← Book details Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 61

Sashe 28

Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Hajiya wanne bangaren nawa kuma bayan daki dayane aciki,muje muyi zaman takura haka kawai...."

"Idanma babu dakin ba matarka bace? Ko zaman gaban takura zakuyi kuyi mana ai canne yafi dacewa da ita,kuma kasan ai daki dayanne amma ka daukosu kuka taho"

"Gaskiya hajiya daki daya yayi mana kadan"

"To ba sai kasake gina muku waniba tunda kana da halin yi amma dai babu tsari ace kana can matarka tana nan,yanzu idan kana bukatar tayi maka wani abu sai kazo kana tasota daga nan tana tafiya can?"

"Hajiya ni kwana nawa ma zanyi agarinne? Dududu kwana hudu fa zanyi ko biyar mutafi umarah nida Aryan...."

"Kaida Aryan? Ita kuma matar taka fa? Wa zaka barwa ita?"

Shiru yayi yana tunanin abinda yadace yafada wanda hajiya ba zata yimasa fada ba,ruwa ya dan kurba sannan yace,

"Ai hajiya bana visa dince tayi wahala kuma da har ita naso hadawa amma abun ya faskara mukuma ai kinga permanent Visa garemu shiyasa..."

"Ai shikenan amma gaskiya banji dadin tafiya kubarta ita kuma ananba da zakuyi gaskiya...."

"Hajiya kiyi mana addu'ar dai Allah yasa hakanne yafi zama alkhairi"

"To amin, Allah yadawo daku lafiya, Allah yatsareka ya kareka ya tsare maka dukiyarka da zuri'arka, Allah ya rabaka da mugun ji da mugun gani ya shiga lamarinka akoda yaushe...."

"Amin hajiya..."

Saida yakai wurin karfe 2 na dare shida hajiya sannan yatashi yafita ya nufi bangarensa aransa yana tunanin ai kamar fa tunda yazo baiga Zaid ba anya kuwa yana nan? Kai duk yanda akayi zaid baya garin nan dan kuwa da yana nan da yaganshi. Duk jikinsa a gajiye haka ya lallaba ya daure yayi wanka yasaka kayan bacci yahaye gado yana kallon agogo,karfe 3 saura na dare,yanzu hajiya da take cewa ya hada daki da yarinyar can ai da takurashi za ayi haka kawai abanza shi harma mantawa yake yi da wai ita matarsa ce kawai abinda yasani ya kawowa Aryan friend wanda zata rinka debe masa kewa.

Washe gari ya dan samu zarafin komawa baccin safe, Aryan kuwa tunda yatashi Hanan ta shiryashi cikin kananan kaya bakar t shirt ta polo da blue din jeans tasa masa combos shima baki bata sake ganinsa ba dan wurin hajiya yaje ta can ya gudu wurin babansa dan shine ma ya tashi Khalil din, rungumeshi yayi yana shafa sumar kanshi,

"Waye ya yi maka wanka?"

"Momy ce.."

"Uhmm dan gatan mommy..."

"Mommy tana sona..."

Murmushi Khalil yayi ya tashi zaune yana daukar wayarshi domin kira yashigo,

"Hajiya ina kwana...... lafiya lau....gashi muna tare dashi ai......ehhhh....kokon dai hajiya.....to shikenan sai na shigo"

Daga haka ya katse wayar yabawa Aryan shikuma yashiga bathroom domin yin wanka,har yafito ya shirya Aryan na kwance kan gadon yana ta faman matse matse awayar kamar tashi cemasa yayi kar dai ya yarda yayi masa deleting din wani abu garin wannan matse matsen nasa,shiryawa Khalil din yayi cikin wata farar shadda yasha turare,ba dan hajiya tace yajira akawo masa breakfast ba da fita zaiyi.

Hanan tunda ta gama shiryawa tayi zamanta adaki saida hajiya ta turo mufida kiranta sannan tafita,wata dark purple din atamfa ce ajikinta doguwar riga tasha turare mai sanyin kamshi,gaida hajiya tayi sannan hajiya ta nuna mata breakfast din Khalil wai idan tagama karyawa shima taje ta kai masa mufida ta rakata ko zarah,tea ta hada ta sha ta danci awarar da aka soya da kwai sannan ta tashi suka fita ita da zarah dauke da kayan breakfast din Khalil,

Part din nashi dan karami ne bawani babba ba saiko kayan alatu da yasha,suna zaune falo shida Aryan wanda keta waya dasu Nawwar awayar Khalil daga jin Khalid ya kirashi suna magana shikenan yakafa rigimar sai anbashi ana bashi kuma suma su Nawwar din suka karbe kan wayar tun dazu suketa hirar da taki karewa domin sai labari suke ta bawa juna,durkusawa zarah tayi ta gaidashi sannan ta ajiye kayan dake hannunta tafita,itama Hanan din gaisheshi tayi suka gaisa kamar yanda aka saba ina kwana lafiya shikenan,ta mike zata fita taji yace, "Zo nan"

Dawowa tayi ta zauna amma baice da ita komai ba saima kayan breakfast dinshi da yajawo yabude ya tsiyayi koko a cup sannan ya bude flask din soyayyiyar awara da kwai ya diba a plate ya zuba vegetables sos akai yasa spoon yafara ci,duk sai taji ta takura domin basu taba zama haka su biyu ba awuri duk da Aryan yana wurin,

Ganin wayar Aryan ba mai karewa bace yasa Khalil kwace wayar ya kashe yace maza ya zauna suci abinci shi baya son cin abinci sai anyi masa dabara,yanzun ma saida dabarar shima yabashi yaci. Suna zaune shiru amma jifa jifa Aryan na yin surutunshi ahaka akayi knocking a jikin kofa, zaid ne amma ganinsu duka sai yakoma Khalil nata kiransa amma bai dawoba,ita dai duk da tana jin dadin zaman wurin amma ta kosa ta tafi domin zuciyarta kamar zata faso kirjinta tafito dan tsananin bugun da takeyi,saida suka gama sannan yace sutafi cikin gida ita da Aryan,shikuma yafita tun daga nan kuma ganinsa yayi mata wahala dan bata ganinsa sai kowacce safiya da zarar yafita kuma shikenan dan lokacin da yake shigowa da daddare tuni sun kwanta,ita kanta hajiya fadan da take yimasa kenan wai bata ga yana jan matarsa ajiki yana kiranta suna hira ba shi kuma sai cewa yayi wai ai duk sanda taje wurinshi da safe kai masa abinci suna tattaunawa. Kwanansu hudu da zuwa yace ashiryawa Aryan kayansa saboda zasu iya tafiya a kowanne lokaci, lokacin ana saka ran ganin watan Ramadan nan da kwanaki biyu zuwa uku,daren asubar da zasu tashi tana daki kwance har tayi shirin bacci hajiya ta aiko kiranta,koda taje hajiya cewa tayi wai ta je wurin Khalil ta kwana acan suyi sallama, innalillahi ita dai gashi ba damar tayi musu da hajiya gashi bata jin zata iya zuwa gareshi a wannan lokacin,jiki a mace ta tashi takoma dakin da ta sauka tafi minti goma tana tsaye tana kallon Aryan dake kwance yana bacci sannan ta dauki hijabi har kasa tasa ta fita rike da wayarta a hannu,gidan tamkar rana dan tsabar haske baka jin motsin kowa sai karar injin bada wutar lantarki da ke tashi,tana sake kusantar sashen nasa faduwar gabanta na karuwa jikinta na rawa ahaka taje,ta jima tsaye a bakin kofar falonshi tarasa ta yadda zata shiga ciki,dakyar tayi ta maza ta bude kofar ta sa kai tana jin numfashinta yana tsinkewa kamar zai fice gaba daya.....................✍️

*_Ummi Shatu_*👌🏻
8/14/20, 10:11 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*26*

***Kasa daga kafarta tayi daga nan inda take tsaye bayan tashiga cikin falon nasa wanda kamshinsa ke kai komo acikinsa,

Wuri ta samu ta zauna saman kujera tana kallon kowacce kusurwa da lungu dake cikin falon wanda yake dan madaidaici sai dai kuma antsarashi yadda yadace dan yayi mata kyau kamar irin dan bangaren nan na ango da amarya auren saurayi da budurwa, ango da yar amaryar sa ya ishesu rayuwa kafin su tara 'yaya,komai na ciki milk ne and coffee colour gashi tsaf tsaf babu datti babu kura yayi kyau gwanin ban sha'awa. Idonta ne yakai kan wayar Khalil dake kan wani center table na glass dake can gefe daya take ta sake jin faduwar gabanta ta karu da kaso tamanin cikin dari na wadda takeji dazu,

Fitowarsa kenan daga wanka yasaka farar jersey mai ratsin blue agefe da gefenta sai wandon rigar shima fari amma dogone dan har ya rufe gwiwarshi,falo yafita domin dauko daya daga cikin wayarshi da ya ajiye acan,yana fitowa yaganta zaune ta tukunkune cikin hijabi ba dan yasan da zuwanta ba da babu abinda zai hana ya tsorata to dan dai hajiya ta sanar dashi ne dazun nan da yashigo tagama kora masa jawabin wai yakamata matarsa taje suyi sallama kuma yaji ko tana da wata damuwa,

"Kowacce irin sallama hajiya take son muyi oho..."

Yafada acikin ransa yana kokarin daukar wayarshi,cikin sanyin murya yaji tana gaisheshi nan ya amsa kamar koda yaushe cikin rashin son doguwar magana,ita dai tun kallon farko da tayi masa bata sake kallonshi ba domin yau yasake yimata kwarjini fiye da sauran ranakun baya gashi kayan jikinsa sun dan kamashi. Wuri shima yasamu ya zauna afalon yadora kafa daya akan daya yana duba tulin sakonnin dake cikin wayar wadanda aka turo masa kuma mafi yawa ba sanin wadanda suka turo yayi ba,

Hanan gyangyadi tafara domin tuni 12 ta dan gota ita kuma ba saba dogon zama tayiba karkarinta takai 11 wannan dinma sai da dalili amma wani lokacin 10 tayi baccinta saboda fitar sassafe. Lura yayi da gyangyadin da take yi dan haka yayi mata magana cikin muryar sa mai cike da sanyi,taushi da kuma gardi,

"Shiga ciki ki kwanta..." Taji yafada amma bawai dan yasoba domin harga Allah shifa takurashi akayi da aka turo masa yarinyar nan,yanzu dole sai taje ta hau masa kan gadonsa shikuma abarshi yayi kwanan takura a falo,

Kasancewar itama bawai awani sake take dashi ba yasata girgiza kanta tace,"A'a nanma ya isa"
Chapter 28 · 0% Book details