← Book details Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 32

Sashe 19

Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki Ali yaja A fili yace Dallah Malama zoki bude mana kofa da idan ki biyu wa zakiyi wa turanci"

Jin Muryar Ali yasa Hannuta na rawa tafara kici kici n zare sakatar ko babu komai tasamu tasaka wani Abin a cikinta duk bala'in Siyama bata isa tace zata takaleta Ba ga ban Ali

Tana bude kofar ya shigo daki yayi gaba da'ita tayi taga taga zata fadi sai ta tsaya da kafafunta Gabanta na faduwa ganin Fuskar Alin babu Rahama ko ta kwabo

Hannuta ya riqe yajata kan gado zugwizugwi take binshi zama yayi ya daurata cinyarshi yana Matsa mata kafadu Fuskarshi a hade yake kallonta ita ma shi take kallo bakinta na motsi tanaso ta sauka daga jikinsa ya dafe qugunta da hannuwanshi biyu yariqe Abinda yake bala'in so ajikinta qam,

Yace me kikeyi ina ta bugu kinqi ki zo kibude min Dan Iskanci har dayimin Turanci wai ke baturiya ko"?

Ni da gidana a dinga bari tsaye ina buga kofa sai kace wani Al'amajiri"

Dariya Maganarshi ta bata Amma batayi Ba kokarinta ta sauka daga jikinsa jin wani salo da yake mata Wanda yafara tafiya da ita a matsayinta na Lafiyayyiyar Mace'
🏵🎗🏵🎗🎗🏵
🏵🎗🏵🎗🎗🏵

Sakinta yayi ganin tana nema taji masa ciwo a fatar hannunshi gurin kwakule hannunasa daga jikinta ya bita da kallo bayan ta sauka daga jikinshi yana tattauna A suwakin dake bakinshi hankalinshi kwance

Can kan Sofa ta zauna tana zumbura baki kamar tafashe da kuka Sai gyara baki take na sabo

Kallonta yake kamar babu gobe yace jeki kawo min Abinci ke ko irin tar6ar Miji baki iya ba haka matan suke dama

Cikin zuciyarta tace Lailama Wannan Mutumin yaushe ya barni na sake da har zan tar6eshi' Shiru tayi bata ce masa komai Ba

Yace ko Ba kyaji ne ?
A nutse tace ban girka Ba nima yunwa nakeji " Cikin Mamaki yake kallonta yace kina nufin baki ci Abinci Ba tun safe?
Daga kai tayi kamar ta fashe da kuka, Yace mai yasa to? Shiru tayi babu bakin Magana,A hasale yace Ba tambayarki nake Ba? Ganin har ya fusata tace bacci nayi ban tashi Ba sai hudu shaura shine dalilina dama yanzu nake shirin in shiga kchin din sai gaka ka shi go", Cikin Nazari yake kallon bakinta sanda take Fadin Haka yace ban yadda Ba idonki bai nuna Alamun bacci Ba ki gaya min maye yafaru bayan fita ta" gabanta yafadi dasss!! Nan da nan tace Da gaske fa nake Bacci nayi kaje ka tambayi Aunty Siyaman mana babu Abinda ya faru sai Alkairi"
Ok naji babu Abinda ya faru Ai sai kitashi kije ki nemi Abinda zaki ci cikinku babu"yar da zan tafi yawon Siyo mata wani Abinci wallahi bayan ina dashi a gidana ko wane Nau'i"

Simi Simi ta Mike ta fita daga dakin gabanta na faduwa tana Addu'ar Allah karsuyi Arba da Siyama, Bayan ta yabi da kallo yana hadiyar yawu ya so yanzu yayi wassanini da ita Wallahi Amma bai zai yiho Ba dole ya sirara mata ganin bataci komai Ba hakan zai sa ya shiga hakkinta

Siyama Na kchin tana ja gwalgwalonta lokacin da D'ija ta shiga da Farko ta tsorata Amma sai ta aro dauriya ta Santa a ranta ta dauke kai tasige kchin din kai tsaye ta hau Aikinta

Abin Mamaki babu Abinda Siyama tace mata har taqarci sabgarta tafice daga kchin din D'ija tayi mamakin hakan cikin zuciuata tace kila sabida yaya Ali yadawo ne shiyasa bata tanka mata bah,

Hannuta riqe daJagwalgwalonta cikin plet ta fito Falon gabanta ne yafadi ganin Ali a zaune cikin kujrea yana kokarin kunna Tv ,Wai gaskiya taji dadi da bata takali Yarinyar can tafada cikin zuciyarta,

Kusa dashi taje ta zauna tace hubby a she ka dawo sannu da zuwa?

Yawwa Ali yace yana kallon Abinda ke cikin plet din dake hannuta yayi saurin dauke kai yana ya mutse fuska yace ke maye wannan kike ci Abin qyamqyami Mtsssss tashi dallah bana son kazanta Wallahi"

*MRS AHAMAD GWADABE*
🏵🎗🏵🎗🎗🏵
*NANA KHADIJA*
🏵🎗🏵🎗🏵🏵

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*🅿198*

Matsawa tayi daga gefanshi tana yaqe tace da har ina cewa ko in zubo maka Abinci jalof ce ta macoroni na dafa"

Kallonta yayi yana ya mutse Fuska yace Lailai baki Da hankali Nine zanci wannan ja gwalgwalon naki Allah yasawaqe miki ke har yanzu kinqi ki koyi komai irin na mata"

Yake takeyi tace Allah na'iya girki ka dandana kaji" Tsaki yayi ya juya ya cigaba da kallonsa bai CE mata komai Ba,

A haka D'ija tafito ta samesu ta kammala tsaf Couscous tayi musu Wanda yaji kayan hadi hade da hanta shar dashi sai Uban qamshi yakeyi ,Cikin wani Plate mai kyau hade da Marufinshi ta zubawa Ali taje ta aje kan danning ta daura masa cokali hade da ruwa da Lemo Masu sanyi, Sannan taqarasa kusa da inda yake zaune tace ga Abincin can kan danning na hada"

"Owk Yace to ke fa Uhumm?

Kasa tayi da kanta,yace Ba tambaryaki nake Ba" Zanyi Wanka ne tukkuna sai inci nawa tafada Cikin kosawa Dan Allah Allah take ta bar gurin

"A'a ban yadda Ba Oya Muje kici Abinci Malama gida na Ba yini ba'aci ba yafada gami da mike wa, babu yadda ta'iya tabi bayanshi zugwi zugwi, Siyama ko da ido tabisu Sauran kadan plate din dake hannuta ya su6uce yafadi ganin yadda suka jera Ali da D'ija sunyi bala'in dacewa tunda take bata ta6a Ankara kafarsu iri daya bace sai yau Abin ya mutukar bata mamaki kawai sai ta tsinci faduwar gaba gabanta nayi a zuciyarta tace Lailai dole nima in koyi girki Wallahi bazan zauna ina kallo suna cin Abinci tare Ba,

Can kan danning ko Cikin Nutsuwa Ali yafara dibar girkinshi D'ija tace kaga wannan bazai ishemu Ba bari in karoma na yace A,a zauna mu cinye sai ki karo wani daga baya" Har ta tazauna sai ta sake Mikewa tace zan dauko cokali ne" Harara ya makama ta yace kinfiye taurin kai *Khadijatu* meye amfanin wannan na Hannuna, Babu yadda ta'iya haka ta zauna yanaci yana bata ita naci sai wani ya tsine ya tsine yake yaqi ya nuna mata yanajin dadin girkin, qarshe ma ca yayi sai ta bashi A baki yagaji shi bai saba cin Abinci da cokali Ba

Kallonsa D'ija take tana hararsa qasa qasa A nuse tace to da waye yake baka abaki,? Yace Siyama CE ko in kirata tabani idan ke baza ki bani bah"

Banza tayi dashi tacigaba da tsakurar Abincinta OK kin yadda in kirata kenan karfa kice an shiga hakkinki" gabanta ne yafadi jin Abinda yace gaskiya ko Dan tabawa Siyama Haushi zata'iya bashi Abincin kamar yadda yace,
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🏵🏵

Bude baki yayi da niyyar kiran Siyaman kamar gaske, Da sauri ta katse shi Cikin zumbura baki tace A,a Nifa Uhm, katsaya mana ba fa cewane ban iya baka bah Shawara nakeyi da zuciyata tukkuna" yace Au har sai kinyi shawara da zuciyarki tukkuna zaki bani Abinci bayan Lada zaki samu Lailai toum bara kafin kigama shawarar In kirata tafara bani yaqara bude baki zaiyi kiran Siyaman a karo na biyu, bubbuga kafarta tayi tace Nifa zan baka katsaya mana tafada gami da ciko cokali da Abincin, dariya yake mata cikin zuciyarsa Yace Ok toum na tsaya Bani ya bude bakin nasa,

Kunya duk ta addabi D'ija haka ta nufi bakinshi da cokalin da yake hannuta, Ya make kafadarsa kamar Wani yaro qarami, Sai tayi saroro tana kallon ta6arar da yake Sai wani lumshe mata ido yake ,Yace ki sanya hannuki ki debo Abincin kibani yafi lada da Albarka kuma sai nafi koshi,

Cikin ranta tace gaskiya wannan mutumin yana bani mamaki Wai dama haka yake ko kuwa yanzu ya zama haka take tambayar kanta,

Tafi Minti Uku tana juya Abincin da "yatsunta takasa debowa tabashi' yace kefa nake jira yunwa nake ji gashi ina da Abin yi bana son Magariba tayi ban Dana Ba,

Haka nan tayi shahada ta debo Abinci tafara bashi Abaki yadinga ci yana tsotse mata yatsu tass sai kace wani Maye Yanda ya dinga tsotsar "yatsunta shine ya kashe Mata jiki Haka ta dinga daurewa tana bashi gashi yace in tabashi loma daya to ita ma sai taci loma daya ,duk A takure D'ija take a gurin Hankalinta yana tashi in tada ga ido ta kalli idon Ali sai taga kamar Ba nasa Ba duk ya wani birkice ya kada yayi jajazir,

Wani dunkolelen Bakinciki ne ya tokarwa Siyama a maqoshi ganin Abinda Ali yakeyi da D'ija babu ko kunya Hankalinta bai qara tashi Ba sai da giftasu buguz buguz da nufin shiga bedroom dinta ta hango idanun Ali tamkar na Mashaya sabida qanqancewa da sukayi Wannan ne ya nuna mata Lailai a cikin bukata yake , saurin bude dakinta tayi tashige tunkafin zuciayrta ta tarwatse Tana shiga tafashe da kuka tana bugs kanta a bango,

Shi ko Ali a daddafe ya karasa cin Abincin jin wata matsiyaciayr Sha'awa da take bijiro masa babu tamtama yau din nan idan bai zubar da Abin nan gaba daya Ba karshenta sai ya kwanta ciwo domin Mararshi ce take wata irin damqemasa,

Tana gama bashi tamike jiki a sanyaye tayi hanyar bedroom dinta domin ita ma Wani irin yanayi tafara ji a jikinta,

Da ido ya raka ta har tashege dakin ya gaza furta kalmar A sabida tsabar Nauyi da bakinsa yayi masa sai faman hade cinyoyinshi yake yana so ya Dan dai daita kafin yatashi yabita Ayi ko wacce Wacce😳

*MRS AHAMAD GWADABE*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*NANA KHADIJA*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*🅿199*

*DEDIGATED TO:*
*My Fan's I'm really love you too*💋💋

*Bissimillahi rahamanirrahim*

*Bin iyaye wajibi Farillah Mutukar kanaso rayuwarka tayi kyau, bin Miji wajibi farillah mutukar kanaso rayuwarka tayi kyau bin nagaba da kai wajibi Farillah mutukar A kwai gaskiya a ciki Tabbas duk Wanda ya girmama iyayenshi yayi dace a rayuwa wacce tabi Mijinta sau da qafa tayi dace a rayuwarta*

Bata fi minti Goma da shiga dakin Ba ya mike ya bi bayanta,

Yana shiga tana kokarin shiga toilet jikinta daure da taeul Amma ta sanya hijabi,
Chapter 19 · 0% Book details