda kun saje da "yan gayya iyi Nene kinajina da yaranan ko!? Nene na kokarin kama Tasha a radio n ta tace Yo ke Altine Ba sai ki kyalesu Ba lalle dai Magani ne Ba kwaliya ka dai Ba duk wacce bataso basai ki kyaleta Ba!h Ummm!

Na'ima tace wai dungulmi laila ma gwaggo ni yanzu kika daura min wannan a kafata ai shikkenan nasan kafar tatashi daga aiki dama dai mai a done Dana yadda!

Da sauri gwaggo tace to ko Aje a siyo salatifi sai in yanka na'iya ai zane mai kyau"

Dariya D'ija tasa tace nidai gwaggo zoki samin A "yan yatsuna na hannu wallahi ina bala'in son Jan lalle daga haka kuwa bazan yadda bah Nima"

Gwoggo tace yawwa "yar gari Amma Dan Allah kubari asiyo salatif din sai in muku dashi kunji ko "ya"yan Albarka!

"Fa'iza tace gwaggo kenan a'ina a ke siyarwa a sayo ni kaman inaso wallahi gwaggo tace tashi muje tare nan nan ne kantin Musbahu! Bayan gida Wallahi idan nayi muku zaku Sha mamaki!!

Tare suka fita su D'ija suna tafaman yi musu dariya Nene ko Uffan batace musu Ba sai bayan fitar su ne ta kalli Na'ima tace ke yau ko kunyi Wanka da ruwan maganin na kuwa?

Na'ima tace Eh mana ai tun sassafe mukayi nida Fa'iza Nene takkali D'ija rai a 6ace tace kefaa!

Inda inda D'ija tafara tace banyi Ba yanzu dai zanyi Nene ta tashi zaune sosai tace bafana son rashin jin magana D'ija wai mai yasa kike saka wasane "yan uwanki gashi duk sunyi ke kina zaune iyi zaman me kikeyi tashi maza kije kiyi shashasha kawai

Simi Simi D'ija ta mike tafita daga dakin taje ta joye ruwan Maganin da'ike cikin wata katowar tukunya ta shiga bandaki dominyi haka kawai sai taji bata son sa ruwan maganin a jikinta Amma Abin mamaki tanayi Wanka dashi tafito zataji kamar an sauke mata dala da Goran dutse a kanta!

Bayan tafito Nene tace to kokefa jeki mayar da Ruwa cikin tukunyar idan An jima sai a mayar da na yamma!!

😄Nene kenan sai kace masu wankan jego

*MUJE ZUWA*

*MRS AHAMAD GWADABE*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADIJA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*ALLAH DAN GIRMANKA DAN KIRMAN ZATINKA DA BUWAYARKA ALLAH DAN QUDARA DA IRA DA R KA ALLAH DAN DARAJAR ANNABI MUHAMMADU RASULLIHI (SLW) KAYI MANA ZA6IN SHUWAGABBANI NAGARI MASU TAUSAYINMU DA KISHIN WANNAN KASAR TA NAJERI'A ALLAH MUNYI TAWWASILI DA ANNABI MUHAMMADU ALLAH KA ZABA MANA DUK ABINDA YAFI ALKAIRI ALLAH KASA AYI ZA6E A TASHI LAFIYA BATARE DA WATA HAYANIYA BA DAN ALFARMAR ANNABI*👏🏻👏🏻👏🏻

*🅿185*

Gwaggo Altine ta kwaba lailai sosai yaji hadi ta zauna ta yanka salatinfi sosai yayi kyau zanen har Na'ima tariqa mamaki

Haka dai suna tarrabi suka mika mata kafafunsu ta kunsawa ko wacce hannu da kafa!

A wanshi hudu suka kwance wai wai Gaskiya abin yabasu Mamaki ganin yadda lailan yayi wani Uban kyau zane fulawar da gwaggo ta zana a GAM din yafito radau dake manya ne yayi wani irin jajazir na ban mamaki!

Sai santin kunshin sukeyi bare ma na hannuwansu "yan ya tsun sunyi kyau gwanin ban sha'awa

Gwaggo tace yo da ba gudu kuke Ba Amman yanzu gashinan bakinku yaki rufuwa!

Nene tace Altine nima kwa6a min Lallan da daddare sai in kunsa naga lallan mai kyaune

D'ija tace nidai gwaggo Dan Allah kar ki qarar dashi zaki sammin in dingayi a "yan ya tsu"

Yo Ai dai in yiwa su talatu waya yanzu in zasu tawo gobe suzo muku dashi domin wannan dai bashi da yawa"

Nene tace Ai na zata zaki sa musu gishirin kunshi Dan yayi Baki

Ai kuwa to bari asiyo sai yafi kyau ma dashi"

Mene gishirin kunshi gwaggo mudai munfi son shi a haka cewar Na'ima

To Ai shikkenan karshenta ma daga an wayi gari yayi baki da kansa tunda lallan mai kyau ne"

Bara na hada mana namu nida Nene da daddare zamu qunsa mukam sai munsa gishirin kunshi ko Nene"

Eh sai Musa mana tunda ado zamuyi Amma dai son samu barshi a jansa yadda zaifi mana magani cewar Nene!
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

Nene tace gobe idan Allah ya kaimu Talatu tazo da wuri zatai musu kitso mai kyau Dan haka kiyi mata waya yanzu sai kifada mata ta tawo musu da lallan"

Gwaggo tace yanzu kuwa zan kirata suna zaune gwaggo ta kira Talatu tayi mata bayani Talatu tace in Sha Allahu zan tawo da Wuri!
Chapter 9 · 0% Book details