← Book details Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 32

Sashe 30

Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hararata yayi kadan yana tabe baki ciki zuciyarsa yace hakan baza tazo ta hau jikina ba sai dole Amma dubi yadda take faman da quma ta tun dazu,

Yana sane ya Dan zame cinyarsa kadan D'ijan tayi taga taga zata fadi tayi Saurin riqe masa wuya da duk hannuwanta biyun tana marairaicewa bakinta sai motsi yake yi da qyar tace yaya Ali dubi fa irin Abinda Aunt Siyama takeyi tamkar mai Aljanu Dan Allah mubar gurin nan wallahi tsoro take bani"

Shan kunu yayi yace babu inda zamu rabuda Mara mutumchi tagama iskancinta a nan gurin,

Sai tafashe da kukan data ke makalewa tace bafa haka akeyi ba Yaya Ali dubah fa ni da bani da lafiya ka kula dani ita mafa hakkinta a wuyanka yake yanzu idan ta mutu a wannan yanayin kacewa Allah me ranar lahira?

Fuskarshi ya cusa tsakanin wuyanta yana shaqar qamshin fatar ta tamkar ya lashi fatar haka yake ji,da qyar muryarshi ta fito yace to Alarama D'ijatu wa'azi kike yimin min ko ko Umarni kike bani? Uhum?

Hankalinta ne yafara dawowa jikinta jin yadda yake goga mata fuskarshi a jikinta gemunshi sai tsikarinta ya keyi ,sai tafara kokarin sauka da ga jikinsa tana gyara baki ,tace ni na'isa in yi maka Wa'azi Abinda kasani ne nake kara tuna sar da kai shi,

Bai ce mata komai ba ya mike ya durfafi inda Siyama ke kwance tagama birgimar da takeyi bacci ne ya kwasheta tamkar mattaciya baka ganin komai sai bugawar nunfashinta bakin ta duk wata farar kumfa ta bushe

Yafi minti goma a tsugune a kan Siyama yana Nazarinta yarasa ma da'abinda zai misalta wannan Abinda tayi yanzu yasan dai tabbas A kwai Aljanu tunda Allah ya fadesu cikin Al'kur ani mai girma,Amma shi a iya saninsa da Siyama bata taba yin iska ba ko a labari yaji tunda duk rabin rayuwarta a gidansu tayi ,dole zai San hakan,

Amma in sha Allahu gobe dole zai zaunar da ita ya tuhume ta sosai,

Hannuwanshi biyu yasa ya kinkimeta yana kauda kai kwata kwata bayason shaqar qamshi qamshin da qarni qarni da yake fita a jikinta babu dadin ji ,yayi hanyar dakinta da ita ,da Sauri D'ija ta taso ta biyo bayanshi Dan baza ta iya zama ita kadai ba'
Sai yau zata taba shiga dakin Siyama tunda take,

*✍🏻,,,,,,,*
A jeta yayi kan bed din ta ya joya da nufin barin dakin ,D'ija na tsaye bakin kofa kamar kace kyatt ta falla da guda,

Hannuta ya kama suka fita daga dakin gami da jawa Siyama kofa,kai tsaye dakinshi ya nufa,

Suna shiga ya nufi toilet domin watsa ruwa yakeso yayi duk da cewar garin babu Alamar zafi duba da yadda damuna ta sauka yanzu haka ma hadari ne a garin Alamun ruwan sama daf yake da ya sauka iska sai kadawa takeyi.

Wannan karon D'ija bata bishi ba zama tayi gefen gadon tana bin dakin da kallo,

Ya waigo yana kanne mata ido daya yace zo ki cuda min baya na ko har kin bar jin tsoran ne?

Shiru tayi masa tana gyara baki na sabo,

Shima bai kara cewa komai ba ya shige toilet din a fili yace D'ijatu sarkin rigima kenan.

Cikin sa'a taji tasamu nutsuwa sai tafara nanata *innalillahi* cikin zuciyarta,

Idonshi a kanta lokacin da yafito domin yayi mamakin yadda ta zauna ita kadai ganin yadda take ta zabure zabure tun dazu

Saurin kauda kan ta tayi ganin yadda yafito dagashi sai towul daure a qugunshi ya rataya wani a wuyanshi yana goge kanshi da jikinshi,

Tabi bayanshi da kallo lokacin da ya nufi Can gurin Mirrow din shi, turare ya dauka yafara feffeshe jikinshi dashi ko mai bai shafa ba, cikin zuciyarta tace Dan jaraba dubi komai ba'a shafa ba ana saka turare kamar ce kai yaya Ali da feleqe yake wallahi,

A kwan ko kallon mai din bai yi ba taga yabude siff din shi ya fito da wata Vest irin ta Unporm dinsu na soja da wandon ta 3Queater ya fara kokarin sawa duk yana lure da kallon da take masa ta qasan idonshi

Sai tayi saurin dauke kanta domin baza ta iya kallonshi a yanayin da yake ciki ba,

Sumarshi ya taje gami da sanya mata mai sosai tayi wani uban kyau,sannan ya joyo yana fuskantar D'ijan,

Saurin dauke kanta tayi ganin ya nufo inda take zaune,

Hayewa yayi kan bed din sosai yana satar kallonta ta kasan idonshi ,ya jawo laptop din shi ya bude cikin Nutsuwa,

Shiru dakin na tsawon minti uku.

Yayi gyaran Murya ba dago kai ba yace zo kiyi min labari mai dadi kinji,

Kallonsa tayi sai taga hankalinshi na kan loptop din shi.

Shiru tayi kan ta a qasa.

Yace ko ba kyaji ne?

Wane irin labari bayan naga Aiki kake yi tafada tana gyara baki Wanda ya zamar mata jiki.

Yace e ae Aikin zai fi dadi idan ina jin muryarki,

Kallonsa tayi cikin mamaki,shima ita yake kallo, yana mata wani tsaddan murmushi ,saurin sunkuyar da kanta tayi ganin yadda kwayar idonsa tayi haske tas Annuri sai sauka yake a fuskarsa ga wani kwarjini dayayi Wanda yayi mugun cika mata ido.

*duk mutumin da zai lazamci fadar subahannallahi walhamdulillahi wala ila ha illalahu wallahu Akabar* tabbas badai mutum ba sai Allah domin duk sharrin mai sharri sai dai yagaji ya qyaleka ,to Ali ba,a tasbihi ya tsaya ba kadai kulum cikin zikiri yake dimun da'iman,

Yace ok toum idan rowar muryar taki kike min je ki dauko Alkur'ani kiyi min karatu ko?

Mikewa tayi ,yabi bayanta da kallo yana sakin a jiyar zuciya duk a takure yake tariga tagama daga masa hankali Rungumeshin da ta rinqa yi daurewa kawai yake yi ,Dole zai rage zaki komai rigimarta domin bazai zauna Abu na tsunkulinshi ba,

Zama tayi gefen kakafun sa,

Yace dawo nan ya nuna kosa dashi

Hannuta riqe da Alkur'anin ta hau gadon sosai ,"yace bissimilh ke nake sauraro"

Cikin Nutsuwa ta bude Al'kurani n tafara kwararo karatu cikin Suratun Yunu's Cikin Muryar ta mai dadin Sauraro, Sosai karatun yake shigar Ali muryarta ta kashe masa jiki ,sai kawai ya rufe loptop din yasa mata ido yana mamakin yanzu dama haka yarinyar take da tajwid lallai Allah yayi masa baiwa da samun kamilar mace

*✍🏻,,,,,,,,,,,*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADIJA*🐾
🏵🎗🎗🏵🎗🏵

*✍🏻WRITTEN BY*
~*Binta Umar*~
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~

~*Mrs Ahamad gwadabe*~

~*DEDIGATED TO:MY FAN'S*~

*🅿2010*

Karatun sai ya fara harde mata a baki sabida idanun da ya sanya mata ,zahirin gaskiya idanun shi suna bala'in kashe mata jiki gashi sai faman lumshesu yake,

Shiru tayi ta dai na ,ya kurawa bakinta ido yace yaya kika dai na yi ?

Tace" ka dauke idon ka daga kai na to"

Murmushi yayi bai ce komai ba ya gyara kwanciya a bed din gami da joya mata baya ,yace cigaba to na daina kallonki

A kuwa A nutse tacigaba da rero karatun ta mai dadin sauraro dama idansa yake Dan kashe mata jiki,

A ta kaice dai sai da tayi wajan izu uku bacci ya fara mamayarta ,jin sautin karatun nata yayi qasa ne yasa ya joyo yana kallonta,

Sai yaga idon ta yayi mici mici Alamar bacci ,ya mike zaune gami da karbar Alku'anin yaje ya aje ,kana ya kalli a gogon bangon dake manne a dakin ,shabiyu saura lallai dole taji bacci dama ga shi an tarashi,

A. Nutse y kalleta tana kokarin sauka daga gadon,"yace ina zaki?

Toilet zani tafada tana kokarin tafiya

Hannunta ya riqe da nufin hanata tafiya,
Yace"mai zakiyi"?

Wanka tafada tana ya mutse fuska,

Girgiza kai yayi "yace ai ke mai tsarki ce ko da yaushe wane irin Wanka yanzu zo ki kwanta idan Allah ya kaimu da Asubah kayi"

Jim tayi tana jin yadda yake mutsika mata hannu Tayi dubarar kwacewa takasa,
Tace"to zan wanke baki na ae ko"?

Wani irin kallo yayi mata mai kamar harara yana Dan cizar lips dinshi yace"A kan me zaki wanke bakinki bayan baki bani na sha ba qarin baiwa ma yau nasan zaiyi dadi sakamakon karatun Alkurani maigirma"

Sun kuyar da kai tayi da sauri tana mamakin karfin halin shi,

Ga wata bala'in kunyarsa data rufe ta lokaci guda jikinta ya mace,

Jan yo ta yayi ta zube a cinyarshi ya sanya duk hannuwanshi ya rungumeta qam yana sauke ajiyar zuciya,

Kwanciya yayi rigingine da'ita ta kwanta kan ruwan cikinsa,yafara laluben Abinda yake mutukar so a Rayuwarshi

_ni kam nan nafice na barsu inai Asubah tagari Ali na D'ija_

*✍🏻✍🏻
Asubar fari Ali ya tashi a nata kiraye kirayen farko kafin sallahe a subah ya mike ya shiga toilet ya tsarkake jikinshi ,ya daura Alwala ya fito ya saka sabuwar jallabiya fara kar da ita kamar ko da yashe ya Shimfida dadduman ya fara gabatarar da *Raka'atanil fajiri* yayi addu'oin sa, kana ya mike jin ana kokarin tada sallah ,ya kalli D'ija dake kwance cikin bargo bacci take sosai sai sauke a jiyar zuciya takeyi ,sosai yarinyar take bashi tausayi, yasan jiya qarfi kawai ya gwada mata Dan San kansa zuciyarshi taki hakura da ita mutukar tana kusa dashi bazai iya jurewa ba,

Girgiza kai yayi ya fice daga dakin da nufin in da yadawo sallahr Asubah ya tasheta tayi Wanka gami da sallah

Kafin ya fita ya tsaya kofa Siyama ya kwankwasa mata shiru yafi minti biyar yana aikin buga kofar shiru bats bude ba yaja tsaki yayi gaba Abinshi,

Ita ko D'ija tun fitar Ali daga dakin ta farka tana ta yunkurin tashi zaune takasa sakamakon jin yadda a ka wani daddadanne ta hatta Dan ya tsanta ya qi motsi gashi dai idonta biyu babu Abunda bata gani na daki dai dai da joyawar da fankar dake tsake a saman celling din dakin tana gani Amma takasa motsi

Ga wani irin kauri da miyan bakinta yayi duk a sarqe yake bakin tamkar an daure Mata shi

Gefen da gefen fuskarta hawaye ne ya fita,

Sai tafara karanta Ayatul kursiyu cikin zuciyar ta *Bissimillahi lazi la ya dirru mas'mihi shai'un fil'arabi wala fi sama wati*
Chapter 30 · 0% Book details