← Book details Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 32

Sashe 3

Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hijab kawai tazira dama ta tawo da nata Wanda Ali ya sai musu ita da D'ija suka fita gami dayi musu Sallamar sai sun dawo Jameel sai faman tsokanar D'ija yake tai masa banza

Yana zauna cikin mota yaga fitowarsu daga gida

Tun Kafin su karaso ya fito daga motar ya dakawa D'ija wata muguwar tsawa yace koma kije ki saka Hijabi karki karaso nan A haka!!

Saura kadan D'ija tasaki fitsari Dan bakaramin razanata tsawar Ali tayi ba sai tace tunda take dashi bai ta6ai mata tsawa irin ta yau ba!

Da sauri ta juya da baya tana kallon filin gurin Allah yasa babu jama'a sosai sai "yan yara kananu duk da cewar. Gurin baya rabo da matasa to Amma babu mamaki. Tunda Tara ta huce duk sun watse daga gurin kowa yatafi kimtsawa domin zuwa kasuwa!
Taji dadin hakan sosai Wannan wulakanci da meyai kama sai kace wata "yar cikinsa ya kewa tsawa
Kamar zata Fashe da kuka ta koma gidan domin dauko hijab!!!

*MRS AHAMAD GWADABE*
👌🏻👌🏻👌🏻
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADIJA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*🅿165*

Nene zata tada Sallah taga D'ija tashigo rai A 6ace tace lafiya kuma kika dawo kina bacin rai?

"Humm Wai hijab zan sa nifa wallahi Nene Dan kin matsa ne da sai inyi zamana. Sai ya dinga yiwa mutum tsawa kamar "yar sa"

"Dariya Nene tayi tace Sai kiyi ai ke har yanzu kin kasa gane halin Ali ko ?
Dan Allah dauki Ku tafi kin San dama baza ya yadda kibishi a haka ba

Hijab din ta nemo ta zira bata cewa Nene komai ba tafice daga dakin da rai a 6ace!

I ita suke jira domin har ya kunna mota Fa'iza na kujarar baya a zaune tayi tsuru tsuru!

Kusa da Fa'iza n take kokarin Zama bayan ta bude motar

Ta cikin miroow din motar yake kallonsu yace daya ta dawo nan domin ni babu yarinyar da zata mayar dani drevar n ta"

Kallon Fuskarsa D'ija tayi taga babu Alamun Rahama Ai ko ita nan da nan ta hau gyara Fuska domin kar yakawo wargi a gurin domin dai tayi bala'in jin ciwo tsawar da yayi mata dazu!

Babu wacce tayi motsi a cikinsu Fa'iza na zungurar D'ija !! D'ija najin ta tayi mata shiru domin ta San Abinda take nufi!!

Babu yadda Fa'iza ta'iya ta Bude mota zata fito.
Ali ya dakatar da ita yace koma ki zauna a inda kike waccan marakunyar dai ita nake so ta dawo nan din

Dadi Fa'iza taji sabida haka sai ta sake gyara zama Abinta

Ta fi minti biyar Kafin ta fito ta kuma kusa da shi din duk yana kallon ta ta miroow din!

Tana shiga yata da mota Suka fara tafiya babu maimagana a cikinsu

Fuskarshi take satar kallo tana so ta tambayeshi Wayarta Amma ganin yadda ya Sha kunu yasa take jin shakkar tambayarshi Amma dai bara ta gwada tagani

Cikin Salonta tace ina wayar tawa kace zaka bani tana cikin motarka!

Kamar da dutse take magana ko kallonta bai yi ba!!

Bata daddaraba ta kara maimaitawa Amma wannan karon sai data kira sunansa

Ta gefen ido ya kalle kadan ya mai da hankalinshi kan tukin motar da yake yace "Anqi Abaki Wayar ki kwata in zaki'iya!

Kallon Shi tayi tana gyara bakinta na sabo tace kamar yaya in kwata fa kace?

"Eh hakana nace"

Zuba Masa ido tayi cikin Mamaki!!

"Yace Dauke min waddannan idanuwan naki daga kaina"

Dauke kanta tayi tace kai kace fa zaka bani har gayawa Nene kayi yanzu"

"Eh ni nace zanbaki yanzu kuma nafasa da A kwai damuwa ne"?

"Tabe baki tayi ta dauke kai tace babu wata damuwa karike wayar ka kawaii in Sha Allah gobe zaka ganni da wata"

"I tama kwacewa zanyi Sai nai ra'ayin ki kiqe waya zaki riqe yarinya"

"Lailai ma D'ija tafada tana dariya kadan tace Meye hujjarka ta riqe min waya harda i kirarin zaka hanani amfani da'ita na Farko dai ba kai ka sai min ba !

Gyaran Murya yayi yace ke bana son shashanci Kina faman yiwa mutane dariya a kan titi ke ko kunya bakiji yanzu da da wannan mayafin zaki fito wai ke Dan Allah mai yasa ba kyaji ne?

"Nifa ka takurawa rayuwata sai ace kullum mutum sai ya sanya hijab tabdijam"! Tafada wani fari da ido

Duk yana kallon Abinda takeyi ta gefen idonsa saurin dauke idonsa yayi daga kanta lokacin datake lumlumshe idonta da sunan fari!
"Cikin ransa yace in na dakata wannan "yar sai tasamu mu fadi a motar nan!!!
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADIJA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*🅿166*

"Yace ke A yanda kike a haka ai in kina yawo a titi batare da Hijab ba dayawa jama'a zasu shiga wani hali wasu har ta kaisu ga hadari!!"

"Nice zan zama hadari ga jama'a? D'ijan tafada domin kwata kwata bata fuskanci inda maganarsa ta dosa ba"

Ko Nuffasa bai bari tayi ba yace kwarai kuwa" gwara ki dinga suturce kanki In kikaja hankalin wani ban yafeba kuma Alhaki a kanki"

Cikin Mamaki D'ija take kallonsa tace Alhaki a kaina fa kace to mai nayiwa Mutune da har zan dauki hakkinsu"?

"Ke kika sani yafada gami da murtuke fuska!

To itama D'ijan shiru tayi bata kara Magana ba

Fa'iza ko na kujerar baya tana jin hirartasu tanawa D'ija dariya Sam bata iya soyyaya ba a cewarta! Gefe guda kuma tana chatting da Dr dinta Sai soyewa suke Abinsu!!

Wayarshi ce tayi kara dama ya jona ta a chaji a jikin motar kallon fuskar water yayi! Siyama ce!

Bude muryar wayar yayi bayan ya daga

"Yace Lafiya wai kar kidameni Malama nace zanzo anjima OK"

Kuka tafashe dashi tace yanzu baza ka fahimci halin da nake ciki ba ya Ali"

"Wani mummunan Labari naji wai zaka Auri Yarinyar nan D'ija "

"Da Sauri ya katseta ta hanyar cewa dakata Siyama dama Abinda zaki tambaye ni ke nan?
Ki ke ta damuna a waya Eh hakane saura kwana Uku daurin Auran ma in haka kikeso kiji to !

Rurucewa tayi da kuka tace shikkenan ni haka zanzo in koma a banza duk a kanka na hadu da cuta mai wuyar magani ni yanzu yaya zanayi ni Siyama"!

"Tabashi tausayi yace kin ga ya isa ki daina kukan haka Mtssss kina so kifasa min dodon kunne OK"!
"Yanzu yaya kikeso Ayi miki? Ko nuffasawa batabari yayi ba tace so nake kazo kai nakeson gani!
Dariya tabashi cikin zuciyarsa yace in zo ki kasheni da Warinki"!
Sai da yasaci kallon D'ija kadan Kafin yace wai in nazo mai zan miki ne nace miki zanzo komai dare ki kyaleni kinji ko!!
Tace to kayi hakuri Dan Allah in takura maka zanyi zaman jiranka tafada kamar gaske"
Yace OK sai nazo ki dinga Addu'a komai yayi tsanani maganinshi Allah kinji ko"
To kawai tace masa Amma bata dauki maganar da muhimanci ba tana nan da qudirinta na ko ita ko D'ija Dan halak kafasa!!

Kallon D'ija yayi da gefen ido bayan ya kashe Wayar tayi kicin kicin da Fuska ya lura tunda yafara Waya da Siyama ta Sha kunu!!

Shareta yayi yaciga ba da tukinsa hankalinshi kwance!

To A haka Suka dinga Faman zaga dangi babu ina da basuje ba Duk in da sukaje sai ai ta jansu da wasa da tsokana ga Amarya da Ango sunzo Sallama!!

"Shi Kam Ali dake muskili ne baya biye musu D'ija ko sai tsagalgala take dake duk kakannita ne Shiyasa take zuba iya shegenta son ranta Fa'iza natayata"

Wata karamar kwanwar su Nene da suke kira gwaggo Altine!
"Tace kuzo muje daki dama muyi wani sirri banaso wan can Malalacin yaji mai zamuce tafada tana kallon Ali"

Bai ce musu komai ba sukazo suka Wuceshi gwaggo Altine na Hararasa
Dariya yasa yace wai ni ina ruwana dake ne tunda nazo kike hararata ko Dan nace banayi dake ne kin min tsofa nafin Son Nene!!

Banza tayi dashi suka shige daki ita dasu D'ija harda bugo kyaure!!

Agogon dake daure a hannusa ya kalla Sha biyu shaura yace Allah kuka jima a ciki sai dai Ku nemi mai mai daku gida domin tafiyata zanyi!!

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADJIA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*ALMUMINU YA ALLAH*

*🅿167*

Zaunar dasu tayi kamar wacce zata koya musu darasi

Wata Leda ta jawo cike da gari kan magani A daddaure gefe guda kuma ga jarkar zuma nan a ajiye ta kalli D'ija tace dauko ko funa gasu can A kwando a kife babu musu D'ija taje ta dauko ta na Binta da kallo!

Ko wanne garin magani sai data hada shi da zumar ta dama shi sosai zumar ma wata iri ce Dan dagani taji kayan hadi sabida irin yajin datake fitarwa ga wani bauri da Dan dano mai kama Baki!

Da Sauri D'ija tacire bakinta tana furzarwa tace anya kuwa gwaggo zan iya Sha wannan Abin kinji bakina kuwa yadda ya dauka!!

Tabb Aje kufin maganin tayi tana tabe baki!

Ita ko Fa'iza duk da tanajin rashi dadin Abin Abakinta ta daure tana Sha kadan kadan! Sabida tasan meye amfanin Abin

Gwoggo Altine tace ke banason shashanci dauki ki shayeshi Tass bayanshi ma sai nakara dama muku wani kun shanye a gabana domin bazan Baku kutafi dashi ba kuje kuyi min Asara tunda baku San Amfanin Abin ba A to!!!
Haka za'a kaiku dakin mijinnaku batare da gyare gyare ba Ku zaku shawahala A can din in Baku tsaya An gyara Ku ba!!

"To wai gwaggo Maganin menene nifa ban fahimceki ba D'ija tafada duk da ta soma dago hasken Abin"

"Ban Sani gwaggo n tafada tana harararta tace Allah sai kin shanye A bin nan zan qyaleki kinga "yar Uwarki ta kusa shanye nata ko

Kallon Fa'iza tayi tabbas ta kusa shanye nata dariya tayi tace lailai sis kin bada Amanna bafa kisan ko maganin menene ba sai faman Sha kike sai dariya take mata!

Hararata Fa'iza tayi batace komai ba sabida tasan Iskancin D'ija ne kawai!

Sai in CE Ku San a tare suka shanye da ita da Fa'izan domin tana saga kufin kurba daya tayiwa Abin ta shayen rabinsa!
Chapter 3 · 0% Book details