Sashe 8
Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai phone number dinshi a k'asa, maganar PA ce ta fado mata inda yake cemata,
"Akwai number dinshi ajiki yace idan kina da bukatar magana dashi ko wani abu mai kama da haka sai ki kirashi...."
Ita bazata kirashi ba amma dole ce zata sa tayi hakan ko dan tunatar dashi kuskuren da yake neman tafkawa dan kawai yana da kudi,saboda kawai yana da dama shine zaiyi amfani da karfin mulkinsa wurin musgunawa wasu,
Number wayar tashi ta kwafa tasoma kira domin so take ta fada masa maganar da zata bakanta masa rai watakila ma idan yaji haushi yace yafasa tunda bata da kunya,
Saida ta kira wayar sau hudu amma bata shiga sai dai ta danyi wata yar kara sai ta yanke,tsaki taja ta harhada kan kayan ta mayar dasu cikin leda tana kokarin tashi tajiyo karar shigowar text massage,
Kamar bazata duba ba sai kuma ta dauka tana dubawa,
_Am Little busy now,text me please._
Shine abinda taga anturo da wata special number mai dauke da 33333, tunani tafara yi to waye kuma wannan? Zuwa can tagane minister ne,kai duk yanda akayi shine tunda ita dai yau bata kira kowa ba sai shi,kai shi dinne ma,
Saida ta duba number tasake dubawa sannan ta mayar masa da reply,
_Ya kamata dai idan angirma asan angirma,duk zawarawan duniyar nan da rikakkun yanmata ka rasa wacce zakace kana so sai ni,nidai ka cuceni kuma kasani kawai zanyi zaman biyayya ne bawai dan ina soba saboda ni inada wanda nake so,idan kuma dan kana da kudine to ni kudinka baya gaba na._
Shine abinda ta rubuta ta tura masa amma shiru babu amsa har tagaji ta daina ma tsammanin zai turo mata da reply, "kaji irin wulakancin nasu ai" tafada aranta kafin ta tashi taje tashiga wanka,har tagama komai nata ta shirya ta kwanta mutumin nan baibi ko ta kanta ba,har tagama yanke tsammanin zai kulata domin 11 tawuce.
***
Lokacin da Hanan ta kirashi yana cikin meeting da yan uwansa ministoci,shi a ka'idar wayarshi idan ka kira asalin layinshi bazai shigaba sai dai idan text massage kayi masa to wannan zai shiga har yagani amma idan kira kayi to bazai shigaba amma dai zai ga kiran a dayan layinshi da akayi forwarding kiran zuwa can,to idan yasanka zai kiraka ta special line dinshi idan kuma bai sanka ba shikenan sai yakyale,itama Hanan dalilin da yasa ya san itace shine abbanta yatura masa number din tunda jimawa tun bayan lokacin da yabashi aurenta da yakirashi domin yimasa godiya yatura masa number dinta wai ko zai kirata shi kuma baice a'a ba amma aganinshi me zai kirata yace mata? Shi baida bukatar number dinta saboda baida case da ita,
To yau yana tsaka da meeting yaga kiranta shine yayi mata text, lokacin da ta dawo masa da reply ma shi ko budawa baiyi ba saboda lokacin har yasake shiga wani meeting din da masu bada shawara ta musamman akan harkokin wasanni da matasa gashi yan jarida suna waje sunyi cincirindo suna son ganawa dashi dangane da wani rade radi dake ta faman kaiwa da kawowa acikin gari na cewa wai gwamnatin tarayya zata sauke wasu masu ruwa da tsaki a harkar gwamnati har su dari daya,
Gaba daya bai samu kansa ba sai wurin misalin karfe 11 sai a lokacin yabar office bayan yagama ganawa da yan jarida yanufi gida,
Agajiye yake mutuka sannan ga ciwon baya dake dan damunsa da kuma ciwon kirji shiyasa tun kafin yakarasa gida yasa nura yakira masa likitansa wato Dr Al'amin,
Duk jikinsa jinsa yake babu karfi ga rashin cin abinci,yana komawa gida yayi wanka yasa jallabiya da gajeren wando aciki,a dan karamin falon shakatawarshi ya zauna ya hada coffee mai zafi yasha yana gama sha yaji amai na kokarin fito masa, bathroom din dake cikin falon yashiga yayi aman sannan yadawo falon ya zauna daidai lokacin da PA yashigo yana sanar dashi zuwan Dr cemasa yayi yashigo sannan ya dan kishingida jikin kujerar da yake kai,
Sai da Dr yagama dubashi sannan ya daure masa hannunshi da wata yar roba yana duba jijiya saboda anan ne zai dan yimasa allura sannan zai kara masa wani dan karamin ruwa leda daya,
Sai lokacin ya dauki wayarshi yasoma duba sakon da aka tutturo masa nafi yawa friends ne da masu neman taimako ahaka har yazo kan na Hanan,ganin abinda tace abin yaso ya bata masa rai,wai yara kanana sai su zagi mutum dan kawai maganar aure ta hadasu, yanzu ita wannan yarinyar ko ahanya ta ganshi ta isa ta fada masa wannan maganar ba dan maganar aure ta shiga tsakani ba?
_Ok_ shine abinda yatura mata kawai,yaci gaba da karbar ruwan dake shiga jikinsa wanda Dr ke kara masa,ajiye wayar yayi agefe ransa adan bace,
"Ranka yadade wallahi stress ne kawai ba wani abuba, sannan kuma yallabai maganar nan tawa dai kamar koda yaushe,dole fa sai ansamu abokiyar debe kewa..... Saboda agaskiya kana bukatar mace ko dan lafiyarka"
Shiru Khalil yayi yana dan sake jingina sosai cikin kujera, so yake idan yagama da Dr yaje yaga Aryan saboda yau throughout bai ganshi ba,yadai ganshi da safe kafin yafita lokacin ko ma tashi daga bacci baiyi ba kasancewar yau asubanci yayi.
Wurin karfe 12 saura sakon minister yashigo wayar Hanan dama har lokacin bata yi bacci ba,tana dubawa taga ok,ranta yayi mutukar baci,inbanda rashin mutunta dan adam Menene zai ce mata wani ok,
Tsaki tayi tasake tura masa da wani text din,
Bai kulata ba sai da Dr yatafi shima PA yatafi, bedroom din Aryan yaje ya dubashi sannan yakoma part dinshi yawuce bedroom ya kwanta domin Dr yace yadan samu bacci akalla na awanni shida. Massage din da yaji yashigo tun dazu ya duba,
"Again?" Yafada ganin Hanan ce ta sake turo masa da reply,
Budewa yayi ya tsurawa sakon nata ido cikin nutsuwa,
" _Ni dai ancuceni anrabani da wanda nake so saboda kawai budurwar zuciya,angirma ma ba za a hakura ba,yadai dace idan angirma asan angirma._"
Afili ya karanta sakon kamar yana karantawa wani,wai shine mai budurwar zuciya, murmushi yayi saboda shi abinma dariya yaso bashi,sai dai gaskiya turancinta ya burgeshi saboda duk sakonnin tana turosu ne da harshen turanci da alama dai ta kware a fannin,
Bai cemata komai ba ya ajiye wayar tashi saman bedside drawer sannan yakashe bedside lamp din dake gefen gadonshi ya lumshe idanuwanshi saboda son bin umarnin Dr,yana son ya dan samu bacci kamar yadda Dr yace......âœï¸
_Ga mai bukatar siyan littafin mijin matacciya zai tura naira 200 ta account dina 3112877210 Aisha Ibrahim first bank sai atura shaidar biya ta 07044644433,ko kuma recharge card na MTN ta wannan number din 07044644433 sannan sai atura shaidar biya ta number da aka turawa._
*_Ummi Shatu_*👌ðŸ»
8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: ©� *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*D'AND'ANO.....*
*MIJIN MATACCIYA......*💞💞
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*9*
***Baccin shi ya takarkare ya shaka kamar babu gobe sosai kwakwalwarshi da gangar jikinsa suka huta daidai yanda ake bukata shiyasa ras yatashi da asubah yayi salla sannan yasake dan komawa ya kwanta hankalinsa kwance wani lafiyayyen baccin yasake kwasheshi bashi yasamu farkawa ba sai misalin karfe 8 nasafe lokacin tuni andade da kai Aryan makaranta shi kansa yayi mamakin dalilin da yasa Aryan yau bai shigo dakinsa ba to kodai yazo yana bacci kuma bai samu nasarar tashinsa ba?
Wanka yayi yashirya cikin dark blue din shadda sabuwa fil sannan yafita,kamar koda yaushe table ashirye yake tsaf da kayan karyawa kala kala,
Shi arayuwarsa yana mutukar kaunar Irish amma yanayi yasa baya zama yaci yau dai ya zauna akan table domin karyawa saboda jiya Dr Al'amin yayi masa maganar rashin cin abinci kuma hakan na iya haifar masa da wata matsalar duk da dama matsala kam sai dai ayi fatan sauki amma yana tattare da ita,
Soyayyen dankali da kwai ya dan zuba sannan yahada coffee kamar yadda yasaba,dan ci yayi ba wani mai yawa ba sannan yasha coffee yana shirin tashi umma barira tashigo ganinshi saman table yasata dan murmusawa tana cewa,
"Mu'azzam yau ansamu damar cin abinci?,ai gara ka rinka dan ci ko kayi kumari..."
Murmushin shima yayi yasauka kasa ya gaidata sannan yamike yana fadin,
"Wallahi kuwa umma, yau banga mutumin ba ko laifi nayi shiyasa ba ako lekani ba?"
Dariya umma tayi taja kujera ta zauna,
"Ai Aryan yau akwai abinda ya dauke masa hankali amma yashiga wajen naka bai dai tasheka bane...."
"Nima nayi wannan tunanin nace duk yanda akayi yashiga bedroom din nawa tashina ne dai baiyi ba,umma ni bari inwuce wallahi mutane na can suna jirana a office tun 7"
"To shikenan adawo lafiya, Allah ya tsare yabada sa'a, Allah yadawo dakai lafiya"
"Amin umma nagode,sai nadawo"
Juyawa yayi yabi ta kofar babban falo yafita,duk da bai son maganar Hanan tazama issue acikin al'amuransa dan baida lokacinta amma sai da ta zama,abun ya tsaye masa arai bai san dalili ba,wai shi ta kira da mai budurwar zuciya,kasa yakice maganar yayi acikin ransa haka ya wuni da ita.
***
Amarya Hanan kuwa kowa yaganta yasan acikin bacin rai take domin fuskarta babu walwala sam, ga haushin rashin baccin da bata samu jiyaba saboda bakin cikin abinda minister yayi mata, dama su masu kudin nan wulakanci garesu basa ganin kowa da gashi sai junansu,
Tana ta faman babbata fuska ta shirya ta tafi gidan anty salaha can ta iske mujahid yana jiranta cikin motarshi a kofar gidan. Bude side din mai zaman banza tayi tashiga ta zauna take tafara hawayen da tajima tana dakonsu acikin zuciyarta,
Tagumi mujahid ya rafka yana kallonta shima nasa idanuwan jajur kamar ya hadiyi kunama,shi kansa badan dauriya da juriya irin na maza ba da tuni yajima da fashewa da kukan amma dai yadaure,sunfi mintuna goma zaune shiru babu wanda yayi ko tari acikinsu sai sautin kukanta da yake fita kadan kadan,
"Hanan.... Ki daina kukan nan da kikeyi domin ahalin yanzu shi yafi komai tayar min da hankali... Kiyi shiru kinji,kiyi shiru kiji abinda zan fada miki"