← Book details Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 61

Sashe 9

Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali take rage sautin kukanta har tasamu nasarar tsayar dashi gaba daya sai ajiyar zuciya da takeyi kadan kadan,

"Kiyi shiru kinji...., Kin dai san ina sonki kuma najima ina son mallakarki a matsayin matata amma yau gashi k'addara na neman rabamu..... Kiyi shiru kar ki sake yimin asarar hawayenki"

Ajiyar zuciya ta ja mai karfi sannan ta kalleshi da idanuwanta wadanda suka yi ja,

"Mujahid ni wallahi idan bada kai ba bazan iya rayuwa ba, wallahi kai nake so...."

"Hanan nima ke nake so amma babu yanda zamuyi,kiyi hakuri ki yiwa iyayenki biyayya idan har na zugaki ko na goya miki baya kan ki bujirewa umarnin iyayenki to ban yimiki adalci ba sannan son da nake yimiki na karya ne,wallahi dagaske nake sonki kuma tsakani da Allah,tunda har k'addara ta raba to ni ina ganin kawai muyi hakuri kuma muyi wa juna addu'a da fatan alkhairi....."

Wani kallo tayi masa mai cike da ma'anoni daban daban kafin daga bisani ta daure fuska cikin fushi da bacin rai tasoma magana,

"Dama ashe son da kake ikirarin kana yimin duk na karya ne kuma na yaudara,idan dagaske kana sona meye naka na fadin haka? Maimakon ka nemo mana mafita shine zaka ce wai inyi hakuri indauki k'addara, mujahid ni zaka yaudara? Ni zaka rainawa hankali? Wannan shine irin soyayyar da kake ikirarin kana yimin? Yayi kyau kuma nagode"

Bata saurari bayaninsa ba ta balle murfin motar tafita ta nufi cikin gidan anty salaha tana sake rushewa da wani sabon kukan mai cin rai.

Ganin shigowar ta tana kuka yasa anty salaha dake wanke wurin da tagama wanke wanke dakatawa da abinda takeyi ta nufi wurinta hankalinta atashe saboda duk zatonta ba kalau ba,

"Hanan.....meya faru kuma? Wanine ya mutu ko hatsari akayi? Ki fada ni abinda yafaru kin barni atsaye cikin zulumi..."

"Anty wai dama haka k'addara take? Idan ta afko maka kowa sai yajuya maka baya? Gaba daya sai ka kasa gane kan kowa? Wai haka k'addara take?"

Ajiyar zuciya anty salaha ta sauke sannan ta nemi wuri ta zauna nan cikin falonta tana kallon Hanan wacce har lokacin bata bar kuka ba,

"Hanan dan Allah ki dauki wannan auren amatsayin hanyar samun aljannar ki,ki dauka cewa wani nauyine iyayenki suka dora miki suke son ki sauke shi,kiyi hakuri dama shi aure mukaddari ne daga Allah,aduk inda mijinka yake sai yazo ya sameka anyi,kuma ke ki godewa Allah ma domin yayi miki gatan da ba kowa yayiwa ba,duk cikin danginmu da kawayenki babu wacce ta taba aurar babban mutum sai ke, minister fa Hanan,kin kuwa san suwa ake kira da minister? Wallahi ba kananan mutane bane....."

"Anty ni babu ruwana da wani arzikinsa ni wallahi mujahid nake so,mujahid shine sa'an aurena shine yaro shine muka jima tare mun san halin juna mun san sirrin juna babu abinda bamu saniba na junanmu....."

Sakar baki anty salaha tayi tana kallonta sannan cikin faduwar gaba tace,

"Hanan kar dai ko wani abu ya taba shiga tsakaninku da yaron nan..?"

Cigaba tayi da kukanta tana jin wayarta ana kiranta taki dagawa tasan bazai wuce mujahid ba,

"Tambayarki nakeyi,wani abu ya taba shiga tsakaninku?"

Girgiza kai tayi alamar a'a sannan taci gaba da kukanta,anty salaha zama tayi taci gaba yimata nasiha tana kwantar mata da hankali.

Dakyar ta daina wannan kukan ta share hawayen ta,wuni guda tayi agidan anty salaha har lokacin mujahid bai bar kiranta ba amma taki dauka yakirata yafi sau 20,sai magriba takoma gida,

Tunda ta koma kuma taci gaba da kuncinta har lokacin bacci yayi nan ta shirya ta kwanta bakin ciki kuma yace muje zuwa,saida taci kukanta ta share sannan ta dauki wayarta,

_Akwai Allah._ shine kadai abinda ta turawa Khalil ta ajiye wayar.

***
Yana kwance saman Rug da laptop agabanshi Aryan na gefenshi yana bacci yaji shigowar text,bai duba ba har saida yagama abinda yake yi sannan yadauki wayar yaduba ganin abinda tace yasashi girgiza kai sannan yasoma tura mata da reply,

_Nifa bawai yimin kikayi ba, kawai zan aureki ne saboda ki rike min yarona amma ni bakida wani abu da zai burgeni ko yaja hankali na atare dake infact ma ni banko san kamanninki ba bare insan ya kike,soo kisan inda yake yimiki ciwo._

Tunda Hanan taga wannan sakon nasa bacin ranta yasake nunkuwa zuciyarta har tafarfasa take yi dan bacin rai,wai ita zai cewa saboda ta rike masa yaro zai aureta,mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki nan tasoma kokarin mayar masa da reply dama haushinsa takeji saboda girman kansa da wulakancinsa dan ko sako ne sakonshi baya wuce layi biyu,

_Nima ai ba sonka nakeba kuma da kake maganar zaka aureni saboda in rike maka yaro to ni ba yar aiki bace kuma ba baiwa bace tun wuri ka nemi mai rike maka yaronka._

Wannan karon sakon nata ya bata masa rai fiye da wancan,wai wannan yarinyar dame take tak'ama da har take fada masa maganganu kanta tsaye ko tsoro bata ji kamar wata sa'arshi,dan kawai yace zai aureta sai aka fada mata sonta yake? Shi yanzu aduniya ai babu yarinyar da zata ja hankalinsa har ya sota,tsaki yayi ya ajiye wayar agefe yatashi ya shiga bathroom.................�

*_Ummi Shatu_*👌🏻
8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: ©� *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect writers)_

*D'AND'ANO....*

*MIJIN MATACCIYA.....*💞💞

*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

*Wattpad-ummishatu*

*10*

***Kamar ya rabu da ita dan har ya shimfida Rug din salla yaji bazai iya kyaleta ba duk da yasan ko tantama baya yi a haihuwar kaji ya haifeta amma gara dai ya nuna mata ita ba kowan kowa bace agareshi. Sai bayan da yagama da ita sannan yaje ya tada kabbarar sallar da yayi haramar yi,

Har lokacin ita kam bata jin ta huce wani irin zafinsa take ji kamar taje har inda yake ta shakeshi saboda yashiga hakkinta da yawa,tana tsaka da sharar hawaye taji shigowar wani sakon wanda ko tantama batayi daga gareshi ne,yanzu kuma Allah ne kadai yasan irin bakar maganar da yaturo mata tunda ta lura shima dan zafin kaine bai da hakuri kamar ba babban mutum ba,

K'wafa tayi sannan cikin bacin rai tace "Ai wallahi idan tsoho baiji kunyar hawa jakiba to kuwa jaki bazai ji kunyar yin totso dashi har ya damfara shi da kasa ba,duk abinda zaka fada am too much ready in baka amsa daidai da maganar ka..."

Text massage din nashi ta bude nan ta soma karantawa afili,

_Ki dauki kanki bakida maraba da mai rainon yarona, sannan ina son infada miki akwai dokoki da sharruda masu yawa wadanda zan kafa miki akan yarona mutukar kika bisu zamu zauna lafiya amma karya doka daya daidai take da rugujewar dukkan dokokin da kika bi,idan har kina son aji kanmu dake to ki gwada saka kafa ki shure daya daga cikin dokokin._

Ranta idan yayi dubu to ya baci saboda wannan sakon da yaturo mata,ai kuwa wallahi sai dai ayi wacce za ayi amma ita ba yar raino bace,

Kiris dama take jira shiyasa ganin wannan sakon nasa yabata damar amayar da abinda ke nukurkusar zuciyarta,

Ko bayan da ta tura masa sakon ji take bata huce ba daga cin mutuncin da yayi mata gashi yana yin komai nasa isa isa iko iko,tasan dan girma kam ya girme mata nesa ba kusa ba to amma Menene zai rinka nuna mata gadara harda wani cewa a yar aiki ya dauketa kamar wata baiwar da yasaka kudi yasiyo a kasuwa zai tsaya yana fadin wai zai kafa mata dokoki da sharruda,

Sakon mujahid ne yashigo mata cikin wayarta adaidai wannan lokaci,ji tayi tausayinsu shida ita duk ya mamaye ilahirin zuciyarta baki daya saboda tasan yanda batayi bacci ba shi dinma gashi can kwance bai samu baccin ba duk kawai dan mutum daya,gaskiya saima Allah ya saka musu ita da mujahid,duk tsawon shekarun da suka dauka suna shirya yanda rayuwarsu zata kasance idan sunyi aure yau kwatsam rana daya wani tsohon banza can mai budurwar zuciya yazo ya rusa musu mafarkin su da suka dade suna yi,

Bude sakon tayi tana kuka kamar wata mai arahar hawaye,

_Dan Allah wify karki cigaba da wannan fushin dani,ki tsaya ki saurare ni,sanin kankine ina mutukar sonki kuma wallahi har na mutu da sonki dankare cikin zuciya ta zan koma ga mahaliccina,dan Allah ki daina fushi dani kijira kiga irin matakin da zan dauka._

Sai lokacin taji ta dan samu nutsuwa jin mujahid yace akwai abinda yake shiryawa, sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske tayi sannan tasoma kiran wayar mujahid din,ada kam ji take bata wani damu dashi ba amma ahalin yanzu tana jin soyayyar sa kamar idan babushi aduniya bazata iya rayuwa ba,ita kanta bata san yaushe wannan soyayyar ta shigeta ba sai yanzu, bata san yaushe tafara son mujahid har haka ba a iya saninta dai sai da aka fara turka turkar auren nan sannan wannan matsananciyar soyayyar tasoma tasiri agareta.

Bugu uku taji ya katse kiran sannan ya kirata,dauka tayi tai kasa da dasasshiyar muryarta wacce ke fita dakyar kamar wacce mura taci karfinta,

"Wify meyasa baki tsaya kinji uzuri na ba,meyasa kika dauki fushi dani har haka? Kema kin san ai ina sonki,u know how much you mean to me and i soo much loves you...."

"To ai dafarko dinne sai naga kamar baka damu da rabamun da za ayi ba shiyasa,naga kamar ni daya keta haukana you didn't make any effort..."

"No wify,ba haka bane,gashi kina gani nakasa bacci...,akwai abinda nake shiryawa, kawai all what i want from you is ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa kima daina nuna kwata kwata cewa kina cikin damuwa,nikuma ina can bayan fage ina shirya abinda nake shiryawa..."

Dan murmushi tayi mai dauke da jin dadi sannan cikin sanyin murya tace,

"Ok har naji relief wallahi,gobe insha Allah zan koma Abuja saboda ban dauki excuse ba nataho dama kawai nataho weekend ne fa"

"Babu matsala zamu hadu before kitafi,yanzu ki kwanta kiyi bacci kinga 2 ta kusa"

Sallama sukayi ta katse wayar tana jin farin ciki yana ziyartar birnin zuciyarta,haba har taji sanyi aranta.

***

Kamar kada ya bude sakon nata amma sai ya dake yabude aransa yana fadin "wannan yarinyar bata da kunya sam"

Yana budewa yaga tace,

_Girma dai ya fadi kasa wanwas masu budurwar zuciya._
Chapter 9 · 0% Book details