← Book details Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 32

Sashe 5

Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kyalkyalewa da dariya Faruk yayi yace Haba Alhji Ashe kawaici ka tsayayi kaiii Amma naso D'r tane yasamu yarinyar nan da sai inga inda kawaicin naka zai tsaya!!

"Fuska Alin Yasaki kamar yana gaban Faruk din yace Ai mutuwa ka wai zanyi kawai nasani in har haka ta kasance Allah yasa D'r ba Alheri bane shiyasa ya musanya mata dani

D'r din ne ba Alheri ba?

E" shi din
OK sai nagaya masa bakasan yanzu sirikinka bane!

Nasani Mana Sai me Dan Ubansa ni daya so ya kashe ni da rai na Dan iska kawai!!
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADJIA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDULWAHABU)

*🅿171*

Dariya Faruk ya dinga kyalkyalawa Ali kamar cikinsa zai yi ciwo

Shima a nasa 6angaran dariyar yakewa kansa yace kai Dan Allah karkafasa min dodan kunne mtsss ko meye Abin dariya oho yakashe wayar yana Murmushi domin a zahiri shima dariya yakewa kansa yanzu inda Dr yasamu nasara yaya zai yi darayuwarshi ta66!!
Aiki jaa!! Yafada A fili sannan yafoto daga motar ya kulleta ya durfafi part dinshi bakinshi dauke da Addu'a kar yashiga ya riski warin nan na Siyama!

Ma'akatan gurin ne suke ta kawo gaisuwa sai da ya tsaya ya Amsa cikin sakin fuska da mutumta mutum kana yasa mukkuli ya Bude gidan!!

"Siyama da Rukyy ne a zaune a falo suna Hira Rukyy ta bararraje kamar wacce take gidanta ko gidan ubanta ga kayan Abinci nan birjiki sunci sun barshi gami da kananu kwalaben na kayan Maye Wanda suka sha!
Rukyy cikin kananun kaya kirjinta duk rabi a waje wando jikinta ya yi bala'in matse cinyoyinta kanta yasha qarin gashi sai tsotsar roci take tana shiryawa Siyama makircin da zata kullawaD'ija in tashigo gidan,!

To Siyama n ma cikin Riga da sket take irin "yan kanta tana zaune kanta babu dankwali tayi parking din gashin ta Wanda da kyar ya hadu guri guda fuskarta takara haske alamu sun nuna tananan tana bleecin din ta farcenta zaqo zaqo har yau Dan bata yankewa tai musu ado da Jan farce ganin Alin baya nan kai da kagansu bazakace "yayan Musulmai ba ne Ar'na sakk!
Rukyy tace Mata tunda kince wan an ruwan ya ki daina fita kamata yayi mu koma gurin Malam ko yadda yace kiyi ne baki yi daidai ba a kasamu matsala Dan wallahi har yanzu kinayin wari duk da irin turararikan da kike amfani dasu masu qarfi!

"Mtssss wallahi narasa yadda zanyi Rukkyy Siyaman tafada tac gaba dacewa yanzu Abin ma ya sauya Wasu irin kuraje ne suke fitowa a gabana masu bala'in kaikayi in suka fara kaikaiyi ko a inane sai na Sosa nakejin dadi gashi Dana gama sosarwa zasu fashe yanzu duk na kwaile fatar gabana!"

Zare ido Rukyy tayi cikin tsoro ta Bude baki zatayi magana sukaji ana kokarin Bude kofaa!

Shine ya An karar da Siyama ta tuna da cewar Ali yace zaizo!!

Nan da nan ta diririce a gigice ta mike tsaye tayi hanyar bedroom dinta da gudu sai kuma tadawo a gigice tana debe kwalaben kayan mayen da suka Sha ta hau tusawa a jakar Rukyy cikin tashin Hankali!!

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADIJA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*🅿172*

Da sallama ya shaga Falon fuskarsa babu yabo babu fallasa!

Gigicewa Rukyy tayi dataga Ali nan da nan ta hau Neman mitsi tsin gyalenta tanaso ta rufe kanta"

Kallo daya yayi musu ya dauke kai !kai tsaye hanyar dakinshi ya nufa cikin zuciyarsa yana Allah wadai da su!

Hada baki sukai gurin yi masa sannu da zuwa!
Sama sama ya Amsa ya wucesu

Da sauri Siyama ta tawo cikin tsarguwa da rashin gsky kanta a sunkuye ta kara so yana shiga dakin tabi bayansa

Gabansa yafadi ganin ta shigo Dan shi kwata kwata yanzu tsoron ta ra6eshi yake!

Ai.ko tana kara sowa kusa dashii yafara jin tashinn qarni!

Da sauri ya juya baya yana kokarin kwance a gogo yace menene kuma kije dakinki zan fito in sameki yanzu Wanka zanyi !

Yaqe tayi tace wai da zan hada maka ruwan Wanka ne!

OK ngd kije kawai zan had a da kaina
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADIJA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*🅿173*

Simi simi ta juya zata fita daga dakin!

Wai wayowa yayi yana Binta da kallon yana ya mutse fuska yace yaya jikin naki?

Cakin Farin ciki ta tsaya tace da sauqi dai "

Masha Allah yafada yana kokarin Bude kofar toilet yace ka fin nafito kiyi kokari ki sallami wancan qawar naki mai makama da Arniya!
Kinji ko!?

To tace jiki a San yaye tafita daga dakin!

Tsaki yaja yashige toilet Abinshi!

Tana ta6e baki ta zauna kusa da Rukyy tace wallahi mutumin nan Dan rainin hankali ne kwata kwata na lura yanzu baya son in tsaya kusa dashi

Rukyy tace ai yana da gaskiya ba zan boye miki ba gaskiya duk Wanda ya ra6e ki dole zaiji babu dadi nima dai Dan babu yadda na'iya ne

Mtss bana son cin fuska Rukyy ! Tafada a fusace!

Humm yanzu dai mubar maganar yaushe zamu koma gurin malam din domin karbo makarin wannan ciwon qila ta bakinnaki ne banyi amfani dashi dai dai ba !

"Duk sanda kika shirya sai muje ko gobe ne!

"A nya kuwa kinga ya dawo dole mubari ya fara hidimar Auranshi sai muji dadin tafiya kinga sai muji dadin yiwa malam bayani nasan zai bani taimako sosai!

Tunda kikace haka za'ayi Rukyyn tafada gami da gyara zama bata da Alamar tafiya

Kallonta Siyaman tayi tace gwara fa ki mike naga kina gyara zama wallahi yace kan yafito ki San nayi !

"Ni din Rukyyn tafada cike da mamaki"

Dariya Siyama tayi tace kwarai kuwa Dan ma bakiji sunan da ya kiraki dashi ba"

Wane sunane?

"Arniya Siyaman tafada tana dariya"

I tama dariya tayi tace Lailai mutumin nan bashi da mutumchi Siyama !

Humm kisa daya cikin biyu sawon ki a likkafa ki fice kar ki jawa kanki duka Dan Wallahi sai ya dake ki shi babu Abinda yadameshi!

"Lailai ko da "anyi "yar doke doke Dan in ya dake ni ba yadda zanyi ba"

"To tunda haka kikace zauna ya fito yasame ki ni "yar kallo ce ca zanyi nace ki tafi kince baza ki tafi bah

Eh din sai sanda naga dama Rukyyn tafada taci gaba da cewa ke kike tsoronsa shiyasa ya rai naki har yake dukanki!

Kinga Rukyy mubar maganar wasa Dan Allah ki tashi ki tafi kar kijawo mana cin mutumchi domin tunda yace ki tafi nasan in yafito yaga baki tafiba abinda zai biyo baya bazai kyau bah!!

"Aikin banza Sai kace wani gidan gwal Rukyyn tafada gami da mikewa tsaye

Karaff! A kunnen Ali yaji lokacin da tafada sabida haka a hangunce yakaraso cikin Falon ya dauke Fuskar Rukyy da mari!!

Dama yana "jin haushin yarinyar sosai duk da cewa bbu wata maganar arziqi da ta ta6a hadashi da'ita!!

Yau so yake yaga iya inda rashin kunyarta ya tsaya!!

*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADIJA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

🅿
*174*

Zabura Rukyy tayi gami da dafa kunchinta domin bakaramin shigar mari taji ba har idonta yafara kawo ruwa sabida radadin Marin!

Idonshi a tsaye a kanta yace wai ke marakunya ko to mai kike nufi da cewar bazaki tafi ba gidan Ubanki ne kokuwa har zaki budi baki kina zagina to duk kunnuwa na sun jiye min Abinda kike fada ina son in San da Abinda kike gadara "yar iska kinzo kina lalata ta duk Abinda kuke shukawa ke da a bayan fage ke da sauran "yan Uwanki muna da rahoto sai in CE kunsan sunanki ne a farko babu irin kayan Mayan da ba kwa ta'ammali dashi to bari kiji mutukar kika daura wannan yafada yana nuna Siyama a kan hanyar da kike bi wallahi sai na sanya bindiga na fasa miki kai Kafin hakan kuwa sai nafara gana miki a zaba kina ji kina gani zan karayraya kafafunki sannan in harbe ki kowa ya huta da mugun iri!!

Yaci gaba dacewa daga yau sai yau na rabaki da Siyama babu ke babu ita mutukar naga kafarki a gidannan karon mu dake bazai kyau ba!!
"Cikin Wata muguwar tsawa yace "Fice min Anan "maramunchi" Ni zaki zowa da Shirme n banza da wofi!!

Da sauri ta sun kuya ta dauki jakarta cikin 6arin jiki tafice daga Falon hannunta dafe da kunchinta bakin kamar yasa zuciyarta tayi bindiga!!

Falon ya ke Nazari Fuskarsa a murtuke!

Tuni Siyama tashiga taitayinta kanta a kasa ta kasa yadda ta kalleshi gabanta sai faduwa yake!!

Zama yayi cikin kujera yana ya mutse Fuska kamar ko da yaushe in ba dole ba babu Abinda zai sanyashi zama a falon Wallahi!

Gyaran Murya yayi yace Siyama dago kanki ki kalle ni bana son Muna Furchi!! Kinji ko

A tsarge ta dago kai ta kalleshi sai kuma tayi saurin sunkuyar da kai!!

Yace so nake ki sanya idonki cikin nawa zamuyi magana ne kar in kara maimaitawa

To a zahirin gaskiya bazata iya jurar kallonsa ba kamar yadda yake nufi gani take kamar zai fahinci Abinda take Ai katawa a bayan fage Wanda yanzu yagama gargadin Rukyy a kansa bayan haka kuma I danunsa suna da wata baiwa da ba kowace mace ce ta iya jurarar kallonsa ba kai ba mata ba har maza domin Allah yama Ali wani kwarjini!!

Abin daga Allah ne!!
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
*🐾NANA KHADIJA*🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*🅿175*

Ai ko zuba mata ido yayi lokacin da ta dago kai tana kallonsa cikin tsarguwa!

I danta yake Nazari ganin sun yi ja gashi suna lumshewa sunyi fici fici dasu!
Lailai zarginsa zai tabbata bai San sanda ya mike ba yakarasa kusa da ita hankali a tashe Dan ya ma manta da wani warinta ya tsaya kusa da ita Fuskarsa a hade yace Bude min bakinki mugani!

Gabanta yana dukan Uku Uku Lailai yau Ana wata ga wata tafada ciki zuciyarta!

Wangame bakin tayi cikin tsoro Harshenta ya zubawa ido yana Nazari!
Yafi minti uku yana Nazarin harshenta gami da hakoranta bai Fahimci komai ba sabida haka komawa yayi yaje ya zauna a inda ya tashi!
Chapter 5 · 0% Book details