Sashe 5
Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A bangaren Hanan kuwa cike da farin ciki da murna ta isa gida tana ta dokin ganin mutanen gida kamar irin ta shekara dinnan bata gansu ba domin dama ita bata saba yin tafiya taje wani wurin tayi kwanaki ba shiyasa wannan dan sati uku zuwa hudun da tayi take ganin kamar watanni ne tayi batare da taga yan gida ba.
Tun aranar mujahid yazo domin shima cike yake da dokin ganinta,
Kamar yadda ta kawowa kowa dake gidan tsarabar turare shima mujahid haka ta kawo masa turaren secret man,
Tallafe kumatunsa yayi yana kallonsa saboda azahirin gaskiya tayi bala'in kyau domin da alama weather din garin Abuja ta karbi fatar jikinta tayi wani luwai luwai sai sheki take yi tana kyalli,
"Wai yallabai menene ka tisani agaba kana kallona kamar yau kafara ganina?"
Murmushi mujahid yayi sannan ya janye idanuwanshi daga kanta ya mayar kan sitiyarin motarshi,
"Wallahi kinyi kyau ba karya,gaskiya Abuja ta karbeki,ko can zamu zauna ne?"
Yar dariya tayi sannan ta shafi fuskarta,
"Wai haka ma su yaya shamsu suka ce,wai nayi kyau kamar bani ba yar dukununun fatata duk ta haska tayi kyau ashe da gaske ne...."
"Allah dagaske ne kinyi kyau amarya ta kamar irin kin fara cin amarci dinnan..."
"Uhmmm zaka fara ko,kai a kullum baka da magana sai ta aure"
"To bashi ne araina ba? Ai dole intayi miki maganarsa ko zaki ji tausayina ki bani dama"
"To nidai yanzu gobe kazo ka kaini gidan anty salaha inje mu gaisa inbata labarin Abuja"
"Duk yanda kikace haka za ayi da girman kujerarki...."
Cikin sati biyun da tayi a kano ta harhada kayanta jimilla gaba daya wadanda zata tafi dasu sannan ta sissiya wadanda take da bukata,ranar da zata tafi yaya shamsu ne da mujahid suka kaita basu suka baro garin abuja ba sai magriba yayinda ita kuma ta zauna zaman shirya kayanta a daya daga cikin dakunan dake cikin quarters din makarantar domin yanzu tabar Lodge hukumar makarantar bright future tabasu masauki a quarters din malamai wanda ke dauke da komai na more rayuwa,
Wallahi sosai abun ya burgeta kuma yayi mata dadi haba zatayi service a dadi komai yana zuwar mata cikin sauki duk ma dai da term din yakare domin exams za afara to amma yazama dole su kasance suna kusa.
Washe gari ashraf ne ya tadata daga bacci wai zaizo yaganta kafin yabar Abuja,tana fitowa daga wanka yakaraso kaya kadai tasa tafita ta sameshi waje yana jiranta,suna tsaye dashi suna hira motar Khalil tashiga cikin makarantar inda zasu ajiye Aryan sannan yawuce kaduna shida nura PA,duk da ba akusa suke ba ahakan Aryan ya hangota,kama hannun Khalil yayi yace,
"Papa kalli mommy can...."
Khalil bai kulashi ba ya saka hannu cikin aljihunsa ya ciro wayarshi ya soma latse latse har suka ajiye Aryan bai kulashi ba sai babbata rai Aryan din ketayi,
Tun daga ranar walwalar Aryan ta ragu ahaka har suka fara exams ita kuwa Hanan bama sosai take shiga cikin makarantar ba saboda jarabawa akeyi aikin da ake basu kadanne ba wani aiki sukeyi sosai ba amma dai suna yin nasu daidai gwargado,ana yin hutu ta tattara nata inata ta nufi gida kanon dabo.
***
Tunda aka gama exams Aryan ke faman yiwa Khalil rigima akan maganar mommynshi, Aryan irin yaran nanne da basa mantuwa kai sai ma ka manta da abu shi bai manta ba,
Rarrashinsa Khalil yafara yi yana cemasa,
"Kamanta da maganar mommy dinnan kaji yaron kirki,ana yimuku hutu zan kaika Jos kaga yan uwan mommynka sannan zan kaika gombe wurin hajiya ai zakaje ko? Daga nan zan daukeka mu tafi new york inda zaka kare hutunka gaba daya acan,kullum zamu rinka zuwa central park kana shan ice cream...."
Makale kafada Aryan yayi yana turo baki,
"Ni wurin mommy nake so..."
"Kai..... Shut up.....ba na hanaka wannan maganar ba? Get out of here ko in bugeka,marar jin magana"
Tsawar da Khalil yayi masa ce ta razanashi yafita da gudu yaje ya zauna a falo yana kuka abunka da yaran hutu wadanda basu saba ba take temperature din jikinsa ta sauya kansa yafara ciwo shikenan sai numfashi sama sama,
Shi kuma uban na can dakinshi yagama shiryawa zai fita zai tafi kano ta'aziyar baban wani classmate dinshi,duk atunaninshi Aryan na wurin umma barira,har zai fita ta kofar side dinshi sai yafasa domin bai yiwa umma barira sallama ba,
Ta babban falo yabi acan ya hango Aryan sheme saman carpet yana wani irin abu kamar mai iska,kansa yaje ya dagashi duk hankalinsa atashe,baima tsaya ya saurari fitowar umma barira ba yanufi waje dashi,
Asibiti suka kaishi nan aka fara bashi taimakon gaggawa,shidai a iya saninshi Aryan lafiyayyen yarone bashi da wata lalura sai dai ko boyayyiya wacce bata bayyana ba,
Abinda likita yafada masa ne yayi mutukar girgizashi wai zuciyar Aryan yar mitsitsiya ce sannan dole aguji bacin ran shi adaina hanashi abinda yake so,to ai dama Khalil a iya saninshi abinda Aryan yakeso yake masa dan shi ko fada bai yarda wani yayiwa yaronsa ba,
Aranar da daddare aka sallamesu,tunda suka koma gida yaketa nan nan da Aryan ranar ma tare suka kwana,da zarar yayi masa maganar mommy kuwa sai yace ehh zai nemo masa ita duk inda take,abun har mamaki yabashi saboda irin yanda yaga yaron yanata murna yana farin ciki,shima farin cikin yaji ya samu kansa aciki domin farin cikin Aryan shine nasa, Aryan ya cancanci dukkan soyayyar da ta dace daga gareshi domin yarasa mahaifiyar shi a lokacin da yake tsananin buk'atarta baiji dumin jikinta ba haka kuma bai sha ruwan madarar dake fita daga jikinta ba shiyasa yanzu dole ya zame masa uwa kuma uba dole yasamar masa da dukkan farin cikin da yake buk'ata koda kuwa hakan zaisa shi yarasa nasa farin cikin......âœï¸
*_Ummi Shatu_*👌ðŸ»
8/14/20, 10:06 AM - Ummi Tandama: ©� *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*D'AND'ANO.....*
*MIJIN MATACCIYA....*💞💞
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*Wattpad:-ummishatu*
بسم الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
*6*
~~~*R* anar hutu Khalil da kansa yakai Aryan makaranta saboda tunda suka tashi daga bacci yaga alamar da rigima Aryan din yatashi dan sai wani tutturo baki yake yi breakfast ma saida lallami yasamu yaci amma da umma barira tayi tayi dashi ya zauna yaci yaki ci daga k'arshe ta kira Khalil awaya,yana kwance yana bacci yaji karar wayar landline ta cika masa kunne wacce ke ajiye saman drawer din gadonshi,dole tasa yatashi ya daga wayar domin yasan daga cikin gidan ake kiransa ko securities ko wani daga cikin jama'ar dake cikin gidan addu'ar shi dai bata wuce Allah yasa ba baki yayi ba da sanyin safiyar nan domin ko wanka baiyi ba,
Muryar umma barira yaji tana cewa,
"Mu'azzam zo kaji da wannan kinibabben yaron naka dan ni bazan iya ba nayi lallashi har nagaji yaki jin lallashina tunda kai kaine ubansa kila zaiji naka....."
Jin abinda umma barira tace yasashi yin murmushi mai dauke da sauti yasauka daga saman gadon yana kokarin zira silifas dinshi dake ajiye gaban gadon domin tana gama fadar abinda ta fada ta katse layin,
Gaban closet dinshi yaje ya tsaya yacire farar riga armless din dake jikinsa yasaka jallabiya kalar ruwan kasa sannan yafita,
A babban falo yasamesu suna drama umma barira nata tura masa soyayyen dankalin turawa wanda ya wadatu da kwai ga plantain shima agefe da wainar kwai sharba sharba amma yaki ci sannan ga tea dinshi nan a dan karamin cup dinshi,
Umma barira na ganin yashigo ta mike ta nufi cikin falon tabar dining room din tana fadin,
"Khalil wannan yaron naka dan jakar ubane ayita shan kansa amma yana sake botsarewa.....to nidai nayi nawa jeka kaima ka gwada taka sa'ar"
Murmushi Khalil yayi yana kallon Aryan wanda ke zaune saman dining yana ta turo baki,
"Ai ni dama tunda naga har yanzu bai shigo dakina ba nasan da walakin.... Bari naje na bashi abincin....."
Daga haka yawuce wurin Aryan ya zauna akusa dashi sannan ya dagashi ya dora kan cinyarsa,
"Baba na yau kuma abinci ake yiwa yaji? Uhmmm? Yau fa za abaku hutu amma banga kana murna ba.... Kana da kiwar zuwa school Aryan,nifa when i was young kamarka banyi gardamar zuwa makaranta ba..."
"Papa ni bazan ci wannan ba..."
"To me zaka ci? Fada min maza adafa maka kaci ka tafi school ka karbo report card dinka"
"Noodles...."
"To ai mai saukine bari adafa maka within 5 minutes...."
Tashi yayi yafita ya kira kuku nan da nan kafin wani lokaci ya dafa noodles din mai kunshe da vegetables aciki da kifin gwangwani sannan ga soyayyen kwai akai,
Zama yayi yabashi abaki yaci ya koshi sannan yaje ya kaishi da kansa daga nan ya juyo gida domin kamar koda yaushe yauma yana da inda zaije.
Tunda yafita bai samu dawowa ba sai misalin karfe 10 saura na dare yayi mamaki sosai da yaga wai idon Aryan biyu a wannan lokacin baiyi bacci ba,yana ganinshi ya ruga da gudu ya rungumeshi yana rike da report card dinshi a hannu,daukarshi Khalil yayi yana karbar report card din,fuskarshi ce ta fadada da murmushi da fara'a har yakai bakinshi kan goshin Aryan yayi masa kiss,
"Yaron kirki this time around baka yarda suhail ya kwace maka first position din ba?? Kayi kokari,zan yi maka duk abinda kake so kaji...me kake so?"
Kwantar da kanshi yayi jikin kafadar uban sannan ahankali yace,
"Mommy..."
"To Aryan din Daddy..."
Tare dashi sabe a kafadarshi yawuce bedroom dinshi ya ajiye shi saman gado shi kuma ya fara kokarin rage kayan jikinsa.
Bayan yayi wanka yayi shirin bacci yana zaune saman Rug da Aryan kan cinyarsa yana bacci umma barira ta kira waya tana tambayar ko suna tare da Aryan domin ta shiga dakinsa bata ganshi ba kuma baya wurinta,niyyar tsokanarta yayi yace,
"Umma baya wurina ni nan ni kadai ne"
"To sai ku bazama nemansa domin nima baya tare dani"
"Umma kenan kin ganshi nan yana bacci,hira ma muke yi yayi bacci ya barni..."
"Aima yayi kokari da har kadawo ka sameshi ido biyu shida kafin 8 wani lokacin yayi bacci amma yau ya dan taba baccin rana wuni yayi yana bacci inajin shiyasa baiyi na daren da wuri ba"
"Ai nima nayi mamakin ganin idonshi biyu lokacin da na shigo"
"Ina ruwan mai gida"