Sashe 32
Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiyarshi kuwa duk lokacin da yaje gombe cikin tambayar sa yajikin Hanan take yana dai kulawa da ita ko? Wannan zuwan da yayi last kuwa hajiya harda bashi sassake sassake na gargajiya wai maganin laulayine na masu ciki yana tsayar da amai da sauran su shidai baice komai ba ya karbo yataho dashi da yazo sai yabawa umma saboda su Hanan basa nan suna makaranta ita da Aryan,
"Umma gashi wai maganin Sa'adatu ne idan ta dawo sai kibata....."
"Na menene?" Umma ta tambayeshi,
"Maganin laulayine wai inji hajiya...."
"Au toh toh, Allah yasa adace Allah sarki dama ai yarinyar nan duk ta zuke ta lalace wallahi cikin nan na wahalar da ita... Allah dai yaraba lafiya"
"Amin" ya amsa daga nan yafita,
Bayan su Hanan sun dawo tana falo tana tsara lesson plan dinta umma tazo ta kawo mata maganin da Khalil yakawo karba kawai tayi tace ta gode,kwalla taji ta ciko mata ido sakamakon damuwar dake ranta gashi kullum mujahid cikin turo mata da massage yake amma tayi biris dashi bata kulawa wallahi kallo daya idan kayi mata zaka fahimci tana da damuwa,sau da dama sai taji kamar ta tura masa da text massage ta fada masa sirrin zuciyarta amma sai taga rashin dacewar hakan,idan tayi haka ta disga kanta kuma bata siyawa kanta daraja ba.
Yau dai tana cikin farin ciki saboda zuwan anty salaha yayarta dan rabonta da ita tun bikinta yau watanni shida kenan kuma wata tara da fara service dinta dan saura yan watanni su gama,
Binta da kallo kawai anty salaha keyi saboda yanda taga ta rame tayi kanjal kanjal da ita kamar ba itace cikin wannan daular ba,
"Gaskiya Hanan banji dadin ganinki ba haka, wannan uwar ramar da kikayi duk ta mecece? Baki rasa ciba baki rasa sha ba meyake damunki?"
Dan jimm tayi dan ta rasa me zata cewa anty salaha,ada tana ta kukan bata son minister bata kaunar shi ayanzu kuma kukan tsananin sonshi da kaunar shi take duk da shi nasa hankalin ba akanta yake ba ko ganinsa yanzu bata samun yi,sai tayi sati daya ko fiye da haka bata ganshi ba,da yake bata da abin fada haka taja bakinta tayi shiru tana sauraren fadan da anty salaha keta faman yimata tana cewa yadace dai yanzu ace ta kwantar da hankalinta ta yi zamanta agidan mijinta tunda ita anty salaha bata san abinda ke cikin ranta ba. Kwanan anty salaha biyu sannan ta tafi kuma ko haduwa basuyi da Khalil ba dan baya nan sai kudi da ya aiko PA dashi ya kawowa Hanan dan tayi masa massage cewa anty salaha tazo.
Tun bayan tafiyar anty salaha tasake shiga cikin damuwa sosai kamar wacce ke cikin kurkuku haka take jinta gaba daya yanzu ta rasa abinda zatayi taji dadi,da yake ranar weekend ne kuka kawai ta zauna tanayi adaki ahaka Aryan yaje ya sameta,ganin tana kuka yasashi fita da gudu zuwa part din Khalil dama suna tare tun safe a dakinshi,yana kwance kan gadonshi sanye da kananan kaya yana aiki a system dinshi dalilin da yasa ma bai fita ba kenan sai ganin Aryan yayi yafado yana fada masa wai ga mommy can tana kuka adaki suje yagani,rufe system din yayi yasa slippers dinshi suka fita suka nufi bangarenta........................âœï¸
*_Ummi Shatu_*👌ðŸ»
8/14/20, 10:12 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*29*
***Tana kwance tana sharbar kuka kamar wacce aka daka haka suka shiga suka tarar da ita,wuri Khalil ya samu ya zauna bayan yacewa Aryan yaje wurin umma ya gaidata saboda yau bai sauka downstairs ba kwata kwata,
Dan bude idanuwansa yayi akanta yana kallon yanda take kuka duk tabi ta cika masa kunne domin kukan yana dan fitane da sauti,
"Me yafaru kike kuka....?" Ya tambayeta idanuwanshi na zagaya dakin yana kallonsa komai dai neat ya ganshi babu Kaya awarwargaje,jin muryar sa yasata rage kukanta amma ta kasa magana sai shassheka take yi,
"Bakya jine? Ina tambayar ki me aka yimiki kike kuka? Ko ciwon Marar ne?" Yasake fada cikin fada kadan domin shi ya tsani kuka babu gaira ba dan dalili musamman ma na karamin yaro ko mace mutane biyun nan yana da weakness akansu,
"Babu komai..." Ta bashi amsa tana jan hanci amma acikin zuciyarta ji take inama zata iya da ta ce masa "sonka da kaunar ka ne" Sai dai amma tasan abune da bazata taba iya furta masa ba duk kuwa da cewa yana azabtar da zuciyarta,
"Kukan jin dadi kike yi?" Taji ya fada kuma wannan karon idanuwanshi suna kanta kyarr hakan yasa ta kasa bashi amsa saima sake tukunkune kanta da tayi,
"Duniyar ce tayi miki dadi shine kika zauna kina yiwa mutane kuka?"
Mikewa tsaye yayi har yana shirin fita idonsa ya sauka kan maganinta da ke ajiye saman mirror wanda hajiya ta bada akawo mata, karasawa yayi ya dauka yana dubawa,
"Meye wannan kuma?"
Daga idanuwanta tayi wadanda suke jajur ta kalleshi,
"Maganin laulayi nane..."
Juyawa yayi ya kalleta cike da mamaki har bai san lokacin da yafurta,
"Laulayi?"
"Ehh mana,ba ana bawa masu ciki maganin tsayar da amai da tara yawu ba shine nima aka kawo min nikuma na ajiye kafin infara....."
Sosai maganganun ta suka bashi mamaki har baima san lokacin da yayi murmushi ba unexpected murmushin ya subuce masa "lallai yarinyar nan yar drama ce" yafada acikin ransa amma afili sai ya ajiye maganin ya kalleta,
"Kin kyauta...."
Daga haka yafita daga cikin dakin yana mamakin bakin Hanan wato magana ta fada masa kenan ko yaya?
Itama mamakin kanta da kanta take yi yanda ta iya bude baki ta fada masa haka amma ai gara da ta fada masa tunda ai shine yayiwa su hajiyan karyar wai tana da ciki saboda kar su zargeshi da tauye mata hakki,
Tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka da ruwan dumi sannan tafito ta zira doguwar riga ta koma ta kwanta yau ita haushin kowa take ji shiyasa ma bata fita ba tunda ta tashi adaki yau tayi rayuwarta umma barira ma da taji shiru sai dakin ta biyota tana tambayar ta ko lafiya bata fito ba yau? Cewa tayi babu komai kawai dai bata jin dadin jikinta ne,
"Sai hakuri ai,rainon ciki haka yake sai anhada da hakuri idan ba haifeshi akayi ba lafiya bata fiya samuwa dari bisa dari ba......"
Shiru tayi tana sauraren umma kuma tana jin tausayin su acikin ranta saboda su duk sun zaci cikinne da ita dagaske basu san gadar zare ce Khalil ya shirya musu ba. Haka taci gaba da zaman takura wanda ba kowa ne ya takurata ba itace kawai ke takura kanta.
***
Mujahid
Duk da cewa idan yayiwa Hanan text massage yanzu bata kulashi hakan baisa ya daina ba, sannan baya jin zai karbi bukatar sumayya har ya amince yafara soyayya da ita,
Rashin kulashin da Hanan keyi shi yafi komai daga masa hankali ahalin yanzu duk da dai dama bawai kalaman soyayya yake tura mata ba gashi ko ta WhatsApp bata kulashi daga baya ma sai yaga kamar tayi blocking dinshi nan abu ya sake hadar masa goma da ashirin,
Sumayya kuwa ganin tana ta faman shassharreshi tana dauke masa kai ba kamar yadda ta saba ba ada hakan ko ajikinsa sai dai wani lokacin sai yakanji babu dadi irin yanda yarinyar ko kallo bai isheta ba gaisuwa ma sai ta gadama take gaisheshi,
Yau da yake weekend ne yana kwance falon mami da remote hannunshi yana kallon kwallon kafa ta bude kofa ta shigo bata ko kalleshi ba tawuce sai yaji hakan ya kona masa rai fiye da tunaninsa,har shi zata zo ta wuce bata gaisar ba?
Bai gama hucewa daga wannan fushin ba yadawo daga masallaci sallar azahar yazo ya tarar dasu ita da mami tana cemata taje dakinshi ta dauko mata bedsheet dinshi zata hada cikin kayan wanki budar bakinta sai cewa tayi,
"Mami ni bana shiga dakinsa yanzu sai dai intura mai aiki ta dauko miki...."
"Yaushe kika daina shiga dakin yayan naki sumayya? Dan uwanki ne fa"
Kafin tasake magana ya sako kai yashigo dama yana tsaye yana ji, yarinyar nan bata taba bashi haushi irin na yau ba,
"Ke je ki zubo min abinci idan kin gadama...." Yafada yana kishingida saman kujera,kamar bata so haka ta tashi ta wuce kitchen tana ta turo baki alamar dole aka yimata,kwafa yayi da karfi ya kalli mami yace,
"Wallahi na kusa balla yarinyar nan tunda bata da kunya,wai ni ban isa ta gaida ni ba? Dazu fa ina zaune tazo ta wuce kamar bata ganni ba...."
Murmushi mami tayi tace, "To me yakawo maganar ballawa dan kawai bata gaida ka ba.."
"Ai dama mami duk kece kike goyon bayanta wallahi"
Daidai lokacin sumayya ta fito rike da plate din Brown rice with prawn, mango and avocado salad,ajiye masa tayi agabansa tajuya zata tafi tana sake turo baki,
"Ke zo nan...dauko min juice adakina cikin fridge...."
Tana sake turo baki tajuya ta wuce,dariya mami tayi tana fadin "To nima sai ki taho min da nawa aiken da nayi miki dazu kika turje wai ke bakya shiga sai kace dakin surukinki".
***
Kwanci tashi yanzu saura wata daya su Hanan su kammala service dinsu,rabon da ta sa Khalil a idonta kuwa anfi sati domin shi baya ma nan yaje k'asar Cameroon kwananshi shida acan sai jiya da daddare yadawo,
Cikin sanyin jiki da damuwa take shiryawa tana ta sakin dan karamin tsaki ada bata da burin da yawuce taganta sanye da kayan NYSC tana yin service amma yanzu da tafiya tayi tafiya bata da babban buri wanda yawuce taga tacire wadannan kayan ta karbi certificate dinta a hannu,
"Mtswwww wallahi na tsani lectures dinnan na tsiya haka kawai dan kar abar mutum yahuta...... Kaki zuwa kuma suce zasu baka query"