← Book details Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 61

Sashe 47

Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayarta ta jawo ta shiga ta tura masa massage tunda dai ita bazata iya kiranba domin koda ta kirashi bata san abinda zata ce masa ba.

Khalil na zaune tare da mukaddashin mai girma gwamnan jihar kwara sakon Hanan yashigo,

_Uncle ya hanya? Ya aiki? Allah yataimaka ya tsareka ya dawo mana dakai gida lafiya._

Mamaki da al'ajabi sakon Hanan suka bashi,to wannan yarinyar lafiyar ta kuwa? Domin daga jiya zuwa yau gaba daya ta sake canjawa fiye da da,sai kace ba itace ta rufe ido a kwanakin baya ta rinka yimasa ruwan tijara da rashin kunya ba,to yanzu kuma ko me ya canjata? Oho,

Reply ya tura mata kamar yanda yasaba da Thanks kawai sannan yaci gaba da harkokinsa.

Hanan kuwa sai la'asar ta shiga kitchen ta shirya lafiyayyen tuwon semovita dinta miyar ganye, sannan ta sake dama kunun gyada wanda yasha lemon tsami sai kamshi yake,

Bayan tagama Aryan taja suka tafi garden suka haye lilo nan suka shantake har magriba sannan suka shiga cikin gida,anty maamy ce kadai a falon kasa tana daddanna waya,ganin Aryan yasata kiransa ita kuma Hanan ta wuce sama bata bi ta kansu ba,salla tayi bayan ta idar ta yi zamanta a daki tana kallon wani kayataccen labari mai dogon zango na hausa,anan Aryan yazo ya sameta suka cigaba da kallon tare.

Misalin karfe 9 Khalil yashigo gidan,babu wanda yasan ma yadawo,wanka yafara yi,yafito yana shiryawa anty maamy ta kirashi,dauka yayi yana tsane jikinsa da dan karamin towel,

"Hello.... Ka shigo ne?"

"Hy mimimi......"

Murmushi anty maamy tayi ta shafi gashin kanta dake bude tana kwance saman gado,

"Kai baka rabo da tsokana Ibrahim,ka dawo dinne?"

"Ehh.... yanzun nan nashigo nayi wanka"

"Ok....to ya? Zamu je dinne?"

"Uhmm bari na shirya,bani 10 minutes"

"Ok"

Katse wayar yayi yaci gaba da shiryawa,mintuna kadan ya karasa shiryawa bama zaka taba ganewa shi bane sai dai idan kayi masa kyakkyawan sani,

Itama Anty maamy dan sake gyarawa tayi sannan ta fito,da motarshi sukayi amfani suka fita PA yana jansu yayinda su kuma suka kame agidan baya bodyguards dinshi na biye dasu,

Wani Park suka je kayatacce ma'abocin sanyi da sanya nutsuwa,zama sukayi suna fuskantar juna da wani dan table a tsakiyar su,

"Maamy...." Yakira sunanta cikin taushin murya,daga idonta tayi ta kalleshi fuskarta cike da annuri,

"Khalil...."

"Maamy bazan boye miki sirrin dake cikin zuciya ta ba..... Ni dake ina kyautata zaton duk abu iri daya muke ji agame da juna....."

Dan murmushi tayi sannan ta tallafi kumatunta da hannunta guda daya tana kallonsa,

"Amma wai me ya rabaki da uban yayanki? Saboda a iya sanina dake ke macece mai hakuri though dai zaman aure yana da banbanci da kowanne irin zama"

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta dan lumshe idanuwanta ta budesu akansa,

"Khalil mahaifiyar shi ce ta rabamu,bata sona aduk shekarun da muka shafe tare da danta,ni babu abinda ya hadani da Bilal..... Mahaifiyar shi ce bata kaunata kuma ta sanadiyyar ta nabar gidan"

Jijjiga kai yayi sannan yayi murmushi mai dauke hankali,

"To insha Allah yanzu zaki samu uwar mijin da take ji dake take kaunarki kamar ranta...... Maamy shin zaki iya karasa sauran kwanakin da suka rage miki a duniya tare dani?"

Duk da tajima tana zargin jin wad'annan kalaman daga bakinsa amma bata tsammaci zata jisu da gardi da zaki irin haka ba,

Rufe fuskarta tayi da tafukan hannunta cikin farin ciki tana jin iska na kadata kamar tana yawo cikin gajimare,

"Woww........ Khalil..... Wadanne irin dadadan kalamai ne wadannan? Wow....."

Murmushi yayi ya dan kalleta bayan ya rausayar da kanshi gefe daya,

"To ko dai ban samu karbuwa bane?"

Murmushi tayi wanda har fararen hakoranta suka bayyana,

"Hmmmm..... Anya kuwa ban yimaka tsufa ba?"

Harararta yayi hararar dake cike da ma'anoni daban daban,

"Nawa kike da har zaki yimin tsufa,nine ma dai nake tunanin kamar zan iya yimiki tsufa"

Wannan karon dariya tayi sannan ta kalleshi,

"Kai ai har yanzu kamar yaro ne,ban san menene sirrin ba amma baka canjawa"

Murmushi yayi yana wasa da agogon hannunshi,

"Maamy kenan.... Ai kin fini kuruciya,wai dan Allah yaran nan waye zai zaci naki ne? Saifa wanda yasani"

Dariya tayi suka cigaba da koda juna daga bisani ya kalleta,

"Me kike so inbaki a matsayin sadaki...?"

Dan jimm tayi alamar tunani,zuwa can ta kalleshi,

"Ring..."

"Na gold ko na azurfa?"

"Diamond gold"

"Angama ranki yadade,kamar nan da yaushe kika shirya yin auren ne?"

"Ka bari zamuyi wannan maganar daga baya"

Misalin karfe 11 suka koma gida, Hanan tun 10 take jiran dawowarsa taci gayu cikin English wears riga da skirt,kamar wacce akace ta sauka kasa tana saukowa suna shigowa,tsayawa tayi tana kallonsu maamy sanye cikin bakar doguwar riga mai adon stones ja ajiki ta yafa jan mayafi marar nauyi,shi kuma Khalil kananan kaya ne ajikinsa jeans da riga long slif mai dogon hannu da p cap duk bakake,kafarsa sanye da bakin combos,sosai yayi kyau abunka da farin mutum cikin bakin Kaya............................✍�

_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._

*_Ummi Shatu_*👌🏻
8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*42*

***Yi tayi kamar bata gansu ba ta wuce dining area taje ta bude fridge ta dauki kwalin lemon abarba guda daya sannan takoma sama tuni lokacin maamy ta shige dakinta shi kuma Khalil yawuce part dinsa zuciyarsa cike da abubuwa guda biyu wato damuwa da kuma farin ciki,bangare daya na zuciyarshi yana farin ciki zai samu abokiyar rayuwa sannan daya bangaren kuma yana bakin cikin tunawa da mosoyiyarshi Ramlat wacce ta tafi ta barshi cikin shauki da kewarta,

Zama yayi a falonshi ya cire p cap din dake kansa ya ajiye sannan yafara kunce igiyoyin dake jikin takalmin combos din dake kafarshi daidai lokacin Hanan ta turo kofa ta shigo tana mai yimasa sallama,

Daga kansa yayi ya kalleta sannan ya amsa mata sallamar yana zare takalman daga kafarshi,

"Masha Allah...." Ta fada acikin ranta saboda yanda yayi kyau ya sake ja cikin kayan jikinsa,zama tayi dan can nesa dashi cikin sanyin murya mai cikeda tsantsar ladabi gamida biyayya tace,

"Sannu da zuwa uncle...."

"Yawwa" ya fada atakaice domin zuciyarshi ce ke wani irin hautsinawa tana yimasa kuna,yarasa meyasa aduk lokacin da yaso yin maganar da ta shafi aure yake samun kansa cikin wannan mummunan halin,

Bata yi kasa agwiwa ba ta sake kwantar da murya tace,

"Ga abinci can saman table,ko akawo nan...?"

Girgiza mata kai yayi sannan ya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanuwansa,shi kadai yasan abinda yake ji kuma yasan abinda yake damunsa shiyasa kadaici kadai yake bukata daidai wannan lokaci,

Ganin yaki kulata yayi shiru baya ko motsi yasata fahimtar cewa yau fa yan miskilancinne akusa wannan dalilinne yasa ta tashi tafita ta nufi sashenta tana zuwa tayi shirin bacci tayi kwanciyarta,sai sake sake take yi a cikin zuciyarta tana ta tambayar kanta to yaushe Khalil suka fita da maamy? Ina sukaje? Tambayoyin da ta rinka jujjuyawa kenan cikin ranta amma bata da amsarsu shiyasa zuciyarta ta cika da kunci da bacin rai,da damuwa aranta ta samu nasarar yin baccin ranar.

Washe gari kamar jiya yauma tunda ta tashi da asubah bata sake komawa bacci ba kitchen ta shiga bayan ta kammala taje ta shirya Aryan shirin makaranta,suna falon kasa tana bashi breakfast yana ci lokacin ba afi 7:30 ba anty maamy tafito zata hau sama, Hanan tasan bazai wuce wurin Khalil ba shiyasa ta gaggauta karasa bashi breakfast din taja hannunsa zuwa sama tana cewa,

"Zo muje kayiwa Papa sallama sai kazo akaika school"

Khalil na zaune afalo sanye da farar t shirt da bakin trouser wanda yawuce gwiwarsa da kadan da laptop gefenshi yana duba wani sako ta email dinsa maamy ta bude kofa ta shiga,

"Ranka yadade har antashi?"

"Ba dole na ba maamy.... Mai girma deputy president da kansa yaturo min sako ai dole intashi"

"Haka kam.... To yakake?" Ta fada tana kokarin zama gefen kujerar dake kusa dashi,

"Alhamdulillah,kefa?"

"Lafiya lau wallahi Khalil"

"Any problem?" Ya bukata idanuwanshi na kan system dinshi,

"Ehh to.... Dan Allah idan zaka fita zaku yi dropping dina wurin saloon ina so zanyi kitso...."

Daidai lokacin su Hanan suka shigo kuma kunnuwan Hanan sun samu nasarar jin kalaman maamy,sam Hanan bata nuna tajiba suka gama abinda zasuyi taja hannun Aryan suka fita,

Bata sake komawa part din Khalil ba sai bayan da tayi wankanta ta shirya ta saka wata pink and blue colour din atamfa riga da skirt sannan ta nufi wurin Khalil tana rike da kayan breakfast dinshi,baya cikin falon lokacin da ta shiga sai dai ga system dinshi nan da wayoyinshi zube saman kujera,fita tayi tai maza taje ta ci nata breakfast din cikin sauri sannan ta dawo tana shigowa yana fitowa sanye cikin farin yadi tissue,bai san ko yaushe Hanan ta koyi wannan abun arzikin ba ko da yake ai kullum mutum girma yake yi hankali na kara shigarshi,

Kan dining din ya karasa ya zauna tana biye dashi abaya,dumamen tuwon daren jiya tayi masa da kunun gyada sai yan soye soyenta da tayi,ga mamakinta sai taga ya wanke hannu ya zuba dumamen tuwon yana ci,wai dan Allah Khalil wanne irin mutum ne shi mai saukin kai haka? A wannan level din nasa da wanine ai ko kallon tuwo bazai yiba bare har yaci,

Shiru ne ya mamaye wurin sai shi dake ta faman cin dumamen sa,dan ajiyar numfashi tayi sannan tace,

"Uncle zan bika.... Ina so zanje gyaran gashi da k'unshi dan Allah sai ku saukeni......"
Chapter 47 · 0% Book details