← Book details Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 61

Sashe 21

Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rungumeshi tayi tana tambayar shi me yafi so wanda zata bashi a matsayin gift da yake yaro akwai shirme wai sai yace cake yake so,dariya tayi tace insha Allah zata yimasa cake,

Khalil kuwa washe garin ranar yatafi kasar Italy kuma aranar da yamma sai ga Zaid yazo saboda wai shine zai kai Aryan wurin birthday dinshi idan ranar tayi,

Sai yau Hanan ta taba ganin Zaid saboda ranar bikinta bata samu damar ganinsa ba tana kunshe cikin mayafi,tunda Aryan yaga Zaid ya makale masa suna ta tafawa da yin games kamar wani abokinsa,shima Zaid yanada haske amma ba sosai can ba kana dai ganinsa kaga bufulatani,gaba daya tana ta tunanin abunda yadace ta bawa Aryan amatsayin birthday gift dinshi amma ta rasa me zata bashi daga karshe dai sai ta turawa da Khalil text message,

_Ina son zan fita zuwa super market nida Aryan_

Shine abinda yaga ta turo masa, lokacin da yaga sakon nata yana daki ya idar da salla, reply yatura mata,

_me akeyi a supermarket din? Ki kular min da yaro saboda ban fiya barinsa yana fita any how ba._

Yana gama tura mata yakira Zaid yace yakaisu supermarket din sannan dan Allah ya kula da Aryan Sosai,

Shiryawa Hanan tayi tasha bakar doguwar riga mai stones tayi rolling tafita kasa inda Aryan da Zaid ke jiranta,umma suka yiwa sallama sannan suka tafi supermarket din,duk abinda Aryan keso barinsa tayi ya dauka sai da yagama jidar abubuwan da yake so sannan taje wurin biya ta ciro ATM card dinta tabasu suka cire kudinsu ta POS,duk kayan ciye ciye da zaki Aryan ya diba dan harda su ice cream,daga can kai tsaye gida suka wuce dama Khalil sai kiran Zaid yake awaya yana tambaya yaji ko sun koma gida saboda shi duk lokacin da aka fita da Aryan hankalinsa baya kwanciya har sai yaji sun koma gida.

Washe gari yakama ranar birthday din aryan kuma tun safe Zaid yafita karfe 2 yakira Aryan awaya yace wai mommyn shi ta shiryashi zaizo masa da kayan da zai saka,suna bedroom dinshi bayan tayi masa wanka Zaid yashigo ya kawo masa wasu tsadaddun kaya shi ba yadi ba kuma ba shadda ba yasha dinki na musamman kalar kayan ash colour ne amma anyi masa kwalliya da baki,ga takalminsa shima baki Aryan yayi kyau kamar babu gobe,

Itama Hanan shiryawa tayi cikin doguwar riga mai shegen kyau ja tayi rolling kamar abun shiri sai kuma mararta tafara yimata wani azababben ciwo dole sai hakura tayi tace suje,

Zaid ne yadebesu a mota banda umma ita kam cewa tayi adawo lafiya,daga shi sai Aryan suka tafi excellent square garden acan ne aka shirya party din cikin wani kayataccen hall mai masifar kyau, Hall din yasha decoration tako ina ga cakes nan manya manya wurin guda hudu kowanne kalarshi daban amma ajiki anrubuta HBD Aryan,yara da manyan dake wurin kwata kwata basu fi guda goma ba nan akayi aka gama saboda Khalil yanata yiwa Zaid takarar wai karsu yarda sukai dare shiyasa ana yin magriba suka tashi bayan anyanka cake anci ansha.

Har suka dawo Hanan na kwance adaki tana fama da kanta saida taji dawowarsu ne ma sannan ta samu dan karfin fita dan ganin gifts din da aka kakkawowa Aryan wadanda ke zube afalonta Zaid yashigo dasu, gifts ne sama da guda goma ko wanne anyi raping dinshi da raping sheet mai kyalli sannan ga manya manyan cakes dinshi nan wasu an yanka wasu kuma ko tabawa ba ayiba banda sauran snacks da drinks, PA ne yazo falon kasa yakira zaid yabashi wani sungumemen gift din shima anyi raping dinshi wai inji oga wato Khalil,

Hanan na zaune da Aryan akan cinyarta suna cin cake Zaid yakawo sakon,itace tafara budewa gift din Khalil din tana cewa Aryan, "Bari mufara ganin na Daddy ko"

Da wani dan karamin greeting card tafara cin karo wanda ajiki aka rubuta,

_Hope your birthday blossoms into lots of dreams come true! May today be filled with laughter and love. Happy Birthday and many happy returns of the day._

Murmushi tayi bayan ta gama karanta masa,wani babban enlargement din hoto tagani mai dauke da hoton Aryan atsakiya yayi kyau sosai ajiki anrubuta HBD boy,sai kuma wani dan karamin akwati koda ta bude agogon diamond ne kirar carat watch sai walwali yake aciki anninke wata yar karamar farar takarda ce wadda ajiki akayi rubutu da biro kamar haka,

_I may not be celebrating your special day with you but I want you to know that I am thinking of you & wishing you a HAPPY BIRTHDAY._

_papa_

Murmushi tayi ta daura masa agogon wanda kamar angwada da hannunsa,gaskiya babansa rikakken dan boko ne jibi rubutu kamar ba hannune yayi ba sai kace injine ya rubuta,raba dare sukayi suna santin gifts din da Aryan yasamu musamman ma na wurin Dad dinshi ga kuma na sauran mutane dan wasu ma ko budesu basu yiba..................✍️

*_Ummi Shatu_*👌🏻
8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*19*

***Duk da cikin bacin rai take sai da hankalinta yayi mugun tashi domin gani tayi Aryan yayi wanwars baya ko motsi wanda da alama suma yayi ko kuma rai ne yayi halinsa,

Rasa ma inda zata dosa tayi waje ko ciki? Da gudu ta nufi kofar da zata sadata da waje amma sai takasa bude kofar ma da yake arude take sai kokarin budewa take amma ta kasa,kamar daga sama Allah ya kawo mata security guda daya wanda yanufo cikin gidan,cikin rudu da rikicewa dan ko maganar ma ta kasa tafara nuna masa Aryan wanda ke can cikin falo asheme kamar wanda ya mutu,

A mutukar hanzarce suka shiga ya daukoshi,umma na can daki tana bacci bata san abinda ke faruwa ba har suka tafi asibiti,suna zuwa Dr Al'amin ya karbeshi dama shine family Dr dinsu nan yashiga bashi agajin gaggawa ita kuwa Hanan na waje ta rasa inda zata tsoma ranta tun daga yanzu tafara nadamar abinda ta aikata, bawai matakin da minister zai dauka shine tsoronta ba a'a shi dama tasan dole ne ya daureta har igiya tayi rara amma tsoronta kashe dan mutum da tayi,

Tafi awa tana kaiwa da komowa tasan idan minister yaji abinda yafaru ai yau sai kwanan prison tunda ta tabo shalele,yaron da yake jinsa kamar ransa, tana nan tsaye tana ta faman kaiwa da kawowa saiga umma barira da daya daga cikin securities din gidan itama ya kawota hankali atashe,

"Sa'adatu..... Me yasamu Aryan din? Ni natashi daga bacci na duba naduba ban ganshi ba sai da nafito nemansa wai ko yafita karatu sai suke fada min kun taho asibiti, me yasameshi?"

"Umma faduwa yayi yabuge da kujera,wallahi babu abinda ya sameshi bayan wannan...."

Kafin umman tasake magana sai ga Dr Al'amin yafito,

"Insha Allah nan da anjima ko zuwa dare zamu iya barinku ku tafi gida saboda ya farfado dama ba wani abu bane furgici ne da tsoro da ya shigeshi shi ya haifar masa da wannan suman amma insha Allah babu komai zai tashi normal..."

Sai lokacin Hanan taji hankalinta ya dan kwanta ta samu yar nutsuwa da taji cewa bai mutuba yana numfashi,umma kuwa ai arikice take dan kallo daya kadai zaka yimata ka fahimci hakan,tana dai tsaye ne kawai amma hankalinta yagama tashi,

Wurin Aryan din suka shiga suka iskeshi yana bacci amma ga numfashinsa nan yana fita yanda ake bukata, dukkansu jugum suka yi babu wanda yake cewa uffan har tsawon wani lokaci. Koda Aryan din ya tashi jikin umma yaje ya boye yana leken Hanan cike da jin tsoronta, murmushi Hanan tayi masa idanuwanta jajur sanadiyyar kukan da tayi,

Hannu ta mika masa, "Zo mana cutie"

Kin zuwa yayi har suka tafi gida yana nanuke da umma suna zuwa gida suka iske miss calls din Khalil yafi abinda yafi yakira Aryan yakira umma saboda tunda yakira Aryan yaji bai sameshi ba yakira umma yaji ko lafiya ita dinma shirun yaji,

Hanan kam sai sake shiga jikin Aryan take tayi tana son yaron yasaba da ita yadaina tsoronta yasake da ita kamar kowa tunda lalura tashigo ciki dan a mota har suka zo gida umma nabata labarin dama haka yake yi tun yana jariri idan yayi kuka yayi kuka sai kajishi difff yasuma shiyasa uban baya son bacin ransa,

Chocolate ta debo masa irin wadan taga umma na bashi idan zai tafi makaranta, "Cutie zaka sha wannan?" Girgiza mata kai yayi alamar a'a da tace yazo yakarba sai ya makale kafada yahaye kan cinyar umma,

Bata hakura ba taje ta zubo masa tuwon semovita miyar egusi wanda ke cikin fridge a ajiye saida ta dumama masa sannan ta zubo cikin plate ta kawo inda yake zaune yana ta danne danne awayarsa yaran yanzu kamar da ilmin danna waya ake haifarsu saboda yanda yaketa latsa wayar sai ka rantse babba ne,

"Cutie zo inbaka tuwo kaci kaji...."

Kallon umma yayi sannan ya kalleta,make kafada yayi,

"Ni umma ce zata bani"

"A'a ni zan baka yaron kirki dan babansa,zo kaci kaji,akwai dadifa tuwone ko incinye abuna? Kaga zan cinye to..."

Kamar baya son zuwa haka ya sauka daga kan cinyar umma wacce ke cemasa maza yaje yaci,tafiya yake kamar yana taka kwalba ahaka yaje wurinta,murmushi tayi ta dorashi kan cinyar ta tafara bashi abaki yana ci,tashi umma tayi tabarsu tashiga daki tana waya da Khalil wanda ya kara kiranta tana dauka tajishi arikice,

"Umma meya samu Aryan ne? Na kira aka ce mun kunje asibiti..."

"Waye yafada maka Aryan muka kai? Matarka muka raka kanta na ciwo kuma tasamu sauki"

Ajiyar zuciya taji yasaki mai karfi,

"Allah yabata lafiya,yanzu ina Aryan din?"

"Gashi can tare da ita afalo tana bashi abinci"

"Ok to bari na kirashi"

Suna zaune tana ta bashi tuwon yana ci yana game din Disney magic awayarshi amma yafi maida hankali kan game din haka dai take ta lallaba shi tana bashi,kiran Khalil ne yashigo sai jinsa tayi yana fadin,

"Papa...."

"Na'am Aryan...."

Bata jiyo maganar uban ta iya Aryan take ji kawai,
Chapter 21 · 0% Book details