← Book details Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 61

Sashe 37

Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manena labarai da yan jarida har gida suka biyoshi suka ji ta bakinsa dangane da batan Aryan da kuma yanda akayi aka ganshi,bai fito fili yasanar dasu yanda aka ganshin ba kawai dai ya basu tabbaccin cewa masu yin garkuwa da mutane ne suka saceshi kuma yana kan yin bincike dan gano ko su wanene,bayan tafiyar yan jarida ya kira emah yasake tsareshi da tambayoyi domin Aryan yace wani ne mai kama da Emah din yazo ya kama hannunshi yakaishi mota to shikuma wannan din yake son gano ko waye saboda yanzu duniya ba abar yarda bace kana tare da mutum sai a iya hada baki dashi a cutar dakai, sai da yagama yiwa emah tambayoyi masu kada masa yan hanji sannan ya sallame shi yatafi yana fita ya danko kunnen Aryan guda daya har cikin bedroom dinshi belt ya dauka yana tambayar shi,

"Nan gaba zaka kara bin wanda baka saniba? Zaka kara bin mutumin da baka san ko waye ba?"

Girgiza kai Aryan yayi yana fadin,

"Allah Daddy bazan sake ba...."

Zaneshi yayi sannan ya sakeshi, cikin fad'a yace,

"Get out of here wawa kawai...."

Fita Aryan yayi yana kuka yatafi wurin Hanan, bata taba ganinsa yana kuka haka ba sai yau tunda tazo gidan,daukarsa tayi tafara lallashinsa tana tambayar meya sakashi kuka,

"Uncle ne ya....zaneni...."

Gwalalo ido Hanan tayi dama Khalil yana dukansa? Tohh ashe dai duk soyayyar yana daukar mataki, rarrashinsa taci gaba dayi har yayi shiru bacci ya d'aukeshi. Tana can wurin umma suna hira Aryan yasauko yazo ya hau jikinta duk jikinsa zafi alamar zazzabi, daukar shi tayi ta nufi sashen uban dashi,samunshi tayi zaune da laptop dinshi kan glass table agabanshi yana aiki, wannan mutum dai ko shine agogo sarkin aiki sai haka dan koda yaushe cikin aiki yake,

Daga ido yayi ya kallesu itada Aryan wanda ya kwantar da kai a kafadarta,

"Ka taba jikin Aryan kaji kamar zazzabi yake yi....."

Mika hannu yayi ya karbeshi,

"Na zaneshi ne shiyasa watakila zaiyi zazzabin...."

Shiru tayi bata ce komai ba ta tsaya tana kallon su yana ta tattaba jikin Aryan yana fadin,

"Am sorry lovely son, zazzabi ne ko? Bari inkira Dr yazo yabaka magani kaci abinci?"

"Baici abincin ba,yanzun nan yatashi" Hanan ta bashi amsa dan tasan Aryan cewa zaiyi yaci saboda baya son cin abinci,

"Ok je ki kawo masa"

Fita tayi shikuma yakira Dr Al'amin ita dai tana ta mamakin Khalil saboda a tsananin son da taga yana yiwa Aryan to bata taba tsammanin Wai zai iya saka hannu ya dakeshi ba. Zazzabin kwana biyu Aryan yayi sannan yakoma school domin yawarke garau haka shima uban ya warware domin har ya soma fita office.

A ranar da yamma mummunan labari ya sameta wai wata matashiya takai Khalil kara babbar kotu akan yunkurin yimata fyade adaren ranar larabar da ta gabata..........................✍️

*_Ummi Shatu_*👌🏻
8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: *33*

***Tsoro,mamaki da kuma damuwa sune suka taru suka rufe Hanan lokaci guda,jin wai wata matashiya takai Khalil kara kuma da laifin yunkurin yimata fyade kai jama'a wannan abu da me yayi kama,

Rasa abinda zatayi tayi kawai sai ta nemi wuri ta zauna nan cikin falonta tayi tagumi,to shin dagaske ne kodai sharrine kawai wannan matar take kokarin yimasa dan dukda cewa ita bata wani zauna tare dashi na tsawon lokaci ba amma sai taga kamar baida lokacin aikata hakan,shiru dai tayi da bakinta bata ce komai ba sannan kuma babu wanda ta fadawa ahaka Aryan yashigo ya sameta yadawo daga makarantar yamma wato islamiyya wadda shi agida ake yimasa tashi,

Kafin kace me tuni labari ya karade kafafan yada labarai wai Khalil yayi yunkurin yiwa yesmin fyade agidanta dake can zubah, nanfa wad'anda basu sanshi ba suka fara Allah wadai dashi wadanda suka sanshi kuma suka fara karyatawa suna fadin ai wannan shaci fadine kawai irin na wasu matan marassa tsoron Allah amma Khalil bazai aikata hakaba dan haka wannan labarin baida maraba da kanzon kurege.

Khalil Kam shi bama ya k'asar dan haka baima san abinda yake faruwa ba yana can Seoul babban birnin k'asar Korea, Khalid ne yaci karo da posting din a Instagram shine yayi gaggawar Kiran Khalil yana tambayar sa, murmushin takaici Khalil yayi zuciyarsa na tafarfasa saboda bacin rai,

"Wallahi wannan karon sai na nemi hakkina awurin yarinyar nan...... Text massage fa tayi min Khalid cewa inje inkarbo Aryan wai yana wurinta kuma kar natafi da securities saboda wani dalilinta marar amfani kuma na yarda natafi ahakan ni daya.... Taje tayita kaiwa k'arar dan Allah karta fasa amma nima yanzu zata ga the other side of me...."

Kitt ya kashe wayarsa cikeda bacin rai saboda yasan zubar masa da mutunci kawai yesmin ke sonyi, so take ta goga masa bakin fenti abanza gashi yan media sam basu iya daukar abuba sai ayita yamididi dakai ana nuna ka kamar watan ramadan, tamkar Khalid ya bude kofar kiran Khalil nanfa yan uwa da abokan arziki suke ta go slow din kiransa daga kiran wannan yashigo sai na wannan,

Bai dauki kiran kowa ba sai na anty saudat babbar yayarshi wacce yake bi,yana dagawa yaji ta rufeshi da fada tana cewa abinda yayi ya kyauta kenan? Yanzu yadace da girmansa da komai arinka buga labarinsa a jaridu da mujallun k'asar nan cewar yayi yunkurin ketawa mace hadddinta? Fada anty saudat take yi ta inda tashiga ba ta nan take fita ba dayake itama mafadaciya ce akwai fada babu laifi, kwata kwata taki tabarshi yayi magana sai zuba masa ruwan masifa take dama shima to afusace yake dan haka ya katse kiran dan ta cika masa kunne da fadanta,

Sake kira tayi tana jin ya daga tafara fadin,

"Ibrahim ni kake kashewa waya? Ni ka katse mawa waya saboda na kiraka ina fada maka gaskiya?"

"To danme zaki kirani ki sakani agaba kina wani yimin fada kamar karamin yaro? Ba zaki tambayeni kiji abinda yafaru ba...."

"Anki atambayeka din..."

"To kar Allah yasa ki tambaya din,duk abinda kikaji akaina ance hakane ina shikenan? Ko da...."

"Kaje kayi fin haka ma idan kaso sunan wa zaka bata? Ba sunanka bane...."

Yana jiyowa daga kusa da ita ana yimata magana kan cewa bai kamata ba wannan abun da sukeyi kamar wasu kananan yara yasan bazai wuce mijinta ba dan kamar muryarsa yaji yana cemata tayi shiru,"Ni baka jin abinda yake fada min? Ba kanina bane shi? Akan me zai rinka gaya min kananan maganganu?"

Shi dai katse wayar yayi yana kokarin ajiye ta kiran lawyer dinshi yashigo wato Barrister muhsin nan ya dauka ya zayyanewa barrister duk abunda yafaru sannan yakara da cewa,

"Barrister nima ashigar min da Kara a nema min hakkina na sace min yaro da tayi har tsawon kwana biyar wanda sanadiyyar hakan har saida ta kaini ga kwanciya a gadon asibiti, sannan a nema min hakkina na bata min suna da tayi..."

"Babu matsala ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai daidaita kuma sai tayi nadamar abunda ta aikata,ai bata san me ake kira da shari'a ba shiyasa har tayi saurin kai k'ara...". Barrister muhsin yabashi tabbaci sallama suka yi suna gama waya da barrister ya kashe wayar gaba daya bayan ya sakata a flight mood. Kwana biyu da faruwar lamarin ya dawo Nigeria yaci gaba da gudanar da harkokinsa, Hanan na son tambayar sa dangane da rade radin da ake tayi akansa amma bata ga fuskar yin hakan ba domin Khalil wani kwarjini gareshi na musamman idan har ya tsare gida to sai kaji tsoron tunkararsa ko kai waye dan su kansu yan jarida suna ta son suji ta bakinsa amma abun ya gagara.

Dawowarsa da kwana biyu yatafi gombe saboda anshirya family meeting akansa amma iya manyanne babu yara, Abban su Khalid tsareshi yayi da tambayoyi to amma da yake mutum idan da gaskiyar sa baya tsoron amsa kowacce irin tambaya haka ya amsa musu dukkan abunda suka tambayeshi daga karshe tattaunawar ta tashi bayan kowa ya yarda dashi. Daga wurin family meeting din nasu gidansu yawuce duk da sun hadu da su hajiya acan sai da suka sake zama da hajiya suka tattauna sannan yatafi ya koma abuja,

Haka dai labari yaci gaba da yaduwa har aka fara zaman kotu shi dai baya samun halattar zaman kotun sai lauyansa shine ke ruwa da tsaki domin acewar lauya shi Khalil ayyukansa bazasu bari ya samu damar zuwa ya zauna a kotu ba.

Ita kam Hanan zaman gida da rashin sanin takamaimai abinyi sune suka taru suka sakata agaba,wata zuciyar sai tace mata kodai ta koma masters degree dinta ne koda kuwa online ne,gashi yanzu inbanda kwadayin zuwa gida babu abinda take yi tana ta son taje gidansu dan wani lokacin har mafarki take yi saboda tsabar yanda ta saka abun aranta haba aima tana ganin kamar tayi kokari wata tara fa yanzu rabonta da gida tasan da akusa da gida tayi aure ai da tuni taje gida yafi akirga,tana son tambayar Khalil amma tana jin tsoro dan tunda abun nan yafaru yasake zama wani marar son magana,daurewa dai tayi ta rufe ido tayi masa text wai tana son taje taga yan gida,reply yadawo mata dashi lokacin yana wurin wani taro acan garin yola shida mataimakin shugaban k'asa,

_Me akeyi agidan?_

Shine tambayar da taga yayi mata, murmushi tayi aranta tace "wai shi dai mutumin nan baya rabo da tambaya ne? To kawai sha'awar zuwa gidan nakeyi" hakan kuwa ta tura masa amma sai taga yadawo da reply yace wai ba yanzu ba,ranar Hanan harda kukanta au dama haka mata keji idan suka bukaci futa aka hanasu? Wallahi sai yanzu take nadamar zaman gida da tayi ta rinka kunshe kanta agida bata fita ko ina daga makaranta sai gidan anty salaha dama ita ba kawaye gareta ba sai abokan mutunci balle ta rinka yawon bin gidan kawayen,ranar har yajin cin abinci tayi sai uban kuka da tasha dan har agaban Aryan tayi.

Bayan sallar ishah Khalil yadawo gidan, Aryan na dakinsa yana game din zumah a laptop dinshi khalil yafito daga wanka sanye da rigar wanka ajikinsa,

"Papa..... Mommy yau tayi kuka.... Kuma taki taci abinci..... Bata da lafiya"

Dakatawa yayi da goge kanshi da karamin towel da yake yi ya kalli Aryan,

"Jeka ka kirawo min ita...."
Chapter 37 · 0% Book details