← Book details Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 32

Sashe 13

Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ganin tana qifqifta ido sai tabashi dariya Yace "*Khadijatu* Amaryar Ali yau Allah yayi Aure da Mara kwabo ko?
Shiru tayi girgiza kai yayi yace namanta fa ashe ban siyi bakinkin Amarya bah gaskiya yau ina cikin farin ciki Allah ya mallakamin Abinda na Dade ina so a rayuwata

Cikin mamaki Dija ta kalleshi shima ita ya zubawa ido
Yace "kina mamaki ko yarinya Tabbas ina sonki kema kuma nasan kinaso na tuntuni Sabida haka sai murufawa kanmu a siri mu zauna lafiya karkiji nace ina sonki raini ya shi go ciki Ranki ne zai baci Dan son danakeminki bazai hanani hukuntaki bah

Cikin nutsuwa tace "Alhmdullah dama wannan ranar nake jira kafurtamin da bakinka cewar kana so na da da'ake fada ban yadda amma yanzu na yadda da gaskiyar magana kamar yadda kasani ni dai kawai zanyi biyyaya ne in zauna dakai Amma babu burbushin sonka ko kwara daya cikin raina shine gaskiyar magana tafada babu Abinda yadameta! ran shi ne yabaci da jin Abinda tace Amma bai nunabah fuska a sake kamar ba'Ali Ba yace" Ok Haka kikace? "ina wannan son nawa da najima ina ganinshi a kwaryar idonki ko shima namiki karya
Shiru tayi taqi magana yace "babu damuwa ai bazan tilastaki lailai sai kin soni Ba Dan ba'abinda nake bukata Ba kenan tunda anyi mai wuyar Amma kisani ni Namiji ne mijin
Mace hudu dama duk Ku biyon bani na za6a Ba cuso min a kai na kar6a in Sha Allahu zan kawo za6i na wacce nakeso take so na kafin ya rufe baki tace "Wallahi ni nafi qarfin cushe A i kai ka furta da bakinka yanzu ma kuma gashi kaqara fada da bakinka wacce a ka cusa maka daban ni daban tafada cikin tsiwa
Abin mamaki yabawa Ali Lailai yarinyar nan Dan tasamu ya kula shine take kokarin tazageshi daga magana yayi da yasanin fada mata Kalmar so ya riqe abinshi cikin zuciyarsa tunda gashi hakan yana nema yajawo masa raini Nan da Nan yahade Fuska tamau! yadawo Ali na da ya na mata wani banzan kallo yace rashin kunya zakiyi min sabida kinji nace ina sonki Tabbas ina sonki babu qarya amma hakan bazai hana in ci Ubanki ba ni zaki ranawa hankali kice bakyaso kina karankada miya cikin manyan Matan dasuke sona gurin Aiki iyi ke kinsan ko ni wanene kuwa? Ta inda Ali yashiga batan yake fita Ba har Siyama tazo ta cimmusu yana zubah wa D'ija bakaken Maganganu. Kwallah CE ta taru idon D'ija Saura kadan ta zubo jin Abinda Ali yake mata gashi yaqi ya daina Siyama Naji wannan Cin mutumci da me yayi kama!
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

Wani Farin ciki ne ya yiwa Siyama dirar mikiya lokaci da ta tsinkayi zantuttukan da Ali yakewa Amaryarsa na rashin mutuchi tace Lailai wannan mutumi Ashe bai ragawa kowa Ba dubi tujarar da yakewa Amaryarsa kai wallahi naji dadin wannan Abin

Kwantar da murya tayi kamar wata mummuna tace haba hubby mai yayi zafi ne yau fa ranar farin ciki CE a gareku idan laifi tayi maka sai kai hakuri ta kalli D'ija tana tabe baki tace ke kuma amarya waya gaya miki anawa ango laifi bakisan lallabashi ake bah

Shiru D'ija tayi mata batace komai Ba ranta yana mata wani mugun zafi da kyar ta samu ta mayar da kwalar dake kokarin zubo mata ta kauda kanta tana kallon tagar motar Tsaki yaja ya kunna motar yana kallon Siyama tajikin mudubi yace ke kuma mai kika zauna yi a ciki kin zaunar da mutane kamar masu gadi Dan iskanci gyara maganarta tayi cikin kwarkwasa tace na Dan tsaya kimtsa wa ne yallabai kasan jikina babu qwari sosai wallahi ta wani langwabe kai yana kallonta ta cikin mudubin yace kina shan magungunnan ki a kan Qa'ida in CE ko? Kwarai kuwa wasu ma sun kusa qarewa yaya kike jin yanayi jikinki kina ganin sauqin Abin?
Eh to da Sauqi zance tafada Cikin wata irin murya ita lailai dole sai ta ja ra'ayinsa A kwain ya fahimta shima Dan haka sai ya dinga biye mata suna hira Dan ya bakantawa D'ija rai sukai mata banza babu mai kulata Kamar zuciyarta tayi bindiga haka tariqaji tanaji kamar ta balle murfin motar tafita ko ta huta da wannan bakinciki da yake cinta Ali kamar bai San anyi ruwanta a gurin bah suna ta hira da Siyama sai faman qyalqyala dariya rakeyi cikin Farin ciki domin wani abin ma bana dariya bane zata sheqe da dariya duk Dan ta bakantawa D'ija rai A takure D'ija take cikin motar duk yana lure da ita sai sakin tsaki yake cikin zuciyarsa yace yarinya zaki San kince Ba kya sona wallahi sai nai miki Abinda zakizo ki furta da bakinki cewar ina sonka Ali!
A haka suka je gurin dinnar Siyama tafito tana jiran fitowar su Dan Samun shiga jira take wai su fito ta riqe hannun Ali domin zuciyarta tana bata cewar tunda Amarya da Ango sunyi fada kowa zai shiga gurin dinnar shi daya tafi minti biyar da fitowa basu fito bah taqagara

Cikin mota kuwa D'ija na kokarin bude mota ta kasa Ranta a bace takara qaimi amma taqi budewa sai kawai tasaki murfin motar tafashe da kukan da yake cin ranta tundazu Jikinshi yayi sanyi kadan ganin irin kukan datake yi gashi yafara tabamasa zucci yace "mai naimi ki kike kuka ko wani sharrin zaki min kwai Dan kin kasa bude mota sai ki saka kuka Dan shagwaba Ba zakiyi magana a bude miki bah"

Shiru tayi masa batace komai Ba kuma bata fasa kicikicin bude kofar Ba ya *Khadijatu* taqi joyowa kawai sai ya janyota ta kwanta jikinshi yana kallon fuskarta kurr Hawayene kawai suke zubah haryanzu jikinshi ne yafara kyarma gabanshi ya hau faduwa ganin irin ruwan hawyen da ke zubah kamar wacce ya zane! shine bai Sani Ba da wannan wulakanci da yayi mata a gaban kishiya ai gara ya gaggaura mata mari zaifi mata
Bakinshi na rawa ya hau sha fa fuskarta da nufi goge mata hawaye yace "wai mai naimi ki mai zafi ne kike wannan kukan xaki bata kwalliyarki. Doke! hannusa tayi tana yunkurin tashi daga jikinshi zuwa yanzu wata irin jarumta tazo mata yakara dam karta yace Allah sai kinga fada min Abinda nai miki zan sake ki ko kishi kike ne? Hannusa tacire daga fuskarta yana tafaman shafawa Tace" kasake ni in tashi babu Abinda kayi min kawai na tuno iyayena ne? Yace banyarda da akwai Abinda yasaki wannan kukan to in dai nine Allah yabaki Hakuri karki qara kada mushiga cikin jama'a kinayi kinji ko banza tayi mishi tana hararsa kasa kasa bayan tasamu ya saketa yace ki gyara fuskarki karkifita haka kinga idonki yayi ja ko Ni ka bude min in fita Dan Allah bana kaunar zaman motar nan tafada A fusace sai daga Murya take Cikin Nutsuwa yake kallonta yarinyar tausayi take bashi Amma rashin kunyarta ita take cutarta hannuta yariqe yace ai tare zamu fita joyo in goge miki Fuskarki kar jama'a su gane kinyi kuka. Qin joyowa tayi tana Faman kunkuni gami da murguda baki kasan Rigarshi Yakama dake tazarce na wata lafiyayyar shadda Ya janyota ta karfi ya kwantar da ita cinyarshi Karo na biyu ya fara goge mata Fuska. Ita ko sai faman kakkauda Fuska takeyi wannan wane irin goge Fuska ne anqi a gama kokarin tashi tayi tana tsaki babu zato taji fuskarsa dab da tata yana kokarin kama bakinta da kyar tasamu ta fincike jikinta a tsorace tana sakin wata muguwar a jiyar zuciya kamar wacce tayi dambe ta zubah masa kallo mai kamar harara tace dama Abinda zakayi min kenan ka fake da zaka gogemin Fuska iyi Babu Alamu Rahama a fuskarta lokacin datake fadin haka idonshi ya zubah mata Wanda suka kada kadan yana laser le6enshi na kasa murya a tsarke yace laifi ne Dan nasha Ai nawa ne bama nan kadai ba ina da "yanci da zan yi yadda nakeso dake cikin motar nan babu Wanda zai ce min don me domin ke din tawace
Wani kalon kayi kadan D'ija tayi mishi Tace sai da ka gwada karfi ka kwata Amma baza kasamu yadda tabah
Ganin Lokaci yana kurewa yasa yashareta bai mayar ma ta da martani Ba ya lalubi glass dinsa yasa ka kana ya saita kansa sosai ya zuro jikinshi jikinta ya bude motar tanajin nauyinshi a jikinta tsigar jikinta tariqa tashi gabanta sai faduwa yake Allah Allah take yabude tafice daga motar kar yasamu galaba a kanta!
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
Chapter 13 · 0% Book details