← Book details Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 61

Sashe 31

Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidan Abba Idris suka fara zuwa wanda ke can sabuwar GRA,gidan babban gidane mai dauke da sassa daban daban, bangaren uwar gidan suka fara zuwa wacce ta karbi Hanan hannu bibbiyu da yake mace ce mai fara'a,shi kuma dama uban gayyar yana can wurin Abban suna gaisawa,bayan tafito daga sashen uwar gidan aka rakata na amaryar itama ba laifi tana da karbar baki,tana zaune ita da Aryan da wasu yara agidan wanda tafi kyautata zaton jikokin gidanne dan harda wadda bata d'ara Aryan a shekaru ba aka leko kiranta wai tafito su tafi,kudi matan gidan suka bata da turaruka,har falon Abba kuma aka rakata suka gaisa shima yabawa Aryan kudi wai gashi nan barka da salla shima khalil rabon kudin yayi agidan kowa da nasa sannan suka tafi,gidan anty Fatu kanwar hajiya suka je wannan kam har falonta Khalil yashiga suka gaisa itama yayiwa yaranta rabon kudi sannan suka fito, Hanan ta lura shi mutum ne mai son zumunci da kaunar yan uwansa domin duka kannensa babu gidan wanda basu jeba yakai mata ziyara, ba dan mai zumunci bane ai hakimcewa zaiyi sai dai shi aje asameshi tunda shine babba kuma yana da kudi amma babu ruwansa yakanje ya gaidasu lokaci zuwa lokaci kuma duk sallar duniya karama ko babba indai yana k'asar sai yaje gidajensu yayi musu barka da salla haka idan anyiwa su Aryan hutu shima kaf dangi sai ya zagaya dashi anganshi sannan yake barin k'asar dashi gaskiya ya rike yan uwanshi kuma ya rike girmansa ya zame musu babban wa uba.

Gidan mai martaba suka je wato fada bayan sun fito daga gidan hamida kanwarshi, Hanan aranta tambayar kanta take tayi to ko dai duk cikin gombe yan uwansu Khalil ne? Saboda sunje gidaje sunfi 20 idan lissafawa zata yi,lallai sai yanzu ta yarda da maganar da taji marokin nan nayi ranar daurin aurenta yanata yiwa Khalil kirari wai ya gaji mulki kuma yagaji sarauta ashe kuwa dagaske hakanne dan tagama kamar gaba daya masu arzikin garin danginsu ne,

Bayan fitowarsu daga fada inda aka hado ta da kayan kamshi kaya guda su turaren wuta,turaren kaya,ban daki da na jiki gidan Khalid suka wuce ta fahimci hakanne dalilin waya da taji yana yi da Khalid din yana cewa gasu nan zuwa,

Acan suka yi sallar magriba duk da Muneerat matarshi bata da saurin sabo amma hakan bai damu hanan ba tayi mata uzuri saboda kowa da irin halinshi. Sai da suka ci abinci sannan suka fito domin tafiya,a compound din gidan suka tarar da su Khalil tsaye shida Khalid suna yin magana amma basu san kowacce iri bace saboda basa jiyo abinda suke fada, sallama sukayi musu suka tafi su Nawwar nata yiwa Aryan bye bye wai suma sai sunzo. Tunda suka koma gida hanan tashiga daki ta kwanta ga gajiyar yawon da suka sha ga ciwon mara saboda tsallaken watan da tayi bata yiba shiyasa take dandana kudarta,tana cikin wannan halin taga text din Khalil wai ta shirya gobe zasu koma Abuja,kasa tashi ta shirya kayan tayi ahaka su zarah suka dawo suka sameta wad'anda suka dawo daga Billiri tare da umma barira...........................✍️

*_Ummi Shatu_*👌🏻
8/14/20, 10:11 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*28*

***Tana daga kwancen tana fama da ciwon mara wanda ke nukurkusar ta su zarah suka shigo ita da mufida kowaccensu da alamun gajiya atare da ita,

Cikin wannan hali ta janyo wayarta tana sake duba sakon nashi wanda yarubuto mata,

_ki shirya kayanki gobe da safe zamu wuce Abuja._

"Anty mun dawo..." Mufida ta fada tana kokarin zama gefen gadon nata batayi magana ba sakamakon yawu da ya tarar mata abaki,tashi tayi taje ta zubar ta dawo ta kwanta,

Wasa wasa tashin zuciya ya sako ta agaba ga shegen rashin dadin baki dake damunta kamar wata mai ciki haka yawu zai yita cika mata baki dayake wani lokacin period yana da wannan tsiyar duk sai yamayar dakai mai laulayin dole,zuwa bayan ishah har ta galabaita dan sai da lamarin ya kaita da yin amai,amai tayita kwarawa kuma tana gamawa cikin ta shima ya rude ta sake komawa cikin toilet din ai tuni su mufida suka tafi suka kaiwa hajiya tsegumin ai ga Anty can tana ta amai bata da lafiya,hajiya tare da umma ai da hanzarinsu suka taho kamar zasu tashi sama,

Tana kwance ta sauya kayan jikinta sakamakon wanda ke jikin nata sun baci da aman da tayi,cikin rudu hajiya da umma keyi mata sannu tana daga musu kai tana kokarin yin magana wani aman yasake turnuko mata cikin sauri ta tashi ta nufi toilet taje ta yi acan,

Fita hajiya tayi ta kira Khalil awaya lokacin shi yana can ma tare da baki suna ganawa,

"Mu'azzam kabar duk abinda kake yi maza kazo matarka babu lafiya amma ka fara kiran likita tukunna...."

Abinda yaji hajiya tace kenan sannan ta katse wayar, Zaid ya kira yace yaje ya dauko Dr,

Hanan na kwance saman gado tana ta karkarwar sanyi suka shigo shida Dr din kowa fita yayi yabasu wuri,yana gaba Dr yana biye dashi abaya,ajiye dan first aid box dinsa yayi likitan yana dan yimata tambayoyi,

"Akwai juna biyu ne?"

Girgiza kai tayi idanuwanta arufe,

"When last kika ga al'adarki?"

"Last month banyi ba" Tabashi amsa cikeda kunya saboda Khalil dake tsaye kyam yana sauraren su,

"Dama kina tsallaken wata ne?"

Girgiza masa kai tayi kuma cikin yamutsa fuska tace "A'a"

"Akwai amai?" Kai ta daga masa,

"Akwai ciwon kai?" Girgiza kai tayi alamar babu,

Dafa wuyanta yayi yaji akwai zazzabi sannan ya dan dudduba idanuwanta bayan ya dan bubbudesu. Magani ya soma duba mata yana cigaba da bayanin cewa ai ba wata matsala bace dama dayawan mata sukan samu irin wannan laulaye laulayen lokacin da zasu yi period, Khalil na tsaye yana daddana wayarshi kamar baya jinsu,ganin hankalinsa yana kan waya yasata dan bude idanuwanta ta kalleshi sannan ta mayar dasu ta rufe,saida yagama hada maganin tsaf sannan ya bata yace taci abinci komai kankantarshi sai ta sha magani daga haka suka fita shi Khalil bai ce komai ba,afalo ya tarar dasu hajiya dukkaninsu zaune suna jiran fitowarsu cewa yayi bari ya sallami Dr yadawo,baifi minti biyar da fita ba sai gashi yadawo amma bai samensu ba sai acikin bedroom din da take ciki ya iskesu anata lallabata ana tambayar wai me take son ci akawo mata? Tsayawa yayi ya harde hannuwanshi akirjinsa yana kallon ikon Allah domin su duk atunaninsu juna biyu Hanan tasamu wai dan sunga tana amai basu san lalurar su ce ta mata ba duk wata,

"Ki daure kici wani abu kinji.... Kinga ai yanzu dole sai kin kula,me za akawo miki?" Hajiya ta bukata cikin kulawa,

"Custard powder kadai zan sha itama kar asa sugar....." Ta fada cikin rashin kwarin jiki,

"Ke zarah maza tashi kuje ku hado mata custard..." Inji umma barira,

Shi abinma sai yaso bashi dariya saboda yanda duk su hajiya suka bi suka rude sunata lallabata,sai da tasha custard din tasha magani sannan suka fita suka barta,

Shima yana shirin fita hajiya tazo ta dakatar dashi,

"Khalil nace yaushe matar taka tafara wannan laulayin ne? Idan tana yawan yin aman ai sai insa asamo mata magani,kasan masu juna biyu sai da kula"

"Toh hajiya"

Daga haka yasamu tabarshi yafita,kulawa sosai ake bawa Hanan dan da safe ma kafin su tafi hajiya nata jawa Khalil kunnen yarinka kulawa da Hanan,da tafiyar ma hajiya cewa tayi sai abari wai har Hanan din ta warware sai da Hanan din tace mata ai itama akwai abinda zatayi idan taje Abujan zatayi clearance to jin haka yasa hajiya amincewa suka kama hanya suka tafi tana sake jaddada wai arinka kulawa da Hanan shi dai bai ce ba juna biyun bane yai shiru yana binsu da ido.

Duk da cewa bata baccin mota yau kam ta yi shi dan tunda suka baro gombe take tikar bacci har lokacin da suka shiga garin Abuja lokacin anata sheka uban ruwa dan tun daga farkon abuja ake zubashi,

Har suka shiga cikin compound din gidan Hanan bata saniba domin tana can tana ta sharar baccinta,sai da Aryan ya bude murya yace,

"Mommy ki tashi anzo gida..."

Firgigit tayi ta mike domin kamar acikin mafarki taji maganar tashi,a dan tsorace ta juya ta kalli Khalil wanda ke zaune kusa da ita,tashi tayi tafita ta nufi ciki tana dan dingishi tana zuwa bedroom dinta ta rage kayan jikinta ta sake kwanciya domin a mutukar gajiye jikinta yake tamkar anyi mata dukan tsiya. Ta jima tana bacci dan sai la'asar sannan ta tashi tayi wanka ta fita wurinsu umma da ke babban falon kasa ita da Aryan wanda ke ta wasa da keken sa,itama zama tayi bayan ta zubo abinci dama aikin kenan daga ci sai bacci bayan shi babu abun yi.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya su Aryan tuni sun koma makaranta shi kuma Khalil yakoma kan harkokinsa shima dan ko ganuwa ma bayayi kullum da inda zaije,

Hanan kuwa tun bata damuwa rashin daidaituwar dake tsakaninta da Khalil har tafara damuwa,bata da aiki sai na tunaninsa da mafarke mafarke akansa gaba daya ta rame ta kanjale gata dai a katon gida lafiyayye zata ci zata sha ba aikin komai take yiba amma da yake akwai damuwa acikin zuciyarta shiyasa duk ta zuke dan ko ganinsa ma bata yi tsakaninta dashi text massage ne idan tana son wani abu ko kuma tana son zataje wani wuri kuma duk abinda ta nema ko ta bukata baya hanata yana sawa a kawo mata,

Shima anasa b'angaren har gobe bai daina kukan rashin matarsa ba domin halin da yake ciki yafara damunsa ada yayi tunanin zai iya rike bukatarsa ba tare da shiga wani hali ba amma yanzu ya ga abun yana neman faskara domin kullum cikin shan pills yake wai ko zaiji dama dama gashi yana yin azumin litinin da alhamis amma duk jiya iyau,
Chapter 31 · 0% Book details