← Book details Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 61

Sashe 53

Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin abinda yace yasata fasa ajiye cup din taci gaba da sha tana jin zuciyarta tana tashi amai yana taso mata, yunkurin amai ne ya addabeta har bata san lokacin da ta rikeshi ba saboda babu tazara sosai tsakaninsu,tare ta wankesu da aman wanda yaki karewa domin gaba daya tea din da ta sha sai da ta amayar dashi, lokacin da tagama aman jikinta duk ya saki babu karfi ko kadan,lagwaff ta sakeshi ta kwanta tana jin wani sabon zazzabi na shigarta,mikewa yayi yafita, bedroom dinshi yaje ya wanke jikinsa ya sauya kaya sannan yadawo tana nan kwance kamar yadda yatafi yabarta,

Baida zabin da yawuce ya gyara ta ya tsaftace wurin da ta bata, tunanin ta inda yadace yafara yayi nan yafara da kan gadon sannan ya dagata itama,tana son tayi masa gardama amma kuma tana tsoro domin yau akwai wani kwarjini na musamman akan fuskarshi,yar doguwar rigar jikinta ya cire ya goggoge mata jikinta sannan ya bude drawer dinta yaciro mata wata,tun dazu ya lura da ita sai faman kakkare kirjinta take yi tanata bobboyewa ko ta manta da yataba ganinta ahakane oho? Amma wanne dare ne wanda jemage bai ganiba ya furta hakan acikin ransa,yana gama saka mata rigar ta tukunkune taja bargo ta rufe jikinta tana rawar dari,

Sai da yagama tsaftace duk wurin da ta bata da aman sannan yafita zuwa sashensa, kwanciya yayi amma ba bacci yake ba,bayan kamar mintuna 30 yasake tashi yafita yaje ya dubata,bacci ya samu tanayi dan haka yakoma sashensa shima ya kwanta zuciyarshi cunkushe da tunani iri iri................................✍�

_Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._

*_Ummi Shatu_*👌🏻
8/14/20, 10:15 AM - Ummi Tandama: 47

***Haka yaci gaba da jinyarta amma koda yaushe fuskarsa ahade babu fara'a alhalin ita kuma bata san abinda tayi masa ba shikuma yaki yasanar da ita sai faman fushi yake yi,

Duk abinda tace tana so yana mutukar yin duk iya iyawarshi wurin nemo mata amma fa tsakaninta dashi babu sakin fuska dan komai yana yine kamar irin anyi masa dole dinnan,

Kwananta biyu akwance ta dan fara samun sauki,itama gaba daya acike take dashi sakamakon auren da taji zai yi kuma wai anty maamy zai aura,tana ta son ta kira abokan shawararta su dan tattauna su bata shawarar da ta dace amma babu waya a hannunta kuma tsoron tambayar Khalil take yi,rasa yanda zatayi tayi daga karshe sai umma barira ta samu da maganar lokacin ita kadaice adakinta tana sauraren fm radio shi kuma Aryan yatafi makaranta,tashi zaune umma tayi daga kishingiden da take sannan cikin alamun tausayawa da tausasa harshe tace,

"Kiyi hakuri Sa'adatu,tabbas kishiya nada ciwo kuma tana da zafi shiyasa ba kowacce mace ce take iya cin rabarta ba, da yawa mata a kishiya jarrabawar su take sai dai amma basu fiya cin wannan jarrabawar ba saboda gajen hakuri da kuma hawa dokin zuciya..... Idan akayi hakuri kuma aka kai zuciya nesa wallahi ba kishiya ba ita kanta rayuwar gaba daya mai wucewa ce,kina zaune mijin zai dawo ya sameki kuma har ma ki zama alkali atsakaninsu amma fa sai kin kai zuciyarki nesa, mutukar baki nutsu kin kama mutuncin kanki ba to a irin wannan gabar ne miji yake rainaki,danginsa suke rainaki,kishiya take rainaki,ke hatta sauran abokan arziki rainaki sukeyi mutukar baki ja girmanki kin yiwa fushinki da zuciyarki linzami ba,shi wannan zafin kishin da kan tasowa mata a lokaci guda shine ke sanadiyyar sasu aikata abinda zasu zo suna nadama da dana sani tsawon shekaru dan da yawan mata a wannan lokacin suke barin damarsu,miji yayita rarrashinsu amma suna fandarewa har shima yagaji yayi watsi dasu daga karshe idan ba ayi sa'a ba shikenan ansamu hanyar lalacewar zamantakewar da aka gina shekara da shekaru....."

Sake gyara zama umma barira tayi sannan ta fuskanci Hanan,

"Shawarar da ni dai zan baki 'yarnan shine..... Kishiya bata cinye uban kowa ba kuma kema bafa zata cinyeki ba,kiyi hakuri kici gaba da kyautatawa mijinki,nima na zauna da ita nasan zafinta kuma nasan ciwonta amma da nayi hakuri wallahi komai sai da ya zamto tarihi,to kema haka taki zata zama tarihi kamar ba ayiba......."

Jijjiga Kai Hanan tayi alamar gamsuwa da bayanan umman shiyasa neman shawarar manya amafi yawan lokuta take da dadi domin ko basu magance maka matsalarka ba zasuyi maka bayanin da kai kanka sai kaji dadi zuciyarka tayi sanyi,

"Nagode umma kuma insha Allah zanyi yanda kika ce......"

Cigaba da bata shawarwari umma tayi har tsawon wani lokaci kafin ta tashi ta shiga kitchen domin dorawa Khalil abinci ada tayi fushi tace bazata sake yimasa girki ba sai dai wacce zai auro din idan tazo ita taci gaba dayi masa amma kalaman da umma tayi amfani dasu wurin bata shawarwari sune suka sanyaya mata zuciya har taga rashin dacewar hakan ta sauya shawara,

Tasan daga shi har dan gaban goshin nasa zasuyi farin ciki da abunda zata girka musu yau shiyasa ta bada himma ta zage wurin ganin ta nuna kwarewarta a wannan fannin,

Zuwa yamma ta kammala komai nata suna tare da Aryan a falonta suna yin game,kokari takeyi taga tayi yaki da duk wani bacin rai tare da damuwa dake kokarin yiwa zuciyarta tsinke har yasamu wurin zama wannan dalilinne yasa take ta biyewa Aryan suka taru suka zama mashirmata.

Tun kafin Khalil yadawo ta shirya masa table bayan ta gyare masa sashensa tsaf yasha turaren wuta dan sudan mai bala'in kamshi,bayan sallar ishah yasamu zarafin dawowa kasancewar yau yaje garin zamfara ya halacci wani taro,

Kamar yadda yasaba wanka yafara yi yashirya cikin kananan kaya sannan yafito falo hancinsa na shakar kamshin turaren da Hanan ta saka masa sannan wani abun sha'awar shine yanda ta kawata table din sannan ta armasa shi da warmers masu kyau kanana,zama yayi yana budewa nan yaga funkaso ne yatashi sosai sannan yayi kyau sai miyar agushi tasha alayyahu itama tayi kyau sosai tun a ido gashi ta wadatu da naman kaji,sai lafiyayyen zobon da ta hada wanda yaji flavors daban daban ya wadatu da kankana da cucumber aciki,zuba funkason yayi yafara ci wanda yayi daidai da shigowar Aryan cikin falon, cinyarshi ya haye shima yasaka hannu yafara cin funkason wanda tunda aka sauke yake ci amma yakasa koshi gashi kuma baiyi wani auki sosai ba dan hatta umma ma saida ta bukaci kari akan guda hudun da Hanan ta zuba mata shi kansa Khalil din kwaya uku yasamu,

"Abba na ba kaci naka bane? Wannan fa nawane nima zanci....."

Makale kafada Aryan yayi yaci gaba da ci yana surutu,

"Nima zan kara ci uncle......."

Tare suka cinye sannan Aryan yafice,shikuma zama yayi nan falonshi aranshi yana tunanin to ko menene kuma yafaru da Abba Idris ke nemanshi? Dan dazu yayi masa text massage akan yaje gombe yana son ganinshi gobe yasan dai baya wuce maganar aurensu shida maamy,wayarshi yatashi yashiga bedroom dinshi yadauko yafito yasoma kiran layin maamy amma number busy,ajiye wayar yayi saboda yasan idan tagama zata kirashi amma kuma ga mamakinsa har ya kwanta bacci bata kirashi dinba shima kuma bai sake kiranta ba. Washe gari asubanci yayi yafita ta can office yawuce gombe domin amsa kiran Abba Idris wanda yake matsayin uba agareshi,

Bayani cikin nutsuwa abba Idris yayi masa akan maganar aurenshi da maamy cewa tsohon mijin maamyn wai yadawo yanata bibiya sai takoma d'akinta kuma dama tun farko matsalar ba daga gareshi bane daga mahaifiyar shi ne dan haka shi Khalil yayi hakuri yabarwa Abban jawad domin mammy takoma gidan tsohon mijinta,dama Khalil yasan za arina kuma za ayi haka dan tunda yaga take taken tsohon mijin mammy yasan da wata akasa,duk da baiji dadin abinda yaji ba amma godiya yayiwa Abba kuma yanuna baiji zafi ko ciwon abinda yafaru ba sai dai har acikin ransa baiji dadin boye masan da mammy tayiba shi baya son boye boye da nuku nuku cikin sha'aninsa koda yaushe yafi son mutum yazama open amma babu komai dan koba alaka ta so maamy ai yar uwarsa ce ta jini, sallama yayiwa abba yatafi batare da yashiga cikin gidanba.

Wannan al'amari shine sanadin rushewar maganar aurensa da maamy wanda ita Hanan bata saniba duk atunaninta maganar aure har yanzu tana nan daram shiyasa taci gaba da kyautata masa da yimasa duk wani abu wanda zai faranta ransa,ranar da aka daura auren mammy sai ranar Hanan tasan anfasa auren da Khalil dan abakin umma barira taji bayan umman sun gama waya da hajiyarsu Khalil,wani sanyi da annuri da farin cikine yarinka ratsa zuciyar Hanan da kuwa duk zuciyarta ta shiga cikin wani hali,babu bata lokaci ta shiga cikin kitchen domin jinta take yi awartsake yanzu,tuwon dai nasu na gado ta dora musu shida Aryan saboda basa gajiya dashi nan ta lailayashi tayishi lafiyayye miyar busasshiyar kubewa mai tsananin yauki wacce tasha kifi wadatacce,man shanu ta soya bayan ta sauke girkin,

Tun kafin Khalil din yadawo su umma ke santin wannan tuwon ita da Aryan ita dai Hanan dariya kawai tayi ta haura sama,bayan sallar magriba Khalil din yadawo daga gombe amutukar gajiye ga wata yunwa dake ciciyarshi,kayan jikinsa ya sauya daga manya zuwa kanana sannan yazo yahau table nan yafara kwasar girkin Hanan wanda ke barazanar cire masa kunne dan tsabar dadi,yana dab da kammalawa Hanan tashigo itada Aryan wanda ta sakoshi agaba wai ya tayata tambayar Khalil wayarta da yarike ya hanata tun sati biyu zuwa uku da suka gabata,

Ganin sun hade kai yasashi kallonsu yana cigaba da cin tuwonsa,

"Papa....."

Kallon Aryan yayi sannan yakai laumar tuwon da ya debo,

"Menene?"

Kallon Hanan yayi sannan ya kalli Khalil,

"Mommy infada?"

Girgiza masa kai tayi,

"Kabari har sai yagama cin abinci tukunna"

"Kai fadi..... Menene?"

"Uncle mommy ce tace wai kabata phone dinta...."
Chapter 53 · 0% Book details