← Book details Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 32

Sashe 28

Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sukace to ba damu wa Hajiya zamuyi miki ,Kan kace kwabo sun hau kan bolar tsakiyarta suka samu wani dogon sanda suka fara tona wa, sosai tayi zirfi san nan suka sakko , sukace an gama Hajiya

Jiki na rawa Rukyy tafito da kudi ta raba musu sannan tace suyi tafiyarsu,

Guri yayi tsitt dake dama can hanyar baka sa fai mutane suke bin ta ba sabida yadda a keyin yawan gamo Sam gurin bashi da kyau ,ga shuri (gidan tururuwa) kusfakusfa A gurin

Rukyy tace maza kifito kije ki binne yanzu babu idon jama'a

Da sauri Siyama ta bude murfin motar hannuta dauke da wannan koko ta dirfafi katuwar bolar nan ga duhun magariba ya karato

Haka ta dinga hawa bolar duk tsayin ta bai dame ta ba sai da ta tadda gurin da suka tona sannan ta tsaya riqe da kokon tafara Surutai kamar yadda A ka Umarce ta duk tafadi bukatarta a kan D'ija sannan ta sunkuya ta sanya kokon ta mayar da tarin bolar da'a ka tono ta rufe gurin staff

Ta sakko Cikin Sauri jikinta sai zabga wari yake tafada mota tana sauke Ajiyar zuciya Rukyy taja motar cikin Azama suka bar gurin!

*✍🏻,,,,,,,,*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
~*DEDIGATED TO:MY FAN'S*~
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

Yamma tayi sosai lokacin da suka karasa gida A gajiye Siyama tace Rukyy ta'aje ta a gida kafin ta wuce ,Ai ko haka A kayi bata shiga da motar ba A waje ta ajeta ,ta joya ta tafi tana kara jadda dawa Siyama dole gobe ma ta San yadda zata fito domin su daura in da suka tsaya,

Buga katon get din tayi ,da sauri wani soja ya taso ya bude kafadarshi rataye da bindiga

Ganin ita ce sai ya matsa ya bata guri domin shigewa gami da gaisheta

Sama sama ta Amsa ta wuce ciki tana bin ilahirin motocin dake gurin A aje ,gabanta ya fadi ganin motar Ali wannan ne ya tabbatar mata da cewar ta dawo,

Ai ko ga gabanta yana faduwa ta durfafi hanyar part din nasu

Karo suka kusa yi dashi fitowarshi Sallah r magariba ganin lokaci yayi jikinshi sanye da jallabiya ruwan toka kanshi sanye da hula irin ta larabawa As'usel Hannushi manne da carbi mai ma dannai

Sauri tayi tabashi hanya bakinta yana rawa tace yaya Ali sannu kadawo A she?

Harararta yayi yana tabe baki yace ke zan wa sannu ,ae daga ina kike?

Cikin harhada kalmomi tace Wallahi in gaya maka Ashe jikin nata yayi tsanani dayawa gaskiya momy na nashan wuya ha wan jini ne yanzu ma daga Asibiti muka dawo,

Bai tsaya ya sauraranta yayi gaba ganin ana kokarin tada sallah yasan duk qarya take yau dai za'ayi ta takare

Sai bayan sallah isha ya dawo gidan ,zama yayi a falo yana kallece kallace

D'ija tafito daga dakin ta jikinta a mace tazo ta zauna kujerar dake fuskantarsa ,kallo daya yayi mata ya gane bata cikin walwala Dan ba haka ya fita ya bar ta ba

Yace yaya Akai ne? Ko jikin ne uhumm?

Shiru tayi tana ya mutse fuska ,

Yace kinyi sallah?

Daga masa kai tayi kawai taqi furta ko A

Nazarin ta yafara yi tabbas A kwai damuwa

Yace dawo nan kanji
Ya nuna gefenshi

Babu musu ta tashi ta koma kusa dashi

Qugunta ya kamo da hannu daya ya manne ta a jikinshi ,yace fadamin Abinda yake damunki ba haka nafita na barki ba ,naga har girki kin mana gashi can kan daining ko?

Daga kai tayi tana ya mutse Fuska ,yace yawwa to fada min kinji ko

Kafin tayi magana Siyama tafito bagaz bagaz tana tabkawa D'ija wata muguwar harara kai tsaye hanyar kchin tayi domin samarwa kanta Abinda zata ci

Ali ya buga mata wata muguwar tsawa wacce tasa babu shiri ta tsaya jikinta na tsuma

Yayi mata kallon banza yace wai ke mai yasa baki da hankali ne har yanzu wa zaki nunawa gadara kinfito buguzun buguzun dake tamkar wata tunkiya babu kintsi mtsssss yaja wani mugun tsaki!!
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADIJA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
*_[Binta Umar*]
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~

~*Mrs Ahamad gwadabe*~

💝💝💝
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
💝💝💝

~*DEDIGATED TO:MY FAN'S*~😘

*🅿208*

Sai tafara kame kame ,yace zo nan

Simi Simi ta karaso inda suke zaune Afakaice tana harar D'ija ganin ta kwance jikin Ali wani bakin kishi yana turnuko mata

.yace mai zakiyi yanzu? Sai ta marairaice kamar gaske tace wallahi yunwa nakeji yaya Ali zan shiga in samarwa kaina Abinda zanci

Kallonta yake a dage yace a in da kikaje yawon naki baki ci Abincin ba?

Haba Ya Ali Mom dina ce fa bata da lafiya yaushe zan samu nutsuwar cin Abinci tafada tana kakalo hawaye

Tsaki yaja yace yaushe rabonki da yin sallah da Alama wannan fuskar taki yau bata ga Ruwan Alwala ba"

Sai tafara inda inda zatayi magana ya daga mata hannu yace bana son dogon magana wuce kije kiyi sallah kafin ki dafa Abin can"

Simi simi ta shige bed room din ta tana zagin D'ija tamkar ita ce tayi mata

Ya mai da idonshi kan D'ija wacce ke kwance gefen kafadarshi sai lumshe ido take kan ta yana Sara mata,

Sai yaga jijiyar kan nata tafito radau da'Alama kan yana ciwo sosai

Yace *Khadijat*
Babu Amsa ,sai ya dago ta kacokan ya daura kan cinyarshi suna kallon juna Fuskarta ya zubawa I do yana Nazari

Yace me ke damunki wai bafa nasan gadda ma uhumm?

Da qyar tabude bakinta tace kaina ne yake Sara min"

Ok zazzabin ki in ce ko?

Uhum ina ji tafada tana matse ido domin zafin da kan yake yaso ya ta6a mata ido

Yace Muce kici Abinci kisha magani ko?

Ba tace komai ba ya mike tare da ita hannunshi Cikin qugunta ya riqe

zuba mana ko yafada bayan sun zauna kan kujerar dainnig din , A ddafe ta hada musu ,ganin bata jin dadi bai shigo da tsirfarshi ba shine ma yariqa bata Abaki

Suna ga maci ya mike ya nufi bedroom din shi domin ya lalubo mata magani domin baya rabo dasu cikin ransa yace dole kiyi ciwon kai ni kaina ba daidai nake jin jikina,

Ita ma D'ija mikewa tayi cikin Mawuyacin yanayi Wanda bata ba ji ba A rayuwarta ta nufi nata dakin

Kai tsaye toilet tashiga ta hada ruwan zafi ta kwabe tashiga ciki domin kara gasa jikinta,

Tana zama Cikin Ruwan tafara jin kokan Mage ,gabanta ya yanke yafadi sai tafara waige waige cikin toilet din ,zabura tayi tana kokarin fitowa ganin wasu lafta laftan qadan garo jikin bangon toilet din sai kallonta suke ,kafin tayi yun kurin guduwa. ,daya ya fado yayo kanta gadan gadan!!
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
~*DEDIGATED TO: MY FAN'S*~
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

Da mugun gudu tafito daga toilet din tana kurma ihu tun karfinta domin ko da can tana bala'in tsoran qadangare sosai ,ta yayi hijab din sallahr ta domin suturce kan ta tafita a gigice sai ihu take gashi ta manta da duk wata Addu'oin tsari ballanta tayi

Dakin Ali ta nufa kafin ta karasa sai gashi yafito da sauri sunyi karo domin yajiyo ihun ta

Kamata yayi ya Rungume qam yana tofa mata Addo'oi jikin ta sai kyarma ya keyi yana jiyo yadda gabanta yake mugun faduwa a qirjinshi

Siyama tafito da Sauri ta tsaya daga bakin kofarta tana kallonsu ,tace yaya Ali mai ya same ta?

Yace zazzabi ne mai zafi take dashi kin San haka yakeyi ballan tana nata typhoid ne haka yake mata dama duk lokacin da ya tashi"

Sai ta karaso gurin tana sakin Murmushi cikin Ranta kamar gaske ta sanya hannuta taka ma D'ijan tace Ayya sannu kanwata kinji Allah yaba ki Lafiya

Da sauri D'ija ta fizge hannta tana dauke kanta daga kan Siyama ganin tana riki de mata kamar wahainiyya gashi lokacin data kama mata Hannu tamkar Allura a kasa a ka caki tafin hannuta haka taji

Bai ce komai ba yaja ta suka shige dakinsa ,suka bar Siyama tsaye a gurin,suna shiga sai tasaki dariya ,tai sauri ta gumtse bakinta ta hanyar sanya hannu kasa kasa tace Ayi dai mugani idan tusa zata hura wuta ,Wallahi dani kike zancan D'ija kin tabo wa kanki bala'i

Tana shiga dakinta taga wasu bakaken kayan saqi a kusurwar gefen gadonta zani da wata bin jimemiyar riga gabanta yafadi ,sai kuma ta tuno dama ae bokan yace zata dinga sawa,mybe Dan duna ne ya aje mata
Kafin taga ma tunanin komai taji kafafunta sun fara karkarwa ,bubo tsoro ta nufi gurin da kayan suke aje taje ta dauko ta sanya a jikinta ,gama sawarta ke da wuya tafadi a gurin
*wa'iya zubillahi*

Tana jikinshi A maqale ya zauna gefan gado yace wai maye kike ta kurma wa mutane iho ne kefa kinfiye shashanci

Sai tafashe da kuka wurjanjan da qyar tace yaya Ali Mage da qadangaro nagani a toilet din na Wallahi na bar dakin Har Abada

Zuba mata I do yayi na minti biyu yana kallo shi dai yasan bata yadda za'ayi qadangare yashigo gidan nan ,gwara ma mage sabida wasu daga cikinsu suna ki wanta a gidan,

*✍🏻,,,,,,,,,*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
~*DEDIGATED TO: MY FAN'S*~😘
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

Riqe ta yayi sosai a jikinshi ganin yadda take zabure zabure sai ya cigaba da tofa mata Addu'oi har tasamu nutsuwa kadan ,yayi gyaran Murya yafara kokarin cire mata hijab din jikinta ganin yadda take faman zabga gumi sai kace wacce tayi tsere'

Rike hannunsa tayi tana kokarin hana shi cire mata hijab din sanin da tayi In yacire mata babu komai wando a jikinta ballanta wata uwa briziyya,

Sai ya zuba mata ido yana kallo ,ganin yadda take takure takure jikinta yasa ya fara bin ilahiri jikin nata da kallo,

Tsaki yayi lura da yayi da Abinda take boyewa ya fahimci babu kaya a jikinta

Yace ki cire hijab din kisha iska ba kya ganin yadda kike gumi ne"

Zumbura baki tayi cikin tsarguwa tace kyaleni A haka"

Ok tashi muje ki nuna min kadan garun da kike maganar kin gani"

Gabanta yafadi sai ta matsa kusa dashi tana qifta ido kamar zata fashe da wani sabon kukan.

Tace Allah ban qara shiga dakin nan yaya Ali ka ga kuwa Labta labtan qadangarun da nagani kuwa baqaqe wuluk ,humumm!! Tafada cikin shagwaba
Chapter 28 · 0% Book details