← Book details Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 32

Sashe 8

Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da toilet zai shiga yada kata yana kallon Faruk din yace wai daga ina kake ne?

"Naje na karbo mana dinkunanmu mana Wanda zamuyi Amfani mu da Amaranmu Faruk din yafada yana kara gyara kwanciya kan kujerar"

Mtsss Ali yaja ya bude kofar toilet din yashige bai kara bi ta kan Faruk din bah!
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

Bayan ya fito daga toilet din Faruk yace meye Abin tsaki tunda a kafara lamarin nan a banji kace bah ana maka kokari kanawa mutane tsaki!!

Ya mutse Fuska Ali yayi yace kai Al'amarin ya shafa ai naga sai wani gargajiga kake sai kace wani sabon Ango!

Rasa Abinda zai ceawa Ali yayi Dan haka hakar ya bude yana fito da Abinda yake ciki

Katikan daurin Aure ya fito dasu ya jefawa Ali Wanda ke zaune gefen gado yace gashi nan in da Wanda zaka bawa domin munan duk tuntuni mun rabah Dan Ba tsayawa sauraran shiriritar ka za muyi bah"

Dariya Ali yasa gami da daukar katin yana dubawa yace dama dai kun tsaya saurarata koko Neman shawarata da Abin sai yafi kyau gami da qayatarwa!

Allah ya sawaqe mu tsaya sauraron Wanda ya rafi yakin Neman za6e gami da kafa gwamnati kaga muda muka kama a hannu babu Abinda ya damemu!

Shiru Ali yayi masa yana duba katin yace yayi kyau kuwa Allah ya sanya Alkairi Ameen!

Faruk yace Ameen suma Ameen"

"Yanzu sai Abu nagaba jiya Munyi waya da Abbah a kan maganar kayan Lefe tuntuni mun sa an hada komai da komai nida Dr Ko bai gaya makaba Dr din?

"Ni babu Abinda ya fadamin Abinda Ba kwa sakani a cikin lamarin yafada kamar gaske"

"Faruk yace musaka cikin Lamarin ka rusa mana wallahi sai dai kaza Dan kallo!!

"To naji in zama dan kallo ni dai in bukata ta zata biya shikkenan Kuje Ku qarata da bukukuwanku yafada babu Abinda ya shafeshi!

"Faruk din yace Abbah yace Maganar lefen yaran A bari sai an daura Aure tukkuna ko wacce za'a kai mata dakin Mijinta Sunanan a a jiya gurina"
Yace ana gama daurin Aure za dungumo a dawo nan sabida gudanar da Walima da shauran sha'anin biki!

Kai kaga kai sha'anin biki yadama nifa banki a wanko min ita a kawo min Ba babu ruwana da wani sha'anin biki yanzu mybe ma bara nar da'aka daura za'a kaiwa ko matarshi Ba sai an tsaya bidi'a mtssss!!

Kaga Ali Faruk din yafada a hasale yace Wallahi bazaka bata mana yadda muka tsara Ba babu ruwanka in kaga dama kafito ranar da'za'ayi launching"to idan baka fito Ba babu Abinda zai hanamu gabatarwa domin Dan kai kadai baza mu fasa bah!

Kwanciya yayi kan gado yana kallon yadda faruk ya hakikance gami da tada hijiyar wuya
"Yace Allah yabaka hakuri Allah ya Sanya Alkairi malam!
"Ni ka rabu dani inji da Masifar da Siyama taje ta jefa kanta ciki!!

*MRS AHAMAD GWADABE*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADIJA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*🅿182*

Daka tawa Faruk din yayi da Abinda yake yana kallon Ali jin Abinda yace!
Mai ya Faru da Siyaman!?

Yana kwancan dai idonshi a lumshe yace bata da lafiya taje ta dauko ciwo mai wuyar warkewa"

Wane irin ciwo ne faruk din fada cikin jimami"

Mtsss nifa bana ce maka Ba garin irin cushe cushen su na mata taje tasaka wani Abu mai dauke da kwayoyin cutarwa ga Dan Adam mussaman mata!
Dr yace mutukar ana son kwanciyar hankali sai an dauke mata mahaifa domin sinadarin kwayoyin cutar daga Mahaifar yake fitowa!

*inallahi wa'ina ilaiyi raji'un*

Faruk yafada cikin tashin hankali yace wai mai yake damun mata ne fisabillahi Dan rashin hankali komai sai su dinga cusawa a gabansu iyi!

Allah ya kyauta Ali yafada yana sakin a jiyar zuciya!

"Yanzu kai mai kace a kan hakan"?

"Ina jira tagama Amfani da magungunan da Dr ya hada mata idan Ansamu nasara Alhmdullh idan a kasin haka aka samu zan wa Abbah magana sai ya sami mahaifinta ya warware masa halin da'ake ciki"

"Allah ya kyauta hakan yayi Allah yasa a dace wallahi tun yanzu har nafara tausayin yarinyar rashin haihuwa bashi da dadi!

"Kwata kwata Siyama ba'abar tausayi bace ko yanzu daka ga ina fadi tashi a kanta sabida hakkinta da yake wuyana ne shiyasa kawai!

"Ni yanzu ma nafara zargin yarinyar kasan Ba cikakkiyar mace na same taba"

"Zan iya lissafah maka Tara ta da ita a tsawon Shekarunnan wannan ma kawai domin hakkinta ne !

"Abin Mamaki gami da daure kai wata kesawa Magani nidai Ba kwanciya nake da'ita bah!"

"Kar kasaka zargin komai a ranka zaka bata Auranka kai dai kacigabah da hakuri gami da tayata nai man magani kawai Allah yasa A dace"

"Amma gaskiya yarinyar nan ta cuci kanta Wallahi"
Faruk din yafada cikin jimami!

Tabe baki Ali yayi yace kanta ta cuta ni babu Abinda zan fasa ina sa ran ma wata shekarar in haihu da yardar Allah!

"Allah ya Amsa Addu'arka Faruk din yafada"
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

"Yace kazo ka dubah kayan nan tashi zanyi in shaga gidah!

Mikewa Ali yayi ya sauko daga gadon yazo ya zauna kusa da Faruk din yana dubah dinkakkon shaddodin dasuke cikin wannan jakar da Faruk din ya shigo da'ita

Riguna ne "yar ciki da babbar riga guda Uku an yi musu Aiki mai bala'in tsada da qayatarwa sai huluna kalar zaran da'a kai dinkin dashi!

Sai ta kallama guda Uku kalar shaddar dai sawu ciki ne safar ma kalar takkalmin ce gaskiya tsarin yayi kyau!

A kwai na Matan ma guda Uku iri daya duk do gayan riguna ne sun Sha Uban Aiki da Manya Manyan duwatsu a jiki sosai dun Ku nan sukayi kyau!
"Faruk yace waddan nan zamuyi Amfani dasu ranar daurin Aure ne kawai Akwai Wasu daban suna gurin Dinki Mussaman nasu matan gobe idan Allah ya kaimu zan karbo musu!!

Ina so dukkaninmu muyi Amfani da kaya iri daya a ranar A kwai nasu Nafisa da Siyama da Matar Dr shima daban ne sai gobe shima zan karbo musu shi "
"Hakan Yayi ko?

"Kwarai Abu yayi kyau cewar Ali yacigabah da cewa ina takalma da zasu saka ai bangan su a nan Ba!

"Faruk yace shaf na manta Wallahi dole gobe mufita tare sai a harhado duk Abinda yai saura dul kun sakar min lamarin ne kai da Dr dole wani Abin in manta dashi!

"Yace duk kai ka daura kanka tunda kaga zaka'iya ai shikkenan sai muzama "yan kallo. Yanzu tunda ka sakani ciki in Allah ya kaimu goben sai in raka ka karasa siyayyarka"

Mi kewa Faruk din yayi da niyar Fita yace idan ma bakaje ba zani da kaina Babu abinda zai kakare min tunda ya zama shaura!!

Tare suka fito Ali ya rakashi waje anan ma sun Dade a tsaye suna tattaunawa kamar baza su rabu Ba sannan sukayi sallama ko wanne ya shige gida!

Yana Shiga ledodin Maganin Siyama ya fito dasu riqe hannunsa ya hau kwankwasa kofar dakinta!

Siyama Na kwance bacci ya soma fuzgarta taji ana bugu da Sauri ta tashi tana Mutsika ido ko tamtama babu Ali ne!

Ta diro daka kangadon daga ita sai wani mitsi sin wando mai kama jiki hade da wata riga mai yankakken hannu mahadin wando duk cikinta a waje domin dai rigar kirjinta kawai ta tare gashi ta dameta da kyau!

Ta bude kofar tana magagin karya tayi kamar zata Afkawa Ali! Yai sauri ya dauke kansa daga gareta ganin irin kayanda suke jikinta Wanda basu da Maraba da tsirara !

Joyawa yayi Da nufin komawa Falo yana tafiya yace kifito nan zan miki bayanin yadda zakiyi Amfani da Maganinki!!

*MRS AHAMAD GWADABE*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADIJA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*🅿183*

Bayanshi tabi zuwa falon bayan ya zauna ya daura idonsa a kanta tana kokarin zama kusa dashi!

Cikin ya mutse fuska yace meye Haka ke wai ba kya kunyar nuna jikinki ne? Gantsaro kirji tayi tana wani fari da ido tace wa zanji kunya kai ne fa kadai a gurin kuma kai halaliya ta ne!!

Yana ta6e baki gami da girgiza kai yace lailai ne sai nagani to dallah malama tashi kije ki sanyo hijab ki suturce jikinki Wallahi shiyasa babu wuya shai danun Aljanu sun shiga jikinku!

Kin tashi Siyama tayi sai ma ta dawo kusa da kujerar da yake zaune ta kamo hannunsa ta riqe cikin nata tana murzawa cikin qwarewa cikin Marai rai cewa tace wai ni yaya zanyi da raina ne ko ina babu dadi haba mijina Abin alfaharina da tunkawo na yanzu laifi ne Dan ka ganni a haka karka manta nifa matarkace ko kaima kafara qyanqyamina sabida lalura tafada cikin Marairaicewa kamar gaske!!

Gabanshi ne ya fadi ganin ta dawo kusa dashi tana naniqarshi shan kunu tayi kamar bai taba dariya yace yanzu meye kike haka sakar min hannuna Malama!
Ke baki da lafiya ma baza kibar jarabah Ba!

Sakin Hannunsa tayi tana share hawayen muna furci tace gaskiya Ali kana cutar dani wallahi wai sai kace kwata kwata bazan rabe ka Ba wannan fa zalunchi ne tafada rai a bace idan kai zaka iya jurewa ni bazan iya Ba gaskiya

Mamaki ne ya kamashi jin irin maganar datake fita daga bakin Siyama !Wai yana zalintarta!

"Yace to yanzu me kikiso Ayi?

Babu kunya tace a matse nake gaskiya kayimin "yan dabaru"

"Kyalkyalewa yayi da dariya domin bakaramin dariya tabashi Ba"

Yanayi yace wai ke Dan Allah mai yasa baki da kunya ne Menene "yan dabaru"
Mtsssss! To ban'iya ke da baki da lafiya ina ruwanki da wani da wani "yan dabaru iyi"?

Shiru tayi yace tambayarki nake fa?

Duk ta muzanta takasa daga kai ta kalleshi gefe guda kuma tana jinjina iskancin Ali wai ita zai kife ya nuna bai gane mai take nufi bah!

"Yace OK toum tunda kinki fada shikkenan ai"

Zazzage magungun yayi a kan kafet yana nuna mata yadda zatayi Amfani dasu daya bayan daya gefe guda kuma yana Allah Allah yatashi yabar mata gurin jin warinta yafara busowa hade da kamshin wani turare Mara dadi sai Abin yabada wani irin Wari da kamshi Mara dadi!
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🎗🏵
Chapter 8 · 0% Book details