← Book details Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 61

Sashe 54

Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaji abinda Aryan din yafada sarai amma sai bai kulasu ba kawai yaci gaba da cin abinsa har ya kammala lokacin tuni har lokacin sallar ishah yayi dan haka bai zauna a falonba yamike zuwa cikin bedroom dinshi hakan ya tabbatarwa da Hanan cewa bazai bata ba shiyasa kafin yafito ta tashi tafita shikuma Aryan yabishi zuwa cikin bedroom din tare sukaje salla suka dawo,itama sallar taje ta yi,bayan ta idar ta na zaune kan abin salla Aryan yashigo yace taje Daddy yana kiranta,tashi tayi batare da ta cire hijabin jikinta ba tabishi suka tafi,

Yana hakimce kan sofa ya dora kafarshi daya akan center table yana ta faman yimata bincike awayar tata,zama tayi akujerar dan nesa dashi kadan,

"Me kuke cewa dazu keda d'anki?"

Taji yafada har lokacin idanuwanshi na kan wayarta yana ta faman yimata bincike ita dai fatanta Allah yasa kar ya kalle mata sirrin da ta ajiye a WhatsApp,dan duk ranar da hajja hasinah tayi posting din abu mai amfani starring dinsu takeyi ta adana bata gogewa,

"Baki jine?"

"Inaji..... Cewa nayi ka taimaka kabani wayata zanyi amfani da ita gida....."

Bai amsa mata ba har tsawon mintuna biyu sannan cikin alamar tuhuma taji yace,

"Waye mujahid?"

Sosai tambayar tabata mutukar mamaki sannan lokaci guda saima ta nemi amsar da zata bashi ta rasa dan sai ta kasa gane wayema mujahid?

"Ina tambayar ki waye mujahid?"

Shirun taso sake yi amma kuma ganin ya tsareta da idanuwanshi mayalwata yasata yin kasa da kanta sannan tace,

"Dan makarantar mu ne..."

"Kar kiyi min karya dan already nasan gaskiya,kawai ina son sake tabbatarwa ne,wayeshi?"

Ji tayi yawun bakinta na neman kafewa,

"Ya taba cewa yana sona......"

"Tsohon saurayinki ne kenan?" Taji yafada bayan yaja wasu sakwanni,

"Uhmmm"

"Bai san kinyi aure bane?"

"Yasani..."

"Ok"

Daga nan cigaba yayi da tambayar contacts dinta kusan kowa sai ya tambayeta waye shi sai dai abinda yabata mamaki shine sam bai tambayeta waye wannan wanda yake turo mata text massage dinba ko bai ganiba?

"Ita wannan hasinah din itace malamar ku kenan?" Taji yafada babu zato babu tsammani, sunkuyar da kanta kasa tayi tana jin kunyar duniya na lullubeta saboda tasan yaga abinda taketa addu'ar Allah yasa kar yagani,

Baiyi mata maganar ba ya mika mata wayarta bayan ya gama karanta duk abinda idonshi yasauka akai,

Hannu biyu tasa ta karba ta tashi tafita cike da murna tana zuwa part dinta ta saka wayar a charge tashiga wanka,bayan tafito tagama shirin bacci ta dauki wayar ta kunna data ta leka WhatsApp domin sosai tayi missing dinshi shiyasa har 12 saura takai yau a online,kai ashe waya ma rahama ce bata san da haka ba har saida Khalil ya kwace mata wayarta.

Washe gari Khalil yabar kasar yatafi k'asar Rwanda,tunda yatafi kuma ta shiga missing dinshi har ta kasa hakuri sai da ta tura masa massage,

Yana kwance adaki har yafara bacci yaga massage din nata murmushi yayi ya mayar mata da reply,

_Me kika fi missing atare dani?_

Itama murmushin tayi lokacin da taga tambayar da yayi mata saima ta rasa amsar da zata bashi dan haka tayi shiru kawai. Satinshi daya yadawo,aranar da yadawo bai shigo gidanba sai dare bayan duk sunyi bacci washe gari da safe yatafi gombe bayan yadawo da daddare yakira Hanan falonshi,

"Ki shirya gobe za muje gombe Muneerat ta haihu....." Ya fada yana rike da wata jotter da pen yana rubutu amma bata san abinda yake rubutawa ba,

Tun adaren tayi shirinta ta hada kayanta set biyu sai ko kayan bacci da inner wears,humrar da hajja hasinah ta kawo mata ranar da tazo ta saka cikin akwatin kayanta sai da ta tabbatar tagama hada komai sannan ta kwanta,

Washe gari bayan ankai Aryan makaranta Khalil yaje office yafito suka nufi gombe bayan sunje store ta sai kayan baby,duk yau tunda ta tashi jikinta babu dadi ahaka dai suka karasa da rana fatse fatse nan ta samu tarba kamar yadda aka saba yimata,saida suka fara zuwa gidan Khalid suka ga baby anan Muneerat ke yimusu albishir din wai sunan Khalil Khalid yasakawa jaririn,ba karamin dadi Khalil yajiba nan ya ajiyewa Muneerat damin kudin da Hanan bata san ko nawa bane amma dai yan dubu dubu ne sabbi fil dasu,daga nan suka tafi cikin gida can Hanan ta samu tarba ta musamman awurin su hajiya da su zarah, bedroom din da take sauka idan tazo yauma anan aka sauketa,tunda tazo tashiga cikinsu sarah suna shan hira har dare, Khalil kuwa dama bata kara sakashi a idonta ba kuma shima agarin zai kwana.

Misalin karfe 11 da wurin rabi tana kwance suna chaten da yaya shamsu nan yake sanar da ita rashin lafiyar abbansu wai ciwon koda sunje asibiti yau,ai agigice tasa hijabi ta fita ta nufi bangaren Khalil tana hawaye,

Fitowarshi falon kenan bayan yafito daga wanka yashirya bata tsaya yin knocking ba ta bude kofar ta shiga, kallonta ya tsaya yi yana son jin ba'asin kukanta,

"Abba nane baida lafiya wai ciwon koda..... Dan Allah kasa akaini kano yanzu" haka take ta fada sam taki barinsa ma yafurta koda kalma daya saiko uban hawayen dake ta faman bin kumatunta kamar anballe bakin fanfo,hannunta yakama akaron farko ya zaunar da ita kusa dashi har jikinsu na gogar juna saboda kusancinsu kuma har lokacin yana rikeda hannunta,hakuri yasoma bata domin dare yayi yanzu bazai yuyu akaita kano a wannan lokacin ba,kuka ta fashe dashi hakan yabashi damar sakata acikin jikinsa yana rarrashinta,tun shigowar ta kamshin jikinta ke neman rikita masa lissafi domin humrar hajja hasinah yau ta shafa wato giredi nan da nan ta tayar masa da hankali,ita kuwa yau mamakinsa ne ya cika mata zuciya ganin ya biye mata harda rarrashi shiyasa ta bararraje taci gaba da shagwabarta.......................✍�

_Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._

*_Ummi Shatu_*👌🏻
8/14/20, 10:15 AM - Ummi Tandama: 48

***D'aukarta yayi gaba dayanta ya dorata kan cinyarsa wanda hakan yayi mutukar bawa Hanan kunya sosai, rungume ta yayi cikin jikinsa yana shafar bayanta alamar rarrashi,ji tayi kamar ta nutse kasa saboda tsananin kunya,shi kuwa gogan hankalinsa ne yakai kololuwar tashi saboda sosai kamshin jikinta ya rudashi kuma ya jefashi cikin kogin bukatarta,

Cikin dabara yasamu ya rabata da hijabin da ke jikinta wannan ba shine karo nafarko da yafara ganinta ahaka ba amma wannan yana da banbanci da na lokutan baya,sosai yau dinnan Khalil ya dauki dumi domin wata irin matsa yayi mata sai faman aikin sinsinar jikinta yake yi sakamakon kamshin da jikinta keyi wanda ke kara masa kaimi yana ingizashi gareta,cak yatashi da ita yanufi cikin bedroom dinshi yana rike da ita,ita kam idanuwanta arufe suke ta runtse su dan ba zata iya hada ido dashi ba cikin wannan yanayi,

A saman katafaren gadonshi yayi musu masauki bayan ya rage hasken dakin izuwa haske marar karfi, jikinta har rawa yake yi saboda rashin sabo ga kuma tsoro duk da cewa abun yazo mata bagatatan batare da shiri ba,tun kafin ya aiwatar da kudirinsa shima nasa jikin ya dauki rawa babu bata lokaci wani matsanancin zazzabi da ciwon kai suka rufeshi nan take batare da ya cimma burinsa ba,

Kasa aikata komai yayi sai ko uban kakkarwar sanyi da gangar jikinsa keyi kamar ana kwara masa kankara,

"Sa'adatu lullube ni........ Sanyi nake ji"

Gaba daya duk ta rude itama ganin abinda ke faruwa domin wani irin rawa jikinsa keyi, lullubeshi tayi da bargo amma yanda yake jin sanyi na kadashi gani yake yi kamar bata rufa masa komai ba shiyasa yayi azamar jawota jikinsa ya rungume jikinsa ya dauki zafi sosai,

Haka suka kasance zuwa wani lokaci yanata kakkarwa har lokacin yana rungume da ita kamar zai mayar da ita can cikin cikinsa,ya dan fara samun bacci sama sama ciwon ciki ya turnikeshi kamar zai mutu har da su yunkurin amai amma kuma yakasa, Hanan kuka tafara yi tana son ta tashi taje cikin gida ta kira su hajiya amma ya riketa tsam kamar me,kuka take ta faman yi tana yimasa sannu shi kam ko magana ma yakasa yi sai yunkurin amai yake ta yi cikinsa na murda masa haka suka kusan kwana dan sai kirjin asubah sannan yasamu ciwon ya lafa masa har bacci yayi nasarar daukarshi,sakashi agaba Hanan tayi tana kallonsa cikin tausayawa har lokacin yana manne da ita yana bacci,ita kam sai bacci barawo domin tana cikin hali na zullumi dan yanda taga Khalil din yayi ba karamin tayar mata da hankali yayiba dan kamar wanda zai mutu haka yazame mata fa,

Misalin karfe 7:30 na safe ta farka nan idanuwanta suka sauka akan bawan Allah Khalil da keta faman baccin wahala duk yagama jigata takai kimanin mintuna biyar tana kallonsa sannan da dabara ta raba jikinta da nashi ta tashi, kayan baccinta ta maida jikinta sannan ta shiga bathroom,bata wani jima acan sosai ba tagama abinda zatayi ta fito tazo tayi salla,bayan ta idar ne ta samu zarafin kallon dakin,daki kam komai yaji ne babu ma abinda yafi burgeta irin dan karamin farin gadonshi wanda ke girke cikin dakin,mikewa tayi ta nufi bakin gadon nan idonta yasauka kan wani madaidaicin hoto dake ajiye kan bedside drawer dinshi,zama tayi ta dauki hoton tana dubawa bakinta abude mamaki karara kwance saman fuskarta domin badan tasan cewa ba ita bace ta dauki wannan hoton to da babu abinda zai hana tace itace saboda tamkar kara aka tsaga da ita da wacce ke jikin hoton tana sanye cikin purple din atamfa tana dariya, Allah mai iko to ko wannan itace mahaifiyar Aryan? Ta kissima hakan acikin ranta,tajima tana kallon hoton kafin ta ajiyeshi ta juya ga Khalil wanda ke kwance ya dunkule wuri daya,so take ta tasheshi yayi salla amma tana tsoron kar kuma yatashi da ciwon cikin tunda ansamu ya lafa masa,
Chapter 54 · 0% Book details