← Book details Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 32

Sashe 22

Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kallon in da D'ija take zaune bai yi bah lokacin da ya shiga dakin nata tasan dai yayi sallama ta Amsa , ya wuce ta a falo ya shige bedroom din ta.

Gabanta yafadi tace waye kuma ya6ata masa Rai haka Ni Khadijatu, domin ta lura fuskarsa kirtif take bakamar sanda yafita Ba,yafi minti goma dashiga taji yana kwala mata kira,

Da sauri ta Mike tana addu'a cikin ranta Allah sa ba'ita bace, tana shiga tace yaya Ali sannu da zuwa,

Banza yayi mata yana zaune gefen gadonta har yaci re kayan jikinshi daga shi sai singlet da gajeran wando , yana daddana Waya , yace je ki dauko mana plate muci Abinci, jiki na rawa ta tafi ,bayan ta kawo ya nuna Mata ledar kusa dashi yace hada mana yadda zai ishemu ,ki zauna kici Abinci sosai Dan na lura dazu bakici da yawa Ba,

Bata ce komai Ba ta zauna kasan kafet ta hau hada Abincin tafito musu da ruwa da Lemo cikin frijin dake dakin,

Yana kallonta takasan idonshi tagama hadawa kanta a qasa tana jin kunyar kallonshi a haka ,yace Oya fara ci mana nima yanzu zan sauko,Bissimillah tayi ta sanya hannu. Cikin Abincin tafara ci gaskiya taji dadin sa sosai Dan haka taci yadda ya kamata duk wata yunwa ta daina ji ,yace yawwa kokefa ,saukowa yayi ya zauna kusa da'ita gami da tankwashe kafafunshi , yace toum tunda kin koshi fara bani nawa yafada gami da tsareta da idanunshi masu kaifi,

*✍🏻,,,,,,,,,*

*INA TAYA DAUKICIN "YAN NAJERIA MUNAR SAMUN NASARAR LASHE ZABE. DA MAI GIRMA BUHARI YAYI ALLAH YA TAYA SHI RIQO ALLAH YAI RIQO DA HANNUSA , YA ALLAH KABAMU ZAMA LAFIYA DA KWANCIYAR HANKALI A NAJERIA*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*NANA KHADIJA*

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*🅿201*

Sun kuyar da kai tayi yace kin bani mana kunyar me kikeji ne "yan mata na Uhm Ai zan can kunya yaqare ko har yanzu da saura sai in cire miki ita babu Matsala"

A jiyar zuciya ta sauke gami da zumbura bakinta ,ta debo Abincin cikin hannta kamar yadda tayi masa dazu ,yace wallahi ki daina zumbura min baki idan Ba haka Ba zan wuce haushi na a kanshi kinji ko?

Saurin gyara bakin tayi tace to ka bude bakinka mana ,Anqi din yafada yana kanne mata ido daya yace dawo nan ya nuna cinyarsa da hannushi,

Gabanta yafadi sai ta maqe kafada irin na yara , yace mai yasa ? Umhum , Cikin zumbura bakin dai tace babu, Dariya yayi qasa qasa yarinyar na burgeshi in tana yin salonta na shagwa6a, bai kara CE mata komai ba ya bude mata bakinshi tafara bashi Abincin , kamar dazu yana lashe Mata hannu"

Tsigar jikinta ta dinga tashi ,da qyar tace Ni ka daina side min ya tsuna babu dadi Wallahi"

Yace karya kike Yarinya nasan dadi kike Ji, idan ke Ba kyaji ni inaji baki San ni Mayan ki bane?😳
*tofa Ali fa ya soma kauce hanya*

Ido ta zubah masa tana kallo cikin Mamakinsa,, yafaga mata girarshi guda yace Billahillazi hakane,ko baki yadda bane yanzu in gwada miki misali"

Da sauri ta daga kai tace na yadda mana"

Sai yasa dariya ganin yadda take zare ido duk ta tsargo ,ita ko D'ija wani mugun Mamaki Aliyu yake bata ganin yadda yake ta sakar mata Fuska kamar Ba wanan mutumin Ba mai dacin rai, wata zuciyar tace mata Ba Dan Allah duk yake miki haka Ba jikinki yake so,tabbas hakane ta Aminta da Abinda zuciyarta tace mata ,sai kawai tahade fuska Dan gaskiya bazata yadda ya yi mata Wani Abun Ba yanzu domin ita kadai ta San yadda yakeji a qasanta,

Tana bashi Abincin yana can bin ilahirin jikinta da kallon kurrula tabbas da gaske Ali mayanta ne domin babu Abinda baya birgeshi a jikinta,

Bayan tagama bashi ne ta gyara gurin tsaff sannan ta zauna can kan Sofa tana ciccin Magani,

Duk yana kallon sauya warta na lokaci guda bai kawo komai ba a ransa ya ce zo nan Ungo, Kallon Hannushi tayi Key din dakinshi ne yake mika mata,
Tace mai zanyi dashi to? Hararta yayi yace daga nan zakiyi min magana ko rashin kunyarki ta tashi zaki sauke a kaina yafada yana gyara fuska'

A nutse ta mike taje ta kar6i makullin tace mai zanyi dashi?

Ki bude ki dauko min loptp dina zaki ganta gan bed"

Wucewa tayi yabi bayanta da kallo yanaji kamar ya kamota ya rungume , A fili yace rigimarmiyar yarinya kawai,

*Bani da chaji Wallahi*😘👏🏻

✍🏻,,,,,, ,
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🏵🏵

Ya na zaune a inda yake takawo masa karba yayi ya gyara zamansa kan gadonta , ita kuma ta wuce toilet domin yin Wanka da'ike anfara zafi a garin ga ruwa yaqi sauka,

Bayan tafito ne sai tafara sinqe sinqe cikin jin nauyin yadda zata canja kaya a gabanshi , sai satar kallonsa take tana duba kaya da qyar ta lalubi wata Riga mai taushi doguwa ce amma tana da yan kaken hannu sai botir a gabanta rigar zatayi dadin sawa da zafi,ta boye cikin hijab ,simi simi tayi hanyar fita daga dakin,

Yana kallonta bace mata komai Ba yaci gaba da danne dannensa , babu a binda yadameshi

A karamin falonta ta qimtsa tsaf sannan ta koma cikin dakin , tafara Neman hula dar da zata sa a kanta Dan baza ta iya zama da hijab Ba ana wannan mugun zafin,

Da qyar ta samu Hular ta sanya a kanta sannan ta kwabe hijab din , hular tayi mata kyau sosai da sosai Ba mai a cuci bace Amma sai ka rantse a cuci tayi sabida yadda gashinta yayi tozo tsakiyar kan nata duk da cewar a kitse yake,rigar tabi ta lafe mata a jiki hatta shedar wandonta naci ki a na gani sabida kwanciyar da tayi a jikinta, turaran gurin Hajiya Rakiya tabude ta lakata ta mutsuke jikinta dashi ai kuwa kan kace kwabo qamshi ya gauraye dakin ,

Ta gabanshi tazo ta Wuce, cikin yanayin tafiyarta,

Kanshi yana qasa Amma duk wani motsinta a idonshi yake , yabasar da ita ne shima ganin tanaso ta raina masa hankali shiyasa yayi watsi da ita,

Amma INA!! Kasa jurewa yayi lokacin data giftashi , da sauri yadago kai yabita da wani mayan kallo, yana ganin zasu hada ido sai yai sauri ya kau da kansa hade da shan kunu yaciga Ba da daddene dannansa cikin loptp,

Zama tayi cikin kujra tana kallonsa kadan kadan , cikin ranta tace ina dai yabani wayata danaji dadi wallahi sai in kura su Fa'iza da Nene, wata zyciyar tace mata ki gwada tambayarsa mana kila in kika ci sa'a yabaki,

Ai kuwa sai ta maqe murya tace Yaya Aliyu"

Cikin Mamaki yadago kai yana kallonta babu yabo babu fallasa,

Kanta ta sun kuyar domin bazata iya jurar kallonshi Ba ,

Yace menene? Kin kirani kuma kin sun kuyar da kai bafa nasan Muna furci,

Umm dama Um! Cewa zan yi Wayata dai zaka bani Dan Allah kaji" tafada cikin shagwa6a
🏵🎗🏵🎗🏵🏵
🏵🎗🎗🏵🎗🎗

Tsaki yayi ya mayar da kansa ya cigaba da Abinda yakeyi,

Sai ta hau maganganu kasa kasa ,humm! Wai mutum da wayarshi ni kabani Abata ko a fashan take sai in lallaba ta haka,

Ya dago kai a karo na biyu yana kallonta yace mai kike cewa zagina kike yi ko? Da sauri tace A'a wallahi cewa nayi kabani wayata , ta canja maganarta,

Yace ban yadda Ba zagina naji kina yi domin kin saba ai dama,

Sai ta hau rantse rantse Allah kuwan ban zageka Ba wallahi cewa fa nayi dama zaka bani wayata da na kira su Fa'iza mun gaisa haka kawai fa nace tafada kamar zata saki kuka tana mamakin sharrin Ali da lauya magana,,

Yace tun wuri ki zo nan kibani hakuri domin bazaki rai na min hankali Ba tsaf najiki lokacin da kike zagina zaki wani canja magana, in dai nazo nan gurin Abin bazai miki kyau Yasin!

Gaban ta ne yafadi tace wai wannan mutumin wane irin ne da kullum Ba yason zaman lafiya sai takale takalen fada , kawai sai ta shareshi taqi zuwa , yace kin gwammace in zo nan A she?

Banza tayi dashi , sai shima ya rabu da ita kawai yaciga da Aikinshi, wayar Faruk tashigo yadaga cikin Sallama Faruk yace gobe fa dole mufita bakin Aiki sabida mutannan sun matsa Wallahi

Yace nima Abinda nake tunani kenan yanzu haka ina qara binkice ne a kai , Faruk din yace yayi kyau Allah ya kaimu gobe" Amin cewar Ali,, Faruk yace ina Amarya take ? Kallon D'ija yayi yace gata can a zaune yanzun nan tagama zagina" ta zageka?,Faruk din yafada" kwarai kuwa,

Gaskiya ban yadda Ba sharrinka ne wallahi D'ija baza ta zageka Ba , dariya Ali yayi yace Dan dai bakansan halin yarunyar nan bane,ae

Humm in ma zaginka tayi kai ka jawo Faruk tafada yana dariya, Shima dariyar yake yace Abinda zakace kenan ko"

Yo mai zan ce maka Ai kunfi kusa, haka dai sukaita shaqiyancinsu a waya D'ija na fahimtar wani Abin wani kuma sunyi mata dungu , sannan sukayi salama ya kashe wayar,

Ko Minti goma bai qara Ba ya rufe loptop din ya Mike ya shige toilet domin yin Wanka, duk tana kallonsa tana kwance kan Sofa tana saqe saqe cikin ranta,

*✍🏻,,,,,,,,,,,,*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🎗🏵

Ko da yayi wankan ko Mai bai shafa Ba sai turaranshi na fama da ya rambada a jikinshi , ya zira Wando gajere ko karamar riga bai saba sabida zafin da a keyi duk da AC a dakin dama can Ali Ba sa shiri da zafi ko kadan,

Yayi daidai kan bed yana lumshe ido , duk tana kallonsa ta kasan ido tayi lokimo a zuwan bacci takeyi,

Yafi minti goma da kwanciya ,kana yabude idonsa daya yana kallon inda take kwance yace *Khadijatu* shiru babu Amsa ,sai yaqara kiranta a karo na biyu , nan tayi lamfo , yace nasan idonki biyu , malama in zakiyi bude ido ki bude ina kallonki ae tunda na fito daga toilet kike kallona , wa zaki karya"
Chapter 22 · 0% Book details