Sashe 7
Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hanan kiyi shiru wannan kukan baida wani amfani,kiyi shiru ki mika al'amuranki ga Allah ki nemi alkhairinsa da kuma albarka acikin aurenki...."
Kamar jira take tasake fashewa da wani hargitsattsen kuka mai tsayawa arai,
"Mamaye abokin Abba ne fa wai,wai abokin Abba,mamaye yanzu ni anyi min adalci kenan idan aka aura min wannan mutumin? Mutumin da ya haifi yani? Mutumin da yafara ban kwana da duniya yana kusantar kabari,inama laifin abani zabi idan ina sonshi a aura min idan bana so abarni amma sai kawai ayi min dole ayanke hukunci batare da anji ra'ayina ba...."
"Ki daina fadin haka Hanan,iyaye sunada damar zabawa yaransu mazaje hakan bai saba ka'idar musulunci ba,kiyiwa mahaifinki biyayya sannan kiyi addu'a insha Allah bazaki tabe ba"
"Mamaye nidai har ga Allah bana sonshi, tayaya zan auri sa'an babana? Abokin Abba fa,sa'an abba ne fa mamaye, yanzu Abba yarasa wanda zai aura min sai abokin sa?"
"To ni me kikeso inyi akai Hanan? Yariga da ya yanke hukunci,aikin gama yagama, k'addara tariga fata sai dai kawai kidau hakuri kiyita addu'a, Allah ya zaba miki abinda yafi alkhairi a rayuwarki"
Daga haka mamaye ta tashi tafita tabarta tana ta faman gursheken kuka kamar ranta zai fita,
Wannan wacce irin k'addara ce? Ita mema yakaita Abuja yin service gashi nan mutum yaganta yazama silar rushewar farin cikinta, duk yanmatan Abuja yarasa wacce yagani yake so sai ita? Dan dai kawai yana da kudi sai yarinka amfani da damarsa yana taka duk wanda yaso? Insha Allah sai Allah yasaka mata,ita dai tasan Abba bawai kudi yabi ba wurin aurar da ita ga wannan bawan Allah,koda yake yace abokinsa ne watakila wannan shine dalilin da yasa ya bayar da ita batare da yajira yaji ra'ayinta ba.
Wayarta ta dauka tana share hawayen dake zuba daga idanuwanta tana face hancinta da tissue,text massage ta turawa mujahid kamar haka,
_Ban taba sanin cewa bakaine abokin rayuwa ta ba sai yanzu da k'addara ta gifta,ashe ba Kaine mijina ba shiyasa kayita bina akan zaka turo gidanmu amma naki gashi yanzu Abba ya bayar dani ga abokinsa,ya zanyi mujahid? Wallahi ina tsananin sonka musamman ma yanzu da ake neman rabamu._
Ai tunda mujahid yaga massage dinta hankalinsa shima yabar jikinsa,jiki yana rawa yakirata,shiru yayi yana sauraren sautin kukanta da yacika kunnuwanshi,
Daga shi har ita sun kasa cewa komai ita sai kuka takeyi murya adashe,
Cikin sanyin murya mai kunshe da damuwa yace,
"Hanan kiyi shiru....kiyi hakuri ki daina kuka kinji,ni nafi cancanta da inyi kuka bake ba domin wallahi ko tantama banayi soyayyar da nake yimiki ta ninka wacce kike yimin.... Ina sonki fiyeda tunaninki,kullum da sonki nake kwana nake tashi...."
"Mujahid tsohone fa,wai minister ne a Abuja, Abba baiyi min adalci ba,abokinsa fa zai aura min"
"Hanan ina son ganinki,yaushe zan ganki?"
"Mujahid sai dai mu hadu agidan anty salaha kaga bazai yuyu kazo nanba Abba yaganka,idan nafita zan kiraka"
"Shikenan babu matsala amma ki daina kuka kinji"
Shiru tayi ta katse wayar amma maganar ta daina kuka kam tasan abune wanda bama zai taba yuyuwa ba, ai dole tayi kuka rabuwa da masoyi sai dole bawai dan ana so ba, mujahid ako ina zata kirashi masoyinta domin yana tsananin kaunarta kamar ita kadaice macen da tayi saura a duniya,
Kuka kam tayi shi ta kara har tagaji, zuciyarta koda yaushe cikin kunci take da radadi Allah ya isa kuwa tayiwa abokin Abba tafi sau dubu domin shine mutum na farko da yafara yunkurin rabata da farin cikinta,
Washe gari ta tashi da niyyar zuwa gidan anty salaha amma Abba yace babu inda zataje tajira saboda zatayi bako domin yau angon yace zaizo su gana,tamkar zata fashe haka tazama saboda tsabar cikar da tayi.
***
Tunda ya fadawa Aryan cewa nanda 3 weeks zai kawo masa Mommyn shi yaron ke cikin farin ciki marar misaltuwa,
Dadi ne ya lullube zuciyar Khalil sosai saboda ganin Aryan cikin farin ciki,aranar ya shirya yatafi gombe yaje yaga Abba suka tattauna akan yanda abubuwan zasu kasance anan Abba kece masa sai yasamu lokaci yashirya yaje su gana da yarinyar,yadai ansawa Abba da toh amma harga Allah ba zuwa zaiyi ba shi ina yaga wani lokacin zuwa zance wurin budurwa yanzu? Acikin ayyukan sa wanne zai tsallake yatafi hira? Duk ma ba wannan ba shifa auren nan kawai zaiyi shine saboda Aryan bawai saboda kansa ba shi idan dan ta shine shida aure sai dai yaga anayi amma ayanzu kam babu macen da ta isa,
Maimakon yaje sai kawai yatura PA dinsa yaje yaga Hanan sannan yakai mata sako,
Lokacin da nura PA yaje Hanan a murtuke taje ta sameshi a dakin saukar baki dake kofar gida,motar ma da yazo da ita kawai abar kallo ce saboda kyanta da tsaruwarta,duk azotanta akwai ubban gayyar sai taga sai iya mutum daya,
Dan russunawa nura yayi sannan yace,
"Ranki yadade barka da fitowa,ayi mana afuwa yallabai bai samu damar zuwa ba da tare zamu zo dashi to sai kuma meeting na gaggawa ya sameshi,amma duk da haka ga sako yabayar inkawo miki...."
Envelope ya ajiye mata da wata babbar leda,
"Babu komai.." shine kadai abinda tace bayan yagama rattabo mata bayanin. Daga haka yamike da niyyar tafiya domin tuni dama tun kafin fitowarta yaci snacks da drinks din da aka tanadar masa,
"Amm yawwa sannan yace idan kina bukatar ganin hotonshi sai in......"
Tun kafin ya karasa ta dakatar dashi,
"Bana bukata...."
Mamaki ne ya addabi ruhin nura PA ita kuwa wannan yarinyar ya take kokarin yin sakarkaba? Ya take kokarin yiwa kanta asara? Ita da Allah yayi mata gam da katar da kabakin arziki ya zabota cikin dubban mata amma shine take nema ta butulce?
Saka takalmansa yayi sannan yasake dan russunawa,
"Na barki lafiya ranki yadade"
"Nagode,ka gaida gida"
Fita nura yayi babu jimawa itama ta tashi tafita batare da ta dauki kayan da nura ya ajiye mata ba sai yaya shamsu ne lokacin da yashiga ya fito mata dasu yabita cikin gida ya kai mata,
Tana daga kwance cikin daki tajiyo muryar abba yana cewa,
"Uwar masu gida kina ina? Inbanda shirmenki uwata kuma akawo miki kaya ki taho ki baraso acan? Ai sai ki dauka ki duba haka akeyi"
Fita tayi ta saka hannu biyu ta karbi kayan awurin Abba sannan tajuya takoma daki zuciyarta nayi mata wani irin tukuki........................âœï¸
_Ga wadda keda bukatar biyan kudin littafin mijin matacciya sai ta aiko da naira 200 ta account 3112877210 Aisha Ibrahim first bank sai atura shaidar biya ta wannan number din 07044644433,ko kuma katin waya na MTN zuwa ga 07044644433 sai atura shaidar biya ta wannan number din da aka tura katin,domin neman Karin bayani za a iya tuntubar marubuciyar kai tsaye ta wannan number 07044644433._
*_Ummi Shatu_*👌ðŸ»
8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: ©� *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*D'AND'ANO.....*
*MIJIN MATACCIYA......*💞💞
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*8*
***Kamar tayi fatali da kayan da ya aiko mata haka taji nan ta watsar dasu saman gado takoma gefe ta kwanta,tsabar yawan kukan da takeyi yanzu har takai takawo ma bata iya kukan sai dai tayi girim tana tunani wanda hakan ba karamin daga hankalin mamaye yakeyi ba ita tsoronta ma kar hawan jini ko ciwon zuciya ko kuma wata lalurar mai kama da haka ta kama mata yarinya hakanne ma yasa mamaye tasamu Abba da maganar tace masa kodai zaiyi hakuri ya janye maganar auren nan yabawa minister hakuri saboda yarinya bata so ita kuma tana gudun fadawarta mawuyacin hali,
Budar bakin Abba sai cewa yayi ai muddin idan suka ga ba ayi auren nanba tofa kwanan dayane acikinsu ya kare amma shi ko bayan ransa bai yarda Hanan ta auri wani miji bayan abokinsa ba,shine kadai mijin da ya zaba mata kuma ya yarda ta zauna dashi,
Haka mamaye tafito jiki babu kwari domin Abba fada yayi ta yimata yana cewa ya zata biyewa shirmen Hanan duk da ta girma ai har yanzu bata san abinda zai amfaneta agaba ko sabanin haka ba tunda abinda babba ya hango daga zaune yaro ko yahau rimi ba lallai ya hangoba,shi yasan mijin da yadace da hanan sannan yasan waye ya kamata yazama tare da ita shiyasa yayi mata wannan zabin.
Kasancewar yanzu bata iya kuka yasata yin shiru tana sauraren fadan da mamaye ke yimata cikin lallami da nasiha tana cewa ta daure ta cije tayiwa mahaifin ta biyayya insha Allah zataji dadi agaba sannan zatayi farin ciki ko dan biyayyar da tayiwa mahaifin ta sannan mamaye ta kara da fadin,
"Insha Allah Hanan sai kin yi alfahari da mahaifin ki,sai kinyi dariya agaba ko dan bin umarnin mahaifinki da kikayi kika masa biyayya,iyaye ba zasu taba cutar da yayansu ba sai dai abisa kuskure,duk abinda kikaga mahaifinki yayi to yayi miki ne dan soyayyar da yake yimiki,ke kanki shaida ce mahaifin ki yana tsananin sonki saboda ma soyayyar da yake yimiki da ace bani na haifeki ba to da bazan iya zama daku ba domin yafi fifitaki akaina... Ko kin manta yanda kuke hade min kai keda shi...?"
Murmushi mamaye tayi,itama Hanan din murmushi tayi tana tuno shekarun baya nan abubuwan da suka faffaru abaya suka soma dawo mata kamar yanzu ne suke faruwa,
Kamar yanda mamaye taso haka ta dan saki ranta tana hira har da su dariya idan mamaye ta fada mata wani abu,sai da aka kira sallar magriba sannan suka tashi,ita da yake bama sallar zata yi ba kitchen tawuce ta zubo abinci dan kadan domin yanzu bata iya ci dayawa,sai da tagama cin abincin sannan takoma cikin daki nan ta bude sakon da minister ya aiko mata,
Ledar tafara budewa nan taga tamfatsetsiyar sabuwar waya kirar kamfanin Samsung mai mutukar kyau da daukar hankali harda sim card aciki,
Tabe baki tayi cike da jin haushi tace,
"Tsabar ya rainawa mutane hankali da wayo shine shi baizo ba saboda yafi karfin yazo sai aikowa yayi,kuma ko waye yace masa bani da arzikin waya da har zai siyo ya bayar akawo min.... Saboda ga yar talakawa ko" kwafa tayi da karfin gaske sannan ta bude envelope din tana tsaki,
Kudi tagani bugun Abuja sababbi fil yan dubu dubu wanda bazata iya kiyasta adadinsu ba sannan kuma ga dan karamin card nan ajiki anrubuta,
_Ibrahim Sulaiman I._