← Book details Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 61

Sashe 18

Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari bayan antashi daga school office yasa aka kawo masa Aryan ba akaishi gida ba,

Tare ya zuba musu abincin da PA ya karbo musu daga gida saboda Aryan,daukar shi yayi yadora saman cinyarshi suna facing juna gani yayi da alama yauma Aryan yayi kuka,cikin damuwa ya dan girgizashi,

"Abba na meke damunka? Andukeka a makaranta ne?"

Girgiza kai Aryan yayi kamar zaiyi kuka dan har yafara murza ido da hannunshi,

"To meke damunka? Maza fada min,kaida na kawo maka mommy gida,ko baka farin ciki da zuwanta?"

Daga kai yayi alamun ehh tun daga nan Khalil yasa alamar tambaya jikinsa yabashi akwai wani abu dake faruwa...............✍️

*_Ummi Shatu_*👌🏻
8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*17*

***Sake tsare Aryan yayi da idanuwanshi yana son gano dalilin da yasa yaron yashiga cikin damuwa kwana biyu tunda ya tambayeshi yaki fada masa damuwarsa,

Kama hannunshi yayi yana murza diamond ring din dake yatsanshi,

"Aryan me mommy din take yimaka? Tana dukanka ne?"

Girgiza kai yayi alamar a'a,

"Tana zaginka ko?"

Nan dinma girgiza kan yayi wai a'a,

"To me take yimaka? Fada min bazan fada mata ba"

"Nidai uncle umma tadawo....umma nake so"

"Umma zata dawo ayau dinnan ma kuwa Aryan amma matsalar baka fada min abinda mommy din keyi maka ba,ko baka son inje umarah dakai bana?"

Kwantar da kanshi yayi jikin uban yana murza idanuwa,

"Ina so..."

"To me take yimaka?"

"Babu komai"

"To shikenan,bari nakira PA yazo maza yatafi gombe yanzu yaje ya dauko umman"

Tunda Aryan yaji haka yashiga murna umma zata dawo wanda har abin yaso bawa Khalil mamaki to ko dama rashin umman ne ke sashi cikin wannan damuwar? Babu mamaki saboda umma bata nanne yasa yaketa wadannan shiriritar tunda da ita yasaba,

Kasancewar shima Khalil din fita zaiyi yanada ganawa ta musamman da shugaban kasa yasashi bawa PA Aryan akan yakaishi gida amma Aryan ya tubure akan shi lallai lallai sai yabi nura dauko umma,cewa nura yayi su tafi taren amma dan Allah kar suyi dare ahanya.

Hanan na gida bata san abinda ke faruwa ba ita dai taga Aryan bai dawo gida ba daga baya kuma sai malamin islamiyyarshi da yazo yana jiranshi yace PA ya kirashi yace yatafi wai Aryan na tare da babanshi a office ita sai a lokacin ma taji abinda ake ciki,

Tabe baki tayi ta zuba abincin ta a plate tawuce sama ta shiga falonta tana ta jan tsaki ita kadai,

"Haka kawai kun dauki son duniya kun dorawa yaro kamar akanka aka fara haihuwa,bama dole yaro ya sangarce ba tunda ba a tsawatar masa...."

Saida tagama cin abincin sannan ta zage tafara gyara falon saboda da alama masu aiki iya kasa kadai suke gyarawa sai ko dakin Aryan amma ita nata basa ko shigowa ma shiyasa ta dage ta shareshi tsaff duk da ba wani datti yayiba tayi mopping ta kunna turaren wuta a burner take falon ya dauki kamshi kamar me, toilet ta shiga ta yi wanka tafito bayan ta shirya cikin doguwar riga yar kanti marar nauyi dark blue ta dauko wayarta ta kira number mujahid kamar a mafarki sai taji ta shiga amma har tayi ta katse bai dauka ba sake kira tayi nan dinma har ta tsinke bai daga ba,

Kwalla ce taji tafara zubo mata daga idanuwanta dan wallahi har yanzu bata ji alamar sonshi yaragu daga cikin ranta ba kuma bata jin zata iya daina kaunarsa a rayuwar da zata gabatar agaba,

Text massage ne yashigo wayarta nan ta dauka ta duba mujahid ne yaturo mata,

_Hanan dan Allah kiyi hakuri ki yafe min sannan ki zauna da mijinki lafiya wannan itace alfarmar da nake bukata kadai daga gareki._

Wasu hawayen ta sake jin suna kokarin zubo mata wai kowa sai yace ta zauna da mijinta lafiya bayan mijin ko sanin kamanninsa ma bata yiba ita yanzu da zasu hadu a hanya tasan sai yawuce ta wuce dan dukkansu ba sanin fuskokin juna suka yiba ita wallahi wannan mutumin yagama cutarta,kamar dama wacce take jira nan tasha kukanta tagama sannan ta sauka kasa har lokacin Aryan bai dawo ba babu shi babu alamarsa amma tunda dai ance tare yake da babanshi shikenan. Haka tayita kaiwa da kawowarta ita kadai acikin gidan har magriba tayi tunda ta shiga daki kuma bata sake fitowa ba har akayi sallar ishah,saida ta tashi ta gabatar da ishah din sannan tafita falonta dake sama,tv ta kunna ta kamo tashar da ake nuna fina finan India sabbi da tsofi bugu da kari akwai fina finai masu dogon zango da tashar ke nunawa dan debe kewa,

Zama tayi zaman dirsham tana kallon film din da suke nunawa a wannan lokacin mai suna Viva,kallon shine ya dauke mata kewa dan ko tashi bata son yi har saida taga karshen film din nan ta kalli agogo domin yunwa take ji tana dan sunkurinta haba ashe dole taji yunwa domin karfe 10 daidai yanzu lallai tajima azaune dama karatu da kallo haka suke idan suka dauke maka hankali sai ka raba dare batare da kasani ba,

Tashi tayi da niyyar zuwa kasa domin zubo abinci wanda zata dan sakawa cikinta,duk da dare ne saida ta yafa mayafi ajikinta sannan ta sauka,gidan shiru kamar koda yaushe sai ko uban hasken fitilu tarwal tamkar rana dan ko allurarka ce ta fadi to babu shakka zaka ganta hankali kwance,falon sai tashin kamshi yake yi kamar koda yaushe kan dining table din kuwa jere yake da abinci reras kamar yadda John yasaba shiryashi,

Tuwon semovita tagani miyar okra,sai sphagettee with beef stew,fish and yam stew sannan ga balangu jalop,fish and yam stew ta zuba a plate sannan ta debi balangun taje fridge ta dauki ruwa da juice takoma sama ta cigaba da kallonta tana tsakurar abincin ta ahaka har ta cinye,ita dai gashi ahaka kamar babu abinda ta rasa amma azuciyarta tana jin tabbas ta rasa wani muhimmin abu atare da ita mai mutukar muhimmanci,

K'arfe 10:30 su umma barira suka dawo lokacin kam tuni Aryan yajima da yin bacci dan lokacin da suka shigo ma PA ne ya daukoshi yashigo dashi falon kasa ita kuma umma ta karasa dashi dakinsa ta kwantar dashi bayan ta canja masa kayan jikinsa,

Falon Hanan ta nufa a karon farko dan ba taba shigarshi tayi ba sai yau,har lokacin Hanan na zaune ta kurawa tv na mujiya amma fa acan zahiri bawai kallon take yi ba kawai tunanin yanda rayuwarta ta sauya a lokaci kankani take yi,ita da tajima tana lissafin sai tagama karatu tagama NYSC sannan zatayi aure ashe abin ba haka yake ba,

Jin ana yin knocking yasa ta dan firgita sai kuma tajiyo muryar umma tana cewa "Ko har matar gidan ta kwanta ne?"

Mikewa tayi taje ta budewa umma kofa fuskarta dauke da murmushi,

"A'a wallahi umma idona biyu ashe kune kuka dawo...."

Karasa shiga cikin falon umma tayi tana cewa,

"Ehh wallahi ai mutumin nawa ne yatada rikici sai da akaje aka dawo dani,basu ma sameni anan cikin gombe dinba ina can Billiri gidan dan uwana ziyara acan suka je suka rakato ni..."

"Allah sarki,ai gara da kika dawo umma amma kin tafi ki barmu?"

"Ai ba tafiya nayi ba 'yarnan,zuwa nayi indawo"

"To ai shikenan umma barka da dawowa ya mutanen gida? Kin baro kowa lafiya?"

"Lafiya lau,suna agaggaisheki"

"Ina amsawa"

Kasancewar umma ta gaji daga haka ta tashi ta tafi taje tayi shirin bacci ta kwanta. Ita kuwa Hanan batayi bacci da wuriba yau tasamu kallo saida takai 1 na dare tana kallo a d'akinta,daga k'arshe ta kashe ta kwanta,

Daidai lokacin kuma Khalil yashigo gidan bai shiga ko inaba sai dakin Aryan kadai daga nan yafito ya dan zazzaga gidan sannan yatafi domin agajiye yake shima.

Washe gari misalin karfe 8 yashiga gidan lokacin har ankai Aryan makaranta,dakin umma yashiga kamar koda yaushe yana sanye da farar shadda kar tasha aiki da coffee colour din zare yadora hula itama coffee yar bama sai kamshin turaren gentleman yake yi wanda yake fita daga jikinshi,

Zama yayi suka gaisa da umma sannan cikin fara'a yace, "umma sai kuma kika ga anje andauko ki...... Wallahi Aryan ne yakasa sakewa da bakya nan"

"Ehh mu'azzamu haka nura ya sanar dani,amma ai da kun barni na danyi koda kwana biyu ne itama matar gidan ta dan sake"

Dariya yayi saboda jin abinda ta fada dama yasan dalilin da yasa ta tafi kenan ganin yadawo ne, "A'a umma ai babu komai kiyi zamanki wallahi,nima kaduna zanje yanzu amma sai na fara zuwa office tukunna zan gana da manema labarai"

"To Allah ya kiyaye hanya yabada sa'a,sai ka dawo"

"Amin umma,mutumin yatafi makaranta ko?"

"Tun dazu ai yajima acan,yatafi yana ta rikicin wai sai anhada masa harda wannan lemon madarar da ka hana abashi cikin lunch box dinsa"

"Kar arinka bashi umma saboda rana wallahi"

"Ehh ai shiyasa ban bashi ba nadai lallabashi nabashi dayan"

Fita yayi yatafi abinshi bai ko nemi inda matar gidan takeba kai to ai shi da zaka saka wuyansa gaba gabas bazaice maka ga kalar amaryar nan ba, ita kuwa umma har yau bata san ba agidan yake kwana ba duk d'aukarta agidan yake.

Hanan sai wurin karfe 11 sannan tafito bayan tayi wanka ta shirya cikin wani jan swiss material dinkin doguwar riga,umma ta iske tana falo tana sak'a muficin roba da alama jiya ta taho da kayan yin,

Tea ta hado ta dawo wurin umman ta zauna suna hira,

"Ashe maigidan kaduna zaije ko? Ai kullum baya rabo da tafiye tafiye,ayi mutum kullum da inda zaije bashida ranar hutu? Wannan aiki nasu da wahala yake"

Jin abinda umma tace yasa Hanan fuskarta akan baban Aryan umman ke magana, murmushin yake tayi amma bata nuna cewa bata saniba,
Chapter 18 · 0% Book details