← Book details Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 32

Sashe 31

Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Addu'ar tariqa nanatawa cikin zuciyarta hade da Ayatul kursiyu, Sai tafara jin wata iska guguwa daga wajen tagar dakin hatta labulayen dake kewaye da dakin sai suka fara kadawa suma ,duk tana kallo babu halin motsi, taci gaba da nana tawa cikin zuciyarta hawaye na fita

Can tayi firgigit! Ta mike zaune a zabure bakin ta dauke da Kalmar *innalillahi wa'innalihi raji'un*

Sai jikinta yafara rawa tafara bin dakin da kallo duk wannan bugawar da labulayen dakin suke yi bata gani ba haka nan wannan muguwar isakar da tariqa cin tafiyarta Sam babu ko Alamarta'

Kafarta tana karkarkawa ta sakko daga kan bed din jikinta nannade da bargon da suka rufa dashi sabili da babu komai a jikinta ,taje ta yaye labulen window din dakin tana leqen waje wai ko zata ga ana iskar ,babu Alama iskar sai Alamu da gari ya nuna an danyi yayyafi cikin dare

Da sauri ta saki labulen tayi hanyar fita daga dakin fuskarta Duk ruwan hawaye sun bushe bakinta dauke da Addu'on ne man tsari,

Ta murda kofar taji a kulle gam ,Ali yasanya Dan mukkuli ya kulle dole sai ya dawo ,

Sai ta zube nan bakin kofar ta nannade jikinta guri guda gami da zubawa Window din dakin ido bakinta na motsi da Alama Addu'a take yi,

Ko da suka fito daga massalacin Ali da Faruk basu tsaya wata doguwar hira ko wanne ya shige part din shi..

Ko da Ali yashi ga kaitsaye dakin Siyama ya nufa domin ganin halin da take ciki

Wannan karon bugu biyu yayi ta bude masa jikinta sanye da kayan jiya idonta duk wata kwantsa koriya shar da'ita fuskarta duk ta tasa tamkar mai Dan yan jego.

Saurin kauda fuskarsa yayi zuciyarshi tana hantsile ganin wannan kwantsar dake idonta wannan shi ya tabbatar masa da cewar batayi sallah ba har yanzu

Ya mutse fuska yayi bai kalle ta ba yace kije kiyi sallah ki fito falo ina son magana dake kan in fita Aiki Allah ya shirye ki in
zaki shiryu ,yafada gami da joyawa ya barta nan tsaye cikin mutuwar jiki,

*✍🏻,,,,,,,,,*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*DEDIGATED TO: MY FAN'S*
🏵🎗🏵🎗🏵🏵

Ya sanya Dan mukkuli ya bude dakin nasa ,da sauri ya tsaya jin yayi tuntube da Abu ya kai ganin shi gurin ,mai zai gani D'ija zaune ta kurawa guri guda ido hawaye ya na kwarara daga idonta ga jikinta sai faman rawa yake yi,

Cikin rashin hayyace ya tsuguna kusa da ita gami da kama hannayenta ya riqe bakinshi na rawa yace"menene kuma "? Kalau fa nafita na barki mai yasa kike kuka a bakin kofa"

Kallonsa tayi ba tafasa hawayen ba ta kura masa ido kurrr!! Kawai sai ta fashe da kuka ta fada kansa ta Rungume da dukkanin hannuwanta tana sheshsheqa gami da Ajiyar zuciya,

Babu zato yaji ta a jikinshi nan yayi zaman "yan bori shima ya qamqameta yana sakin a jiyar zuciya tamkar ya taya kukan haka yake ji yarasa yadda zai yi da Al'amarinta wallahi yana Jin yadda zuciyarta take wani irin mugun bugu,

Sai da ta Dan nutsu sautin kukan nata ya rage fita,

Sannan yayi gyaran murya yana shafa bayanta hade da Dan bubbugawa Alamar rarrashi ,daidai kunnen ta ya saka Bakinta yana hura mata iskar bakinsa,kadan da kyar ,yace "kiyi hakuri ki fadamin menene kinji ko ki daina daga min hankalina bana son wannan koke koken da kike yi ,in dai Dan na kwanta dake ne kike kuka to bazan kara ba"

Tausayi ya bata tana tausawa kanta tana tausaya masa sake riqe shi tayi ,sosai tace"babu komai Mafarki nayi irin Wanda ban taba yinshi ya bani tsoro wallahi"

"Ok to maimakon kiyi Addu'a sai ki zauna bakin kofa kina koka Dan shirme ,yafada yana dago kanta da nufin kallon ta, su ka hada ido tayi sauri ta sunkuyar da kanta tana matse fuska,

Yace" kinyi sallah ko Kuwa"girgiza kai tayi Alamar bata yi ba,

Ran shi ya 6aci ,yace shirme kenan bakiyi Wanka kin tsarkake jikinki ba kinzo kin zauna kin 6arewa mutane baki kina kuka Mtssss,tashi ko yanzu ranki ya baci yafada rai a bace,

Mi kewa tayi daga jikinta tana zubaro baki gaba gami da gyara bargon dake jikinta Wanda ya ke barazanar faduwa kasa tayi sauri ta riqe da kyau Amma ina sai rabin qirjinta yafito muraran ta dalilin haka ,tayi sauri ta rufe tana satar kallonsa ,

Tsaki yayi ya mike yana mamakinta ko me zata boye masa a jikinta Wanda bai San shi ba oho ,
Kai tsaye toilet din ta nufa ,har zata bude sai gabanta yafadi ta joyo tana kallonsa ,yana kokarin Ciro kayan Aiki dake saqale a hangar' ya waiwayo yana kallonta yace" menene kuma?" Gyara baki tafara kafin tayi magana cikin harhada kalmomi tace" kazo ka tsare min bakin kofa tsoro nake ji"

Joyawa yayi ya cigaba da Abinda yakeyi bai ce mata komai ba,

Sai tafara buga qafafu irin na yara tace"kaji fa Abinda nace ko"

Wai gowa yayi a slow yana kallon Abinda ta ke yi ,dariya yasa kadan gami da girgiza kai ya joya ya cigabah da Abinda yake yi a karo na biyu,
Yace "sai kibari idan kin hafi danki kya bashi Umarni ,Amma bani ba"

Tsaff ya shirya ya waiwayo A karo na Uku yana daura Agogo ya nufi in da ta kalmansa suke aje,Abin mamaki tana nan a tsaye a jikin toliet din,kallon a gogo n hannunsa yayi karfe shida da minti biyu,batayi sallah ba wai mai yake damun yarinyar nan ne?ya ke tambayar kansa

Fuska babu walwala ya kalleta yace wallahi ranki zai baci *Khadijatu* zamu bata dake bana son shirme da shiririta karki sake ki dauki sarar da ba taki ba ki dubi time fa shida na safe har ta gota bakiyi sallah"

"Ita ma cikin Nutsuwa tace wallahi tsoro nakeji Dan giman Allah kazo ka tsaya min ko a nan ne nayi ,ni ban San yadda zanyi ba ma in kafita tafada tana matsar fuska,

Bai ce komai ba ya mike bayan yagama daure takalmi ,ya durfafi in da take tsaye

Yace shiga muje in yi miki wankan tunda haka kike so"

Gabanta yafadi cikin inda inda tace"ae ba ca nayi bazan iya wankan ba cewa nayi ka tsaya min a nan "tafada tana nuna gurin

Hannuta ya kama suka Afaka toilet din "yace sai kiyi kuma ni ba yaro bane da zaki rainawa hankali sarai na fahimci Abinda kike nufi"

Bin shi da ido tayi tana mamakin qarfin halinshi tana tsaye taga ya hada ruwan zafi da na sanyi ya surka gami da ciro soso a ma'ajiyarsa ya ,aje ya zo inda take tsaye yana kokarin fincike bargon jikinta ,da sauri ta riqe bakinta yana rawa ,tagaza cewa komai,

Fizga daya yayiwa bargon sai gashi a hannunshi ,D'ija tumbur a gaban Ali,

Sai tayi sauri ta tsuguna ta kudindine jikinta guri guda tamkar tafashe da kuka,

Ko kallonta bai yi ba yazo ya sungumeta a haka ya aza cikin ruwa yafara wanke ta babu Abinda ya dameshi

Tariqa kaukauda da Fuska ita lallai baza ta kalleshi ba ranta a bace yake sai faman zunguro baki take gaba

Yace "mudun baki dai na hararata ba gami da zubaro min wannan Abin Wallahi yanzu zanyi maganinki ae kin Sani ko"

Fashewa tayi da kuka tana buga Ruwan da kafafunta Wanda ruwan sai tsalle yake yana tamfatsi duk yajiqa masa kayan Aiki,cikin kuka race"ae ni ba Abinda nace kayi min kenan ba ni zan iya wankana"

Yace babu wani Malama Sam ba haka kike nufi ba ae nagoki,kuma tunda kika jiqamin kayan Aiki sai na dau fansa ae kin gane ko"

Yafada yana daga mata girarashi guda,yacigaba da cewa Amma ba yanzu ba sai anjima daddare zan rama,"

Cire hannushi yayi daga cikin ruwan bayan yagamacu data ,ya ce kiyi wankan tsarki ki fito ki sameni kina zama da najasa a jiki ae dole ki dinga mugan mafarkai, yafada yana kokarin fita daga tolite din,

*✍🏻,,,,,,, ,,,*
Qeyarshi tabi da harara tana ya mutse fuska ita tarasa wane irin mutum ne Ali yanzun nan sai ya canja maka magana ita ga Abinda tace dashi yayi mata yazo yayi mata Wanka, Wani ruwan tasake hadawa mai tsabta sannan tafara Wanka kamar yadda Addini ya tanada.

Yana fita daga toilet din kai inda kayansa na Aiki suke a saqele yakara nufa a karo na biyu cikin sauri ya cire na jikinshi sakamakon jike masa su da D'ija tayi garin sangar tarta ya canja wasu tsaff ,sannan ya fita daga dakin yana duba a gogon hannunsa.

Siyama na zaune a falo a hakinmce tana Allah Allah Ali yafito ya fada mata maganar da yace zasuyi gefe guda kuma tana so ya fita itama tafita domin su tafi Ai watarwa da danduna aikinshi Dan jiya kwanatayi batansan inda kanta yake ba tana ta mafarkinshi har garin Allah ya waye.

Kallo daya yayi mata ya dauke kai gami da yin hanyar kchin ,cikin Sassarfa,tayi sauri ta mike tabi bayansa ,yana shiga kchin din tashiga, tace"yaya Ali mai za'ayi maka naga ka shigo kchin? Tafada tana wani langwabe kai ,

Ban za yayi da ita yana kokarin kunna gas kokarinshi ya dafa ruwan tea ko Dan D'ija Shima kuma bazai fita bai duma ma cikinshi ba.

Da sauri tazo ta karbi Ashanar hannusa tace"kabari in dafa maka kome ye Dan Allah bai dace mu barka ka shiga kchin ba"

Kallonta yayi a dage yace sai yanzu kikasan da haka sarkin iyayi da kinibibi"

Raurau tayi tamkar zatayi kuka tace" ba haka bane wallahi"

Baice mata komai ba ya bita da ido har ta kunna gas din .

Ta daura tukunya da ruwa a kai,

Yace"mai zakiyi a nan "

"Wai da indomee zan dafa maka"

Mtsss dallah kauce kibani guri malama waye zai ciki miki indomee?

Da sauri ta Matsa daga gurin ya sauke ya aza karamar botar da yake tafasa coffee nashi a kan gas din yayi hadin kayan kamar yadda ya saba ,yana tsaye ya tafasa ya joye a cup mai Dan zurfi ,ya kalleta yana ya mutse fuska yace"kina iya dafa duk abinda ranki yakeso,ya kama hanya barin kchin din

Bayansa tabi zugwizgwi domin ta dokanta taji Abinda zai fada mata shiyasa ko yunwa bata ji duk da cewa yanzu gari yawaye,
Chapter 31 · 0% Book details